PART 01
by @soulpen
AMRAH
©Hussain Yusuf✍️
GARGAƊI Ba a yarda wani mutum ko wata hukuma ta yi amfani da wannan littafin ba, ta kowace siga, ba tare da rubutaccen izini daga hannun Marubucin ba. ©Hussain Yusuf
TSOKACI Wannan labari kirkirarre ne gaba ɗaya. Kowane suna, wuri, ko al'amari da ya bayyana a ciki, tunani ne na marubucin. Idan labarin ya yi kama da wani ɓangare na rayuwarka ko na wani, to arashi ne kawai; an rubuta shi ne don isar da saƙo da kuma nishaɗi.
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai.
Kallo ɗaya Amrah ta yi wa farin mutumin, sai ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, hakan bai taɓa faruwa da ita ba, tun lokacin da ta fara azabtar da mutanen ƙauyen. Jikinta ya hau rawa da zafi, tsigar jikinta ta tashi. Wani irin tsoron baƙon ya mamaye ta, wanda hakan yake nuna cewa baƙon mutumin nan ya fi ƙarfin duk wata mugunta da ta sani. Cikin ƙanƙanin lokaci, ta dawo ainihin siffarta, sannan ta yanke ƙauna ta ɓace ɓat daga wajen, tamkar iska.
Farin Mutumin, wanda ke kan dokinsa, ya ja linzami dai-dai inda Amrah ta ɓace. Ya tsaya, yana ƙare wa wajen kallo. Ya ɗan jima yana kallon sararin samaniya, sannan ya juya dokinsa, ya nufi cikin ƙauyen da gudu... _________________________________
*Lifecare Specialist Hospital* Alhaji Kabir yana ta kai-kawo a ƙofar labor room. Gabansa sai dukan uku-uku yake. Ya jike sharkaf da zufa, saboda tsananin damuwa. Kowane kuka da matarsa Laila take yi tana kiran sunansa, ƙara hargitsa masa lissafi yake, musamman yadda muryarta ke nuna tsantsar azabar da take sha. Amma ba dama ya je inda take, ƙofar a kulle take kuma an hana shi shiga. Rashin natsuwa yana bayyana a kowane motsinsa.
Bayan kimanin awa biyu Laila tana fama da azabar nakuda, cikin ikon Allah ta haifi 'yan biyu mata masu kama da juna, ba abin da ya bambanta su. Da ƙyar ta juyo ta kalli jariran, duk da ba ta da cikakkiyar natsuwa, ta gane yan biyu mata ta haifa. Wani irin farin ciki ne marar misaltuwa ya mamaye zuciyarta. Nan take, ma'aikatan asibitin suka shiga ba ta taimakon gaggawa, wasu kuma suka shiga gyara kyawawan jariran, farare tas kamar ƴaƴan turawa.
Lokacin da aka faɗa wa Alhaji Kabir cewa matarsa Laila ta haihu lafiya, kuma an samu kyakkyawar jaririya, sai ya cika da tsananin murna har ya kasa gane lokacin da ya ciro kuɗi masu yawa daga aljihunsa ya ba wa ma'aikaciyar da ta yi masa wannan albishir ɗin. Bayan kusan awa guda, Laila ta dawo cikin hayyacinta, aka kawo mata jaririyarta, amma sai ta ga guda ɗaya ce kawai.
Nan take ta tambayi ma'aikaciyar asibitin, "Ina ɗaya jaririyar take?" Cikin rashin fahimta ma'aikaciyar ta amsa, "Madam, ai ɗaya ce ki ka haifa."
Duk da kasala da rashin ƙwarin jiki, Hajiya Laila ta tashi zaune da sauri, ta kalli ma'aikaciyar sosai ta ce, "Ban gane ba, wai an yi gabas da kare! Ta ya ya za ki ce ɗaya na haifa? Da idona na ga 'yan biyu na haifa, kuma duk mata ne, 'yan tagwaye masu kama da juna."
Ma'aikaciyar ta ɗan yi murmushi, tana zaton Hajiya Laila wasa take yi, sai ta ce, "Hajiya, lokacin da ki ka haihu ba kya cikin hayyacinki sosai, don haka ba lallai ki iya gane ainihin yawan jariran ba. Wataƙila zafin naƙudar ne ya sa ki ka ga kamar 'yan biyu ki ka haifa. Amma guda ɗaya ki ka haifa, kuma ita ce wannan."
Nan da nan Hajiya Laila ta sauko daga gadon, ta yi kukan kura, ta damƙo wuyan rigar ma'aikaciyar, ta matse ta jikin bango, ta ce, "Ki faɗa min inda ki ka ɓoye min ƴata, ko kuwa na kashe ki yanzun nan!"
Ma'aikaciyar ta yi shiru, ta kasa magana. Hajiya Laila ta ƙara fusata, ta ce, "Za ki faɗa min ko sai na aika da ke barzahu?" Jikin ma'aikaciyar ya hau karkarwa, ta rasa abin da za ta ce wa Hajiya Laila ta fahimce ta, ga shi kuma su kaɗai ne a ɗakin. Shirun da ma'aikaciyar ta yi ya ƙara harzuƙa Hajiya Laila, ta shaƙe mata wuya tana cewa, "Wallahi yanzun nan zan aika da ke lahira idan ba ki fito min da ƴata ba!" Ganin da gaske Hajiya Laila ke son kashe ta, domin ta fita hayyacinta, ma'aikaciyar ta ƙwalla ihun neman taimako da ƙarfi.
Kafin a ce wani abu, likitoci da sauran ma'aikatan asibitin suka banko ƙofar ɗakin. Alhaji Kabir yana biye da su a baya, hankalinsa a tashe, yana zaton wani abin ne ya samu matarsa da yake matuƙar so da ƙauna. Da ƙyar aka kwaci ma'aikaciyar daga hannun Hajiya Laila. Da sauri Alhaji Kabir ya nufe ta, ya riƙe hannunta ya ce, "Laila, me ya faru? Me wannan ma'aikaciyar ta yi miki?" Hajiya Laila ta fashe da kuka ta ce, "Alhaji, sun cuce ni! Sun raba ni da ƴata!" Cikin rashin fahimta, kowa ya kalli inda jaririyar take kwance a kan gado tana barci. Da sauri likitoci suka nufe ta suka shiga duba ta ko wani abu ne ya same ta.....
Hussain Yusuf✍️*AMRAH*