AMRAH

PART 27

by @soulpen

"Kabiru," in ji Alhaji Sambo, muryarsa cike da izgilanci. "Wata ɗaya kacal na ba ka za ka dawo gare ni da kyakkyawar amsa. Idan kuma ka ci gaba da yi min taurin kai to ka sani, babu wata doka ko hukuma da za su hana ni, na auri ƴarka Hamrah." Ya tashi tsaye, yana niyyar tafiya. "Kuma na sani cewa yanzu ka haɗa Hamrah da masu tsaronta. Amma hakan ba zai canza komai ba. A wata mai zuwa, za ta zama matata."

Alhaji Kabiru ya dafe kansa da hannu biyu, zuciyarsa na bugawa da sauri. Ya kasa cewa uffan, sai dai numfashi mai zafi da yake fitarwa. Alhaji Sambo ya yi dariyar mugunta, ya fice daga falon da sauri.

Da fitarsa, Alhaji Kabiru ya miƙe tsaye, ya nufi babban falon gidan, a nan ya tarar da Hajiya Laila tana kallon Talabijin.

Yana shigowa Hajiya Laila ta kalle shi, sai ta ga kamar ba a hayyacinsa yake ba, da sauri ta tashi tsaye tana tambayarsa, "Alhaji me ya faru, na ga ka canza gaba ɗaya?" Alhaji Kabir ya nemi wuri ya zauna, ya dafe kansa da ya sara masa ciwo, Hajiya Laila ta dafa kafadarsa ta ce, "Alhaji wai mene ne ya faru? Ina ta tambayarka amma ka yi min shiru."

"Laila! Mun shiga uku!" Alhaji Kabiru ya faɗa, yana fitar da numfashi sama-sama. "Yanzu Alhaji Sambo ya zo! Kuma ya sake jaddada min barazanar cewa dole ne in aura masa da Hamrah nan da wata ɗaya. In ba haka ba, zai aure ta da ƙarfin tsiya!"

Hajiya Laila ta tashi tsaye cike da damuwa da zulumi. Ta kalli Alhaji Kabir tana son kwantar masa da hankali ta ce, "Alhaji, ka kwantar da hankalinka, babu abin da zai faru Allah Ya fi shi. Kuma zuwa yanzu yakamata mu sanar da Ƴan'sanda abin da yake faruwa.."

"Ba zai yiwu ba, Laila! Mu ƙyale maganar Ƴan'sandan nan, saboda ba abin da za su iya yi masa. Ba ki san waye Alhaji Sambo ba. Yana da ƙarfin ikon da zai iya juyawa komai baya." Alhaji Kabiru ya faɗa cike da ruɗani....

Tafiya take a gefen titi, tana ɗauke da buhun ƴan kayanta a kan kanta, ƙarar motoci da hayaniyar mutane, sai suka haddasa mata ciwon kai mai zafi..

Duk wani abu da ta gani a birnin ɗaure mata kai yake. Manyan gine-gine masu tsayi sun yi mata wani irin kwarjini. Ta yi ta tafiya, tana kallon mutane. Waɗansu su faɗa mata baƙar magana, wasu kuma su yi mata dariya, saboda yadda ta yi futu-futu, da kuma yanayin da take tafiya a hankali kamar matsoraciya..."

Sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta zauna a gefen titi ƙarƙashin wata bishiya. Yunwa ce take nuƙurƙusar cikinta, ta rasa yadda za ta yi saboda ba ta san inda za ta je ta samu abinci ba. Kallon hannunta ta yi, kuɗin da Malam Bala ya ba ta, suna nan, cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta tashi ta ci gaba da tafiya...

Kwatsam sai ta ci karo da rumfar wata mata mai sayar da abinci, tsayawa ta yi a ɗan nesa da rumfar tana kallon yadda jama'a suke zuwa su sayi abincin, wasu su zauna su ci a wajen, wasu kuma a saka musu a leda su tafi da shi. Kallon kuɗin hannunta ta yi, da ƙarfin gwiwarta ta ƙarasa wajen matar ta miƙa mata kuɗin..

Cikin siririyar muryarta ta ce, "A bani abinci," ta ce tana mikawa matar kuɗin, sai da matar ta ƙare mata kallo sannan ta karɓi kuɗin ta irga sai ta ga dubu uku da ɗari biyar ne. Ɗago kai ta yi ta kalli Amrah ta ce, "Daga ina kike?" Amrah ta ce, "Daga ƙauyenmu nake." Matar ta ɗan yi shiru na ɗan lokaci kafin ta sake tambayarta, "Wajen wa kika zo?"

Amrah ta ce, "Inna ce ta ce na zo nan birni zan ga dangina." Matar ta ce, "A ina dangin naki suke?" Amrah ta ce, "Ni ma ban sani ba. Kawai dai ta ce na zo nan birni zan gan su." Matar ta ɗan yi shiru tana kallon Amrah ta ganta ta yi futu-futu, da alamun ta jima ba ta yi wanka ba, fatar jikinta ta bushe, sai tausayinta ya kama matar ta ce, "Ungo sauran kudinki, ɗari biyar ma ta ishe ki, ki sayi abincin.." Ta mikawa Amrah sauran kudin naira dubu uku, ta ce, "Shiga ciki ki zauna sai na zubo miki abincin..."

Hussain Yusuf✍️AMRAH

©Hussain Yusuf✍️