PART 16
by @soulpen
Bayan Alhaji Kabir ya shigo da Alhaji Sambo da Habu cikin babban falonsa. Ya sanya aka kawo musu abubuwan ci da sha kala-kala, yana mai ba su haƙurin cewa bai san da zuwansu ba ne da ya shirya musu girki da tarba na musamman.
Bayan sun gama kimtsa cikinsu, Alhaji Kabir ya dubi Alhaji Sambo, ya ce, "Alhaji, ina fatan dai ba wani gagarumin laifin na aikata ba, har ka tako da kanka ka zo gidana?"
Alhaji Sambo ya yi murmushi, ya ce, "Kar ka damu, Alhaji Kabiru, alheri ne yake tafe da mu."
Alhaji Kabir ya gyara zama ya fuskance shi. Alhaji Sambo ya ci gaba, "Alhaji Kabiru, ba komai ne ya sa na tako da kaina na zo wannan gidan naka ba, sai domin ina son haɗa jini da kai."
Alhaji Kabir ya kalli Alhaji Sambo da sauri, ya ce, "Alhaji, Ƴarka za ka ba ni aure? Idan don haka ka zo, don Allah ka yi haƙuri. Ba wai na ƙi karɓar tayinka ba ne, amma Wallahi ba ni da ra'ayin ƙara aure. Matata tana yi min duk abin da nake so."
Alhaji Sambo ya fashe da dariya mai sauti. Ya kalli Habu wanda tun da suka zauna bai yi magana ba, ya ce, "Kai Habu, yi masa cikakken bayanin abin da yake tafe da mu."
Nan fa Habu ya fuskanci Alhaji Kabir, ya ce, "Alhaji Kabiru, ba komai ne ya kawo Alhaji Sambo gidanka ba sai don yana son ya zama sirikinka." Ya dakata, sannan ya ci gaba, "Ya ga 'yar wajenka mai suna Hamrah. Lokaci guda ta shiga zuciyar Alhaji, ta yi kane-kane har ta hana shi rawar gaban hantsi. A dalilin haka ne ya tako ƙafa da ƙafa ya zo gidanka domin ya nemi aurenta a wajenka da kansa. Saboda ka san ya ɗauki abin da muhimmanci."
Daga nan suka yi shiru, suka zubawa Alhaji Kabir ido domin su ji amsar da zai ba su. Ya daɗe a zaune cikin shiru, yana nazari a ƙwaƙwalwarsa. Ya san dai maigidansa Alhaji Sambo sam ba mutumin kirki ba ne. Ya yi shuhura a ƙasar nan wajen safarar miyagun ƙwayoyi. Sannan ana yawan zarginsa da aikata wasu muggan laifuka a ɓoye waɗanda suke kawo masa maƙudan kuɗaɗe. Don haka, ba ya jin zai iya aura masa 'yarsa wadda yake matuƙar ji da ita.
Ganin shirun ya yi yawa ne ya sa Alhaji Sambo yin gyaran murya, ya ce, "Alhaji Kabir, amsarka muke sauraro."
Alhaji Kabir ya yi murmushin yaƙe, ya ce, "Alhaji, da farko dai, kun tattauna da ita Hamrar, ta amince tana son ka?"
Gaban Alhaji Sambo ya faɗi. Da sauri ya kalli Habu sannan ya kalli Alhaji Kabir, ya ce, "Haba Alhaji, wacce irin magana kake haka? Dole sai ta amince za ka aura min ita?"
Alhaji Kabir ya ce, "Ƙwarai da gaske. Sai Hamrah ta amince sannan zan iya aura maka ita, saboda na yi mata alƙawarin cewa ba zan taɓa yi mata auren dole ba. Kuma a halin yanzu ma tana da wanda take so, har an yi musu baiko ma."
Da sauri Alhaji Sambo ya ɗaga wa Alhaji Kabir hannu, ya ce, "Ya isa haka Alhaji Kabiru! Ban taɓa zaton zan nemi abu a hannunka ka hana ni ba. Ba komai. Amma ina son ka san ba a cin amanar Alhaji Sambo a zauna lafiya. Ka fi kowa sanin halina, ban taɓa son abu na rasa shi ba. Ka saurari abin da zai biyo baya."
Yana faɗin haka ya tashi da sauri ya fice daga falon a fusace. Habu ya tashi, ya kalli Alhaji Kabir, ya ce, "Alhaji, ya kamata ka canza shawara. Ka san halin maigida, wallahi zai iya yin komai a kan ya mallaki wannan 'yar taka." Wani kallo Alhaji Kabir ya watsa masa, da sauri ya fita daga falon ya bi bayan maigidansa.
A ƙauyen Kiyawa, Amrah ta sake tattaro jama'ar ƙauyen a karo na biyu suka yi wa Innarta jana'iza, ciki har da Maigari da Gargaji. Kowannensu idan ka kalle shi, a tsorace yake. Cikin ƙanƙanin lokaci suka gama kintsa gawar Inna suka kai ta kushewarta.
Suna dawowa cikin garin, sai suka hango Amrah a saman wannan tsaunin da ya zagaye garin, cikin wata siffa mai ban tsoro. Nan take cikin kowannensu ya ɗuri ruwa. Yara da manya suka rinƙa kuka, suna roƙon Amrah a kan ta rabu da su sun tuba.
Amrah ta fashe da wata dariya mai amsa kuwwa, ta ce, "Ai gaba ɗaya jama'ar ƙauyen nan munafukai ne. Ku ne waɗanda kuka rinƙa zuga maigari a kan a yi wa Baffana bulala, to an yi masa bulala har ta zama ajalinsa. A dalilin baƙin cikin mutuwarsa Inna ma ta kamu da ciwon zuciya ita ma ta mutu. Yadda kuka yi wa Inna jana'iza yanzu, haka za a yi jana'izarku nan ba da daɗewa ba!"
Tana faɗin haka, ta bushe da wata mahaukaciyar dariya. Ta dunƙule hannunta na hagu, ta rintse idanunta. Tana shiga cikin wannan yanayin, mutanen ƙauyen Kiyawa suka tabbatar da cewa da zarar ta buɗe idanunta, to ba abu mai daɗi ne zai faru ba. Nan take sai suka hau kuka, wasu har da birgima. Mata kuwa sai ihu suke. Wajen dai kowa hankalinsa a tashe yake.
Amrah tana buɗe idanunta da suka canza launi zuwa ja, sai ta buɗe hannunta da ta dunƙule. Nan take sai wani baƙin hayaƙi ya hau fitowa, yana zagaye mutanen ƙauyen. A hankali, ya rinƙa rikiɗa zuwa baƙaƙen kunamai suna ta zagaya mutanen.
Ba zato ba tsammani, sai gani aka yi wata guguwa mai ƙarfin gaske ta zo, ta kama kunaman da wuta. Cikin ƙanƙanin lokaci, suka kone kurmus.
Cikin tsananin ɓacin rai, Amrah ta kalli inda guguwar ta fito. Sai ta hango wani ƙyamurarren tsoho wanda ko kaɗan bai yi kama da mutane ba. Jikinsa duk gashi fari fat. Fatar jikinsa duk ta yamutse ta yankwane, alamun ya daɗe a duniya. Sai faman kyakyata dariya yake yana kallon Amrah. Ita ma shi take kallo cikin wani irin ɓacin rai wanda ba ta taɓa yin irinsa ba a tsawon rayuwarta.
Hussain Yusuf✍️AMRAH