AMRAH

PART 23

by @soulpen

Suka ɗan taɓa hira, Hamrah ta ɗauki jaririyar ta rungume ta. Bayan sun ɗauki kusan minti arba'in suna hira, sai Jawad ya kalli agogon hannunsa, ya ce, "Hamrah, ya kamata mu tafi, Daddy ya ce kada ki daɗe."

Suka yi wa Kamal da Zeenatu sallama, suka fito daga asibitin. Yayin da suke kan hanyar dawowa gida, Hamrah ta kasa natsuwa. Maganar Daddy game da barazanar da yake fuskanta a kanta tana matuƙar damunta. Ta rinƙa waiwayen bayan motar, tana fargabar ganin farar motar da ta biyo ta jiya.

Dai-dai lokacin da suka kusa shiga layinsu, sai Hamrah ta hango wata mota a tsaye a gefen titi, kamar ta lalace. Ta kasa gane motar sosai saboda duhu ya yi. Haka kawai ta ji ba ta yarda da motar ba, duk da ba ta ga kowa a kusa da ita ba...

Amrah ta bar bakin kogin saboda takurawar da Hisham yake yi mata, ta koma wani wuri a cikin daji inda ta fi son zama ita kaɗai. Tana ɓoye kanta ne, saboda kullum tunaninta shi ne hanyar da za ta bi ta ɗauki fansa a kan mutanen Kiyawa. Duk lokacin da ta yi wannan tunanin, da zarar ta tuno Hisham yana cikin ƙauyen, sai ta ji gabanta ya faɗi. Ba ƙaramin kwarjini yake yi mata ba. Haka kawai ta ji ba za ta iya aiwatar da komai na mugunta ba, matuƙar yana cikin ƙauyen. Ta rasa mene ne dalili.

Babban abin da ya fi ɗaure mata kai shi ne, duka inda ta je ta ɓuya, sai Hisham ya sani. Hisham ya zama Malamin ƙauyen Kiyawa, inda ya koya musu yadda ake ibada ta addinin Musulunci, ya hana su bin maganganun bokaye da matsafa. Yanzu tsoron Amrah ya ɗan ragu a ransu, saboda kwantar musu da hankalin da Hisham yake yi kullum.

Yau ma Amrah ta sake canza wani wurin, saboda yadda Hisham ya takura mata. Tana kwance a saman wani ɗan ƙaramin dutse da ya yalwatu da inuwar wata sassanyar bishiyar kaɗanƴa, kwatsam ba zato ba tsammani sai ta ga Hisham ya bayyana a wurin. Ya tsaya a nesa da ita, yana ci gaba da furta mata kalamai masu daɗi kamar yadda ya saba:

"Amratu, wannan kyakkyawar zuciya ba ta dace da damuwa da takura ba. Ni na zo nan ne don in ɗebe miki kewa daga kaɗaici. Ki bari na zama mutumin da zai mayar miki da murmushi a wannan fuskar taki."

Amrah ta yi shiru, ta ki amsa masa. A wajenta, kalamansa takura ne gare ta kuma suna hana ta samun natsuwa. Amma a cikin zuciyarta, tana jin daɗin lallashinsa, wanda ya shiga jini da jikinta. Duk da haka, ta tilasta wa kanta yin shiru, ta ci gaba da ɗaure masa fuska.

Hisham ya san cewa tana jin daɗin kalamansa, shi ya sa ya ƙi daina bibiyarta. A hankali ya matso kusa da dutsen da take kwance. Da sauri ta tashi zaune ta kalle shi kamar za ta yi magana, amma sai ta yi shiru, ta kau da kai. Tana son ya tafi, amma kuma tana son ya ƙara furta mata wasu kalaman. Ta kasa yin magana, kawai dai ta rabu da shi, ta yi kamar ba ta ma lura da shi ba.

Hisham ya yi murmushi, ya gane cewa yana cin nasara a kan zuciyarta. Ya ce, "To, zan tafi Amratu. Amma ki sani, ko da yaushe, kina cikin tunanina." Ya juya, ya bar wajen. Amrah ta rinƙa kallonsa yana tafiya cikin nutsuwa har sai da ya ɓacewa ganinta. Sai ta koma ta kwanta, ta ci gaba da kallon sararin samaniya.

Daga nan ta fara tunanin iyayenta. Bayan su babu wanda ya nuna mata kulawa a ƙauyen kamar Hisham. Kowa gudunta yake yi. Haka kawai ta ji tunaninsa ya ƙi barin ranta. Tuno maganar da Inna ta faɗa mata ta yi kafin ta bar duniya, da sauri ta tashi zaune kamar an tsikare ta. Cikin ranta ta ce, 'To yanzu idan na tafi Birni neman dangina na asali kamar yadda Inna ta faɗa, ta ina ya kamata na fara? Idan ma na haɗu da su wane bayani zan yi musu su fahimce ni?' Wannan tunanin shi ne ya addabi zuciyarta. Haka kawai ta ji tana son cika wasiyyar da Inna ta yi mata na cewa ta bar ƙauyen ta tafi neman danginta.

Da sauri ta sauko daga kan dutsen ta nufi gidansu, wanda rabon da ta koma cikinsa tun lokacin da aka binne gawar Inna. Tana shiga ta tarar da komai yana nan yadda yake, babu abin da aka taɓa. Cikin bukkarsu ta shiga ta haɗa iya abin da za ta iya ɗauka a cikin wani ɗan ƙaramin buhu, sannan ta ƙulle ta ɗora a ka, ta fita daga gidan. Saboda gudun kar wani ya ganta, ta bi wata siririyar hanya wacce mutane ba su saba bin ta ba, ta nufi bakin titi inda za ta samu motar zuwa Birni. Duk da ba ta da ko sisi a jikinta.

Hussain Yusuf✍️AMRAH