PART 13
by @soulpen
Kafin wani ɗan lokaci, ƙofar gidan su Amrah ya cika da jama'ar ƙauyen Kiyawa, yaro da babba. Amma idan ka dubi fuskar kowa daga cikin su, a tsorace yake da Amrah. Don tana tsaye tana kallon yadda suke ta ƙoƙarin suturta Baffanta. Duk wanda ya waigo ya ganta a tsaye, sai ya zage ya ci gaba da aiki. Cikin ƙanƙanin lokaci, suka gama yi masa sutura, suka ɗauke shi zuwa makwancinsa. Kafin su tafi, Amrah ta ce idan sun kai shi, kowa ya dawo, tana son ganin su gaba ɗaya.
Yayin da suka dawo, Amrah ta kalle su gaba ɗaya da jajayen idanunta masu firgitarwa, ta ce, "Su waye da waye a wajen da Maigari ya saka aka daki Baffana?" Nan fa aka hau kallon kallo, wannan ya kalli wancan, aka rasa mai magana a cikinsu.
Nan take fuskar Amrah ta ƙara cika da ɓacin rai, ta daka musu tsawa, ta ce, "Ba da ku nake magana ba? Za ku ba ni amsa, ko sai fushina ya tabbata a kanku?"
Wani dattijo ne ya tashi tsaye ya ce, "Amratu, ni dai ba na wajen da aka daki Malam Buba. Lokacin, ina gonata ina ta aiki..." Nan fa mutane suka rinƙa tashi suna faɗin su ma ba sa wajen da aka daki marigayi Malam Buba.
Cikin ɓacin rai, Amrah ta daka musu tsawa, ta ce, "Da wanda yake wajen, da wanda ba ya nan, duka babu wanda zan bari daga cikin ku! Don haka, ku jira abin da zai biyo baya!"
Tana faɗin haka, ta shige gida. Nan fa jama'a suka kaure da hayaniya. Wasu suna yi wa Maigari Allah Ya isa a kan dukan Malam Buba da ya saka aka yi. Wasu kuwa kuka suke yi, domin sun san matakin da Amrah za ta ɗauka a kansu ba mai sauƙi ba ne.
Alhaji Sambo yana zaune a ofishinsa, ya zuba tagumi. Tunanin Hamrah ya hana shi sukuni. Ya lumshe idanunsa. Take gyangyaɗi ya kama shi. A cikin barcin, ya hau mafarki. Ya gan shi tare da Hamrah a cikin wani ƙayataccen lambu, ma'abocin korayen furanni masu ƙamshi mai saukar da nutsuwa. Sun zura ƙafafunsu a cikin wani ƙaramin tafki, mai ɗauke da ruwa garai-garai. Ga wasu ƙananun kifaye masu kyau suna ta ninƙaya. Samansu, wasu tsuntsaye ne suke kewaya su, suna rera wani kuka mai daɗin sauraro, mai kama da baitocin waƙar soyayya mai daɗin gaske.
Hamrah tana ta zuba masa shagwaba, tana yi masa fari da fararen idanunta. Hamrah ta kawo bakinta saitin nasa za ta sumbace shi. Shi kuma ya lumshe idanunsa, yana jiran ya ji bakinta ya haɗu da nasa...
"Alhaji! Alhaji!! Alhaji!!!" Firgigit ya yi, ya dawo cikin hayyacinsa. Ya kalli wanda yake kiransa. Habu ne, wanda ya saka ya yi masa bincike a kan Hamrah. Tsaki Alhaji Sambo ya ja, ya kawar da kansa gefe, ya ɓata rai.
Habu ya ja kujera ya zauna, ya ce, "Alhaji, lafiya kuwa? Tun ɗazu na shigo ina ta magana, amma ba ka amsa ba."
Alhaji Sambo ya sauke ajiyar zuciya a hankali, ya ce, "Kai dai bari Habu. Wallahi tunanin yarinyar nan ne ya hana ni sukuni. A halin yanzu ma wani mafarki nake yi tare da ita a cikin wani yanayi da yake nuna tsantsar soyayya. Da wani ne ya katse min wannan ƙayataccen mafarkin, wallahi da sai na hukunta shi! Kawai don kai ne shi ya sa na yi maka afuwa."
Habu ya yi murmushi ya ce, "Alhaji, dama na zo na ba ka rahoton binciken da ka saka ni a kan yarinyar."
Alhaji Sambo ya gyara zama, ya fuskanci Habu sosai, ya ce, "Ai Alhaji ka taki sa'a a kan yarinyar nan! Ashe ƴar gida ce."
Alhaji Sambo ya ce, "Ƴar gida kuma? Faɗa min na ji ƴar waye?"
Habu ya yi murmushi a karo na biyu, ya ce, "Da farko dai sunanta Hamrah. Kuma ƴa ce a wajen Alhaji Kabiru, babban yaronka kuma amininka."
Nan take, murmushin farin ciki ya mamaye fuskar Alhaji Sambo. Ya ce, "Ka ga ai sai a yi tuwona maina, ko?"
Habu ya ce, "Ƙwarai da gaske. Amma Alhaji, yanzu ya kamata ka je ka samu Alhaji Kabir ku tattauna. Ka san da zafi-zafi ake dukan ƙarfe."
Alhaji Sambo ya ce, "Habu, daɗina da kai akwai hangen nesa. Bari na ƙarasa ɗan wani aiki, sai ka raka ni mu same shi. Na san ba zai watsa mini ƙasa a ido ba."
Amrah tana shiga cikin gida, ta tarar da Innarta a kwance, tana nishi sama-sama. Da sauri ta ƙarasa wajenta, tana kiran sunanta, "Inna, me ya same ki? Me ya faru da ke?"
Da ƙyar Inna ta buɗe bakinta, muryarta can ƙasa, ta ce, "Amratu, mutuwa zan yi." Da sauri Amrah ta girgiza kai ta ce, "A'a Inna, ba za ki mutu ba."
Inna ta ci gaba da cewa, "Amratu, ina so ki saurare ni da kyau. Zan faɗa miki wani ɓoyayyen sirri da babu wanda ya sani, daga Allah sai Baffanki sai kuma ni." Amrah ta nutsu sosai, ta ce, "Inna, ina sauraronki."
Cikin muryar wanda ciwo ya yi wa tsanani, Inna ta ci gaba da cewa, "Amratu, a duk lokacin da wa'adina ya cika, ki shirya ki bar ƙauyen nan. Ki tafi neman danginki na asali a cikin birni..."
Ku bi channel dinmu domin karanta ci gaba...
Hussain YusufAMRAH
©Hussain Yusuf✍️