AMRAH

PART 03

by @soulpen

Lokacin da suka iso gidan Boka Rubbas, Amrah tana ta wani irin ihu, tana ƙoƙarin kwacewa daga hannun mutanen da suka riƙe ta. Malam Buba ya haɗa zufa tamkar an kwara masa ruwa, domin bai taɓa yin gudu irin na yau ba. Zuciyarsa tana dukan tara-tara, saboda a hasashensa irin wannan cuta ba ta taɓa samun Amrah ba.

Bayan sun ɗan jima a tsaye, sai Boka Rubbas ya fito daga cikin bukkarsa. Yana riƙe da wata baƙar tukunyar ƙasa, kuma yana ta zuba wasu surkulle irin nasu na bokaye. Ruwan da ke cikin tukunyar ya watsa wa Amrah. Nan take jikinta ya mutu, ta daina ihu da fizge-fizgen da take yi. Aka kwantar da ita a kan wata tsohuwar tabarmar keso.

Da sauri Malam Buba ya nufe ta, amma Boka Rubbas ya dakatar da shi da sauri. "Wannan ba huruminka ba ne! Idan ka taɓa ta a wannan lokacin, babu shakka kai ma za ka yi irin wannan haukan da take yi. Aljanin da ya sarƙe ta ba zai bar ka ba. Ja da baya, ka bar mu mu yi aikinmu."

Jiki a sanyaye, Malam Buba ya ja da baya. A daidai wannan lokacin, Ladidi, mahaifiyar Amrah, ta shigo cikin fitar hayyaci. Ta tsaya tana kallon Amrah kwance. Ba bacci take yi ba, kuma ba suma ta yi ba, kawai tana kwance ne, idanunta farare tas, sun fi na mutum haske, sun kafe sararin samaniya da kallo. Da sauri Ladidi ta nufi Amrah, amma Malam Buba ya riƙe hannunta ya ce mata, "Boka ya hana a taɓa ta yanzu." Ba shiri, ta koma baya, ta tsaya cikin 'yan kallo don ta ga yadda Boka Rubbas zai cire wannan hatsabibin aljanin da ya shiga jikin tilon 'yarsu da suke matuƙar so da ƙauna.

Boka Rubbas ya daɗe a tsaye kan Amrah yana karanto surkullen bokaye. Duk lokacin da ya karanto surkullen, sai ya yarfa wa Amrah wani baƙin ruwa mai wari kamar na mushe. Ya daɗe yana yin haka, sannan ya dubi wasu ƙartin yaransa da ke tsaye gefe ya ce su shiga da ita cikin ɗakin tsafinsa. Ya ce musu wannan ba ƙaramin aiki ba ne, domin aljanin da ya shiga jikinta hatsabibi ne, sai an yi masa shiri na musamman.

Bayan an shiga da ita ɗakin tsafin, sai Boka Rubbas ya ce kowa ya fice daga gidan ya jira a waje. Ba tare da gardama ba, kowa ya fice har da Malam Buba da Ladidi.

Boka Rubbas ya shiga cikin bukkar, ya tarar da Amrah an kwantar da ita a kan gadonsa na kara, wanda ya gada daga kakansa na biyar. Ya tsaya a kanta yana ƙarewa kyakkyawar surarta kallo. Duk da cewa Amrah ba ta haura shekara goma sha uku ba, amma surar jikinta ta nuna tamkar ta kai shekara goma sha takwas. Tana da kyakkyawan diri da cikar halitta da ake buƙata a wajen budurwa.

A hankali, Boka Rubbas ya ci gaba da bin kyakkyawan jikin Amrah da kallo, yana haɗiyar mugun yawu. Jikinsa ban da wari babu abin da yake yi. Ba komai ya fi jan hankalin Boka Rubbas ba kamar ƙirjinta; yadda suka taso sosai suka cika 'yar ƙaramar rigar baccin da take sanye da ita.

Wani mugun tunani ne ya ɗarsu a ransa. Ya kai hannunsa da nufin ya taɓa albarkatun ƙirjinta. Ba zato ba tsammani, ya ji an riƙe hannunsa! Riko ne mai tsanani, har ji ya yi kamar ana karya masa ƙasusuwan hannu. Saboda zafi da raɗaɗi da suka shige shi a lokaci guda, ya tsandara ihu.

Nan take ƙofar ɗakin ta rufe da kanta, haka ma tagar. Duk wata ƙofa da hasken rana ke ratsowa ta cikinta ta doɗe. Hankalin Boka Rubbas ya tashi. Ya bugi jakar tsafinsa da nufin ya wanzar da haske a wajen, amma ta ƙi aiki.

Hankalinsa ya tashi matuƙa! Ya gaji bokanci a wajen mahaifinsa Boka Sarduƙ shekara ashirin, amma bai taɓa shiga irin wannan yanayin ba. Nan take ransa ya ɓaci, ya fara kiran sunayen aljanunsa da ya dogara da su don su yaƙi wannan hatsabibin aljanin, amma shiru, babu wanda ya zo. Kafin ya gama karanto surkullensa, sai ya fara jin sautin wani motsi marar daɗin ji daga kowace kusurwa ta cikin ɗakin.

Ya tsaya a wuri guda yana rarraba idanu. Nan take, ya ga an kunna wuta a jikin itace, an manne ta jikin bango, ɗakin ya gauraye da haske. Da sauri ya kalli inda Amrah take kwance, sai ya ga wajen wayam, babu kowa! Ya fara waige-waige a cikin ɗakin yana mamakin inda ta shiga. A jikinsa, ya fara jin cewa lallai yau ya samu matsala a aikinsa, tun da har akwai wani aljani da ya gagare shi, kuma yake yi masa barazana.

Hussain Yusuf✍️AMRAH

©Hussain Yusuf✍️