Allura Ta Tono Garma complt
by @soulpen
Introduction
ALLURA TA TONO GARMA 1
A cikin birnin Kano akwai wani magidanci mai suna Malam Hassan. Yana zaune a unguwar Badawa, sana'arsa ita ce tuƙa adaidaita-sahu (napep) da wannan sana'ar tasa yake kula da iyalinsa ko kaɗan bai bar su cikin wahala ba.
Matarsa ta farko sunanta Asabe. Asabe masifaffiyar mata ce, marar mutunci, hatta mutanen unguwarsu tsoronta suke saboda bala'inta. Ko kai waye idan ka taɓo ta sai ta ƙare maka wankin babban bargo, ba ta ragawa kowa ba a gida da waje, hatta mijinta Malam Hassan ɗin yana matuƙar shakkarta.
Ƴaƴanta biyar uku mata biyu maza. A duniya babu abin da take so sama da waɗannan ƴaƴan nata, a kansu an sha yin dambe da ita a cikin unguwa, ga shi ƴaƴan nata Allah Ya yi musu shegiyar tsokana, ga rashin kunƴa. Ko a makaranta ba sa ragawa kowa, idan suka yi laifi malami ya dake su, har makarantar take zuwa ta zage malamin tatas. A kansu an sha kai ta police station a kulle, dakyar Malam Hassan yake harhaɗa ƴan kuɗaɗensa ya yi belinta.
Sai matarsa ta biyu me suna Hauwa'u. Ita Hauwa'u babu ruwanta, mace ce mai matuƙar kirki da girmama mutane. Ga uwa-uba haƙuri da Allah Ya hore mata, don duk abin da Asabe take yi mata ba ta taɓa tanka mata ba, sai dai idan abin ya dame ta sai ta shiga ɗakinta ta sha kukanta ta godewa Allah. Kuma ko Malam Hassan ba ta taɓa sanarwa ba, saboda ta san ba abin da zai iya yi a kan lamarin.
Tun da Malam Hassan ya auro Hauwa'u tsawon shekara takwas ba ta taɓa haihuwa ba, ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba. Haka ne ya sa take fuskantar gori da cin mutunci daga wajen Asabe a kan rashin haihuwa kamar ita ta hana kanta. Ko da aike ba ta isa ta aiki ƴaƴan Asabe ba, idan kuwa ta matsa sai sun je, haka Asabe za ta ci mata mutunci a gaban yaran.
"Idan kin ji haushi ke ma ki haifa mana." Maganar da take yawan faɗa mata kenan a duk lokacin da ta yi yunƙurin aiken ƴaƴanta. Wani lokacin ma da "Juya," take kiranta, haka ya sa Hauwa'u ta haƙura da aiken ƴaƴan Asabe. Sai dai ta aiki ƴaƴan maƙwabtansu...
Da wata safiyar ranar asabar Malam Hassan ya shirya zai fita sana'arsa ta tuƙa napep. Ya fito daga ɗakin Asabe ya leƙa ɗakin Hauwa'u cikin sigar zolaya ya ce, "Amarya ni zan fita nema." Hauwa'u ta yi murmushi ta ce, "Malam Allah Ya kiyaye ya bayar da sa'a.." Ya amsa da amin yana niyyar barin ɗakin, Hauwa'u ta yi saurin cewa "Malam dama ina son na faɗa maka zan je Na'ibawa na dubo yayata yau kwana biyu ba ta jin daɗi."
Malam Hassan Ya ce, "Ba damuwa. Allah Ya kiyaye kuma ki ce mata ina yi mata sannu Allah Ya sawwake." Hauwa'u ta amsa, "Amin."
"Ai da kin shirya sai na tafi da ke, tun da yanzu Ƴanlemo na nufa," In ji Malam Hassan. Hauwa'u ta ce, "Ai dama a shirye nake bari na ɗauko hijabina." Ta tashi ta buɗe wardrobe ɗinta tana neman hijabin...
Kamar daga sama suka ga Asabe ta faɗo cikin ɗakin ta hau bin su da wani irin kallo mai kama da na tuhuma, fuskarta a murtuƙe kamar an aiko mata da saƙon mutuwa. Cikin ɓacin rai Malam Hassan ya daka mata tsawa ya ce, "Ke Asabe lafiyarki ƙalau kuwa? Mene ne haka kawai ki faɗowa mutane ɗaki ba sallama?"
"Ban iya sallamar ba, ubana bai koya min ba" in ji Asabe "Kuma ko da na iya ba zan yi ba."
Cikin faɗa Malam Hassan ya ce, "To me ya shigo da ke?"
"Ji na yi kuna cin dunduniyata," ta kalli inda Malam Hassan yake, "Yanzu kai Malam ka yi adalci a wannan lamarin? Fisabilillahi ran nan na ce ka rage min hanƴa zan je unguwa amma ka ƙi, ka ce min ba can ka nufa ba. Yanzu da yake ƴar'gwal ce za ta yi tafiya har da cewa ta taho ka rage mata hanƴa, yanzu ka yi adalci a nan?" Malam Hassan yana niyyar magana ta riga shi da faɗin, "Billahillazi! Babu inda ka isa ka tafi da ita, ta yi tafiyarta daban kai ma ka yi taka daban. Idan kuwa ka ce dole sai ka tafi tare da ita, sai dai ka haɗa mu duka ka tafi da mu kowace ka kai ta inda ta nufa..."
Hussain Yusuf✍️
ALLURA TA TONO GARMA 2
Da Malam Hassan ya ga kawai so take ta tayar musu da fitina da safiyar nan, sai ya cewa Hauwa'u, "Ni na yi gaba sai kin taho." Ya fita daga ɗakin da sauri, Asabe ta watsawa Hauwa'u wani irin kallo ta ja dogon tsaki ta ce, "Ai indai ina raye a gidan nan, ba ki isa ki samu wannan tagomashin daga wajen Malam ba." Ta fice daga ɗakin ta bar Hauwa'u a tsaye riƙe da hijabi.
Zama ta yi a gefen gado tana tunanin irin wannan rayuwar da take yi a gidan Malam Hassan, ba ta isa ta keɓe da mijinta ba, sai Asabe ta yi musu laɓe. Ta rasa me ta tsare mata a rayuwa. Ta daɗe a zaune ita kaɗai tana tunanin wannan rayuwar da take, zaman haƙuri kawai take yi, don sai abin da Asabe ta faɗa shi ake yi a gidan, duk wanda ya bijirewa umarninta to ranar ba zai yi wunin daɗi a gidan ba. Bayan ta gama tunaninta sai ta tashi ta ɗauki hijabinta ta saka ta fice daga gidan zuciyarta cike da tunani kala-kala a kan irin zaman da take yi a gidan Malam Hassan.
Rana tana daf da faɗuwa. Ta rine nahiyar sararin samaniya na yamma da launin ja, a wannan lokacin idan ka kalli motoci da adai-daita-sahu da suke kan titin Zaria Road kowa burinsa ya isa gida. Ba a bar Malam Hassan a baya ba, shi ma cikin sauri yake tuƙa napep ɗinsa domin ya isa gida da wuri, don ba ya so magriba ta riske shi a hanya. Yana tsaka da tafiya, ya ga wata mata a tsaye ita kaɗai a gefen titi, fuskarta rufe da baƙin niƙab ta rungume wata jaririya da take ta faman kuka sai faman jijjiga ta take yi amma ta ƙi shiru.
Yayin da Malam Hassan ya ƙaraso kusa da ita sai ya ja burki ya tsaya, ya leƙo ya kalle ta ya ce, "Hajiya ina za ki je?"
Muryarta tana rawa kamar za ta yi kuka ta ce, "Malam don Allah ka taimaka min, Darmanawa zan je."
Malam Hassan ya ɗan yi jim, sannan ya dube ta ya ce, "Gaskiya ba can haka na nufa ba, da a ce dai Hotoro za ki je sai na ɗauke ki, amma ba Darmanawa na nufa ba."
Kamar za ta fashe da kuka ta hau roƙonsa a kan ya daure ya taimaka mata, ta daɗe a wajen ba ta samu abin hawa ba, kuma ga jaririyarta ta gaji sai faman kuka take a ƙarshe ta ce indai zai kai ta Darmanawa za ta biya shi ko nawa ne.
Ba yadda Malam Hassan ya iya, dole ya yarda ya ɗauke ta saboda tausayinta da ya mamaye zuciyarsa lokaci guda. Suna tsaka da tafiya yayin da suka zo dai-dai wani shago da ake sayar da kayan sanyi, sai ta tsayar da shi ta ce, "Malam don Allah ka ɗan yi min haƙuri zan shiga shagon can na sayo drinks."
Malam Hassan ya ce, "Ba damuwa, amma ki yi sauri."
Ya tsaya a gefen titi, ta ajiye jaririyar da take hannunta a kan kujerar ta fita da sauri ta nufi shagon sayar da drinks ɗin. Malam Hassan ya gyara zama a cikin adaidaita sahun yana jiranta, wasa-wasa yana zaman jiranta har ya shafe fiye da minti talatin ba ta fito daga shagon ba. Nan take ransa ya fara ɓaci, ya fito ya shiga shagon ya duba ko lafiya ba ta dawo ba.
Yayin da ya shiga ya tambayi masu shagon ko wata mata ta shigo ta sayi drinks, sai suka ce masa babu matar da ta shigo ta sayi drinks. Kan Malam Hassan ya ɗaure sosai, 'Ina wannan matar ta nufa ne?' Shi kaɗai ya yi wa kansa tambayar da ya gaza samun amsarta.
Cikin sanyin jiki ya dawo cikin napep ɗin nasa ya zauna ya ci gaba da jiran matar. A hankali duhun magriba ya fara saukowa, hankalin Malam Hassan ya ƙara tashi sosai ya fito ya tsaya a jikin napep ɗin yana hangen hanƴa don ya ga ta inda matar za ta ɓullo.
Babban tashin hankalinsa ma shi ne jaririyar da ta tafi ta bari a cikin napep ɗinsa. Yana nan tsaye har aka yi kiran sallar magriba, amma ko alamun matar bai gani ba, kowa ya tambaya sai ya ce masa bai ganta ba. Hankalin Malam Hassan bai ƙara tashi ba, sai da jaririyar ta farka daga baccin da take yi ta fashe da kuka, nan take sautin kukanta ya cika wajen da yake gaba ɗaya.
Jikinsa yana rawa ya sunkuya ya ɗauko jaririyar yana jijjiga ta a jikinsa, amma ta ƙi yin shiru. Kafin wani ɗan lokaci mutane sun fara kewaye shi suna yi masa tambayoyin da shi kansa bai san amsarsu ba, dakyar ya rarrashi jaririyar ta yi shiru. Yana niyyar shiga napep ɗinsa ya tafi, mutanen wajen suka ce babu inda zai je sai ya faɗa musu inda ya samo wannan jaririyar.
Zuciyar Malam Hassan ta hau bugawa da ƙarfi, nan take zufa ta fara kwaranyo masa yana sharewa, duk bayanin da ya yi wa mutanen wajen da rantsuwar da yake yi musu amma sun ƙi yarda da shi sun kasa fahimtarsa, har wasu fusatattu daga cikinsu sun fara surfa masa zagi suna yi masa barazanar duka idan bai faɗa musu inda ya samo wannan jaririyar ba..
Ana cikin haka sai ga motar ƴan'sanda ta iso wajen, nan take suka saka Malam Hassan a mota, wani daga cikin ƴan'sandan ya tuƙo napep ɗin suka nufi division ɗinsu da shi..
HUSSAIN YUSUF✍️
ALLURA TA TONO GARMA 3
Yayin da ƴan'sanda suka isa police station da Malam Hassan, kai tsaye ofishin DPO suka wuce da shi. Yana rungume da jaririyar a ƙirjinsa, jikinsa sai faman rawa yake kamar mazari.
A kan kujerar da take gaban tebur ɗin DPO aka ba shi umarnin zama, bayan ya zauna sai ya kwantar da jaririyar a kan cinƴarsa ya ƙura mata idanu sai sharar barcinta take hankalinta kwance, tausayinta ya mamaye zuciyarsa ba zato ya ji ƙwallar tausayinta ta taru a cikin idanuwansa..
Kyakkyawa ce sosai, kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar da haka, yanayin tufafin da suke jikinta da tawul ɗin da take kwance a kai kaɗai, ya isa ya tabbatar maka da cewa ƴar masu hannu da shuni ce. 'Ko me ya sa matar nan ta tafi ta bar jaririyarta a wajena?' Tambayar da take ta maimaituwa a cikin zuciyar Malam Hassan kenan, 'Ko kuma ta manta wajen da ta bar ni ne?' Har yanzu zuciyarsa ta kasa yarda cewa matar guduwa ta yi ta bar jaririyar a hannunsa ba...
Yana tsaka da zancen zucinsa DPO ya shigo ofishin, har ya zauna a kan kujerarsa Malam Hassan bai san da wanzuwarsa ba. Sai da ya yi gyaran murya sannan ya dawo daga duniyar tunanin da ya tafi.
DPO ya kalle shi ya ce, "Malam tunanin me ka ke yi?"
Malam Hassan ya ɗan sosa kansa ya ce, "Yallaɓai ina tunanin ƙaddarar da ta afko mini ne, ta inda ban taɓa zato ba."
DPO ya gyara zama, "Amma ni haka aka ce min ka sato jaririya za ka sayar da ita."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Malam Hassan ya ce, "Yallaɓai waye ya zo ya yi mini wannan mummunan ƙazafin?"
DPO ya ce, "Mutanen da suka shigar da report ɗinka a wajenmu su ne suka ce sun ganka da jaririya tana ta faman kuka, kuma ga dukkan alamu ka yi kama da mai safarar ƙananun yara.." Ƙwallar da ta taru cikin idanunsa ta ƙarasa zubowa kan fuskarsa yana matse ƙwalla ya dubi DPO ya ce, "Yallaɓai wallahi summa tallahi, ba sato wannan jaririyar na yi ba, su ma kansu waɗanda suka sanar da kai, sun san ba sato ta na yi ba.."
DPO ya gyara zama ya ce, "To ya aka yi ka samu jaririyar kuma ina uwarta take?"
Nan take Malam Hassan ya faɗawa DPO duk abin da ya faru, tun daga lokacin da ya ɗauko matar har zuwa sanda ta tsayar da shi ta ce za ta je ta sayo drinks a wani shago dawowar da ba ta yi ba kenan, kuma ta bar jaririyarta a wajensa..
Sosai DPO ya gamsu da duk bayanin da Malam Hassan ya yi masa, ya dube shi cikin nutsuwa ya ce, "Yanzu za ka iya bayyana mana kamannin matar?"
Malam Hassan ya girgiza kai da sauri ya ce, "A'a Yallaɓai ba zan iya bayyana maka kamanninta ba, saboda ta rufe fuskarta da baƙin niƙab idanunta kaɗai ake iya gani."
DPO ya ce, "Tirƙashi! To za ka iya gane launin tufafin da suke jikinta?"
Malam Hassan ya ɗan yi jim, kana ya dubi DPO ya ce, "Eh doguwar riga ce baƙa sanƴe a jikinta irin wacce mata suke yayi mai suna abaya.."
Cikin nutsuwa DPO ya rubuta duk bayanin da Malam Hassan ya yi masa, sannan ya ɗago ya ce da shi, "Malam Hassan na ji duk bayanin da ka yi min, kuma na gamsu da kai. Yanzu ka rubuta min adireshinka da lambar wayarka. Za mu saka jami'anmu su saka ido a wajen da matar ta tsayar da kai ko za a dace a ganta. Sannan za mu iya nemanka a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso."
Ba tare da gardamar komai ba, Malam Hassan ya rubuta duk abin da DPO ya umarce shi.
DPO ya ce, "To yanzu za ka iya tafiya mun sallame ka."
Malam Hassan ya tashi tsaye ya ce, "Yallaɓai to jaririyar fa? A nan zan bar ta?"
DPO ya ce, "A'a ka tafi da ita gidanka, ka bai wa matarka ta kula da ita kafin mu kammala bincikenmu a kan lamarin.."
Nan take wani farin ciki marar misaltuwa ya mamaye zuciyar Malam Hassan. Dama abin da yake ta fata kenan a cikin ransa, a bar masa jaririyar ya tafi da ita gidansa ya riƙe ta, don tuni ya ji ƙaunar jaririyar tana zagaya jikinsa kamar yadda jini yake zagayawa.. Gani yake idan aka raba shi da ita zai iya faɗawa cikin damuwa mai tsanani. Sosai ya yi wa DPO godiya ya fito ya tafi.
Ƙarfe tara da rabi na dare ya isa gidansa, da yake yanayin zafi ne a ƙofar ɗaki ya tarar da Asabe ita da ƴaƴanta duk yaran sun yi bacci sai ita da take zaune tana firfita da mafici.
Tana ganin Malam Hassan ya shigo gidan rungume da jaririya a ƙirjinsa, sai ta firgita ta miƙe tsaye tana rafka salati tana ja da baya kamar wacce ta ga wani mummunan abin tsoro....
HUSSAIN YUSUF✍️
ALLURA TA TONO GARMA 4
Malam Hassan ya yi tsaye yana kallonta fuskarsa shimfiɗe da mamaki. "Asabe ya na ga kina ja da baya kamar kin ga dodo?"
Cike da masifa ta ce, "Ya ba zan ja da baya ba? Ka fita kai kaɗai kuma na ga ka dawo tare da jaririya ai dole ka ba ni tsoro."
Malam Hassan ya yi murmushi ya kalli jaririyar sannan ya kalli Asabe ya ce, "Wannan jaririyar da ki ke gani wata kyauta ce ta musamman da Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba ni..."
Ba ta bari ya gama maganarsa ba ta tari numfashinsa, "Malam ban gane ba, wai an yi gabas da kare.."
"Abin da ki ka ji na faɗa shi nake nufi." Kafin ta ƙara yin magana ya riga ta da cewa, "Ki shimfiɗa min tabarma mana na zauna sai na faɗa miki duk yadda lamarin ya faru har na samo wannan jaririyar."
Bayan ta shimfiɗa masa tabarmar ya zauna, ya kwantar da jaririyar a kan cinyarsa, ta kawo masa ruwa ya sha, sannan ya shiga ba ta labarin yadda ya samo jaririyar.. Nan fa Asabe ta tayar da masifa ta ce ita sam ba ta yarda da duk abin da ya faɗa mata ba..
Malam Hassan ya ce, "Asabe me ya sa ba ki yarda da labarin da na faɗa miki a kan jaririyar nan ba?"
Asabe ta ce, "Haba Malam! Ai ko jikina duk kunnuwa ne ba zan taɓa yarda da wannan daɗin bakin naka ba. Kawai ka fito ka faɗa min gaskiya, ka je ka yi lalata da dadironka, an samu akasi ciki ya shiga ta haife maka abin ka, ta kawo maka ƴarka. Shi ne ka ɗauko ta ka kawo ta gida za ka yi min zaƙin baki don na yarda da kai ka cuce ni, to wallahi kar nake kallonka, ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa. Tun kafin mutane su farga da abin kunƴar nan da ka aikata mutuncinka ya zube a unguwa, gara yanzu ka tafi da wannan jaririyar ko ka jefar da ita, ko kuma ka kai ta gidan marayu, ka san dai duk yadda za ka yi da ita kai ya shafa.."
Nan take ran Malam Hassan ya ɓaci ainun! Ya dubi Asabe ya ce, "Asabe dama za ki iya zargina da aikata zina?"
Ta taɓe baki ta ce, "Haba Malam kai waliyyi ne da ba zan zarge ka ba? Kawai ka je ka yi abin da na ce idan kana son zaman lafiya, don wallahi wannan jaririyar ba za ta kwana a cikin gidan nan ba."
Ran Malam ya ƙara ɓaci sosai ya ji kamar ya rufe Asabe da duka saboda haushi, cike da takaicin maganganun da ta faɗa masa ya ce, "Asabe idan ki ka ga yau jaririyar nan ba ta kwana a gidan nan ba, to wallahi ba na numfashi a doron ƙasa.."
Cikin fushi Asabe ta ce, "Haka ka ce ko?" Cikin ɓacin rai Malam Hassan ya ce, "Eh haka na ce ki yi duk abin da ki ka yi niyya, wannan jaririyar sai ta zauna a gidan nan, tun da gidana ne ba na uban wani ba."
Asabe tana jin wannan maganar daga bakin Malam Hassan sai ta fice waje da gudu tana kuka haɗe da ihu kamar wacce ake ƙonawa da wuta, nan take jama'ar unguwar suka fito gaba ɗayansu suna tambayarta abin da ya faru take ihu, amma ta ƙi dainawa kuma ta ƙi ta yi wa mutane bayanin abin da ya faru...
Sai da wani babban aminin Malam Hassan mai suna Malam Nura ya ƙaraso wajen ya daka mata tsawa ya ce, "Ki faɗa mana abin da ya faru mana ki ke wanann ihun, duk kin bi kin tayar wa da mutane hankali cikin daren nan kuma kin ƙi yi mana bayani.." Da yake tana jin tsoronsa sai ta sassauta ihun da take, tana matsar ƙwalla, cikin muryar kuka take faɗin, "Ɗazu ne bayan sallar Isha wata yarinya ita da mahaifiyarta suka zo gidanmu da wata jaririya ƴar wata uku a duniya, suka ce wai ƴar Malam ce..." Malam Nura ya sake daka mata tsawa ya ce, "Asabe ya isa haka, mu je cikin gida mu ƙarasa maganar.."
Ba ta yi masa gardama ba ta wuce cikin gidan ya bi bayanta, nan fa mutanen unguwa suka samu abin tattaunawa. Bayan sun shiga cikin gidan, Malam Nura ya ga abokinsa Malam Hassan a zaune riƙe da jaririya ya yi tagumi, ya ƙurawa jaririyar ido, kwata-kwata ma bai san da shigowarsu ba sai da Malam Nura ya yi gyaran murya sannan ya dawo daga duniyar tunanin da ya tafi.
Malam Nura ya jawo kujera ƴar tsugunne ya zauna, ya umarci Asabe ita ma ta zauna a gefen tabarmar da Malam Hassan yake zaune. Malam Nura ya sake haɗe fuska cikin ɓacin rai ya dubi Asabe ya ce, "Asabe abin da ki ka yi sam ba ki kyauta ba, yanzu ke ba za ki iya rufawa mijinki asiri ba, sai ki fita unguwa kina ihu kamar wata ƙaramar yarinƴa? Kuma kin saki baki za ki bayyanawa duniya halin da mijinki yake ciki? Wallahi sam ke ba matar rufin asiri ba ce, yakamata ki gyara halinki...yanzu faɗa min abin da ya faru ina sauraronki.."
Sai da ta kalli Malam Hassan da ya sunkuyar da kansa ƙasa cikin muryar kuka ta fara faɗin,
"Ɗazu ne bayan Malam ya dawo yana cin abinci, sai ga wata dattijuwar mata tare da wata budurwa wacce ba ta fi sa'ar Fauziyya ba, (babbar ƴarta) sun shigo cikin gidan nan ransu a ɓace ko sallama ba su yi ba kai tsaye suka je inda Malam yake zaune yana cin abinci cikin ɓacin rai dattijuwar matar ta ce da budurwa ta ba shi ƴarsa su ba za su iya rainonta ba. Nan take budurwar ta kunce jaririyar daga bayanta ta ɗora ta a kan cinƴar Malam.
"Ni dai ina tsaye ina kallon ikon Allah ban ce komai ba saboda abin ya ɗaure min kai sosai. Cikin ɓacin rai dattijuwar ta dubi Malam ta ce, 'Ga ƴarka nan da ka yaudari ɗiyata ka ɗirka mata ciki ka gudu, to ta haihu kuma ba ka isa mu yi maka rainon ƴa ba, sannan ka jira sammaci.' Tana gama faɗin haka ta ja hannun ƴarta suka fice daga gidan, shi ne a kan na tayar da masifa na ce ni ma ba zan zauna da ƴar gaba da fatiha ba, ya kama ni ya yi min shegen duka kuma ya ce sai na bar masa gidansa, shi ne raina ya ɓaci sosai hankalina ya tashi na rasa zan yi shi ya sa na fita unguwa ina ihu wallahi ba a son raina na yi ba, ban san na yi ba ma..."
Tana kai wa nan ta sake rushewa da kuka kamar gaske...
Hussain Yusuf✍️
ALLURA TA TONO GARMA 5
Malam Hassan ya ɗago kansa ya kalli Asabe cike da mamakin ƙaryar da ta ƙera yanzu a kansa. Ya jinjina kai ya ce, "Asabe Allah Ya shirye ki, ban taɓa tunanin za ki iya jifana da irin wannan mummunan ƙazafin ba, amma ba komai Allah yana nan."
Nan ya dubi abokinsa Malam Nura ya yi masa duk bayanin yadda aka yi ya samo jaririyar, ya ƙare da cewa, "Wallahi ko a yanzu sai na kira maka DPO a waya domin ka ji gaskiyar lamarin. Tun da nake a rayuwata ban taɓa aikata zina ba, hasalima babu abin da na fi tsana kamar ta, amma yanzu Asabe ni ta ke jifa da wannan mummunan ƙazafin?" Ya ƙarashe maganar cikin rawar murya kamar zai fashe da kuka..
Cikin ɓacin rai Malam Nura ya dafa kafaɗarsa ya ce, "Ka yi haƙuri abokina." Ya dubi Asabe ya ɗaure fuska ya ce, "Yanzu abin da ki ka yi kin kyauta? Na tabbata duk abin da ki ka faɗa min ƙarya ki ke yi. Asabe ki ji tsoron Allah ki daina wannan abin da ki ke yi wallahi sam bai dace ba.."
Ta ja dogon tsaki ta juyar da kanta gefe tana magana ƙasa-ƙasa, tana cewa "Wallahi ko sama da ƙasa za su haɗe wannan jaririyar ba ta isa ta kwana a cikin gidan nan ba, ba a isa a yi min daɗin baki a cuce ni ba. Ko ka ɗauke ta ka san yadda ka yi da ita, ko kuma na kashe ta cikin daren nan.." Tana faɗin haka ta tashi da sauri ta shige cikin ɗakinta.
Malam Hassan da Malam Nura suka bi ta da kallon mamaki, cikin tsantsar ɓacin rai Malam Hassan ya ce, "Don Allah kar ki fasa kashe ta, kuma sai ta kwana a gidan nan. Ban ga uban da ya isa ya hana ta kwana ba, ni da ke mu zuba mu gani..." Da sauri Malam Nura ya kwaɓe shi ya ce, "Haba Malam Hassan bai kamata ka rinƙaa biye mata ba, ka rabu da ita idan ta kashe ta, ita ma babu abin da zai hana a kashe ta, tun da dai rai bai fi rai ba.."
Bai gama rufe bakinsa ba sai ga Hauwa'u ta yi sallama cikin gidan, da sauri Malam Hassan ya ɗago ya kalle ta. Sai a wannan lokacin ma ya lura ba ta gidan, saboda kansa ya riga ya kulle gaba ɗaya, da kyar ya ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali ya ce "Sannu da zuwa," ta amsa cikin kulawa.
Ta durƙusa har ƙasa ta gai da Malam Nura sannan ta ƙurawa jaririyar da take bacci a kan cinyar Malam Hassan ido fuskarta ɗauke da alamun mamaki. Da Malam Nura ya lura da ita sai ya ce da ita ta zauna ya yi mata bayani. Bayan ta zauna Malam Nura ya yi mata bayanin komai, har masifar da Asabe ta tayar da zargin da take yi wa Malam Hassan sai da ya faɗa mata.
Cikin tausayawa Hauwa'u ta karɓi jaririyar daga hannun Malam Hassan ta ƙura mata ido tana murmushi. Nan take Malam Hassan ya ji wani sanyin daɗi ya ratsa zuciyarsa, kafin ya yi magana Hauwa'u ta riga shi da faɗin, "Malam ka yi haƙuri saboda na daɗe, na tarar da jikin yayar ne babu daɗi sam, sai da muka koma asibiti muka yini a can sai bayan sallar Isha muka dawo gida. Amma yanzu Alhamdulillahi jikin nata ya yi sauƙi.."
Malam Hassan ya ce, "Ayya! Allah ya ƙara sauƙi, in sha Allahu gobe idan na fita zan biya gidan na yi mata sannu." Hauwa'u ta ce da Malam Hassan za ta riƙe jaririyar a hannunta ta kula da ita, har zuwa lokacin da za a ga mahaifiyarta, idan ma ba a gan ta ba, za ta riƙe ta tsakani da Allah tamkar ƴar da ta tsugunna ta haifa.." Nan fa Malam Hassan da Malam Nura suka rinƙa zuba mata addu'a da godiya.
A cikin daren sai da Malam Hassan ya je ya nemo madarar da ake bai wa jarirai kafin safiya su je asibiti a ba su shawarwari...
Washe gari da sassafe Malam Hassan ya ɗauki Hauwa'u suka nufi asibiti domin a duba lafiyar jaririyar. Suna fita Asabe ita ma ta fita daga gidan ta nufi gidan maƙwabtansu, inda wata ƙawarta take mai suna Rabi.
A zaune ta tarar da ita tana dama koko, sai da ta jira ta ta gama ta rabawa yara, sannan suka shiga ɗaki, nan fa Asabe ta faɗawa Rabi duk abin da ya faru a daren jiya. Nan take ran Rabi ya ɓaci sosai saboda an taɓo ƙawarta, Asabe ta ce, "Rabi zuwa wajenki na yi ki taimaka min da shawara me yakamata na yi a kan wannaan al'amarin wallahi kaina ya kulle, yanzu haka ma ya ɗauke ta sun tafi asibiti a dubo lafiyar jaririyar. Ni babban tashin hankalina ma ko yaran da muka haifa tare da shi, bai taɓa ba su kulawa kamar yadda yake bai wa wannan tsintacciyar shegiyar jaririyar ba.."
Rabi ta ɗan jima tana tunani cikin shiru, daga bisani ta dubi Asabe ta yi mata raɗa a kunne, suka fashe da dariya suka tafa. Asabe ta ce, "In sun san wata ai ba su san wata ba".
Asabe ta yi wa Rabi godiya ta fito ta wuce cikin gidanta da sauri, saboda tana tsoron Malam Hassan zai iya dawowa a kowane lokaci don ba ta son ya san ta fita..
HUSSAIN YUSUF✍️
ALLURA TA TONO GARMA 6
Bayan Malam Hassan da Hauwa'u sun dawo daga asibiti sai suka tarar da Asabe a tsakar gidan ita kaɗai, suka yi mata sallama amma ko kallonsu ba ta yi ba balle ta amsa sallamar da suka yi mata. Su ma babu wanda ya kalli inda take Hauwa'u ta shige ɗakinta tare da jaririyarta, shi kuma Malam Hassan ya sake fita sana'arsa.
Fitar Malam Hassan ke da wuya Asabe ta ɗauki hijabi ta fita, a ƙofar gida ta tarar da ƙawarta Rabi tana jiranta, ba tare da wani jinkiri ba suka nufi bakin titi suka tare napep suka hau...
Bayan sallar Isha Malam Hassan ya dawo daga masallaci yana niyyar cin abinci, sai ya ji ana buga masa ƙofar gida. Da hanzarinsa ya tashi ya nufi ƙofar gidan, wani mutum ya tarar a tsaye yana jiransa.
Sallama Malam Hassana ya yi masa mutumin ya amsa cikin sakin fuska, Malam Hassan ya ce,
"Kai ne ka ke sallama?"
Cikin murmushi mutumin ya ce,
"Na'am! Ni ne nake sallama ko kai ne Malam Hassan ɗin?"
Malam Hassan ya ce,
"Na'am ni ne lafiya dai ko?"
Mutumin ya ce,
"Eh lafiya amma ba lau ba."
Malam Hassan ya gyara tsayuwarsa ya ce,
"Ina sauraronka..."
Mutumin ya ciro farar takarda daga aljihunsa ya miƙawa Malam Hassan ya ce,
"Sunana Malam Garba. Ni ɗan aike ne daga kotu, matarka Asabe ce ta shigar da kai ƙara ranar litinin Alƙali yake so ka halarci kotun.."
Ya yi wa Malam Hassan sallama ya tafi.
Ya daɗe a tsaye ƙofar gidan ya rasa abin da yake yi wa ransa daɗi, sai yanzu ya gama gane cewa Asabe ba matar rufin asiri ba ce, burinta kawai ta ga ya wulaƙanta a idon duniya. Cikin ransa ya ce,
"Ba komai ai Allah Yana tare da mai gaskiya.."
Cikin ɓacin rai ya koma cikin gidan, ya hau cin abincinsa kamar babu abin da yake damunsa. Ko kaɗan bai yi wa Asabe magana a kan ƙararsa da ta kai ba, ya zuba mata idanu kawai so yake ya ga iyakar gudun ruwanta. Lokacin da ya faɗawa Hauwa'u ƙararsa da Asabe ta shigar ta nuna ɓacin ranta sosai a kan lamarin, amma sai Malam Hassan ya ba ta haƙuri ya ce ya san matakin da zai ɗauka a kan Asabe ta bari a gama shari'ar shi ya san a kan gaskiyarsa yake kuma ba zai tozarta ba..
Asabe tana ta kasa kunne ta ji Malam Hassan ya yi mata magana a kan ƙararsa da ta shigar, amma ta ji shiru, sai ta fara shakka a ranta, 'Ko dai ba a aiko masa da sammacin ba?' Har ta yanke shawarar tuntuɓar kotun ta ji yadda aka yi, sai ta fara neman shawarar ƙawarta Rabi.
Rabi ta ba ta shawarar ta bari ranar zaman kotun ta yi, idan bai zo ba sai su ji yadda aka yi. Haka kuwa aka yi, da ranar zaman kotun ta yi, Asabe da Rabi sun halarci kotun da wurwuri lokacin ma babu mutane sosai a kotun don ko Alƙali bai shigo ba. Suka samu ƙarƙashin wata bishiyar darbejiya da take harabar kotun suka zauna...
Sannu a hankali mutane suka fara shigowa, duk wanda ya shigo idon su Asabe yana kansa, burinsu kawai su ga shigowar Malam Hassan don ba sa so shirin da suka yi ya wargaje.
Suna nan zaune Alƙali ya shigo, kowa ya shiga cikin kotun aka fara gudanar da wasu shari'oin amma babu Malam Hassan ba alamarsa..
Cikin tashin hankali Asabe ta dubi Rabi ta ce,
"Rabi dama na faɗa miki ba lallai an aika masa da sammacin nan ba.."
Rabi ta ce, "Amma ai tare da ke muka tambaye su, suka ce mana sun aika masa, kuma ya ce zai zo.."
Asabe ta taɓe baki ta ce, "Wallahi ni ban ga alamar zai zo ba, dubi fa ki gani har an kusa zuwa kanm..."
Ba ta ƙarasa faɗin maganar bakinta ba idanunta suka sauka a kan Malam Hassan da ya shigo cikin kotun, fuskarsa a sake. Ba za ka iya bayyana yanayin da yake ciki ba, na farin ciki ne ko na baƙin ciki......
Hussain Yusuf✍️
ALUURA TA TONO GARMA 7
Karaf! Asabe ta haɗa ido da Malam Hassan, ta sunkuyar da kanta ƙasa da sauri saboda wani irin kwarjini da ta ga ya yi mata. Cikin nutsuwa ya je ya samu wuri mai kyau ya zauna yana kallon shari'ar da Alƙali yake gudanarwa cikin nutsuwa. Ko kaɗan bai kalli inda su Asabe suke zaune ba, duk da ya lura hankalinsu gaba ɗaya yana kansa...
Suna nan zaune har aka yi shari'ar mutum biyar aka zo kansu, bayan magatakarda ya kira Asabe da Malam Hassan sun fito gaban kotu.
Sai Alƙali ya kalli Malam Hassan ya ce,
"Shin Malam Hassan ko ka san a kan wanne dalili matarka Asabe ta yi ƙararka a wannan kotu mai adalci?"
Malam Hassan ya girgiza kai da sauri ya ce,
"A'a Akramukallahu ban san dalilin da ya sa ta yi ƙara ta ba."
Alƙali ya ce, "Ta yi ƙararka ne a kan wata rana ka fita sana'arka ta adai-daita-sahu da daddare ka dawo da jaririya a hannunka, ka shaida musu cewa a adai-dai-sahunka uwarta ta bar maka ita.. Matarka Asabe ta nuna sam ba ta yarda da wannan maganar taka ba domin babu sha-sha-shar uwar da za ta iya tafiya ta manta ƴarta a abin hawa, kawai dai ka je ka yi zina da wata matar ta haife maka cikinka, ta kawo maka ƴarka ka rasa yadda za ka yi da ita, shi ya sa ka kawo ta gidanka ka faɗi wannan maganar don ka kare kanka, su yarda da abin da ka faɗi. An yi haka?"
Malam Hassan ya ce, "Tabbas an yi haka Akramukallahu! Amma ni tun da nake a rayuwata ban taɓa aikata zina ba, hasalima babu abin da na fi tsana a duniyar nan sama da zina. Ban taɓa sha'awar aikata ta ba, balle har na yi wa wata ciki..." Nan take ya faɗawa Alƙali duk yadda aka yi ya samu jaririyar, a ƙarshe ya ce idan ana so a tabbatar da abin da ya faɗa a kirawo DPO shi ma shaida ne a kan duk abin da ya faru game da jaririyar..."
Alƙali ya yi rubuce-rubucensa sannan ya ɗago ya kalli Malam Hassan da Asabe ya ce, "Kotu ta ɗage wannan shari'ar sai nan da sati biyu masu zuwa, kuma kotu za ta gayyato DPO domin ya bayar da cikakkiyar shaida a kan Malam Hassan...."
***
Da suka dawo gida hankalin Asabe ya tashi sosai, ta kasa tsugun ta kai gwauro ta kai mari ta rasa mafita, domin tana ji a jikinta indai aka gayyato DPO kotun nan to tabbas ƙaryarta ta ƙare domin zai faɗi gaskiya ne, kuma kotu za ta amfani da duk abin ya faɗa..
Tana nan zaune cikin ɗakinta ta rasa yadda za ta yi, can sai wata dabara ta faɗo mata cikin ranta ta ce, "Bari na je wajen ƙawata Rabi na san ba za ta rasa shawarar da za ta ba ni ba.."
Tana gama wannan zancen zucin ta ɗauki hijbinta da sauri ta nufi gidan Rabi.
"Kwata-kwata hankalint ya ƙi kwanciya, gani nake a wannan shari'ar mu za a kai ƙasa.."
Rabi ta ce, "Me ya sa ki ka ce haka?"
Asabe ta cire hijabin ta ajiye a kan gadon Rabi ta dube ta fuskarta ɗauke da tsantsar tashin hankali ta ce, "A jikina nake jin Malam ya fi mu gaskiya tsinto jaririyar nan ya yi, saboda har shaidu ne da shi a kan haka.. Mu wacce shaida za mu nuna a yarda cikin shege ya yi?"
Rabi ta yi murmushi ta dafa kafaɗar Asabe ta ce,
"Haba Asabe wallahi kin ba ni mamaki, gaba ɗaya kanki ba ya ja...wannan ƙaramin abun ya daina ɗaga miki hankali.."
Asabe ta ce, "Rabi dole hankalina ya tashi, tun jiya na kasa bacci tunanin mafita kawai nake amma na rasa, ba na so wannan shari'ar ta ka da mu, idan haka ya faru da wanne ido zan kalli Malam?"
Asabe ta ce, "Akwai mafita.."
"Wacce mafita ce?"
"Ƙwararren lauya za mu ɗauka, na tabbata ba zai ba mu kunya ba.."
Asabe ta yi shiru tana nazarin maganar cikin ƙwaƙwalwarta daga bisani ta dubi Rabi ta ce,
"Kuma kin zo da shawara mai kyau. Amma ta wacce hanya za mu samu lauyan cikin sauri kafin sati biyun?"
Rabi ta ce, "Ki bar komai a hannuna, ke dai kawai ki tanadi kuɗi masu kauri waɗanda za mu ba shi.."
"Indai kuɗi ne ba ni da matsalarsu, domin kuɗin gadona har yanzu suna nan a ajiye ban taɓa ba.."
"To shikenan ki kwantar da hankalinki, na yi miki alƙawarin lauyan da zan samo mana ba zai taɓa ba mu kunya ba.."
Asabe ta ji hankalinta ya kwanta sosai, ta yi wa Rabi godiya ta bar gidan ranta ya yi fes, ta samu nutsuwa.
Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah ranar zaman kotun ta sake kewayowa, kowa ya hallara har da DPO da kotu ta gayyato shi ya zo ya bayar da shaida..
Wannan karon Malam Hassan tare da Hauwa'u da jaririyar suka zo kotun, bayan Alƙali ya shigo Lauyan su Asabe ya tashi tsaye ya yi gaisuwa ga Alƙali sannan ya ce, "Sunana Barrister Tahir. Ni ne lauyan Asabe.."
Bayan ya zauna Alƙali ya dubi Malam Hassan ya ce, "Kai ka samo lauya?"
Malam Hassan ya girgiza kai ya ce,
"A'a! Ni ban samo lauya ba."
Alƙali ya girgiza kai ya ce, "To za mu ba ka lauyan gwamnati idan kana buƙata."
Malam Hassan ya ce, "A'a! Nagode Akramukallahu ba na buƙata."
Sannan Alƙali ya buƙaci DPO ya fito gaban kotu ya bayar da cikakkiyar shaida a kan jaririyar da Malam Hassan ya ce an bar ta a cikin napep ɗinsa..
Da ƙwarin gwiwarsa ya fito ya tsaya a gaban kotu, sannan aka saka shi ya yi rantsuwar zai faɗi iyakar gaskiyar da ya sani... Alƙali ya buƙaci ya faɗi iyakar gaskiyarsa a kan jaririyar da Malam Hassan...
Nan take DPO ya yi bayani dalla-dalla kamar yadda Malam Hassan ya yi a ƙarshe ya ƙare da cewa,
"Har yanzu muna kan bincike, amma har zuwa yanzu ba mu gano inda matar take ba. Amma muna daɗa ci gaba da zurfafa bincike. Wannan jaririyar va ƴar Malam Hassan ba ce, tsintar ta ya yi ba cikin shege ya yi wa wata ta haif..."
Da sauri Asabe ta tashi tsaye kamar an tsikare ta, cikin ɗaga murya mai bayyanar da ɓacin rai ta ce,
"Wallahi kar ka yarda da wannan maganar ya maigirma mai shari'a, kawai Malam ya ba shi cin hanci ne don ya kare shi....
HUSSAIN YUSUF
ALLURA TA TONO GARMA 8
Alƙali ya tsawatarwa Asabe tare da yi mata barazanar ɗauri idan ta sake yin magana ba tare da izini ba.
Bayan Alƙali ya gama sauraron duk wata shaida daga bangaren Malam Hassan, sai ya kalli Lauyan Asabe ya ce ko yana da abin cewa. Tashi tsaye ya yi ya ce, "Ba ni da abin cewa ya mai shari'a."
Alƙali ya yi rubuce-rubucensa sannan ya ɗago ya kalli jama'ar kotun ya ce,
"Kotu ta ɗage wanann shari'ar zuwa ƙarshen wannan watan. Sannan kotu ta ba da izini a je asibiti a yi gwajin DNA a tabbatar an zo da sakamako kafin zama na gaba wanda shi ne zama na ƙarshe..""
Daga nan kowa ya watse yana faɗin albarkacin bakinsa. Asabe da Rabi suna tafe a hanya babu mai cewa kowa komai, kowanensu da abin da yake saƙawa a cikin ransa..
Da Rabi ta ga shirun ya yi yawa, sai ta dubi Asabe ta ce, "Asabe lafiya kuwa na ji shirun naki ya yi yawa?" Asabe ta ce, "Ke dai bari Rabi, ba ki san abin da yake damuna ba. Wallahi wannan lauyan da ki ka ɗauko mana ban ga amfaninsa ba, babu fa abin da ya ce a kotun har aka gama zaman.."
Rabi ta ce, "Ni ma wallahi abin ya ban mamaki. Zan je na same shi, idan har ya san ba zai iya wannan aikin ba, gara ya ba mu kuɗinmu mu nemi wani.."
Asabe ta ce, "Gaskiya dai kam, ni ma na ga kamar ba shi da ƙwarewa a aikin nashi."
Haka dai suka yi ta hira har suka yi ƴar tafiya me ɗan nisa, sannan suka tare napep suka nufi gida. A cikin gidan ta tarar da Malam Hassan a zaune ƙofar ɗakin Hauwa'u yana yi wa jaririyar wasa cikin fara'a. Kallo ɗaya za ka yi masa ka hango tsantsar farinciki shimfiɗe kan fuskarsa.
Sallama kawai ta yi ya amsa, sannan ya ci gaba da yi wa jaririyar wasa tana dariya. Baƙin ciki kamar ya kashe Asabe, har ta shiga ɗaki ta ji zuciyarta tana yi mata suya.. Ba ta san lokacin da ta fito waje da sauri ta nufo Malam Hassan da masifa ba.
Tashi tsaye ya yi ya kalle ta a fusace ya ce, "Wallahi kina matsowa nan sai na sauya miki kamanni. Banza kawai wacce ba ta san abin da take yi ba."
Fashewa da kuka Asabe ta yi ta hau faɗin, "Wallahi Malam ka ji tsoron haɗuwarka da Allah. Tun da nake haihuwa a cikin gidan nan, ko ɗaukar jaririn ba ka yi sai sun yi wayo. Kuma ba ka sakar musu fuska, amma da yake wannan tsinanniyar shegiyar ce, ga shi har wasa ka ke yi mata. To wallahi sai Allah Ya yi mana hisabi ni da kai..."
Malam Hassan ya harari Asabe ya ce, "Kar ki ƙara sheganta min ƴa. Koda shegiyar ce to ni ba haka take a wajena ba, idan kuwa har ki ka ƙara sheganta min ƴa sai na ɗauki mummunan mataki a kanki..."
Kafin Asabe ta yi magana Hauwa'u ta fito daga ɗaki da sauri ta karɓi jaririyar a hannun Malam Hassan Tana faɗin, "Malam kawo ta na ba ta madararta, wallahi ina son ta har cikin zuciyata, koda shegiyar ce a haka nake sonta, in sha Allahu har abada ba za ta yi kukan rashin uwa ba..."
Tana faɗin haka ta shige ɗaki ta bar Asabe riƙe da baki tana bin ta da kallon mamaki....
Hussain Yusuf✍️
: ALLURA TA TONO GARMA 9
Malam Hassan ya tashi tsaye ya leƙa ɗakin Hauwa'u ya ce, "Ni na fita, idan zan dawo sai na taho mata da madararta na ga ta kusa ƙarewa." Hauwa ta ce, "To Malam Allah Ya kiyaye hanya, ya ba ka sa'a a kan duk abin da fita nema." Cikin jin daɗi ya amsa da amin.
Har ya kusa kai wa ƙofar fita, sai ya juyo ya ƙwalawa Hauwa'u kira. Da sauri ta fito daga ɗaki tana amsa kiran.. "Malam lafiya kuwa?" Kallonta ya yi ita da jaririyar da take hannunta ya ce, "Hauwa'u don Allah ki kula min da wannan yarinyar sosai kin ji."
Hauwa'u ta ce, "In sha Allahu Malam karka samu damuwa.."
Godiya ya yi mata ya fita, yana fita Asabe ta watsowa Hauwa'u wani kallo. Ita ma Hauwa'u ta watsa mata kwatankwacin wanda ta yi mata ta ja tsaki ta yi shigewarta cikin ɗaki.
Asabe ta ɗauki hijabinta ta fice daga gidan, kai tsaye gidan aminiyarta Rabi ta nufa. Tana zuwa ta tarar da Rabi tana surfen dawa a turmi, Asabe tana shiga gidan ta fashe da kuka. Da sauri Rabi ta jefar da taɓaryar ta riƙe hannunta tana faɗin, "Haba Asabe mene ne ya faru? Mu je ɗaki nan akwai yara.."
Suna shiga ɗaki suka zauna a gefen gado, Rabi ta ce, "Asabe mene ne ya faru?" Cikin sheshsheƙar kuka Asabe ta ce, "Rabi wallahi na rasa yadda zan yi a cikin gidan nan, kullum cikin jefa min habaici da baƙaƙen maganganu suke yi. Ko Hauwa'u da take shakkata a da yanzu ta daina, tsakanina da ita sai harara da baƙar magana."
Rabi ta ce, "Ki kwantar da hankalinki, in sha Allahu a ranar zaman ƙarshe na kotun nan, sai sun gane ba su da wayo. Sai sun san sun taɓo tsuliyar dodo, Asabe shawarar da zan ba ki ita ce, don Allah ana yankewa Malam Hassan hukunci, ke ma ki tashi ki nemi takardar sakinki a wajen Alƙali. Sannan ki nemi ya mallaka miki wani abu daga cikin dukiyarsa wanda za ki kula da yayanki bayan ya sake ki, ga maza nan a gari sai ki samu wani hamshaƙin Alhajin ki yi wuf da shi, dukiyar da aka ba ki kuwa sai ki fara kasuwanci. Ba tun yanzu nake faɗa miki ba, Malam Hassan ba tsaran auranki ba ne, amma kin kasa ganewa.."
Asabe ta yi shiru na ɗan lokaci sannan ta gyaɗa kai alamar gamsuwa ta ce, "Rabi kuma fa kin zo da shawara mai kyau, Allah dai Ya kai mu ranar zaman kotun nan.."
Rabi ta ce, "Ban faɗa miki ba, ina dawowa muka yi waya da lauyan namu, ya tabbatar mini da cewa in sha Allahu mu ne za mu yi nasara a zaman ƙarshen nan da za a yi. Saboda akwai shirye-shiryen da yake yi.." Cikin jin daɗi Asabe ta rungume Rabi tana zuba mata godiya.
Da ranar zaman kotun ta zagayo kowa ya hallara don ya ga irin hukuncin da Alƙali zai yanke a kan wannan shari'ar. Bayan Alƙali ya shigo kowa ya tashi, bayan ya zauna kowa ya zauna. Ya yi rubuce-rubucensa sai ya fara tuntuɓar lauyan masu ƙara ko yana da abin cewa..
Barr. Tahir ya tashi tsaye ya ce, "Ya maigirma mai shari'a ina so kotu ta ba ni dama, na gabatar da shaiduna."
"Kotu ta ba ka dama."
Daga nan Barr. Tahir ya gabatar da wasu mutane a gaban kotu ya dubi Alƙali ya ce, "Ya mai shari'a waɗannan mutanen su ne waɗanda suka yunƙura za su daki Malam Hassan a lokacin da suka gan shi da jaririyar.."
Ɗaya bayan ɗaya Barr. Tahir ya rinƙa kiransu yana tambayarsu suna bayar da shaidar ƙarya, suna faɗin abin da bai faru ba a wajen..
Har Malam Hassan ya yunƙura zai yi magana Hauwa'u da take kusa da shi ta yi saurin dakatar da shi. Bayan Alƙali ya gama sauraron shaidun nan da Barr. Tahir ya gabatar. Sai ya nemi Likitan da ya yi gwajin DNA ya fito ya faɗi sakamako a gaban kotu..
Doctor Mansur ya fito gaban kotu cikin nutsuwa ya fara karanto takardar da take hannunsa.
"Sakamakon binciken da muka yi, ya tabbatar mana da cewa ƙwayoyin halittar da suke jikin Malam Hassan ba su da ƙarfin da za su iya samar da ciki balle har a haifi ɗa. Wannan sakamakon shi ya tabbatar mana da cewa wannan jaririyar ba ƴar shi ba ce.."
Zaro ido Malam Hassan ya yi ya tashi tsaye da sauri ya ce, "Likita wacce irin magana ka ke faɗa haka? Kana nufin ni juya ne ba na haihuwa?"
Likita ya gyaɗa kai ya ce, "Ƙwarai da gaske, a dogon binciken da muka gabatar a kan ƙwayoyin halittarka abu ɗaya yake nuna mana shi ne; har abada ba za ka iya yi yiwa mace ciki ba, balle har ta haihu."
Malam Hassan ya cire hular kansa gumi ya wanke masa fuska, Asabe ta zazzaro idanu cike da mamakin maganganun likita, so take ta tashi ta ƙaryata shi amma sai ta ji ta kasa aiwatar da hakan.
Malam Hassan ya kalli Likita jikinsa yana tsuma ya ce, "Likita ka ce ba na haihuwa. To su ƴaƴan da na haifa har guda biyar na waye? Waye ubansu?" Ya yi maganar da ƙarfi cikin ɗaga murya...
Hussain Yusuf✍️
ALLURA TA TONO GARMA 10
Alƙali ya cewa Malam Hassan ya zauna. Daɓas haka ya zauna, duk tufafin jikinsa sun jiƙe da zufa..
Likita ya ce, "Ya maigirma mai shari'a na gama bayanina zan iya tafiya?" Alkali ya ce, "Za ka iya tafiya."
Malam Hassan ya sake tashi tsaye ya ce, "Ya mai shari'a ina roƙon alfarmar wannan kotu mai adalci ta tuhumi matata Asabe inda ta samo waɗannan yaran tun da an ce ni har abada ba zan iya haihuwa ba."
Da sauri Asabe ta tashi tsaye ta ce, "Wallahi duk wanda ya faɗi wannan maganar tantirin maƙaryaci ne, kawai so yake ya haddasa fitina a tsakaninmu." Yanayin yadda ta yi maganar jikinta sai tsuma yake..
Alƙali ya ce "Yanzun nan za mu saka ki ki yi rantsuwa tsakaninki da Allah waɗannan ƴaƴan na Malam Hassan ne." Asabe ta ce, "Ya mai shari'a ba sai an kai ga haka ba. Amma ni na san waɗannan ƴaƴan nawa na Malam Hassan ne.."
Alƙali ya ce, "Dole sai an yi wannan rantsuwar sannan za mu iya tabbatar da gaskiya."
Alƙali ya umarce ta da ta fito gaban kotu ta rantse, jikin Asabe yana rawa ta fito. Wani shehin malami wanda shi ne zai rantsar da ita ya tashi tsaye ya ce, ta ɗaga hannunta sama.. Fashewa da kuka ta yi ta ce, "Ya maigirma mai shari'a ba zan iya rantsuwa da Alƙur'ani a kan ƙarya ba, na yi alƙawarin zan faɗi gaskiya..."
Alƙali ya ce, "Muna sauraronki.."
Fashewa da kuka ta yi ta kasa magana, Alkali ya daka mata tsawa ya ce, "Muna sauraronki ki faɗi duk abin da ya faru. Kar ki ɓoye mana komai.."
Cikin kuka Asabe ta fara faɗin, "Gaba ɗaya yaran da na haifa su biyar, gaskiya ne ba ƴaƴan Malam Hassan ba ne. Ƴaƴan maƙwabcinmu Ɗantani ne mijin ƙawata Rabi.."
A fusace Rabi ƙawar Asabe ta tashi tsaye ta ce, "Asabe kina hauka ne? Kin san abin da ki ke faɗa kuwa? To wallahi karki kuskura ki haɗo da mijina a wannan rigimar taku, don babu ruwansa ehe!."
Alƙali ya daka mata tsawa, sannan ya dubi Asabe ya ce, "Ci gaba muna sauraronki."
Asabe ta ci gaba da faɗin, "Lokacin da muka yi aure da mijina Malam Hassan. Sai da muka yi shekara biyar ban samu juna biyu ba, rashin haihuwar yana damuna sosai, amma shi Malam Hassan ba ya nuna damuwarsa a kan hakan.
"Duk lokacin da na nuna damuwata shi yake kwantar min da hankali ya ce haihuwa lokaci ne. Allah ne bai kawo lokacin ba. A wancan lokacin har ga Allah na damu sosai a kan rashin haihuwar da ba na yi, saboda ƴan'uwana waɗanda aka aurar da mu tare duk sun haihu daga mai ƴaƴa biyu sai uku ni kuwa ko ɓatan wata ban taɓa yi ba, kuma ba mu taɓa tunanin zuwa asibiti a bincika lafiyarmu ba.
"Wata shekara mijina Malam Hassan ya shirya ya ce zai tafi kudancin Najeriya neman kuɗi, don haka sai ya damƙa amanata a hannun amininsa kuma maƙwabcinsa Ɗantani. Duk wani abu da nake buƙata Ɗantani nake faɗawa, shi kuma ya kawo min nan take. Ko mijina ne ya yi min aike ta hannun Dantani yake isowa gare ni, idan kuwa ya zo gidana kai tsaye yake shigowa bai damu da halin da zai iske ni ba.
"Har abin da mijina ba ya iya yi min Ɗantani yana yi min, kullum sai ya siyo min kaza ko kifi ya kawo min, ga yawan kyautar kuɗi da yake ba ni, da haka ya ruɗe ni na fara biyewa ra'ayinsa. Ranar da ya fito fili ya nuna min zalamarsa a kan abin da yake so, bai sha wahala ba wajen janyo ra'ayina bayan ya yi min alƙawarin maƙudan kuɗaɗe masu yawa na biye masa muka rinƙa aikata....." Fashewa da kuka ta yi ta kasa ƙarasawa, cikin fushi Rabi ta tashi ta ce, "Amma dai ke Asabe an yi tsinanniyar mace, ashe duk amincin da yake tsakanina da ke cin amanata kuke yi, Allah Ya isa tsakanina da ku wallahi ba zan taɓa yafe muku ba kuma in sha Allahu sai kun girbi duk abin da ku ka shuka..."
Alƙali ya ɗaga mata hannu ta yi shiru ta zauna tana matsa ƙwallar takaici, Asabe ta ci gaba.. "Da haka Ɗantani ya mayar da ni tamkar matarsa, a duk lokacin da ya ga dama sai ya zo mu aikata abin da muka aikata, kafin ya tafi sai ya dire mini maƙudan kuɗaɗe.. A duk lokacin da Malam ya dawo daga kudu har matsuwa muke yi ya koma, idan kuwa ya ƙi komawa da wuri sai na shirya na bi Ɗantani har wani ginannen gidansa da yake wata unguwa nesa da tamu inda babu kowa a ciki mu yi duk abin da za mu yi na dawo gida. Da haka har na samu juna biyu, ni kaina na san ba na Malam ba ne, amma hakan ya yi min daɗi ko ba komai za a daina yi min gorin haihuwa..."
Saboda tsananin ɓacin rai jikin Malam Hassan har tsuma ya rinƙa yi, cikin ransa ya rinƙa tuno irin tsananin yardar da ya yi da Ɗantani. Abokinsa ne tun na yarinta tare suka yi makarantar allo suka gama, shi Ɗantani Allah Ya ɗaukaka shi fiye da Malam Hassan amma hakan ko kaɗan bai taɓa alaƙarsu ba. Lokacin da rayuwa ta yi wa Malam Hassan tsanani sai Ɗantani ya ba shi kuɗi masu yawa ya ce ya je kudu ya rinƙa sayo manja yana aiko masa nan Arewa shi kuma yana sayar masa yana aika masa da ribar, ashe ya yi amfani da wannan damar ne don ya ci amanarsa nan take Malam Hassan ya ji babu wanda ya tsana a duniya sama da Ɗantani ji yake a yanzu da zai gan shi babu abin da zai hana shi hallaka shi.. A fusace ya tashi zai fita daga kotun, Alƙali ya dakatar da shi ya ce, "Ina za ka je ba a gama zaman shari'ar ba?" Cikin ɗaga murya ya ce, "Zan je yanzun nan na samu Ɗantani ko ni ko shi..." Alƙali ya ce, "Dawo ka zauna, kotu za ta gayyato shi."
Alkali ya kalli Asabe ya ce, "Muna sauraronki ci gaba.."
Hussain Yusuf✍️
ALLURA TA TONO GARMA 11
Sai da Asabe ta gama shan kukanta sannan ta ci gaba, "Lokacin da mijina ya gan ni da ciki ba ƙaramin daɗi ya ji ba, har sujjadar nuna godiyarsa ga Allah Ya yi. Ya rinƙa hidimta mini, ya hana ni yin duk wani aikin wahala, wani lokacin idan na ga ɗawainiyar da yake ta yi da ni alhali ba cikinsa ba ne a jikina sai na ji wani iri a zuciyata. Bayan na haihu Dantani ya ci gaba da zuwa wajena muna yin abin da muka saba, har sai da na haifi ƴaƴa biyar amma babu ko guda ɗaya na Malam Hassan gaba ɗayansu ƴaƴan Ɗantani ne.
"Auren da Malam Hassan ya ƙaro shi ne ya sa alaƙata da Ɗantani ta yi baya saboda gujewa zargi, ya daina shigowa gidan ko Malam ba ya nan amma lokaci bayan lokaci muna haɗuwa a gidansa da yake can wata unguwar amma ba sosai ba."
Rabi ji ta yi ta kasa zaman kotun, cikin ɓacin rai ta tashi da sauri ta fita a fusace. Napep ta tsayar a bakin titi ta shiga, kafin wani ɗan lokaci sai ga ta a ƙofar gidanta. Yanayin yadda ta buga ƙyauren gidan shi zai tabbatar maka da cewa a fusace take, Ɗantani yana zaune yana irga wasu kuɗaɗe da ya karɓo biyan bashi ya kalle ta da mamaki ya ce, "Rabi lafiya kuwa? Me ya faru na gan ki haka duk kin birkice?"
Maimakon ta ba shi amsa sai ta shaƙe shi tana faɗin, "Wallahi sai na kashe ka, ba ka isa ka ci amanata kuma ka ci gaba da rayuwa ba, rayuwarka ba ta da wani amfani gara na kashe ka saboda na rage mugun iri. Allah Ya isa tsakanina da kai, nan take aljanunta suka motsa ta saki Ɗantani ta rinka ɗauko abubuwa tana maka masa, hannunta ne ya kai kan wuƙa ɗauko ta ta yi ta nufo Ɗantani za ta caka masa da ya ga da gaske kashe shi take son yi, sai ya kwasa da gudu ya fita waje yana ihu itama ta biyo shi hannunta riƙe da wuƙar tana faɗin sai ta kashe shi. Dakyar mutanen unguwa suka rirriƙe ta, bakinta ban da baƙaƙen maganganu da tsinuwa babu abin da suke furtawa..
Dakyar aka kai ta gida, Ɗantani ya kirawo wani shehin malami ya yi mata addu'a bacci ya ɗauke ta.
Wani aminin Ɗantani ya lallaɓo ya faɗa masa duk abin da yake faruwa a kotu, lokacin da ya ga Rabi ta fito daga kotun sai ya biyo bayanta don ya san dole haka za ta faru. ƊANTANI yana jin haka sai ya shiga gidan da sauri yana tunanin mafita don ya san idan ya tsaya to tabbas yanzu za a zo nemansa.
Alƙali yana gama sauraron Asabe ya bai wa ƴan'sandan kotu umarnin su je su kamo Ɗantani su kawo shi kotu. Aikuwa nan take suka fice don cika umarnin Alƙali.
Malam Hassan ya tashi tsaye ya ce, "Ya mai shari'a ina da magana."
Alƙali ya ce, "Kotu ta ba ka dama."
Malam Hassan ya fito gaban kotu ya tsaya ya ce, "Ina son jama'ar da suke wannan kotun su shaida cewa na saki matata Asabe saki uku! Na saki matata Asabe saki uku!! Na saki matata Asabe saki uku!!!" Ya kalli Asabe ya ci gaba da cewa, "Saboda haka kar ki sake ki koma min gida, ki kama gabanki. Amma kafin ki tafi ki je kwashe shegun yaran can naki ba na son ganin ko ɗaya a cikin gidana.."
Ya zauna yana huci kamar tsohon zaki. Ɗora hannu Asabe ta yi a kai ta fashe da kukan nadama...
Ƴan'sandan da aka aika ɗauko Ɗantani ne suka dawo, Alƙali ya kalle su ya ce, "Ina Ɗantanin?"
Ɗaya daga cikinsu ya ce, "Ya Maishari'a mun je har gidan nasa, mun tarar ba ya nan. Amma mutanen unguwa sun shaida mana cewa sun gan shi da ƙatuwar jaka ya hau ɗan'acaɓa ya nufi tasha. Amma su Sajan Bello sun nufi tashar su duba.."
Jim kaɗan su Sajan Bello suka dawo suka ce sun duba ko ina ba su gan shi ba. Daga nan Alkali ya yi rubuce-rubucensa sannan ya ɗago kansa ya ce, "Saboda wasu manyan dalilai ba za a samu kammala wannan shari'ar a yau ba. Sai mako mai zuwa, amma kafin a dawo zaman, kotu ta bai wa hukumar ƴan'sanda umarnin duk inda Ɗantani ya shiga a ƙasar nan a nemo shi, sannan wannan kotu mai adalci tana roƙon Malam Hassan ya bar matarsa Asabe ta zauna a gidansa kafin a gama yanke hukunci.. Kooooot....!!!!" Daga nan kowa ya watse.
Tun da Asabe take a rayuwarta ba ta taɓa yin nadama irin ta wannan ranar ba, gabaɗaya ta ji ta tsani kanta. Ji take dama mutuwa ta zo ta ɗauke ta, ko kuma ƙasar da take takawa ta haɗiye ta ko za ta samu sassaucin abin da take ji a ranta. Ko haɗa ido da jama'a ta kasa yi, duk inda ta gifta mutane sai nuna ta suke yi da hannu wasu da baki suna zunɗenta. Ƴan'jarida kuwa sai bin ta suke yi suna yi mata tambayoyi, amma ta kasa sauraron su, don ba ta da wannan nutsuwar.. Malam Hassan kuwa ko tsayawa a harabar kotun bai yi ba ya fice da sauri, ko tsaya Rabi bai yi ba.
Dakyar Asabe ta iya fitowa bakin titi ta tari adaidaita sahu, a hanya ta rinƙa tunani yanzu da ba ta tayar da jijiyar wuya a kan jaririyar da Malam ya tsinto ba, yanzu tana nan cikin kwanciyar hankali kuma da aurenta, ta so ta tonawa Malam asiri ta kunyata shi a idon duniya yanzu ga shi nan abin a kanta ya ƙare, lallai wannan shi ake kira 'Ƙaikayi koma kan masheƙiya' Yanzu ga shi nan ta tayar da hankali kan ƙaramin abun da bai kai ya kawo ba, ga shi ya zama babba 'ALLURA TA TONO GARMA' ta gina ramin mugunta ƙarshe ita ce ta faɗa ciki, kuma babu damar fitowa har abada. Tana isa unguwarsu ta tarar da Rabi tare da ƴaƴanta da wasu daga cikin ƙawayenta tsaye a ƙofar gidanta hannuwansu riƙe da itatuwa, suna ganinta suka yo kanta suka rufe ta da duka kamar sun samu jaka, haka suka yi ta dukanta tana ihu mutanen unguwa suna ji amma babu wanda ya zo cetonta a cewarsu dara ce ta ci gida, kaf babu wanda take shiri da shi a unguwar sai Rabi, yau kuma ta kacame musu sai su ci kansu, sai da su Rabi suka haɗa wa Asabe jini da majina suka yi mata jina-jina har karyata suka yi a hannunta na hagu, suka yi mata targaɗe a duka ƙafafunta.
Hancinta da bakinta ban da jini babu abin da suke fitarwa, tun tana ihu har sai da muryarta ta dakushe sai da suka kusa kashe ta sannan mutane suka cece ta saboda suna tsoron kar a yi kisan kai a unguwar abin ya shafe su. Haka aka shigar da ita cikin gida kamar matacciya, saboda dakuwar da ta yi. Yayin da ƴaƴanta ƴan'matan suka dawo daga talla suka tarar da mahaifiyarsu a haka, suka yi ta tambayarta abin da ya same ta.
Saboda jigatuwar da ta yi kwata-kwata ta kasa ba su amsa, ba ta san ma wacce amsa za ta ba su ba. 'Shin haka za ta ce musu su ƴaƴan gaba da fatiha ne? Ko kuwa haka za ta ce musu su ba ƴaƴan Malam Hassan ba ne?' Wannan tunanin take ta saƙawa a cikin ranta.
A haka Malam Hassan ya shigo tare da Hauwa'u suka tarar da su. Tana ganin shigowarsa kamar an tsikare ta ta tashi zaune da sauri tana bin su da ido, kamar ba ita ce ta kasa tashi ba.
Wani kallo Malam Hassan ya watsa mata ya ce, "Asabe kin cuce ni kin cutar da rayuwata. Duk faɗi tashin da nake yi a kanki sam ba kya gani, kin haɗa kai da aminina kin ci amanata. Ai dama haka ne duk abin da mutum ya shuka shi yake girba, ba zai yiwu ka shuka gero ka je girbar dawa ba, ko ka shuka masara ka je girbar alkama. Tun ba a je ko ina ba ga sakamakon da ki ka fara samu nan, wallahi kaɗan ma ki ka fara gani.
"Ni ina matuƙar godiya ga Ubanijin halittu da ya nufe ki da kai ni ƙara kotu. Kin je da nufin ki tozarta ni a idon duniya, ki watsa mini suna sai ga shi nan take reshe ya juye da mujiya. Allah Ya yi mini sakayya cikin gaggawa. Saura shi abokin fasiƙancin naki shi ma dole sai ya gamu da masifar da za ta hana shi sakewa a duk inda yake. Kuma bari ki ji na saka gidan nan a kasuwa har na samu mai saya, zan canza unguwa na koma inda babu wanda ya sanni balle har ya haɗa ni da ke. Sai ki san yadda ki ka yi da waɗannan shegun yaran naki, babu ni babu su tun da ba ni na haife su ba. Idan masu gidan nan sun zo ruwansu ne su bar ki ki ci gaba da zama a ciki ko kuma su kore ki ke ya shafa....
"Kuma wannan yarinyar da ki ke shegantawa ƴar halak take a wurina. In sha Allahu ita ce za ta ci gadona, kuma na saka mata sunan matar kirki wacce ta san darajar aurenta Hauwa'u ko da kin haɗu da ita nan gaba sunanta kenan. Ballantana ma ba na so ko haɗuwar hanya ta haɗa ku."
Da sauri ya nufi ɗakin matarsa Hauwa'u zai shiga babbar ƴar Asabe ta sha gabansa da sauri ta ce, "Baba ni fa ban gane abin da yake faruwa ba. Na ga su Inna Rabi sun yi wa Inna duka kuma kai ma ka zo kana faɗa mata wasu maganganu marasa daɗi, har kana cewa mu ba ƴaƴanka ba ne, don Allah me yake faruwa?"
Hussain Yusuf✍️
ALLURA TA TONO GARMA 12
Wani kallo ya watsa mata ya ja tsaki ya ce, "Ki je ki tambayi uwarki ita ce take da cikakkiyar amsar tambayarki." Ya bankaɗa labule ya shige ya bar ta a tsaye. Nishi kawai Asabe take yi tana faɗin wayyo hannunta. Waya ƴarta ta biyu mai suna Fadeela ta ɗauko ta kira wani Kawunsu a kan ya zo ya taimaka su kai mahaifiyarsu asibiti.
Faɗa ya hau yi mata ya ce shi ba ruwansa ya fita daga sabgarsu duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa yake duka. Da taimakon wani saurayinta wanda suke sheƙe ayarsu a hotel suka kai Asabe asibiti aka gyara mata karayar da ta yi suka dawo gida.
Tun kafin su dawo ma masu sayan gidan suka zo, ba a ɗauki wani dogon lokaci ba aka daidaita Malam Hassan ya sallama musu. Nan take ya nemo mota suka kwashe kayansu suka koma Tudun Maliki inda suka kama wani ƙaramin gidan haya. Saboda Malam Hassan ya riga ya rantse ba zai sake kwana tare da Asabe a cikin gida ɗaya ba.
Da su Asabe suka dawo sai suka tarar an watso musu kayansu waje an saka wa gidan key, ga ƙanninsu nan mazan su biyu zaune a ƙofar gidan sun dawo daga makaranta sun tarar da gidan a kulle. Tilas suka nemo mota suka kwashe kayansu suka nufi gidan kawunsu. Shi ma sam ya ƙi amincewa su zauna a gidansa, ya ce su tafi can su nemi gidan ubansu shi ba zai zauna da shegun ƴaƴa gida ɗaya ba. Asabe sai kuka take ga raɗaɗin karaya ga kuma raɗaɗin da zuciyarta take yi mata. Ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji sanyi, dama kawunta ne kaɗai wanda take tunanin za ta je wajensa ta samu sassauci shi ma ga abin da ya ce musu..
Ƴaƴanta sai tambayarta abin da ta aikata suke yi, amma sai kuka take ta kasa ba su amsa. Sai da suka yi mata barazanar za su yi tafiyarsu su bar ta idan ba ta faɗa musu abin da yake faruwa ba, sannan ta feɗe musu biri har wutsiya. Cikin fushi biyu daga cikin ƴan'matan suka ce tun da kuwa suka zo duniya a shegu to za su shiga duniyar su yi zaman kansu. Tun da ba uba gare su ba.
Suka juya suka yi tafiyarsu duk da kiran da mahaifiyarsu Asabe take yi musu cikin raunin murya mai alamta tsananin ciwo, amma ko waigen ta ba su yi ba. Suka bar ta a zaune ƙofar gidan ɗan'uwanta tana rusa kuka, har mutane sun fara taruwa suna kallon su. Fadeela ce kaɗai ta tsaya tare da ita, ita ma kawai don tana tausayin ƙanninta ne mazan, amma da don ta mahaifiyarsu ne da tuni ita ma ta yi tafiyarta. Da ƴan kuɗin da Fadeela take da su ta kama musu gida a wata tsohuwar unguwa suka zauna a can.
Amma ta mayar da Asabe tamkar ba mahaifiyarta ba, ko ya ya ta yi ɗan kuskure sai ta rufe ta da faɗa tamkar ba ita ta haife ta ba.
Da yake ita Asaben ba ta iya taɓusawa kanta komai, hatta ruwa sai dai a ɗebo mata tana zaune. Ƴaƴanta mazan ƙananu ne sosai amma su ne suke ɗawainiya da ita, ita kuwa Fadeela tana zaune tana danna waya ko kallon inda mahaifiyar tata take ba ta yi.
Har cikin gidan take shigo da saurayinta su shiga cikin ɗakinta su yi abin da suke so ya sallame ta ya tafi. Wannan abin ba ƙaramin damun Asabe yake yi ba, sai dai ba ta da halin yin magana yanzun nan sai Fadeela ta rufe ta da faɗa tamkar za ta dake ta. Tana faɗin ta daina saka mata ido a lamuranta.
Ɗantani kuwa da ya samu dama ya bar unguwar, ko a tasha bai tsaya ba, kai tsaye tashar da ake lodin dabbobi zuwa kudu ya nufa, yana isa ya tarar an cika wata babbar mota da shanu za a kai su jahar Enugu. Samun direban ya yi ya biya shi ya ɗauke shi a gaban motar suka tafi. Suna tsaka da tafiya dare ya yi musu a tsakiyar dokar daji, amma a haka suka ci gaba da tafiya, kawai sai suka ga an saro ƙaton reshen bishiya an gindaya shi a tsakiyar titin, direban babbar motar yana ganin haka sai ya ci burki ya fito da gudu ya ce kowa ya yi ta kansa. Nan su Ɗantani da sauran mutanen motar suka fito suka rinƙa gudu a cikin daji suka bar motar tasu tare da shanun a kan titin, suna jin ƴan fashin suna ta harba bindiga suna ihu, ba su daina gudun ba har sai suka daina jiyo harbin bindigar sannan suka tsaya suna haki.. Yayin da Ɗantani ya dawo cikin hayyacinsa sai ya lura cewa ba ya tare da jakar, ya bar ta a cikin mota kuma gaba ɗaya kuɗaɗensa da komai nasa suna ciki.. Fashewa da kuka ya yi, mutanen da suke tare da shi suka tambaye shi dalilin kukan, ya faɗa musu yana ci gaba da matsar ƙwalla. Ran wasu daga ciki ne ya ɓaci suka ce idan bai yi musu shiru ba sai sun yi masa dukan tsiya, bai ga su shanunsu suka baro ba? Ko kuwa kudin nasa sun fi shanunsu.. Ba yadda Ɗantani ya iya tilas ya yi shiru amma ya ci gaba da kukansa a zuciya. A zahirin gaskiya kuɗin da suke cikin jakar nan tasa masu yawa ne don sun haura miliyan ashirin ya ɗebo su ya taho ne don ya kafa kasuwancinsa a kudu, don ya sha alwashin ba zai koma Kano ba har sai an manta da abin kunyar da ya aikata...
Ba su koma wajen da motarsu take ba, sai da gari ya yi haske sosai. Lokacin da suka isa wajen motar, ba a taɓa ko Sa ɗaya ba. Da sauri Ɗantani ya duba gaban motar inda jakarsa take, sai ya tarar babu komai a wajen sun ɗauke ta.. Dantani kamar ya yi hauka haka ya rinƙa ji, amma ƙarfi da yaji mutanen nan suka hana shi kuka..
Lokacin da suka isa Enugu ba shi da komai daga shi sai kayan jikinsa, ga yunwa ta dame shi sosai babu kuɗin sayan abinci. Zagayawa ya yi ta yi shi kaɗai a cikin gari ya rasa inda zai nufa, bai san kowa ba don bai taɓa zuwa Enugu ba sai yau, a baya yana zuwa kudu kasuwanci amma iya Lagos da Ibadan yake zuwa, yana tsaka da yawonsa sai ya hango wata Inyamura mai sayar da abinci kai tsaye ya nufi wajenta ta yi masa kyakkyawan haɗi ya zauna ya cinye tas ya sha ruwa yai gyatsa ya godewa Allah, ya shafa aljihunsa ya ji empty sai ya faki idon Inyamurar ya lallaɓa ta bayan benci zai gudu aikuwa wani yaronta ya gan shi ya yi masa ihu..
Inyamurar nan ta saka masu fushi da fushin wani suka yi masa dukan tsiya, suka karairaya shi suna shirin saka masa taya su ƙone shi Allah Ya kawo wani Bahaushen Bakano ya cece shi. Brayan ya biya duka kudin da suke binsa ya dauke shi ya kai shi asibiti. Bayan an yi masa treatment ya saka shi a mota ya ce a kai shi gida, haka aka kawo shi gida gaba ɗaya jikinsa raunika ne babu kyawun gani.
Matarsa Rabi sam ta ƙi yarda a shigar da shi cikin gidan, ta ce ita ba za ta yi jinyar fasiƙi ba, duk yadda aka so shawo kanta amma sam ta ƙi amincewa. Tilas sai ƴan'uwansa ne suka ɗauke shi zuwa gidansu, a can ɗin ma ba ya samun wata kyakkyawar kulawa. Ga shi a zaune ba ya iya yi wa kansa komai, hatta bandaki sai an kai shi saboda ƙafafunsa duka biyun a karye suke.
Hankalin Malam Hassan ya kwanta sosai a unguwar da ya koma, a Zoo road ya samu shago yake sana'arsa yana kula da iyalinsa da ƴarsa da ya raɗawa sunan matarsa Hauwa'u, amma suna kiranta da Jiddah.
Bayan kamar wata shida da dawowar Malam Hassan sabuwar unguwa DPO ya kira shi cewa ya zo station tare da yarinyar nan ta wajensa, hankalin Malam Hassan da na matarsa Hauwa'u ya tashi sosai saboda fargabar za a raba su da Jiddah yarinyar da suke tsananin so a rayuwarsu.
Bayan sun je suka tarar da wani sanannen attajiri wanda an san shi a ciki da wajen Najeriya yana zaune gaban teburin DPO ya yi tagumi. Bayan sun zauna DPO ya umarci Hauwa'u ta kunce jaririyar daga goyo, tana kunto ta mamaki ya rufe Attajirin da Malam Hassan Hauwa'u har da DPO saboda kamannin Jiddah da attajirin nan kamar an tsaga kara..
Jikin attajirin yana rawa ya karɓi yarinyar hawaye yana zuba a idanunsa. Mamakin da ya lulluɓe fuskar su Malam Hassan shi ya hana su magana.
DPO ya kalli Malam Hassan ya ce, "Malam Hassan ba sai na faɗa maka sunan wannan mutumin ba, Alhaji Iliyas ba ɓoyayyen mutum ba ne a faɗin ƙasar nan." Da sauri Malam Hassan ya gyaɗa kai ya ce, "Tabbas haka ne ina ganin shi na gane shi."
DPO ya ce, "To shi ne mahaifin wannan jaririyar da aka bari cikin adaidaita sahunka."
Malam Hassan ya ce, "Allahu Akbar Kabiran! Allah mai yadda ya so a lokacin da ya so."
Alhaji Iliyas ya buƙaci Malam Hassan ya faɗa masa duk yadda aka yi ya tsinci jaririyar. Malam Hassan ya gyara zama ya faɗa masa komai tun daga lokacin da matar da ya ɗauko ta hau adaidaitansa, har tarin ƙalubalen da ya fuskanta a sanadiyyar barin yarinyar a cikin adaidaita-sahunsa sai da ya faɗa musu.
Har hawaye sai da Alhaji Iliyas ya zubar na tausayin Malam Hassan. Ya dube shi ya ce, "Tabbas Malam Hassan kai mutumin kirki ne kuma kai jajurtacce ne mai tsayawa a kan gaskiya." Ya ja numfashi ya ci gaba "Na san kun matsu ku ji dalilin da ya sa wannan matar ta bar maka jaririya a cikin adaidaita-sahunka ko?"
Da sauri Malam Hassan da DPO har da Hauwa'u suka gyaɗa kai. Alhaji Iliyas ya ce, "To ku saurare ni.." Ya faɗi haka yayin da ya gyara zama ya fara ba su labarin kamar haka...
Hussain Yusuf✍️
ALLURA TA TONO GARMA 13
"Shekarata ashirin da yin aure, amma ban taɓa samun haihuwa ba. Wannan matsalar tana yawan damuna, na sha zuwa wajen likita ya gwada ni, amma abu ɗaya yake faɗa min shi ne; lafiyata ƙalau kawai lokacin haihuwar ne bai yi ba, amma matana sun ƙi yarda sam a yi musu gwajin a ga lafiyarsu kuma sun hana ni ƙarin aure wai lafiyarsu ƙalau amma a cewarsu. Watarana ina zaune a office abin duniya ya ishe ni, sai na shirya na tafi wajen aminina tun na yarinta, domin na faɗa masa matsalata ko yana da shawarar zai ba ni. Ina isa shagonsa ya tarbe ni cikin girmamawa ina zama sai ga wata matashiyar budurwa ta kawo masa fura da nono a cikin ƙoƙo ta durƙusa har ƙasa ta miƙawa abokin nawa cikin girmamawa..
"Yana karɓa ya miƙo mini ya ce na sha, duk da na nuna masa na ƙoshi amma sai da ya tilasta ni na sha. Haƙiƙa na ji daɗin fura da nonon nan ba kaɗan ba, har ce masa na yi ya rinƙa saya min kullum zan rinƙa aikowa a karɓa min. Daga nan muka fara tattaunawa har na faɗa masa matsalar da ta kawo ni wajensa.
"Ba tare da wani dogon nazari ba ya ce min aure kawai zan ƙara shi ne maganin matsalata. Nan take kuwa na yarda da maganarsa, amma ban san wacce mata zan aura ba, ya kalle ni da murmushi ya ce "Ai Hafsatu yakamata ka aura Alhaji Iliyas." Cike da mamaki na ce, "Wace ce kuma Hafsatu?" Ya ce, 'Ita ce wacce ta kawo min nonon nan da ka sha, ita yakamata ka aura, saboda tana da hankali. Alhaji na tabbata idan ka auri Hafsatu sai ka zo ka yi min godiya, kuma ƴaƴanka za su samu tarbiyya mai kyau..' Na tambaye shi inda take, ya ce min mahaifinta daga ƙauye ya dawo birni yake gadi a gidan wani mai kuɗi, suna zaune a unguwar Darmanawa amma dukkansu Fulani ne.
Ban yi ƙasa a gwiwa ba, da daddare abokina ya raka ni gidan su Hafsatu muka samu mahaifinta da maganar amma sai ya nuna sam bai amince ba. Ba ya so ya yi wa ƴarsa auren dole, ko kuma ya aura mata wanda bai dace da ita ba. Duk yadda muka so ya fahimce mu a lokacin nan, amma ya gaza hakan. Tilas muka taho muka rabu da shi, a hanya abokina ya rinƙa kwantar min da hankali tare da cewa bayan kwana biyu mu koma zai amince. Amma kar mu nuna masa kuɗi, don indai muka nuna masa kuɗi to har abada ba zai bamu aurenta ba, tsatstsauran ra'ayi gare shi...
"Hafsatu matashiyar budurwa ce kyakkyawa ce sosai jinin Fulani. Tana da hankali nutsuwa da kamun kai, kuma ƴar talakawa ce sosai amma yanayin suturar jikinta ne kawai zai nuna ma hakan, amma ba fatar jikinta ba.
Bayan mun koma wajen mahaifin Hafsatu an kai ruwa rana kafin ya amince ya ba ni aurenta, sai da Hafsatun da kanta ta ce ta yarda za ta aure ni sannan ya yarda. Ya ce ya bamu ita ne don ta furta cewa tana sona, amma ta sani duk abin da ya same ta laifinta ne don shi ya fita haƙƙinta. Dalilinsa na ƙin amincewa ya ba ni aurenta shi ne ba ya son ya kai ƴarsa cikin kishiyoyi musamman ma waɗanda suka girme ta, suka fi ta sanin rayuwar aure. Ba mu baro wajensa ba, sai da na yi masa alƙawarin cewa ba zan bar Hafsatu ta sha wahala ba. Ba a ɗauki dogon lokaci ba aka ɗaura aurena da Hafsatu a kan sadaki naira dubu hamsin. Da farko dubu ɗari biyar na bayar da sadakinta, amma sai ya ce kuɗin sun yi yawa shi ba sayar da ƴarsa zai yi ba, na biya yadda ake biyan sadakin duk wata ƴar talaka.
"Ranar da aka ɗaura aure da yamma aka ɗauke ta zuwa gidana da yake Hotoro GRA, part huɗu ne a gidan matana kowace da part ɗinta shi kuma sauran part ɗin shi ne nawa. Amma tun da Hafsatu ta shigo gidan nan na tare a nata part ɗin, idan ka ga na je part ɗina to wanka zan yi, daga ƙarshe ma a part ɗin Hafsatun na tare gabaɗaya duk da hakan bai yi wa sauran matana daɗi ba. Tun da aka kawo Hafsatu gidan nan, ba ta taɓa hayaniya da kowa ba saboda tsananin haƙurinta. Tana yi wa sauran matana biyayya tamkar su suka haife ta, da farko ƙiyayya da wariya ta fara fuskanta daga wajen kishiyoyinta. Amma kyawawan halayenta ya sa suka fara sassauta mata, har suke shakkar nuna mata ƙiyayyar a bayyane.
Watan Hafsatu shida a cikin gidana Allah Ya ba ta juna biyu, na yi murna sosai da samun wannan cikin. Sai dai ba haka yake ba daga wajen matana, a gabana su ma suna nuna jin daɗinsu da samun juna biyun amma a bayan idona kullum hanyar da za su lalata cikin suke nema.
"Da wata amintacciyar ƴar aikin gidana mai suna Dije ta same ni ta faɗa mini duk irin makircin da suke shiryawa Hafsatu a kan wannan juna biyun da ta samu. Ni kuma da na ji haka sai na hana ta cin duk wani abinci da ya fito daga hannunsu, hatta abincin gidan ma gaba ɗaya wanda ƴan aiki suka girka na hana ta ci, kuma na hana ta girkawa da kanta saboda ba na so ta rinƙa shan wahala saboda juna biyun da yake jikinta. Duk abin da ta ce tana so komai wahalarsa sai na nemo mata shi.
"Yayin da ta shiga watan haihuwarta ma daina fita ko ina na yi. Da kaina nake tarairayarta, don ba na so naƙuda ta zo mata matana su zo kanta ban san abin da za su shirya mata ba. Da yake ba a yi wa Allah wayo kuma mutum ba ya gujewa ƙaddararsa sai wata ranar litinin aka kira ni daga kamfanina cewa na yi baƙi daga U.S.A suna jirana urgent. Dole sai na zo, tilas na shirya na tafi, ba don raina ya so ba, sai don ba yadda zan yi. Ina fita naƙuda ta zo wa Hafsatu, da taimakon Dije da sauran matana aka kai ta asibiti, ta haihulafiya amma ta jigata sosai ta fita daga cikin hayyacinta.
"Sai sauran matana suka haɗa kai da likitan asibitin suka ba shi maƙudan kuɗaɗe suka ɗauke jaririyar da Hafsatu ta haifa suka bai wa wata mata da ban san kowace ce ba ta je ta jefar da ita. To shi ne da ba ta samu inda za ta jefar da ita ba, sai ta bar ta a cikin adaidaita-sahunka ta gudu.."
Malam Hassan ya jinjina kai ya ce, "Haba koda na ji, ai na san babu uwar da za ta haifi ɗa kuma ta gudu ta bar shi a cikin adaidaita-sahu. Kuma wallahi Alhaji lokacin da na ɗauko matar nan, a jikina nake jin cewa ba ta da gaskiya, kawai don na ga tana buƙatar taimako ne shi ya sa na taimaka mata."
Alhaji Iliyas ya ci gaba..
"Sai da matana Suka yi wa Dije ƴar aiki barazanar kisa idan har ta tona musu asiri, sannan suka ba ta maƙudan kuɗaɗe masu yawa a kan ta yi shiru a kan lamarin. Lokacin da Hafsatu ta dawo cikin hayyacinta sai suka kira ni cewa naƙuda ta tasowa Hafsatu amma sun kai ta asibiti, sun kira ni ba su same ni ba amma har ta haihu ɗan bai zo da rai ba. Har an binne shi.
"Daga yanayin yadda suke ba ni labarin sai na ji ban yarda da su ba, kuma batun kira tabbas sun kira ni a lokacin da muke meeting. Dalilin da ya sa ban ji kiran ba na saka wayata a silent sai da na fito na ga kiran, kafin na kira sai na ga sun sake kirana. Cikin sanyin jiki na zo asibitin na tarar da Hafsatu a kan gado tana barci, yayin da ta farka aka shaida mata cewa ba ta haihu da rai ba, sai da ta sha kuka sosai ni ne na rinƙa ba ta haƙuri tare da kwantar mata da hankali duk da ni ma abin ya taɓa ni sosai sai dai na miƙa duka lamurana ga Ubangiji wataƙila hakan shi ne mafi alheri a gare mu. Bayan sati guda ta samu lafiya sosai muka dawo gida.
"Amma kullum Hafsatu a cikin damuwa take, tilas na dawo zaman gida na rinƙa kwantar mata da hankali har ta manta da batun haihuwar da ta yi ba rai.. Bayan wasu watanni ina zaune a falona da safe sai ga Dije amintacciyar ƴar aikina ta shigo cikin falona fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye.. Cikin tashin hankali na hau tambayarta abin da ya faru take kuka, nan ta durƙusa a gabana tana kuka tana faɗin na yi mata afuwa na yafe mata ta ci amanata.
"Cikin rashin fahimta nake tambayarta abin da ya faru, kuma wanne laifi ta yi mini. Sai da ta share hawayenta sannan ta fara faɗa min duk abin da ya faru tun daga lokacin da Hafsatu ta fara naƙuda har zuwa sanda ta haihu da barazanar da matana suka yi mata cewa idan har ta tona musu asiri sai sun kashe iyayenta da suke ƙauye, kuma ita ma sun hallaka ta.. Cikin kuka ta ƙarashe da faɗin 'Wallahi Alhaji babu hannuna a cikin lamarin nan, ina son iyayena ba na son na rabu da su shi ya sa na kasa sanar da kai gaskiyar abin da ya faru. Kuma wallahi duk kuɗin da suka ba ni a matsayin cin hanci suna nan a cikin ɗakina ko naira biyar ban taɓa ba.' Wani abu na ji ya zo ya tsaya mini a zuciya kamar ƙashi a maƙoshi, na ji wani irin fushi da ɓacin rai suna taso mini daga can ƙasan zuciyata..."
Hussain Yusuf✍️
ALLURA TA TONO GARMA 14
END
"A fusace na tashi tsaye na sa ƙafa na harbar da Dije na ɗauki wayata na kira DPO cikin ƙanƙanin lokaci ya bayyana a cikin gidana tare da yaransa. Nan take na ba shi umarnin tafiya da matana har da Dije. Wasu daga cikinsu suka je asibitin da aka kai matata suka taho da likitan da ya karɓi cin hanci daga wurinsu.
"Cikin nutsuwa DPO ya rinƙa bincikarsu ɗaya bayan ɗaya suna faɗa masa duk yadda abin ya faru, matar da suka saka ta jefar da jaririyar ce kaɗai ba a samu ba. Wai ta tafi ƙasar Saudi-Arabiyya. Ni kuwa na ce ko birnin Sin ta tafi sai na saka an kamo min ita.
"Bayan DPO ya gama duk bincikensa, sai ya ce min akwai wata jaririya da aka bar ta a cikin adaidaita-sahun wani dattijo, ko a kawo min ita na ganta. Cikin ikon Allah da aka kawo ta, kallo ɗaya na yi mata na gane ƴata ce, saboda tsananin kamar da nake yi da ita, to a taƙaice wannan shi ne dalilin da ya sa ka tsince ta a cikin adaidaita-sahunka."
Kowa ya yi shiru yana mamakin lamarin a cikin ransa. Alhaji Iliyas kuwa ya zubawa yarinyar ido sai murmushi yake na farin cikin dawowar ƴarsa zuwa gare shi.. Nan take DPO ya umarci a shigo da matan Alhaji cikin ofishinsa, cikin ƙaramin lokaci aka shigo da su duk sun canza kamanni, saboda sun sha duka a wajen ƴansanda kafin su faɗi gaskiya. Dije ce kaɗai ba a daka ba, saboda ita ta fara tona sirrin.
Alhaji Iliyas ya kalli matan nasa ya ce, "Kun raba ni da ƴata Allah ya tseratar da ita, Ya haɗa ta da mutumin kirki Malam Hassan ya bai wa matarsa ta raine ta cikin gata da kulawa. Yau kuma ta dawo gare ni.."
Mamaki haɗe da ɗan tsoro ne ya bayyana a fuskar matan nasa. Saboda tsananin kunya suka sunkuyar da kawunansu ƙasa Alhaji Iliyas ya ci gaba da faɗin, "Saboda haka ina son ku sani cewa na sake ku saki uku. Kar ku sake ku koma min cikin gida, Hafsatu kaɗai ta ishe ni rayuwa. Ban yarda ku ɗaukar min komai a cikin gidana ba, tun da dama babu abin da ku ka zo da shi, alfarma ɗaya zan iya yi muku ita ce zan ƙyale ku, ku ɗauki tufafin sakawarku. Bayan shi ban yarda ku ɗauki komai ba.. Dije kaɗai na yarda ta dawo cikin gidana da zama, saboda na lura babu saka hannunta a cikin lamarin barazana ku ka yi mata."
Kukan nadama suka saki gaba ɗayansu, suna bai wa Alhaji Iliyas haƙuri amma ko kallon inda suke ba ya yi ya kawar da kansa gefe guda.
Ya kalli DPO ya ce, "Yallaɓai ka sake su kowace ta tafi gidan ubanta, amma ka fara haɗa su da yaranka su je su ɗauko tufafinsu a gida. Bayan shi ban yarda su ɗauki komai ba."
Nan take DPO ya umarci yaransa ya ce su tafi da su gidan Alhaji su ɗauko kayansu su kama gabansu.
Hauwa'u ta fashe da kuka ta ce, "Alhaji don Allah kar ka raba ni da Jiddah! Wallahi ina tsananin sonta kamar ni ce na haife ta."
Alhaji Iliyas ya yi murmushi ya ce, "Ma sha Allah! Har raɗa mata suna mai daɗi kuka yi Jiddah?"
Malam Hassan ya ce, "Eh na saka mata sunan matata ne saboda yadda na ga tana nuna mata soyayya.."
Alhaji Hashim ya ce, "Sunan ya yi min daɗi Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi. Sannan batun na bar muku Jiddah ba hurumina ba ne, idan ta ni ne wallahi na bar muku ita halak malak, sai dai mun ji daga bakin mahaifiyarta.."
Godiya sosai Alhaji Iliyas ya yi wa DPO sannan suka ɗunguma gaba ɗayansu zuwa gidan Alhaji Iliyas.
Yayin da Hafsatu ta ga ƴarta wacce ta tsugunna ta haifa, ba ƙaramin kuka ta sha ba. Ta rinƙa yi wa su Malam Hassan godiya, har rungume Hauwa'u ta yi.
Bayan sun zauna Alhaji Iliyas ya ba ta duka labarin abin da ya faru. Ta sha mamaki sosai. Alhaji Iliyas ya sake faɗa mata buƙatar da su Malam Hassan suke da ita a wurinsu. Nan take ta amince ta ce dama ba ta shaƙu da yarinyar ba, tun da ta fi shaƙuwa da su kawai su je su riƙe ta, su raine ta. Ita ma Allah zai ba ta wasu nan gaba..
Har ƙasa su Malam Hassan suka durƙusa suna yi musu godiya. Alhaji Iliyas ya ce ba komai.
Yinin ranar a gidan Alhaji Iliyas su Malam Hassan suka yi shi.
Bayan sati biyu, Alhaji Iliyas ya bai wa Malam Hassan danƙareren gida a kusa da shi. Ya siyowa Jiddah kayan sakawa masu kyau da tsada masu yawan gaske, ya biya masa Umrah shi da Hauwa'u har da Jiddah duk suka tafi. Bayan sun dawo Alhaji Iliyas ya bai wa Malam Hassan kuɗaɗe masu yawan gaske domin ya ja jari...
Kafin wani ɗan lokaci Malam Hassan ya zama hamshaƙin mai kuɗi. Yana da shaguna sun fi guda goma da yake gudanar da kasuwancinsa, zumunci mai ƙarfin gaske ya ƙullu tsakanin Alhaji Iliyas da Malam Hassan.
Alhaji Iliyas ya mayar da Malam Hassan tamkar mahaifinsa, duk lokacin da ya buƙaci shawara a kan wani abu da ya shige masa duhu, kai tsaye wajen Malam Hassan yake nufa kuma da ya ba shi shawara zai ga haske. Yayin da Jiddah ta fara girma sai ta zaci ma Alhaji Iliyas shi ne mahaifinta, Malam Hassan kuma kakanta ne yake riƙon ta.. Rayuwa ta yi musu kyau saboda sun riƙe gaskiya da amana kuma sun ga ribar hakan....
A ɓangaren Ɗantani kuwa al'amuran sun ƙara rikice masa, karayar da ya samu a ƙafafunsa tsawon shekara guda ba ta warke ba. Sai wata mugunya da take fitarwa mai warin tsiya,a cikin ƴaƴansa kuwa babu wanda ya taɓa zuwa duba shi ko sau ɗaya. Ƴan'uwan nashi ma sun gaji da ɗawainiya da shi, tun suna kai shi banɗaki ya yi fitsari ko kashi har sun gaji sun daina. A inda yake zaune yake yin fitsarinsa da kashinsa, har sai lokacin da wata ƴar'uwarsa ta zo daga ƙauye take gyara shi.
Matarsa Rabi ta sayar da gonarsa da take ƙauye ta sayi ƙaramin gida a can wata unguwar ta koma saboda bakin mutane ya yi yawa a kansu.
Asabe rayuwa ta ƙare rikice mata, ta ɗan samu lafiya amma sam ba ta da kuzari. Ga tarin baƙin ciki da nadama da suka mamaye ta, a kan idanunta Fadeela take shigowa da maza kala-kala cikin gidan su yi abin da ransu yake so su biya ta su tafi. Kullum Asabe cikin kuka take ta rasa yadda za ta yi da ranta.
Ita yanzu babban burinta ma bai wuce ta ga Malam Hassan ta roƙi yafiyarsa ba. Amma ba ta san inda za ta gan shi ba, ga hukuncin kotu yana jiransu idan sun samu lafiya abu goma da ashirin ya haɗe mata ta rasa yadda za ta yi da ranta. Ga Fadeela kullum cikin cusa mata baƙin ciki take, ƴaƴanta biyu kuwa ba ta san inda suke ba a yanzu.. Ƴan yaranta mazan su ne suke ɗan ba ta kulawa, sai dai ƙarfinsu bai kawo sosai ba.
Wata rana tana zaune tunanin duniya da abin da ta aikata ya ishe ta, kawai ta ga Fadeela a tsaye bisa kanta tana watsa mata wani kallo. Cike da rashin kunya tamkar ba mahaifiyarta ba ta ce, "Inna ni fa na gaji da biyan kuɗin hayar nan da nake yi, yau za su zo su tashe mu don ban ba su kuɗin waccan shekarar da wannan ba. Don haka ni zan yi tafiyata na kama gabana, na yi miki iya abin da zan iya. Ke ma sai ki kama gabanki ki san inda dare ya yi miki, idan kuma ki ka tsaya suka same ki duk abin da suka yi miki babu ruwana..." Ta yi shigewarta cikin ɗakinta ta fara tattara kayanta... Asabe ta rushe da kuka, tare da tunanin mafita...
Malam Hassan yana zaune a office ɗinsa, P.A ɗinsa ya shigo da sallama. Bayan ya amsa sai ya ce masa "Yallaɓai wasu mabuƙata ne a ƙofa wai suke son ganinka, suna cikin damuwa suna tsananin buƙatar taimako."
Malam Hassan ya ce, "Ka shigo da su cikin reception yanzu zan zo na gan su." Bayan ya kammala abin da yake ya tashi ya fita, turus ya ja ya tsaya ganin Ɗantani a zaune a kan tayis da yankakkiyar ƙafa an naɗe ta da bandeji. Gefe kuma Asabe ce ta haɗa kai da gwiwa sai hawaye take. Tufafin jikinta duk sun koɗe sun fita daga hayyacinsu. Ita ma kanta ta yi wata irin rama kamar wacce cutar ƙanjamau ta kama..
Tun da Malam Hassan ya fito daga office ɗinsa, suka zuba masa ido mamaki shimfiɗe a kan fuskokinsu.. Asabe cikin ranta ta ce, "Kaicona! Dama ban ci amanar Malam ba, haƙiƙa Ɗantani ka cuce ka cutar da rayuwata.." Tana gama wannan zancen zucin sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.. Ta rarrafo gaban Malam Hassan ta riƙe ƙafafunsa tana ba shi haƙuri cikin kuka... Shi kuwa Ɗantani ya yi shiru kamar wanda ruwa ya cinye, sai matsar hawayen nadama yake, ko haɗa ido ya kasa yi da Malam Hassan.
Dakyar dai ya yi ƙarfin hali shi ma ya fara roƙon yafiyarsa a kan cin amanarsa da ya yi... Malam Hassan ya zuba musu ido ya yi shiru....
ƘARSHE!
Ko Malam Hassan Zai Yafe Musu Kuwa? Allah Masani Ni ma Dai Iya Nan Na Samu Damar Rubuta Muku Sauran Sai Ku Yi Nazari Da Ƙwaƙwalwarku Ku Ba ni Amsa. Bissalam.
ALHAMDULILLAHI!
A nan na kawo ƙarshen wannan ɗan gajeren littafin mai suna ALLURA TA TONO GARMA Allah Ya sa mu amfana da darasin da muka ɗauka a cikin labarin..
Domin gyara ko sharhi sai a tuntuɓe ni ta wannan lambar ***.