KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Ranan sunga 'yan jaje kala kala amma Mami bata barin kowa yaga Na'iman ta kaita can falonta asama, kowa yazo iya falon qasa yake zama sai Mami da su Nafisan suce "tana bacci" daga nan kuma su gama gaisuwa su tafi ahaka har aka kai dare, a daren ne kuma flight dinda  Lauren zata tafi zai tashi sai da Nafisa suka kaita airport din ita dasu Abu da Al'ameen sannan suka dawo ta samo Na'iman zaune a daki tana shan tea, nan ta bude drawer ta dauko mata babban hijab tana fadin "muje gasu Yaya can sunzo dubaki tare dasu Yaya Adam" sai kuma jikin Na'ima yayi sanyi tuna rabonta da suyi magana ta nutsuwa ita dashi tun kafin incident dinnan ya faru, ahankali ta miqe ta ajiye tea din kan bedside drawer dan itama har ranta tana matuqar son ganinsa, sai Nafisa ta miqo mata hijab din ta saka suka fita, zuwa sannan ciwukan kafan nata sun dan daina mata ciwo sosai da haka suka tafi guestroom din Nafisa na gaba, shigan su suka same su hudun duk suna zaune sai Ahmad ya miqe ahankali yana kallon Na'iman, asannu ta qarasa cikin falon kanta a qasa sai taji ya kamo hannunta tareda hadata da qirjinsa suna tsayen duk su Lamin na kallonsu suna murmushi, Nafisa takai hannunta baki tana murmushi itama, rungume Na'iman yayi batareda jin nauyin ko dayansu ba a falon itama sai tayi luf a jikinsa tanajin kuka na zuwa mata, ahankali ya fara shafa bayanta yace "I'm sorry kinji" sai ta gyada kai hawayen na fita daga idonta, Adam na murmushi yace "Bazaka jira mu baku guri bama" sai sannan Ahmad ya saketa tareda riqo hannunta suka zauna a kujera daya kafadunsu na gogan na juna, yana kallon abokan nasa har da Faruk sannan yace "Sai ku rufe idonku ai" duk sukayi dariya har Nafisan sai Na'ima ta duqar da kanta tana murmushi itama, sarqe yatsunsa yayi da nata yana kallonta fuskansa dauke da murmushi wanda yasa 'yan'uwan nasa suka rinqa kallonsa dan this is another side of him da basu taba gani ba, ahakan dai suka gaisa da Na'iman tana maganan sai sunkuyar da kanta take najin nauyinsu, shi kuwa Ahmad ko a jikinsa haka yake hiran dasu, Nafisa ma nan ta samu waje ta zauna ana maida zancen da ita, sai da sukayi spending fin hour suna hiran kuma Na'ima ta fara hamma sai Ahmad yace Nafisan ta rakata su tafi sai da safe, da haka Na'iman ta miqe suka musu sallama sannan suka fice daga falon...
Washegari ya kasance Monday, tun da safen bayan Alhaji sun gamo komai daga station din suka dawo gidan Abban atare, nan falon Abban yasa ai masa magana da su Hajiya ranan zasu wuce Kano tunda lamuran sun dan daidaita, dan yanda Abba suka tsaya akan lamarin shi dasu Ahmad kadai ya basu assurance na zasu yi komai dan ganin sun kwatarwa Na'iman hakkin zarafin ta da akacin, nan zaune falon su Abba suka fara bayanin yanda case din ke tafiya a station din ta yanda yaron dake hannun su Imam din yace baisan actual matar da ta bada aikin ba saboda Tiyagah ne kadai yake communicating da ita, babu irin wahalar da jami'an basu gana masa ba amma sam baisan komai ba, ahalin yanzu sai anjira lokacin da su Tiyagahn zasuzo hannu tukunna dan har sannan sun bace ba'a samesu ba, su Mami na saurarensu cike da gamsuwa sai Alhaji yace zasu tafi aranan suma, su Ayuba ma suka fadi hakan sai Mami tace "Wai da nace ko zaku biya gidan yarinyar ku gani tunda yau din mijin nata zai tafi da ita" sai Ayuba ya amsa da "toh Hajiya hakan ma yayi" Abba ya kalli faruk yace "Ka kaisu anjiman" ya amsa da toh sai Abban ya sake cewa su Mamin "Mu dan basu guri zasuyi magana da ita" sai ta gyada kai Abban ma ya miqe suka bar Na'iman da 'yan'uwan nata kadai a falon, nan su Alhaji suka gyara zama suka hau yi mata nasiha mai ratsa jiki kuma, fadi suke ta yi biyayya ga bayin Allahn nan da suka riqeta da amana, tayi biyayya ga mijinta dan kowa ya shaida yana sonta ba kadan ba, halin da sukaga ya shiga a wannan qanqanin lokacin kadai ya shaida irin soyayyar da yake mata, ta riqe surikanta hannu bibbiyu dan mutanen kirki ne matuqa kuma masu qaunarta, haka dai suka rinqa mata nasihohi iri irin ba abunda take sai kuka, Hajiya ta riqo hannunta tace "Kiyi hakuri da duk abubuwan da suka faru, Dan Adam ajizi, ki yafe mana sannan kibi mijin ki da bayin Allahn nan sau da kafa" Na'ima na kuka ta gyada kai kawai da haka suka mata sallaman zasu tafin, nan ma ta hau wani kukan Umma jummai na bata baki, ahaka suka fito main falon gidan inda su Mamin ke tsaye sai suka fara sallama dasu Abban akan a lokacin ma zasu wuce sai Faruk ya fita suka bi bayansa tare dasu Mamin, aikuwa nan compound din suka ga Ahmad da Adam din a tsaye sai ya qaraso suka sakeyin musabaha dasu Ayuban, dan tare sukaje station din kuma tun lokacin sun fada masa batun tafiyan tasu a yau din, suna tsayen ya fada musu drivern sa zai maidasu gidan ga motoci biyu a wajen suna jiransu duk lokacin da suka shirya sai kawu Nasiru yace "ai shirin kenan ma yanzu" Na'ima na tsaye kusada Mami duk jikinta yayi sanyi, dan jini dai jini ne because ayanzu kuma sai takejin kewansu tun kafin su tafin ma, amma haka tana gani suka tafin....Yan'uwan Na'ima basu sake mamakin arziqin Ahmad ba saida sukaje gidan, su Ayuba bakinsu kasa rufuwa yayi sunabin ko ina da kallo, lallai in baka mutu ba toh baka gama kallo ba, wai yarsu ce zata rayu cikin wannan daular,  sai da Hajiya taji hawaye na zuwa mata tanajin tsoron Allah na sake shiganta, wato duk yanda ka kai karka kuskura ka raina dan Adam dan bakasan inda Allah zai kaishi ba watarana, Na'iman da ta raina abayan, yarinyar da ke yawo cikin gidanta da kodaddun kaya yau itace cikin wannan daular, ita Allah ya bawa tarin nasarori haka a rayuwa, sun yaba gida iya yabo barin ma su Umma jummai da Ayuban, sai da umma jummai suka shiga har part din Na'iman suka ga komai suna yabo sannan suka bar gidan...
Daren ranan Mami ta hau shirya Na'iman bayan sun sanar da Ahmad din yazo su tafi, bayan ta sata tayi wanka nan Nafisa ta dauko mata wani tsadaddaen lace baqi mai hade da flowers orange color ajiki wanda daga gani basai anfada ba zai haska Na'iman, sai da Mami ta gama shafa mata taurarruka masu matuqar qamshin nan sannan ta bata kayan ta saka, jikin Na'ima a sanyaye ta miqe, ganin kamar zatayi kuka yasa Mamin ta fara mata nasiha as tana saka kayan, aikuwa nan ta fara kukan da take riqewan, Nafisa na zaune gefenta  duk jikinta yayi sanyi sai ta fara hawaye tuna cewa Bobon zata tafi ta barta, maimakon Mami taji da Na'iman kadai sai duk suka rinqa kukan tare har su Abu suka shigo suka samesu ahakan, Al'ameen ne ya koma ya fadawa Abba baidade ba sai gashi ya shigo falon Mamin yace su fito suzo, saida Mami ta gama shirya Na'iman sannan ta kamo hannunta dana Nafisan ta fito dasu duka suna kukan har sannan, sai duk suka bawa Abban tausayi shima nan yace duk suzo gabansa su zauna, a tsakiya suka sashi suna zaune a qasan shi yana kan kujera sai ya hau lallabi da farko dan Nafisa tsakaninta da Allah ta ke rusa kuka, anutse yace da Nafisan "ai kunanan baku rabu ba daughter, it's just a few hours ride" ya kalli Mami yace "Ya ma kai hour din kuwa?" tace "Hour dayan ne" sai ya juya gun Nafisa yace "kinji dai, hour daya ne ma, duk lokacin da kikeson ganinta it's just 1 hour ride" Nafisa ta gyada kai tana hawaye har sannan, Na'ima har sannan kukan take itama sai Mami ta riqo hannunta nan kuma Abba ya fara mata nasiha Mamin na tayasa, atare suka rinqa kukan da Nafisa har sannan, Faruk ne ya shigo falon yace "Abba..ya iso" sai yace "ka fada masa ya iso nan" da haka Faruk ya juya bai dade ba ya dawo falon Ahmad na biye dashi a baya cikin manyan kaya, nan tsakar falon ya tsugunna shima sai Nafisa ta tashi ta fita tareda Faruk din dan su Abu basu shigo ba daman, Nasiha sosai Abba ya musu mai ratsa jiki kan Ahmad a duqe, Na'ima ji take kamar ta shiqe a wajen dan kuka, saida Abba ya gama sannan Mami ma ta dora nata sama sama da haka ta kira Nafisan ta dawo falon sai tace mata ta riqe Na'iman suje mota, da haka Ahmad ya miqe jiki a sanyaye ya fita sai Nafisa ta dago Na'iman dake ta kuka suka fita daga dakin, sai sannan Mami ta fara share hawayenta Abba na kallonta yana murmushi yace "Nasani kema danne wa kike" sai ta duqar da kai tanajin hawayen na zuwa babu qaqqautawa....Na'ima na kuka suka qarasa bakin motan Ahmad su Abu na biye dasu a baya sai Ahmad ya bude front seat tareda kamo hannunta suka sata amotan, Faruk dai na tsaye can balcony yana kallonsu jikinsa duk a sanyaye shima..Nafisa na kuka Abu ya dafa ta yana bubbuga bayanta Ahmad yayi reverse yabar gidan suka dau hanyar gidansu, ahanya Na'ima ta rinqa kuka kamar ranta zai fita Ahmad na juyawa yana kallonta time to time, shima this whole process has been too emotional for him gashi jin kukan nata yake har zuciyarsa, miqa hannunsa yayi ya kamo nata sai ta kwace hannun nata, ganin haka sai yayi parking a gefen street yana kallonta, ahankali ya duqo kansa tareda dago habarta da yatsansa ta kallesa, sai ya kwantar da murya yace "Bakyason zuwa? Kinason mu koma?" sai tayi saurin gyada kai, murmushi yayi sai ya fara share mata hawayen ya sake kwantar da murya kamar me rada yace "Bakyason mu tafi gidanmu?" sai ta kauda kanta ganin kallon da yake mata, sake matsowa yayi ahankali yace "Bakyason mu tafi gidanmu mu zauna atare, mu rayu tare, kullum mu kasance tare" qin juyo da kanta tayi tana kukan tace "Toh ai ban shirya ba" sai yayi murmushi tareda sake kamo hannunta yace "Toh muje kiga gidan, in yaso sai in maidake gida daga baya har zuwa lokacin da kika shirya din" kallonsa tayi sai ya gyada kai yana murmushi yace "Muje kiga gidanmu kinji wife, gobe zan sa akawo miki Simba da kikace kinaso"  shiru tayi shiru sai yakai hannunta baki yayi kissing ahankali yace "Let's go home Babe" da haka ya sake tada motan suka sake daukan hanya, Na'ima kanta na kwance a jikin window tana Jin duk illahirin jikinta a sanyaye, sai da Ahmad yayi parking abakin wani babban restaurant sannan ya kalleta ahankali yace "Bari na shiga yanzu in fito kinji" kallonsa kawai tayi har ya fitan yayi locking motan ya shige gurin, bai dade ba ya dawo hannunsa riqe da ledoji manya ya bude back seat ya ajiye sannan ya shiga motan ya tayar suka tafi, kan Na'ima na juye tana kallon street din har suka isa estate din  Ahmad ya tsaya bakin gate din Babban gidan nasu, tun kafin yayi horn wani security ya fito da saurinsa ya bude gates din da suka kasance guda biyu, kana shiga na farko nan zaka samu dakin securities din sannan na biyu da za'a bude a shiga main babban compound din gidan dake cike da shuke shuke na alatu, ga water fountain mai ban sha'awa yana flowing a filin gurin, haske ne tas a ko ina kamar rana, sai da Ahmad ya qarasa har bakin balcony na main entrance din gidan da motarsa sannan yayi parking, juyowa yayi yana kallonta ahankali yace "Babe" sai ta dago kanta ta kallesa, yace "dan bani minti biyu zanje gurin securities dinnan kinji" nan ma ta gyada kai ahankali sannan ya fita daga motan ya koma can gate na farkon, sai da ya tabbatar ya sake tunatar da securities guda biyun da ya dauko din akan su kula sosai sannan ya dawo gurin Na'iman dake zaune a mota har sannan, anutse ya bude side dinta yana kallonta ahankali yace "kin yi addu'an" sai ta gyada kai batareda kallonsa ba, nan ya duqo kawai ya fara kokarin daukan ta tana ware ido ganin abunda yakeyi, bai bi ta kanta ba ya dauketa a kafadarsa ya nufi entrance din gidan da ita, hannunta takai tadan bugi bayansa tace "Ahmaad... they'll see us" sai ya fara dariya qasa qasa bai sauketan ba ya qarasa gaban giant door din tareda danna pin sannan ya tura suka shiga ahakan.....




Bintuuu ✍️ 📚