Page-55
*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
(*F.W.A)*©✍️
⭐⭐⭐
Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد.
❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁
Free book📓
By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_
Page5️⃣5️⃣
Ko da ta isa manyan mutane ta tarar duka fiskarsu à haɗe, a ciki har da malam Auwal abokin mahaifin Nuriyyah, wanda shine silar auro Innar ma, ganin yadda su ke hakan ya yi sanadiyyar sanya zuciyar Inna faɗuwa tun kafin su buɗe baki. Menene dalilin zuwansu?.
ko da ta miƙa musu gaisuwa su ka amsa, nan su ka sanar da Inna cewa, abun da ya kawosu shine, ba za su iya cigaba da zama da ita a cikin unguwarsu ba, sun ji labarin abun da ya faru da 'yarta Halima har ya yi sanadiyyar mutuwarta, kuma dama ita che ta lalata 'yarta da kanta, suna tsoron suma za ta lalata musu 'ya'yansu, gwara ta bar unguwar ta koma wani guri shine mafi salama agaresu. Inna ta yi mamakin ta yadda aka yi su ka ji labarin.
_Sai dai ba ta sani ba wancan ranar da ta ke magana da Halima bayan ta dawo gida, wata 'yar maƙwabciyarsu da aka aika karɓar canji a wurin Inna, anan ne ta ji komai da komai cikin labarin da Halima ta bayar, wanda bayan ta je ta sanar da mahaifiyarta, su ka ƙara sukari da gishiri cikin labari su ka je su ka samu manyan unguwa su ka sanar da su, kuma dama sun san Innar yadda ta ke a baya_
Inna ta shiga cikin tashin hankali mara misaltuwa, ba ta gama da wutar ɗaki ba, sai ga shi ta kama rumbu. Idan ba haka ba wannan wache iriyar masifa ce sabuwa ta ke shirin zuwar mata? Kamar ya ta bar unguwar? Ya su ke son ta yi da rayuwarta? Ko da ta tambayesu to ya za ta yi da gidanta? Sai cewa su ka yi su ba abun da ya damesu ba kenan, duk abun da ya faru da ita ai ita ta jawa kanta.
Roƙonsu ta fara yi ganin abun na su ba da wasa su ka zo ba, amma fa bayin Allahn nan su ka ce sam su ba abun da su ke so ba kenan, kawai ta bar musu unguwa.
Inna ta share hawayenta, ta sauke idanu ƙasa, muryarta cikin rauni ta fara cewa, "kalamanku suna kan gaskiya, kuma ban isa in kare kaina ba, na riga da na san laifina, sannan na yarda da shi. Yanzu haka zuciyata ita ce ke mini hukunci kullum kafin ma ku".
Ta yi ɗan shiru, hawaye na sauka, ta ci gaba da faɗin, "na yi kuskure a rayuwata, kuskuren da à yanzu ba ni da damar gyarashi, na gallazawa yaran da ba nawa ba, na manta cewa ubangijina na kallona, na ɗora tsauri a inda ya kamata tausayi ya kasance. Yau ni ce nake shan sakamakon abin da na shuka, ban ce ku yafe min ba, ban kuma ce ku manta ba. Amma ina roƙonku da Allah, ku tausaya mini kamar yadda ku ke fatan Allah ya tausaya muku, ga rayuwa ta min tsanani".
Sannan ta ɗago tana dubansu, da alamu kalaman Inna na shiga jikin mutanen, don haka su ka natsu sosai suna sauraronta. Ta kuma sa hijabinta ta share hawayen idonta, muryarta na rawa kamar za ta fashe da kuka ta kuma cewa, "ba na neman zama barazana ga ‘ya’yanku, halin da nake ciki kaina ma kaɗai ya isheni nadama da hukunci. Idan kun kore ni, zan tafi, sai dai ku sani ba ku yi min adalci ba, ina roƙonku ku ba ni damar gyara abin da ya rage a rayuwata do Allah".
Ta ƙarashe haɗi da sa kuka, gaba ɗayansu babu wanda bai tausaya mata ba, kalamanta sun shige masu jiki ba kaɗan ba, tattaunawa su ka fara yi à tsakaninsu. Inna ta yi shiru tana tunanin abun da za su ce, yayin da zuciyarta ke ta bugawa. Vayan sun ɗan yi magana a tsakaninsu.
Malam Auwal ya ɗago ya dubi Inna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "uwargida, mun ji maganarki, kuma mun ga nadama a zuciyarki, ba mu zo nan don mu ƙara miki raɗaɗi ba, sai dai don mu kare al’ummarmu".
Ya yi ɗan shiru, ya ƙara da cewa, "amma duk da haka, adalci yana da kyau, mun fahimci cewa kin gane kuskuranki, kuma kin buɗe zuciyarki ba tare da gardama ba, wannan abu ne mai wuya, kuma ba kowa ke iya yin haka ba".
Ya kalli sauran manyan, su ka ɗan girgiza kai alamar yarda, Inna kuma ta ɗan samu sassauci a cikin ranta, Malam Auwal ya ci gaba da faɗin, "saboda haka, mun janye batunmu, ba za mu kore ki daga unguwa ba, muna fatan ki cigaba da gyara kanki da kuma addu'a, Allah ya yafe mana baki ɗaya".
Da ameen sauran su ka amsa sannan su ka bar ƙofar Inna su ka wuce. A sannu ta ke takawa har ta koma cikin gida, ta godewa Allah da mutanen nan su ka haƙura, inba haka ba da ya za ta yi kenan? A baya Malam Auwal ya taɓa zuwa wurinta da faɗakarwa, akan abun da ta ke yi a unguwa, da kuma tambayarta inda Nuriyyah ta ke, sai dai Inna ta yi masa tatas ba tare da ta ga darajarsa ba, tun daga ranar ya daina saka baki akan al'amuran gidanta.
FAMILY HOUSE. bayan wasu kwanaki.
Momy gaba ɗaya ta canzawa mutanen gidan, ɗan gawara manyan tana ɗan sake musu fiska, amma sauran kuwa ko sannu ba ta ce musu, musamman Abba da Asma'u, ko Dady ma ba tsira ya yi ba. A gefe ɗaya kuma sun gane cewa Sadiya na ɗauke da ciki, sun yi murna sosai da yi mata tarin addu'o'i, yau kwana uku kenan da zuwan Baaba da Aisha gaishe da Momy, gobe ne ranar da za su koma tare da Sadiya Kano, su Momy sun so Sadiyar ta zauna har sai bayan ta haihu, amma Baaba ta sanar da su kada su damu suna tare da Sadiya akan komai, sannan su ka nemi yafiyar Momy akan abun da ya faru, kan Momy ya kulle, ba ta fahimci akan me ake yafiyar ba.
Gefe Momy ta kira Sadiya don ta yi magana da ita, "yata wani neman yafiya surkanki ta ke yi min ne? Me ya faru?" Sauke numfashi Sadiya ta yi, don ita ba ta ma yi niyyar sanar da Momy ba, amma tun da ta tambaya ba za ta ɓoye mata ba, ko ba komai ai yanzu komi ya daidaita. Don haka ta sanar da Momy duk abubuwan da su ka wakana.
Momy ta share hawayenta cikin jin ƙuna, wai duk wannan abun da 'yarta ya faru amma ita ba ta sani ba, hasalima duk ita che ta ja komai, furucin da ta yi ba tare da wani zato ba ya zamewa 'yarta babban matsala a rayuwarta, "ki yafe min 'yata, ni ce SANADIN ja miki duk wannan à cikin rayuwarki, ni na manta da wannan maganar, ashe ke kin ajjye shi cikin zuciyarki, na faɗi akan abun da ba babba ba ashe ya zama babbar ajiya a ƙwaƙwalwarki, ki yafe min 'yata" ta ƙarashe hakan tana fashewa da kuka.
Sadiya ma cikin kukan ta ke rarrashin Momy ta ƙara da cewa, "Momy na yarda duk wanda ya yi haƙuri yana da riba, kalamanki ba munana ba, kuma ga shi haƙurin da na yi shine yasa komai ya zame min kamar ba ayi ba, ke uwa ta gari ce a gareni Momy, don Allah ki daina kuka", Momy ta share hawaye ta ƙara da cewa, "daga yanzu don Allah Sadiya duk abun da ya sameki ki sanar da ni kin ji? Kada ki ɓoye min". Murmushi Sadiya ta yi da cewa insha Allah Momy.
Washe gari su Sadiya su ka koma gidan mijinta, inda ya buɗe mata sabon shafi na kulawa da kuma ƙauna.....
Rumaisa da kanta ta zo ta sami Hajiya Kaka, don ta cike gurbin da ya rage musu yanzu, bayani ta fara yiwa Hajiya Kaka ta sanar da ita cewa, tun da dama tun farko sun yi maganar cewa Abba zai auri 'yarta Ayusha, to me zai hana yanzu a dawo da batun? Hajiya Kaka ta ce da ita shikenan za su yi nazari, sannan za ta yi magana da Dady, da haka Rumaisa ta koma gida, bayan sun kuma ƙullah wata hanyar da Ayusha.
Da daren ranar Hajiya Kaka ta samu Dady da maganar, shi ko ya ce ya amince kuma ya ji daɗin haka, sai a yi auren à ranar da aka sa tun farko ba sai an canza ba, tun da yanzu bai wuce saura wata biyu ba ma, ko da ya sanar da Momy batun ba abun da ta iya cewa sai Allah ya kaimu lokacin.
Washe gari aka sanar da wannan haɗin, Ayusha da mahaifiyarta sun yi murna sosai, burinsu ya kusa cika. Abba kuwa gaba ɗaya bai ji daɗin lamarin ba, wannan karon ko neman ra'ayinsa ma ba'a yi ba. Rumaisa har da sake neman Ayusha ta yi aiki tare da Abba, nan ma duk da baya so haka ya amince.
BAYAN WATA ƊAYA.
Abba na zaune akan kujerar office ɗinsa, yayin da tunaninsa ya tafi da nisa, shi matsalolin kansa ma sun yi yawa, ga canjin da Momy ta yi masa ko gaisuwa ba ta amsa masa, gefe ɗaya kuma ga batun Nuriyyah da ya cunkushe masa zuciya, ya yi neman duniyar nan bai san ina ta shiga ba, ya yi nemanta har ya gaji, ko da ya sanar da Momy ta kuma ƙara ɗaukar gaba ɗaya haushi ta ɗora masa, shi sam baya jin daɗin komai.
Duk rama ya gama zama a jikinsa, ya dawo kamar ba Abba ba, magana idan ba ya zama dole ba baya yinsa. Ayusha ce ta shigo ko sallama babu, ita har wani ji da kanta ta ke yi don yanzu bai fi wata ɗaya ya rage ba ta zama matarsa, sai dai har ta shigo bai san ta shigo ba.
A hankali ta matso kusa da shi tana kallonsa, yayin da ta lura idonsa yana a wani wurin, ko da ta juya don ta ga me ya ke kallo, kwatsam ta ga ashe idonsa kan laptop ɗinsa ya ke, ba ma wannan ba, hoton Nuriyyah ne akan fiskar laptop ɗin. Haɗe girar ƙasa da sama Ayusha ta yi sosai, wani baƙin kishi ya fara taso mata, da sauri ta isa gun computern ta sa hannu ta ɗauka.
Wanda hakan da ta yi ya dawo da Abba daga mafarkin tunanin da ya ke, ya ɗaga ido yana kallonta fiskarsa ko murmushi babu, "Abba, why do you still keep a picture of that wicked girl? Ko ka manta abun da ta yi maka ne? Ka cire hoton! Or I will remove it!" Ta faɗi tana neman inda za ta shiga ta cire, zuciyarta na wani tafarfasa, sai dai babu damar shiga don akwai password.
Fizge computern da Abba ya yi ne yasa ta juyawa tana kallonsa, ta ga fiskarsa a haɗe tamau idanuwansa sun yi jazir, "that’s none of your business! Ki maida hankalin akan aikin da ya kawoki kawai!" Abba ya faɗi yana kallonta ba wasa, sannan ya fice riƙe da computern ya barta tsaye, dama Rumaisa cewa ta yi idan suna aiki tare hakan zai zama hanya me kyau don Abba ya so ta, sai dai akasin tsammani ta ke gani, yanzu Abba ya dawo me zafin zuciya a gareta, kenan yana nufin har yanzu yana son Nuriyyah?.
FAMILY HOUSE.
Hajiya Kaka na zaune a cikin ɗakinta kan sallaya, yayin da Asma'u ke kwance akan cinyarta, idonta cike da ƙwallah tana cewa, "Hajiya Kaka don Allah ki yiwa Momy magana, har yanzu ba ta tankani, ɗazun nan ma sai da ta kusa marina akan na yi mata magana, ta rufeni da faɗa. Hajiya Kaka duk da bai kamata ace ankori Nuriyyah ba, amma abun da ta yi ba abu ne mai sauƙi ba, me yasa Momy ta ƙi fiskanta?" Ta kai ƙarshe da share hawayen da ya ɗiga akan fiskarta.
Hajiya Kaka da abun itama da kanta yana damunta, cikin tausayawa ta ce, "karki sa damuwa a ranki, insha Allah zuwa nan da wani lokaci za ta dawo daidai kin ji?" "Hajiya Kaka har zuwa yaushe? Yau an shafe wata ɗaya fa amma hakan bai faru ba" Asma'u ta faɗi, sauke nannauyar numfashi kawai Hajiya Kaka ta yi.
Asma'u ta kuma cewa, "zan je inkuma samunta yanzu, inba haka ba zan cigaba da zama cikin rashin walwala" sannan ta tashi daga ƙafar Hajiya Kaka, ba ta dakatar da ita ba ta barta har ta fice daga ɗakin.
Asma'u na isa falo Abba ya shigo bayan ya dawo daga asibiti, ta gaishesa ya amsa ba yabo babu fallasa ka na ya wuce ɗakinsa, ya zama kamar mace da ya dawo sai zaman ɗaki. Ayusha ce ta biyo bayansa ta shigo haɗi da zama akan kujera, ta buɗe jakanta ta ciro wayarta ta fara latsawa, da kallo Asma'u ta bita ta juya za ta wuce, Ayusha ta ɗago kai tana cewa, "ke Asma'u, kawo min ruwa mai sanyi da ƙishi na dawo", kamar Asma'u ba za ta tanka ba, sai kuma ta wuce kitchen don ɗauko mata ruwan.
Ita kam murmushin mugunta ta yi har da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, domin kuwa burinta gaba ɗayayana dap da cika, "oh my god!" Ta furta sannan ta miƙe, ta manta akwai inda ta ke son ta je bayan ta tashi daga aiki, amma sai ta manta, don haka ta ɗauki jakarta kawai ta fice daga falon.
Bayan Asma'u ta dawo da ruwa a hannunta, amma ba ta ga Ayusha ba, ijje ruwan kawai ta yi a kan table, har ta juya za ta fita, ƙarar wayar Ayusha da ta manta ya hanata wucewa, ta waigo tana kallon wayar, "ina ta je ta mance da wayar kuma? Ita da ko da yaushe wayarta ke hannunta?" Ta faɗi tare da ɗaukar wayar, idonta ne ya sauka akan suna da kuma numbern da ke kiran, ta tsaya sosai tana kallon fiskar wayar, yayin da zuciyarta ya hau bugawa, mamaki ya gama bayyana akan fiskarta, me wannan numbern ya ke yi a cikin wayar Ayusha? Ta tambayi kanta.......
Last page
___________________________________________________
Ya ku ka ji? Momy fa har yanzu ba ta lafa ba. Wani number Asma'u ta gani da da har ta ke mamaki haka?
_*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_