3
***********Duk abinda ake yi Abbah ba zai taba ɗaga kai ya kalle ka ko yace wani abu ba, koda za'a yi kisa a gabansa, amma yau shine da ɗaga kai ya kalla Baby dake maidawa da Yayarsa magana. A iya saninsa babu wanda ya taɓa maida mata da martani tunda take ta kawo wannan munzalin kuwa. Ba iya Abbah kawai hatta Sahal maganar ta jiƙa shi sosai. Dan sai da ya bita da kallo dan ba ƙaramin mamaki ne ba ya ji. Su kan su Mujahid tsayawa suka yi suna kallan Mamin na su da Baby. Ba wata magana ba ce ta faɗa mata, amma yanzun nan zata koma babba. Ina ruwan ta itama? Komai ta gani sai ta mayar da shi abin magana.
"Mu je ka duba mata ƙafar".
Ummie ta faɗa tana kallan Sahal. Ficewa ya yi ya bi bayansu zuwa wajen. A kan kujera ta zauna tana jin ɓacin rai sosai a ran ta. Ummie komawa ta yi ta cikin gidan, yayin da shi kuma ya je ya ɗauko kit ɗin ya yi tsugunne yana fara cire mata bandage ɗin.
"Taya kika ji ciwo?
Ya yiwa zuciyarsa tambayar sai kuma ya ji ashe wai a fili ya faɗa.
"Bugewa na yi".
Ta faɗa amsa a hankali tana jin hawaye na cikowa idan ta. Ƙafar ya kalla sannan ya kalleta yarda fuskar ta yi wani baƙim kwalli ga su foundation nan sun yi wani dabbaro dabbaro a fuskar. Haka nan ya ji tsaki yana kwace masa.
"Dan Allah meye Jahila, Meye tarbiyya yake nufi? Tinkiya kuma na nufin waya dabba ko? Na taɓa ji a wurin wata Iya Yelwa ta ce tinkiya dabba ce ko? To su dabbobin su waye su? Wai tace ba su da hankali ko?
Kawai tsayawa ya yi daga shafa mata ointment ɗin yana kallan ƙafar batare da ya cigaba da abinda yake yi ba. Meke cikin kan wannan yarinyar? Ina ta taso ta yi rayuwa da bata san all wannan abubuwan ba? A hankali ya kalleta yaga yarda take share hawaye. Zuciyarsa haka nan ya ji tana bugawa batare da wani dalili ba. Da sauri ya fizgi ƙafar ya yi mata massaging, yana sautin kukanta ta tsakiyar ƙwaƙwalwar sa da zuciyarsa. Sosai ya naɗe ta ƙafar sannan ya bata magani yana tashi batare da ya kwashe kayan ba.
A kan gado kawai ya kwanta yana dafe ƙirjinsa dake tsananin yi masa zafi, ruwa sanyi ya je ya ɗauko ya sha ko zai ji sauƙin abin, amma a banza kamar zafin ya ji ya ƙarawa kan sa. Kafin a hankali ya dafe kan sa yana jin stress sosai acikin kan sa yana damun sa. Kawai bejin kan sa dai-dai a kwanakin nan, ba kuma tare da ya san dalilin yin hakan ba. Sake kwanciya ya yi akan gado yana kulle idan sa wai ko zai samu bacci,amma inaaa ko kaɗan bacci be kwashe ba, sai kuma ya ji wani sassanyar ƙamshi a kan gadon nasa, da yake da shi jin wani yanayi na daban mai kama da nutsuwa. Kafin de ya yi ƙarfin kulle idan sa yana hana kan sa kallon direction ɗin saboda zai iya ganinta muddin ya maida kan sa wurin....
******Yayin da Mami ke daskare tana kallan Abbah dasu Mujahid, kafin Ummie ta dawo tana bawa Mami haƙuri.
"Ishaq a gaban idan ka aka ci min mutunci".
"Ki yi haƙuri".
Cewar Ummie tana sunkuyar da kan ta sam bata san rashin jituwa wallahi.
"Ai zancen haƙuri be ta so ba. Ba zan sake dawowa gidan nan ba har sai wannan yarinyar ta dena zuwa wannan gidan".
Cike da ladabi Ummie ta ce, "Hakan ma ba zata sake faruwa ba".
Sauke numfashi take yi kamar wanda ta yi gudun tsare take neman ɗauki.
"Ki yi haƙuri".
Cewar Abbah shima cike da ladabi kamar wata uwarsa.
"Daman ba wani abu bane, zuwa na yi na gan ka na duba jikin naka kuma".
"Alhamdulillah da sauƙi. Na warware har na fara fita".
Jinjina kai ta yi kawai. Mujahid da su Salimah kawai kallanta suke yi, uban na su ya yi jinya kamar zai mutu bata zo dubiya ba and now ta nuna kamar ta fi kowa son shi. Su har sun manta da ya yi wata jinya ta tashi. Yanzun ma ba takanas ta zo ba, taron da suka yi ne yasa ta zuwa.
"Ni zan wuce. Idan kana son wani abu sai ka faɗa".
"A'a".
Ya bata amsa a gajarce. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Idan anyi hutu a tabbatar da an kawo wannan yaran sun yi hutu wurina. Suma suke ganin gari, ka dena ƙunshe su a cikin gida".
"Za su zo in sha Allah".
Idan wannan ya kalla wannan sai wannan ya kalla wannan, duk da suna son zuwa dan rayuwa ce suke yi free ba hayaniya sai abinda ka ke so, ka fita sanda kaga dama ka dawo sanda ka ga dama. Ba takurawa ba komai. Yayin da Ummie ta kalli Abba sannan ta kalli yaran na ta, wallahi sam bata san zuwan su, saboda irin rayuwar da suke yi acan, sam bata so, bata ƙaunar duk wani abu zai rabata da yaran ta, muddin suka je suka dawo sai taga wani sabo a tattare da su. Raka ta duk suka yi kafin suka dawo suka ci abinci da bata ci ba, sannan suka shirya suka wuce Islamiyya har Mujahid ba'a barshi ba a gida.
"Abbah".
Ummie ta faɗa a hankali tana kallansa.
"Ko ka yi bacci?
Ya sake faɗa a hankali tana zama a kusa da shi. Tashi zaune ya yi yana kallon ta kafin a hankali ya sakin mata murmushi yana miƙa mata hannu. A gefensa ta zauna tana sunkuyar da kan sa. Be taɓa ganin mata mai kawaici ba alkunya irin Ummie. Ba ruwanta da hayaniya balle tashin hankali kullum cikin bada haƙuri take amma banda ƴar uwarta Lailah yayarta kenan.
"Ina jin ki".
Ya faɗa a hankali yana kallon ta.
"Batun zuwan su hutu...
Sake riƙe hannunta ya yi yace, "Kin san ba zan iya cewa a'a ba ko? Yayata ce, bana iya musu ki yi haƙuri dan Allah".
Jinjina masa kai ta yi tana jin ƙwalla na taruwa sosai a idan ta.
"Shikenan".
Ta faɗa a hankali tana tashi.
"Ki zo mu zauna mana, ina zaki je?
Tana ɗan murmushi ta ce, "A'a zan ɗaura abincin dare ne, yau zan fita da yamma".
Jinjina mata kai ya yi yace, "Mu je na tayaki".
Itama murmushin ta yi suka fito daga ɗakin. Tashin Sahal kenan daga juye-juyen da yake ganin bazai kai shi ko ina ba yasa shi tashi dolensa ya ɗan watsa ruwa. Ya tsaye a wurin window kenan ya hango Ummie da Abbah a kitchen, Ummie na dariya da'alama wani labarin yake bata. Dariya take yi sosai, shi kuma yana tsaye jikin sink yana wanke wanke. Ita kuma tana daga kusa da shi akai kai tana zuwa wurin gas ta duba abu ta sake dawowa kusan shi. Ya jima a tsaye kawai yana kallon su har aka fara kiran la'asar kafin ya sauke ajiyar zuciya, yana tunanin iri-iri a cikin kan sa. Shima wucewa ya yi kawai ya shirya ya saka kaya ƙanana sannan ya fito.
Da ita ya fira cin karo ya zo zai fita daga gare ɗin su ya ganta, ta ci uwar kwalliya sosai, ansha ƙwalli anyi hawayen masoyi, an zuba jambaki raɗau, fuskar nan ta sha ɗigo-ɗigo ta ko ina. Sai de yau ba'a da foundation da concealar ba. Ga wata shegiyar baƙar filawa a hannunta. Kuma ya tabbatar duk a yanzun ta yi su ba'a jima ba. Be ma tsayawa jin gaisuwar ta ba ya wuce yana yin gaba daga kallo ɗayan da ya yi mata ba. To me zai ce mata?
***********A hankali ya shiga bude idan sa, sakamakon, jin irin kukan da ya ji irin na jiya. Hakan yasa shi buɗe idan sa sosai, sai de be je ga tashi ba. Amma jin an fara iska mai masifar ƙarfi yasa shi kulle idan sa, bacci yake ji sosai, kan sa har wani bugawa yake yi da sarawa. Wannan iskar ma kawai ta isa ta hana shi bacci, balle kukan da yake jin sa har cikin zuciya da ƙwaƙwalwarsa. Duk da irin iskar da ake yi mai masifar ƙarfi hakan be hana shi kasa jin kukan ta dake fita ba, wanda kuka ne take yi da ga dukkan zuciyarta, na wani abu na damun ta. Rintse idan sa ya yi sosai kafin a hankali ya sauko yana sakin ajiyar zuciya sosai.
"Me kike anan?
Ya faɗa yana kallanta. Da sauri ta ɗago tana share hawayenta tana nema ta tashi. Sai kuma ta yi saurin rintse idan ta sosai saboda zafin da ta ji a ƙafarta.
"Ki nema wurin kukan ki. Amma ba nan wurin ba".
Ya faɗa yana juyawa zai koma.
"Abdulmajeed....
Tsak ya tsaya batare da ya juyo ba. Babu mahaluƙin da ya taɓa ambatarsa da wannan sunan tunda yake a cikin tarihin rayuwarsa, zai yi wahala a ambaci wannan sunan, a gida ana ce masa Sahal ne, a waje a kira shi da AM inda ya yi karatu kuwa a ƙasar waje sai de suke kiran sa da sunan Family ɗin sa. Amma yau shine aka kira da wannan sunan, hatta Abbah Sahal yake ce masa ko yace masa Abdul. Amma gashi yau an kira shi da sunan, a tarihi tabbas ita ta farko. Kai ko ya faɗa sunansa a wani wajen sai de a gajarta ace Abdul, amma ba de a faɗe shi kai tsaye duka ba....
Batare da ya juyo ba ta ƙaraso gabansa tana ƙarasa share hawayen da ba dena zubowa ba yake daga idan ta. Fuskar nan ta yi murtuk da ita da hawaye duk idan ya kumbura, abin tausayi wallahi muddun ka kalleta ba zaka iya yin bacci ba.
"Ga abinka".
Ta faɗa tana miƙa masa, kit ɗin sa. Haka nan ya ji a ran sa be da ce ba, bata iya godiya ba ne? Be karɓa abin ba ya kalleta yana haɗe fuskarsa.
"Ke baki iya godiya ba?
Ɗagowa ta yi tana sake share hawayenta, amma wasu na zubowa, haɗa idan da suka yi ne yasa shi kulle idan sa yana jin zuciyarsa na bala'in bugu sosai, dan kuwa idan ta ta rine tamkar ya dawo jajir da shi, tsabar kuka.
"Godiya?
Ta maimaita tana kallansa. Tsaki ya ja zai wuce,ya taka ƙafarta by mistake, aikuwa ta saki uban ƙafara tana yar da kit ɗin, tare da damƙe gefen rigarsa, hakan kuma ya yi dai-dai da tsawar da aka saki mai ƙara da yawa , tuni ta sake damƙe hannunsa tana matsowa kusa da shi, sai kuma aka ɗauke nepa ɗib. Ita da take kuka, neman hawayen ta yi ta rasa tas a idan ta, tana sake ƙanƙane hannunsa sosai, farcen dake hannunta sai da ya shiga cikin fatarsa sosai, hakan yasa shi kulle ido dan akwai zafi. Tsawar da sake saki ce ta sa sake rikicewa sosai tana sake ƙanƙame shi. Sai kuma aka shiga ruwa mai bala'in ƙarfi lokaci guda ga iska da ake zubawa, irin ruwan nan mai duka. Hakan yasa shi nema ya ɓanɓareta daga jikin sa, amma taƙi yarda, dole a hakan ya shigao balcony da ita tana jikinsa. Kafin ya nema bulb ɗin balcony ɗin da already akwai shi dc ne wanda yake aike ko da nepa ko baba. Kunnawar da ya yi ce yasa shi kallan hannunsa da ta ƙanƙame shi ga dukkan hannunta tana luma masa farce a cikin hannun nasa. Itama kallan wurin ta yi da sauri ta saki wajen tana zaro idon ta da ke a kumbure sosai gashi ya yi ja.
"Dan Allah ka yi haƙuri".
Ta faɗa a raunane tana jin ƙwalla na zubo mata sai kuma ta kalla farcen na ta. Da suka fito zaƙo-zaƙo da su. Sake kallan wurin ta yi ganin irin yarda yake kallanta yasa ta komawa cikin ruwan da gudu tana manta ciwon dake ƙafarta. Ta ɗauko kit ɗin da ta faɗi ta dawo ta na fara kama hannunsa da hannunta da ya gama jiƙewa.
"Ka yi haƙuri".
Ta sake faɗa hawaye na cika idon ta. Wani mummunan tsaki ya ja yana jin ran sa ba daɗi. Be taɓa jin haushin kan sa irin na yau ba, wannan rashin abinda zai ce ɗin ba ƙaramin damunsa yau ya yi ba. Ina ma ace kamar Yaya Bashar yake? Ko kuma Mujahid? Da yanzu an wuce wajen ba wannan lamarin ba ake ba tun ajiya. Da yanzu ya san meye ce matsalarta. Me ye kuma yake damunta, sannan ya duba ya bi ko zai gyara. Allah tabbas tana sawa zuciyarsa a cikin wani mummunan yanayi....
Ja baya yi kaɗan yana yin banza da ita ya juya ya koma cikin ɗakin ya sauya kaya, ya yi kwanciyarsa. Yayin da ita kuma take tsaye sai rawar sanyi take sosai. Yana daga kwance yana hango ta dan be kashe wutar wurin ba. Sai kuma yaga ta samu waje ɗaya ta rakuɓe ta yi kwance daga ƙasan wurin. Ga feshin ruwa, sannan ga sanyi tiles, amma a haka ta kwanta, kuma ace bacci zata yi?
A hankali ya tashi zaune yana cigaba da kallanta, dagaske jefa zuciyarsa take yi a cikin wani irin hali, tausayin ta fal a cikin a ran sa. Shikam ya zai yi da wannan abar da ta zo cikin rayuwarsa? Me yake damun sa? Me ya ke samun sa? Ya zai yi da wannan rayuwar da be jin daɗin ta sam a kwana biyun nan, ga wancan matsalar ta aiki, ga wannan abar da ta zo masa cikin kan sa. Me yasa kan sa da ƙwaƙwalwar suke sashi cikin wani irin mummunan yana yi saboda ita?.
Wani irin rintse ido ya yi sosai, kafin a hankali ya tashi ya fita wurin ya yi mata daukan cak har zai ajje ta a gado, sai kuma ya shiga kallan kayan jikinta, sai kawai ya ajjeta akan a carpet, Kafin a hankali ya zare mata su tas yana hana kan sa kallanta. Ya kawo nasa kayan ya sanya mata, sannan ya sa masa wasu kayan sa masu dubi kafin ya ajjeta akan gado yana rufe mata jiki. Kafin ya ƙurawa fuskarta ido sosai, dake cike da baƙin kwalli duk ya dame mata fuska. Kayan ya kalla basu da maraba da tsumma, wasu tsumma ma sun fi su.....