Kuncin zuci
by @bintuuu
Sai da Ahmad ya wuce dan qaramin corridor sannan ya isa cikin babban falon gidan, nan ya sauketa a hankali sai ya kai hannu ya taba wall din gefensa nan take haske ya gauraye a falon Na'ima na kallo, dan bin falon tayi da kallo idanunta dauke da mamaki ganin komai na cikinsa fari ne da sirkin baki, exactly irin interior din office din Ahmad na London da taba fada masa ya burgeta, ji tayi ya sako hannayensa daga bayanta ta rungumota zuwa jikinsa tareda dan dora kansa a kafadarta suna kallon falon tare, ahankali ya rada mata "Do you like it?" sai tayi shiru bata ce komai ba nan ma ya sake rada mata "ko achanja" da sauri ta dan girgiza kai tace "No..I like it" sai Ahmad yayi murmushi jin tace ya mata, dan matsawa Na'ima ta farayi daga jikin nasa dan wani irin nauyinsa takeji yau, physical contact din nasu yana sa ta jin wani iri, Ahmad bai hanata ba har ta bar jikinsa sai ya kamo hannunta ahankali ya fara takawa zuwa babban stairs din cikin falon da shima ya kasance fari, jiki babu laka Na'ima ta bishi hannunta cikin nasan suka fara takawa zuwa saman, sai da ya kaita har cikin falonta sannan suka zauna akan sofas Na'ima na bin nan din ma kallo ganin girmansa sannan shikuma ya kasance komai na cikinsa brown hade , kujerun ma two colors ne in mixture of brown and milk color din, ba ta wani tsawaita kallo ba ta duqar da kanta tareda gyara mayafinta, Ahmad dake zaune gefenta sai kallonta yake ganin yanda kayan jikinta yayi mata wani irin kyau na musamman, ga qamshi mai sanyi dake tashi a jikinta, hannunta ya riqo a nutse, sai ta dan dago kai tana kallonsa taga wani irin sanyayyen murmushi yake mata, ahankali yace "Welcome Home Na'eemah naa" sai ta duqar da kai tanajin itama murmushin na zuwa mata, dan damqe hannunta yayi cikin nasa sai basu sake cewa komai ba suka zauna shiru na wasu lokuta, can ya fara qoqarin miqewa sannan ya duqa ya dago ta miqe itama da haka ya sake riqo hannunta ya nufi dakin ta dake nan cikin falon, wani babban daki Na'iman taga sun shiga, wall din dakin ta gefen babban gadon sai ya kasance na glass ne da manyan curtains, a bayan glass wall din kuma balcony ne da wasu artificial grasses masu kyau, sai da ya zaunar da ita a bakin gado sannan anutse yace "freshen up Babe, sai muyi sallah ko" gyada kai kawai tayi da haka ya juya ya fita daga dakin tana kallonsa, sai sannan ta sauqe dogon numfashi, yau din wani irin nauyinsa takeji fin misali, ahankali ta sauqe mayafinta tareda dan ware dankwalinta, har sannan ciwon kan bai saketa gaba daya ba gashi kuma daure gashinta da tayi sai yake qara mata wani ciwon kan, hannu takai ta zare ribbon din gashinta ya sauqa jikinta sannan ta zauna shiru tana tunani, so this is it, wani rayuwan auren ta sake shiga a karo na biyu, but this time tareda wanda takeso kuma yake sonta, was this the end of all the chaos in her life ko akwai sauran jarabawan a gaba? sai taji hawaye na zuwa mata tuna wani nauyin ne ya sake hawa kanta for the second time in her life....tananan zaune tana share hawayen sai ta juya tana kallon balcony dake bayan glass wall din dakin da ya kasance a rufe, sai kuma ta juya tana bin dakin da kallo ganin kofofi guda biyu aciki, ahankali ta miqe ta nufi wadda ke kusa da ita ta tura nan taga wani babban walk in closet ne cike da kaya kala kala, ko wanne shelve a jere yake da kayan sawa da takalma, jakunkuna, accessories da kuma sauransu, juyawa tayi ta fita ta sake shiga kofan dake other side of the room nan kuma taga babban toilet ne me dauke da wani farin bath a tsakiyarsa, komawa tayi cikin closet din nata ta fara cire kayanta sannan ta dauki wani babban towel tasaka tareda dora babban hijab akai ta nufi toilet, ba ta dauki mintina ba ta fito sai taga Ahmad zaune a bakin gadon ta sanye cikin jallabiya, ganinsa yasa ta danyi stiff a bakin toilet din sai taga ya miqe yana gyaran murya kadan yace "in kin gama ina falo" sai ta gyada kai da haka ya nufi kofa ya fita, saida ta shirya cikin wasu dogayen kayan bacci riga da wando masu kauri sannan ta sake dora babban hijab din akanta ta fita, samunsa tayi zaune kan daya daga cikin sallayun da ya shimfida musu a falon, ganinta ya sashi miqewa yana gyara tsayuwa alamun sallah zasuyi, qarasawa tayi ta bi bayansa suka tada sallah, bayan sun idar suna zaunen ya juyo yana facing dinta while kanta a duqe, ahankali ya kamo hannuwanta duka biyu cikin nashi sai ya fara karanto addu'o'i masu dadin sauraro a kunnenta, bata tabajin muryarsa cikin sautin larabci haka ba sai ta samu kanta da jin sanyi arai tana sauraronsa, sai da ya dauki mintuna yana addu'an sannan ahankali taji yace "Na'eemah" dan dago kanta tayi ta kallesa sai kuma ta kasa jure kallon da yake mata tayi saurin maida kanta qasa, anutse taji yace "Ina sonki Na'eemah, dan Allah ki bani hadin kai mu gina rayuwan aurenmu cikin aminci kinji" ahankali ta gyada kai sai ta dago kanta ta kallesa, yana kallonta ahankali ya sake cewa "Allah ya cire duk wani sharrin da zai shiga tsakanina dake wife" ahankali tace "Amin", da haka Ahmad ya miqe ya fita daga falon, tananan zaune kuma ta miqe tana cikin linke sallayun ya dawo hannunsa riqe da handbag dinta data bari a motansa da kuma ledan abincinsu da ya siya a restaurant dazu, da dan hanzari ya ajiye kayan ya iso gareta ya karbi sallayan yace "Let me do all the work Babe" sai tayi murmushi tace "zanyi ai" yace "No..banason kiyi lifting komai yau kinji" bata bar murmushin ba ta sake masa abun hannun nata ya qarasa linkewa ya ajiye sannan ya dauki handbag dinta yakai mata dakin ya dawo, nan ya sake fita ya dawo hannunsa da plates yafara serving dinsu Kazan dake cikin takeout din da Kuma milk drink me kauri a cups, Na'ima na zaune a gefensa har sannan kanta a duqe, dakyar yasamu ta fara cin kazan wanda ba wani dadinsa takeji a baki ba, sai ya dauko yanka daya ya kai mata bakinta yana kallonta da murmushi a fuskansa, murmushi ta fara itama bata karban ba kunya na cikata, sai ya kwantar da murya "I want to feed you..wife" cike da kunya ta dan bude bakinta ya saka mata, yana kallonta take taunan, ji yake kamar yafi kowa sa'a a rayuwansa yanzu, Him and Her bound together in marriage, ga ta kuma a cikin gidansa under his care, mafarki ne da ya dade yana fatan faruwansa tun daga ranan da ya fara ganinta...Ahaka suka tattaba naman basu wani ci sosai ba shida itan, sai ya fara tattare gurin tana tayasa, ya miqa hannu zai dauka ya fita dashi sai ta hanasa ta dauka dakanta suka miqe tare, bai barta ba saida ya dauki daya daga ciki suka fitan, Babban falon downstairs din Ahmad yayi leading dinta suka koma, sai taga yabi wani qaramin corridor sannan suka tadda babban kitchen, so spacious and neat, nan kan kitchen island din suka ajiye kayan hannunsu sai Na'ima ta fara ware empty ones din takai sink, gurin makeken fridge Ahmad ya nufa hannunsa dauke da wani plate din ya bude tareda dauko apple da grapes, cikin sink ya wankesu sannan ya dawo gurin Na'ima dake tsaye jikin island din ya ja mata kujera daya da suke jere agurin, saida ta zauna sannan ya ajiye mata plate din agabanta yace "Here, eat this" sannan shima yaja daya ya zauna agefenta, shiru sukayi while sunacin fruit din ahankali, saida Ahmad yakai yankan Apple bakinsa sannan anutse yace "kinsan calories nawa ne acikin Apple?" sai ta juya ta kallesa, dariya ma ya bata, ina hadin mutumin da ya karanci codes da food nutrition kuma, sai tace "30??" yace "haka kika raina Apple" dariya ta danyi yana kallonta sannan tace "Yaushe ka chanja field?" yana murmushi yace "Inanan a field dina" sai ta girgiza kai, can tace "Duk snacks dinda Nafisa zataci sai ta duba calories" dan ware ido yayi yace "Itadin?" anutse ta amsa da "Barin ma lokacin da muke school" sai yadan gyara zama bai bar kallonta ba yace "Ranan dana fara zuwa sai da fridge dinku yaban tsoro, how do you eat junkies like that?" dan dariya Na'ima tayi.. she's finding the mood so relaxing kuma, sai tace "Aikin Nafisa ne, ni ban cika ci ba" Ahmad yace "me dame kikafi son ci?" nan Na'ima ta gyara zama tana bashi labari sama sama idonta na kan plate din gabanta yana kallonta, labari take bashi kan dishes din da take choosing a lokacin da suke oxford, saboda ba kowanne kalan abincin turawan takeci ba, sai Ahmad ya hade hannunwansa guri daya ya dora habarsa akai duk yana kallonta, sai da takai grape daya bakinta tana maganan anutse sannan tadan tsaya ta dago kanta ta kallesa ganin har wani murmushi yake idonsa akanta, kauda kai tayi tana murmushi ahankali tace "Ka daina kallona haka" aikuwa nan ya matso ahankali yace "Yau dai ki fadamin ya nake kallon ki ne kam" bata juyo ba tace "uhm uhm nidai ka matsa" sai yayi murmushi ya kai hannu tareda Juyo da fuskarta ta kallesa, ganin idonta cikin nasa yasa tayi saurin rufe idanun tanajin zuciyarta na bada sauti, ahankali Ahmad ya duqo ya hade bakinsu guri daya, dan stiff tayi da farko sai taji ya fara exploring bakinta ahankali, yanda yake mata yau din ya sha ban ban da wanda tasani yake mata a baya, it was more than soothing, ji take har zuciyarta na karban saqonsa wanda hakan yasa batasan lokacin da takai hannunta ta sarqo wuyansa ba, Jin haka Ahmad ya daga ta cak ya dorata kan Island din sannan ya sake hada bakinsu guri daya in a hurried manner, Na'ima batasan lokacin da ya rabata da hijab din ba because she was lost in the way yake taba jikinta yau din, har sannan kuma yana tsaye a tsakanin kafafunta while exploring her, sai da taji ya saka hannunsa under riganta sannan ta fara dawowa hayyacinta, nan kuma jikinta ya dan fara rawa jin hannunsa a qirjinta, da sauri ta raba bakinta da nasa suna maida numfashi ataren, sai ya hade goshinsa da nata yana kallonta, kamar me rada yace "Allow me please Na'eemah" har sannan jikinta na rawa sai ta sake damqe idonta, tsayawa kallonta yayi sai ya rungumeta yana shafa bayanta, saida yaji ta nutsu sannan ya sake rada mata "I can wait zuwa lokacin da kika shirya kinji" sai sannan ta bude bakinta cikin rawan murya tace "Ahmad I....I..." nan ma ta kasa cewa komai sai ya dagota yana kallonta yace "Shhhh.. it's okay Babe, i can wait" nan ya hau gyara mata gashinta da ya ware, sai da yazo gyara mata wuyan riganta yaci karo da tabon nan dake kafadarta, ahankali ya sake sauqe rigan yana kallo, sai Na'ima ta kai hannu ta rufe cike da Jin nauyinsa, tasani zai gansu asannu har na bayan nata but yanzu kuma sai takejin wani iri ganin yanda yake kallon tabon, cikin kwantar da murya yace "Muje ki kwanta" ta gyada kai yakai hannun tareda taimaka mata ta sauqo qasa sannan ya tsugunna ya dauki hijab dinta dake yashe a qasa ya saka mata, har suka qarasa upstairs din babu wanda ya sake cewa komai cikinsu, saida suka tsaya adaidai inda kofofin part dinsu ke kallon na juna Na'ima ta zare hannunta daga nasa ta juya ta shiga falonta while shima ya juya ya shiga nasa, shigan ta ta qarasa cikin dakinta da sauri tana dafe qirjinta Jin yanda yake gudu da sauri sauri, sai ta zauna nan bakin gadonta tana tuno abunda ya faru tsakaninsu, tananan zaune shiru har dare ya fara nisa sai ta miqe ahankali ta cire hijab dinta ta linqe sannan ta kwanta a gadon tareda jawo duvet, batafi 10 minutes akwancen ba taji shigowar Ahmad dakin, shima zuwa sannan yayi changing into kayan bacci na maza masu tsadan gaske, cikin nutsuwa ya hau gadon ya kwanta while Na'ima na kwance adayan bangaren tana kallon wall din dakin bata juyo ba, sai da ya daidaita kwanciyarsa shima ya jawo duvet din sannan ya ajiye wayoyinsa nan kan side drawer, shiru sukayi kowa da abunda ke yawo a ransa, can Ahmad ya juyo yana kallon bayanta cikin rada yace "Babe" sai Na'ima ta amsa da "Uhm" yace "Bakiyi bacci ba" ta sake cewa "Eh" ahankali har sannan bata juyo ba dan wani irin nauyinsa takeji, bata taba sanin farkon hada makwanci da miji na saka bugawar zuciya ba sai yau, dan wanda tayi da Bilal tsoro ne ba nauyi ba, wani irin feeling takeji ganin wai gata gashi at thesame bed, can kuma ahankali Ahmad ya mirgino gareta yakai hannunsa ya rungumeta ta baya, sai sukayi shiru ahakan tana jiyo bugun zuciyarsa shima, da sanyinta tace "Ahmad" ya amsa da "Na'am" tace "Sun kira sunanka ranan" dan stiff yayi sai ta sake cewa "Wa'inda suka kaini jejin nan naji sun kira wadzani" Jin yayi shiru sai ta gyara kwanciyan ta miqe zaune tana kallonsa tace "Ka fadamin wa suke nufi please, waye wadzanin da yake alaqa da babbansu" sai shima ya miqe zaune yace "it's me, and it's not what you think, ni banayin irin abunda sukeyi" cike da shock tace "Amma meye alaqarka dasu, who are you?" ganin ta fara birkicewa yasa ya kamo kafadunta, cikin lallami yace "Heeyyy...Babe it's still me, Billahi bana yin kidnapping, ban taba yin kisa ba, ban taba yin sata ba, ban taba shan ko taba ba, shugabansu kawai nasani shima tun a Toronto muka hadu during my Msc" tace "Amma to meyasa, why?" Yace "I'm a business man Na'eemah, a koda yaushe Ina cikin threats, many people want to see me fall, inada competitors dayawa da basa son ganin na zauna lafiya" sai ya dan dakata yana kallonta sannan ya cigaba "Da shugabansu kadai nake alaqa kuma shima ba wani mummunan abu nake sawa yayimin ba, matsar min da duk wanda ya shigo gonata yakeyi, so i can go forward" sai sannan Na'ima tace "Kai ka batar da Bilal?" sai Ahmad ya dan tsaya yana kallonta, tace "Please answer me, kasa an dauke shi ne?" ransa ne yaji ya baci sai ya sauqa daga gadon ya miqe yana kallonta yace "Do you still think about him?" tace "Dan Allah kar kayi changing topic dinnan" yace "No Na'eemah, do you still remember him this much?" Sai ta girgiza kai tanajin kuka na zuwa mata, Ahmad yakai hannunsa fuska ransa na baci yace "Billahi bana sonsa, akansa na fara Jin zan iya kashe mutum Na'eemah, and to think that har yanzu yana ranki shi yafi komai yimin zafi" muryanta na rawa tace "Dan Allah ka saurareni wallahi baka fahimceni bane, bai kamata ka batar dashi ba Ahmad, bawai yana raina bane, what you did is not right" murya a dage yace "it's not my fault that i want all of you Na'eemah, not my fault that i want to consume every thoughts of you, call it selfishness amma hatta tunaninsa banason kiyi, bana sonsa da duk abunda ya shafesa and that's final" da haka ya juya ya bar dakin sai Na'ima ta fashe da kuka har sannan tana zaune akan gadon...Har agogo yayi ticking 1 na dare Na'ima na nan zaune tana tunanin Ahmad, yanda ya fita ransa a bacen ne ma yafi tada mata hankali, sai ta sauqa daga gadon ahankali ta fita daga dakin da nufin ta je gurinsa kawai tana bude kofan falonta suka kusa cin karo da juna, ta danyi baya alamun tsorata sai ya taho gareta yace "Babe it's me" da saurinta ta rungumesa sai shima ya sa hannu ya qara matseta ajikinsa, kuka ne yazo mata sai taji yace "I'm sorry kinji" itama tace "I'm sorry too" yace "Na'eemah wallahi bana ko daya daga cikin abunda na lissafo miki dazu, ki yarda dani" dago kai tayi tace "Na yarda da kai, amma babu kyau din ka rinqa sa su suna mugun aiki" yana kallonta yace "Sai an min muguntan nake ramawa, in bansa an ramamin ba watarana kasheni za'ayi" da sauri ta girgizai kai tace "Ba zasu kashe ka ba, stop saying this please" sai yayi murmushi yace "it's a messed up world out there Na'eemah, you won't understand" tace "ni dai ka daina zancen kisan nan" sai ya dauke ta cak ajikinsa yana murmushi ya juya zai bar falon da ita yace "Naji toh, muje dakina mu kwanta yanzu" tana murmushin itama ta rufe idonta cike da kunya tace "uhm uhm nidai, mu zauna nan din" ya girgiza kai yana nufar part dinsa da ita har sannan bai bar murmushin ba, a master Bed dinsa ya direta tareda yi mata rumfa, cikin sanyinta tace "Nidai mu koma can din gaskiya" sai ya hade goshinsu guri daya ya rada mata "Sai dai in kin yarda inyi" da sauri ta turasa baya tana dan dariya tace "Ahmaaad" yana dariya qasa qasa shima yace "Kadan zanyi fa" ai da sauri ta juya zata sauqa daga gadon sai ya kamota bai bar dariyan ba yace "Naji, zo mu kwanta, bacci kawai zamuyi" nan kuma tayi luf ajikinsa, ahankali ya sake cewa "Babe banason fadanmu, kar mu rinqa yin fada kinji, I'll suffer the most" ta riqo hannunsa dake sarqe a waist dinta tace "Me too....amma kayi hakuri, zan kiyaye" sai yace "Nima zan kiyaye"......da haka kuma Ahmad ya kashe bedside lamp sannan ya sake rungumota nan suka samu baccin da ke idonsu tun farkon daren....