"Huyaam you know I love you right? "Baka Sona Yaya baka Sona da kana Sona bazaka

Book 2

by @naja76

Follow this link to join my WhatsApp group: ***


*๐ŸŒนHUYAAM๐ŸŒน*


*NA*


*__NAJA'ATU UMAR FAROOQ__*


*__(MRS SARAKIES ๐Ÿ’‹)__*



*Bismillahirrahmanirrahim*


My channel link ๐Ÿ‘‡ 
***


*Alhamdulillah! people of paid book well come to the new group,na gaisheku kyauta ๐Ÿ˜‚ . lallai kud'in mutanan arziki ne Ina yinki Irin Sosai din nan๐ŸŒน.*



*TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!*


*Ina kuke manyan mata masu capacity ๐Ÿ˜‚๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ? Nace Ina kuke hajiyoyin gidan nan, to Maza ku Bud'e kunnuwanku ku saurarareni ๐Ÿง da kyau.Dan a yau nazo muku da Wani kyakkyawan albishir๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ wanda zakuji dad'insa fiye da yadda zan fad'a muku.Nace ba, Bakuda Labarin hamshak'iya shahararriyar 'yar Kasuwar nan wacce tai K'aurin suna wajen kawo muku kayayyakinta na 'yan Gayu masu quality wato H.Empire ๐Ÿฆ Lagos Mai gidan kayan sawa na mata na k'walisa da Kuma kayan kitchen?..."*

*To idan yau kuka tab'a ji ya kamata ace kun saurareni kunji da abinda nazo muku dashi. Kayan sawa kike so Wanda zaki zama tauraruwa a cikin 'Yan uwanki mata harma da Mai gida wato oga kwata kwata Hajiya ta , ko ko so kike duk inda kika gifta kallo ya koma kanki?. Ko Kuma kayan kitchen kikeso masu kyau da aminci daki bari. To Maza ku garzayo H.Empire ๐Ÿฆ Lagos anan zaku samu duk Wani Irin Abu da kuke so, Dan mu kayan mu quaranti ne Hajiyata bakida tan tama akai, kudai ku gwada siya kawai zakusha mamaki Dan sai Kun bani labari. Muna Saida kaya kamar haka ka* ๐Ÿ‘‡

*1,Atamfofi*
*2, lesses*
*3, Abaya*
*4, kayan kwalliya ko Wani iri ne*
5,*D'an kunnaye(jiwelleries)*
*6,takalma*
*7,hand bag*
*8, mayafai*
*9, sai Kuma kayan kitchen shima Muna sai dawa, Dan duk Wani kayan kitchen d'in da kike nema harma da Wanda Baki tab'a Gani ba ko sani to idan kikazo H.Empire ๐Ÿฆ Lagos anan zaki samu duk Wani Irin kayan kitchen muna Saidawa akan farashi Mai sauk'i da rahusa siyan D'aya ko sari*.

*domun magana damu kai tsaye ko Kuma Neman K'arin bayani ku tun tub'emu ta wad'an nan numbers d'in kai tsaye kamar haka ๐Ÿ‘‰*** /****


*Siyan na gari Mai da kud'i gida Hajiya ta*

*Sai mun Jiku๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ*


      ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน


*Bismillahirrahmanirrahim*



PAGE 4๏ธโƒฃ3๏ธโƒฃ


____________โšก


Firgigit Ammie ta farka daga mummunan Mafarkin da tai yanzu cikin daren nan.mik'ewa zaune tai tana salati ta tana kalle kallen d'akin kafin ta tsaida idonuwanta akan agogon bangon Dake manne da a bangon d'akin.yanzu k'arfe uku da Rabi ne na dare dafe k'irjinta tai Ganin eh da Gaske mafarki tai bawai faruwa abun yayi a zahiri ba,tabbas mafarki tai Wata iriyar wawuyar ajiyar zuciya ta Sauke tana hamdala aranta ganin abun ba faruwa yayi a gaske ba.Bata tab'a Irin wannan mugun Mafarkin ba a duk tsawan shekarunta, Koda wasa bata tab'a yi ba.take ta fara Tariyo da mafarkin da tai daki daki .duk abinda ya faru suka shiga dawo mata a cikin kwanyar kanta bit by bit azuciyar ta ta fara tunanin "Fulani Salamatu fa? Itace tazo har b'angarenta take faffad'ar Irin Wad'an nan mugayen magan ganun marasa Dad'in Ji.sauke numfashi tai tana furta Alhamdulillah a fili ganin Mafarkine ba da Gaske bane ba.har lokacin Bata dawo daga shock d'in ta data tafi ba.hularta ta d'auka Dake nan kusa da filon data kwanta akai. ta sauko daga saman gadon tana gyara zaman doguwar rigar baccin jikinta, ta juya ta kalli muneefa Dake baccinta Saman gadon hankali kwance cikin nutsuwa.nan ta d'aga k'afarta da k'yar ta nufi hanyar toilet d'in Dake d'akin nata Dan d'auro alwala dazo tai sallah ko zataji ta dawo dai dai, Dan har lokacin jikin yayi Wani Irin mugun sanyi ga fad'uwar gaba ahaka har ta Isa toilet d'in ta Bud'e k'ofar a Hankali ta shiga ciki.bayan wasu mintuna ta fito tana goge ruwan Dake saman fuskarta nan ta K'arasa press ta d'auko gogegen hijab d'inta sannan ta k'arasa inda darduma take ta d'auko ta shimfid'a anan tsakiyar d'akin ta fara gabatar da nafil filu. Ammie ta Dad'e tana sallolin Wanda Batasan adadin nawa tai ba har Wajen k'arfe hud'u da Rabi, nan ta dakata dayi bayan takai raka'ar k'arshe ta zauna ta dinga jero addu'o'i har na tsawan lokaci tana addu'ar Allah yasa kada wannan mafarkin da tai ya zama gaskiya. Dan har ga Allah ba k'aramin tsorata tai ba saidai wannan sallar da tai taji da samu wata iriyar nutsuwa ba kad'an ba.mikewa tai Ganin ana K'iran sallahn farko na asubahi nan ta tashi ta fara yin raka'Atul fijr bayan ta idar tana zaune tana addu'o'i taji ana k'ok'arin shiga sallahn ASubahi a masallacin Dake cikin palace d'in,nan itama ta mik'e tabi jam'i.bayan tayi sallama ta Dad'e a zaune tana addu'o'i har wajen k'arfe shida na safe kafin ta mik'e ta k'arasa bakin gadon ta fara tashin muneefa akan ta tashi itama tai sallahn.muneefa ta tashi tana mutsuka ido tare da yin Mik'a ta sauko daga saman gadon ta wuce toilet. Ammie Kuma ta d'auki Al'qur'ani tana karantawa.har muneefa ta idar da sallah Ammie tana karatun Al'qur'ani.muneefa ta taso ta Zauna kusa da Ammie ta ce "Ammie Ina kwana" tsayawa Ammie tai da karatun bayan ta kai aya ta shafa kan muneefa tana ansa mata. Kafin muneefa ta koma saman gadon ta kwanta ta koma bacci Dan yau basuda school suna hutu.saida Ammie ta gama karatun Al'qur'anin ta sannan itama ta mik'e ta Maida Al'qur'ani inda yake sannan ta cire hijab d'in jikinta ta linke ta ajiye itama ta koma saman gadon ta Kwanta Kafin k'arfe 7:30am ta tashi......



A cikin masarutar zazzzu kuwa a wannan lokacin rik'o lurwanu yayiwa Shakundum bana wasa ba. tai tai ta k'wace ta k'asa Ganin asirinta na gab da tunowa Kuma tasan idan ya tonu ta shiga uku yasa tai dabarar dagewa ta jawo lurwanu da iya k'arfinta dama yafara tsufa saboda haka ba wahalar jawoshi zatai ba, nan suka fito k'ofar babban falon suna kowawa ha Sauran dogarayen kwance har lokacin bacci suke Basu San Mai yake faruwa ba.lurwanu na shakundum baya ita Kuma tana janshi gaba da haka har suka fito daga falon gabad'aya suna fitowa lurwanu zai murd'e ta kawai sai jin saukar Wani Abu yay a saman kansa Mai bala'in nauyi akansa anbuga masa,ai take Babu shiri yay saurin sakin shakundum ya fad'i a k'asa wanwar Yana dafe da kansa baya ko motsi saboda azaba.tare Wanda ya bugawa lurwanu wannan k'arfen suka gudu shida shakundum sukai bayan b'angaren gimbiya Aysha da gudu suka b'ace b'at tun kafin Wani yayi yunk'urin binsu.adai dai lokacin da Hajiya inna da Anty Amina suka k'araso wajen.Hajiya inna tana haki tana waige waige ta kasa tsayuwa waje D'aya tana Neman lurwanu da Wanda ta ce ya rik'e d'in tana Cewa "yauwa lurwanu rik'e shi da kyau karya k'wace ka rik'e shi da kyau kana ina ne? Ta fad'a tana lek'a gefe da gefen ta kamar wacce take tantamar Wani abun. Anty Amina data lura da lurwanu Dake kwance a k'asa ta ce cikin rawar murya "Hajiya ai kinganshi kwance a k'asa" ta fad'a tana K'arasawa inda lurwanu yake Dan bata kula da lurwanu ba sai Yanzu. Hajiya inna ta juya inda Anty Amina ta nufa tana nuna mata lurwanu adai dai lokacin da mutanan cikin masarautar duk suka firfito suka k'araso wajen suna tambayar lafiya? su kansu dogarayen Dake b'angaren sai alokacin suka tashi daga baccin da suke a Gigi ce Jin hayaniyar mutane ana tambayar lafiya? Hajiya inna na tsaye kan lurwanu Wanda jini ya gama wanke masa fuska saboda k'arfen da aka buga masa aka sun ma manta sun bar gimbiya Aysha a d'aki.hajiya inna tasa kuka ta ce "mun shiga uku lurwanu Ina Wanda nace ka kama d'in kardai ya gudu ko shine ya ji maka wannan raunin?"sai Kuma ta fashe da Kuka. waziri ya matso kusa inda su Hajiya inna suke tsaye kan lurwanu Yana kallanta ya ce cikin alhinin Dake saman fuskarsa "lafiya Hajiya Mai ya faru naga duk kun fito a wannan tsohon daren?a dai dai lokacin da Mai martaba ma ya K'araso wajen tun daga b'angaren sa ya jiyo hayaniya na tashi ya lek'o ta window nan yaga a b'angaren gimbiya Aysha ne hayaniyar ke tashi shinefa ya taso Babu shiri d'aukar sama Wani mummunan labari zaiji.sai dai Yana zuwa ya tadda Dan dazon mutane sun taru anyi cirko cirko ana ta hayaniya abun mamaki harda Shakundum Dake tsaye tana tambayar meke faruwa itama fuskarta duk damuwa.Hajiya inna ta juya tana kallon waziri ta ce "Amina ce tasan komai ni kawai mutum na gani" Mai martaba yay gyaran murya wajen yayi tsit kowa ya Bada attention d'insa kansa .Mai martaba Yana kallan Anty Amina ya ce cikin nutsuwa "Amina Maike faru ne? Anty Amina ta ce cikin rawar murya "Wani ne ya shigo b'angaren gimbiya Aysha har cikin d'akin zai cutar da ita". Ta fad'a tana k'ok'arin Maida hawayen Dake son zubo mata.Ai Mai martaba na Jin haka yay saurin katse ta ya ce da "mamaki har d'akin Fulani Kuma? Gyad'a masa kai Anty Amina tai tana share hawayen daya zubo mata tunowa da tai abinda taga mutumin yana k'ok'arin chusawa gimbiya Aysha Abu a Baki ko tsoron Allah baya ji. Mai martaba ya fara kalle kallen kowa Dake wajen cikin nutsuwa kamar anan ne zai ga mutumin da Anty Amina ta ambata sai kuma ya dawo da kallansa kan Anty Amina ya ce "Ina yake yanzu? Anty Amina ta ce "ya gudu tun d'azu rankai Dad'e, da har lurwanu ya kamashi to kuma muna fitowa sai muka ga Shima lurwanu a kwance cikin jini" Mai martaba ya ce "Kuma bakiga ta inda yayi ba?Hajiya inna ta ce "yanzu Mai martaba Ina zata ganshi bare ta inda yabi? bawan Allahn nan lurwanu nace ya kama mana shi to Kuma ya kamashi d'in har muna k'ok'arin zuwa kawai muka ga lurwanu a kwance a k'asa shame Shame Ina ga Wani abun ya doka masa ya samu ya gudu" Mai martaba kasa cewa komai yayi sai can ya Kalli mutanan wajen ya ce "kowa ya tafi yaje ya kwanta" tafiya suka farayi D'aya bayan D'aya har shakundum suna barin wajen harsu Kansu dogarayen Hajiya inna tana kallan dogarayen b'angaren gimbiya Aysha Dake k'ok'arin barin wajen tana nuna su da yatsa ta ce cikin fad'a "ba laifin kowa bane saina wad'an nan mutanan wallahi nidai banga amfanin kuba, wato ko kashe mu akazo Yi sai dai ayi Babu abinda zaku iya.yanzu saboda Allah Kuna Ina har ace mutum ya shigo ya wuce harabar gidan ya wuce falor harya tsallake ya shiga cikin d'aki ace Baku ganshi ba ko kuma kuji motsi ba" gabad'ayansu suka dakata da tafiyar da suke suka zube a k'asa suna sunkuyar da kansu k'asa suna sauraran Hajiya inna.mai martaba ya ce " kiyi hak'uri ki Rabu dasu Hajiya mu barwa safiya" hajiya inna ta ce a fusace "bacci muka tarar sunayi har mu da muke cikin d'aki Muka fito Amma su Ina kallan su wallahi Abdallah bacci muka Tarar dasu suke nidai banga amfanin suba acikin masarautar nan sakaran banza Dana wofi kawai "ta fad'a tana huci hak'uri kawai suke bawa Hajiya inna suna cewa wallahi ko kad'an basu san Maiya sasu bacci ba" Hajiya inna ta Daka musu tsawa ta ce su tashi su Bata wuri. Mik'ewa sukai bayan sun K'ara Bata hak'uri tai banza ta k'yalesu.shi dai Mai martaba har lokacin mamaki wannan al'amari kawai yakeyi sau biyu kenan fa? Sau biyu Irin wannan na faruwa acikin palace d'in nan, na ashiga har b'angaren gimbiya Aysha za'a cutar da ita.maike faruwane Haka? su waye suke aikata wannan abun zuwa yanzu kuma ya fara gasgata maganar Hajiya inna tabbas akwai lauje cikin Nad'i.kallan Hajiya inna yayi wacce take tai masa magana Bai jiba Yana wannan tunanin ya ce "Na'am Hajiya akwai Wani Abu ne? Hajiya inna Ta ce "haka nace akai wannan bawan Allahn asibiti ai ba'a barshi haka ba" Mai martaba ya kalli sauran dogarayen Dake gefe kansu a k'asa ya ce "ku kaishi clinic Dake cikin palace" ko rufe Baki Mai martaba baiyi ba suka kinkimi lurwanu sukai clinic d'in cikin fadar dashi.mai martaba ya Kalli Hajiya inna ya ce "Hajiya ko Koma ciki ku gano halin da Aysha ke ciki Allah ya tashe mu lafiya" zaro ido Hajiya inna tai tunowa da gimbiya Aysha da tai Dan har ga Allah ta sha'afa wannan abun duk ya Mantar ta da ita halin da gimbiya Aysha ke ciki tuni ta nufi k'ofa cikin sauri har tana had'awa da gudu,Anty Amina itama ta bita a Baya cikin Sauri.Mai martaba ya tsaya Yana tunanin ya bisu ko karya bisu? Dan har ga Allah tunda yazo wajen hankalinsa gabad'aya Yana kan matarsa kawai dai ganin Hajiya inna ne yasa baiyi Wani yunk'uri ba, amma sai jira har Hajiya inna ta koma d'akin ta in yaso sai yaje ya gano halin da gimbiya Ayshansa ke ciki.sauke numfashi yayi Bai bar wajen ba Saida ya zagaye b'angaren gimbiya Aysha ya duddu ba ko Ina duk da ba ganin mutumin zaiyi ba kafin ya koma part d'insa yana mamakin wannan al'amari..

A falo su Anty Amina suka tarar da sultan zaune Saman kujera ya k'urawa waje D'aya ido Yana ganin sun shigo ya mik'e da sauri ya nufi d'akinsa.hajiya inna ta kalli Anty Amina ta ce "shi Kuma wannan yaushe ya tashi? Anty Amina ta ce "May be Shima yaji maike faruwa ne shiyasa ya fito" Hajiya inna ta jinjina kai suna cigaba da tafiyar da suke cikin sauri ta ce "Amina ba sai muka fita gabad'aya bamu bar D'aya daga cikin mu ya tsaya yaga halin da Aysha ke ciki ba" tun kafin Hajiya inna ta rufe Baki Anty Amina ta Bud'e ido ta ce " wallahi inna shaf ban kawo wannan araina ba kawai burina na kama mutumin na sha'afa gabad'aya sai kuma tai salati ta ce "innalillahi wainna ilaihi raji'un" ta fad'a tana bin bayan inna da har ta k'arasa Bak'in k'ofar zata Shiga..da sauri inna ta k'araso har bakin gadon Anan suka tarar da gimbiya Aysha kwance a gefen gadon k'iris ya rage ta fad'o k'asa, Anam data farka tun d'azu bayan ihun da Anty Amina tai taga yadda tabi Wanda ya shigo da gudu yasa ita ta farka a figice ta sauko daga saman gadon Babu inda ta nufa sai wajen mamin ta. nan ta tazo tasami Mamin ta Wanda k'iris ya rage ta fad'o daga saman gadon ganin haka yasa tai ihu ta rik'o ta Dak'yar tana kukan Azo a tai Maka mata. da d'aga ta taso tayi saboda ba iyawa zatai ba yasa ta zauna a kusa da ita tai k'ok'arij d'ora kan gimbiya Aysha a Saman cinyar ta tana hana ta fad'owar.nan Hajiya inna ta k'araso cikin d'akin da sauri tana cewa inna Lillahi wainna ilaihi raji'un Amina Kinga Anam ce ke rik'e da ita Yi Maza ki k'araso mu kamata" da sauri Anty Amina ta K'araso wajen Itama tana salatin suka d'aga gimbiya Aysha wacce kanta ke kan cinyar Anam suka Kwantar da ita suna faman jera mata Sannu ganin Babu abinda ya Sameta yasa sukai hamdala.hajiya inna ta Kalli Anam ta ce "sannu takwara kinyi k'ok'ari Allah yay miki albarka ya bawa mamanki lafiya su Kuma duk Wanda ke da sa Hannu a ciwon Aysha Allah ya Maida musu shi Kansu" Anty Amina ta ce "Ameen" a Sanyaye.ita dai Anam tana zaune kusa da mamanta tana kallan ta hawaye na zubowa a fuskarta.Hajiya inna ta kalli Anty Amina ta ce "wai Amina Mai ya farune da har aka shigo d'akin Aysha?. Anty Amina ta sunkuyar da kanta k'asa tana share hawayenta itama nan ta Shiga bawa Hajiya inna labarin yadda akayi. Hajiya inna ta Jin jina kai Bayan ta gama sauraran Anty Amina ta ce "lallai akwai sake kenan acikin masarautar nan dole ai zama na musamman agidan nan Muji daga Ina matsalar take waye yake mana zagon k'asa sannan yake aikata mana wannan Abu Dan dole wannan D'an gidane yake shigowa b'angaren gimbiya Aysha Dan ya cutar da ita aidama na Sha fad'a miki Amina ciwon Aysha akwai sa hannun mutum Aciki" Anty Amina ta Jin jina kai ta ce "na yarda Hajiya inna tunda har cikin d'aki fa idan ba Dan gida ba waye zai aikata haka? Waye yasan har bedroom d'in Yaya gimbiya?" Hajiya inna ta ce "k'warai kuwa dole mu tsananta tsaro Amina dole mu canza lokacin bacci" Anty Amina ta ce "hakane Hajiya" Hajiya inna ta sauke numfashi ta ce "Kinga ki zauna da ita ni bari naje na gano sultan" Jin jina mata kai Anty Amina tai tana kallan Hajiya inna harta fita daga d'akin ta kullo Musu k'ofar kafin itama ta k'arasa kusa da gadon gimbiya Aysha ta zauna kusa da ita tana kallanta ganin ta rufe Idonta. Anam ma dai na zaune kusa da Mamin nata ta dayan side d'in ta zuba mata ido tana kallan ta..Hajiya inna na sauka stairs ta Had'u da Mai martaba zai hawo upstairs d'in shima Dan zuwa duba gimbiya Aysha....



____________โšก


Gabad'aya mutanan Dake cikin palace babu Wanda Babu acikin babban falon Mai martaba ciki kuwa harda bayin gidan suna zaune a b'angaren Mai martaba ta dalilin Taron gaggawar daya tara. Yana kallan kowa D'aya bayan D'aya har Hajiya inna wacce ke Zaune saman kujerar dake gafen ta Mai martaba ta had'a rai tana kallan kowa Rai b'ace.sai Shakudum da itama ke zaune a Saman kujera nesa data Mai martaba ta sunkuyar da kanta k'asa tana Wasa da zoben hannunta ta nutsu kamar wata Mutuniyar kirki.gefen hagun Mai martaba Kuma su waziri ne dasu barwa da yaran gidan irinsu sultan zaune suma a k'asan carpet sai Matan su waziri Suma Dake zaune a k'asa tareda Anty Amina da sauran Yara matan dake cikin palace d'in duk suna zaune suna Saura ran Mai martaba.wajen yayi tsit baka Jin komai sai muryar Mai martaba dake tashi harya Kai k'arshen zancensa.hajiya inna ce ta fara magana da cewa "ai Rankai Dad'e Babu Wanda zai fito yace shine ko kuma Yana zargin Wani acikisu,tun da dai kowa yaji labarin da Amina ta Bada Akaro na biyu na abinda aka je za'a yiwa gimbiya Aysha har b'angaren ta Dan Rashin tsoron Allah Irin na mutane? Mai baiwar Allah nan tai muku ne da har ake son cutar da ita a sabauta mata rayuwar ta" ta fad'a tana kallan kowa Dake falon wanda duk suka sunkuyar da kai suna sauraran Hajiya inna. ta cigaba ta ce "mudai da Allah muka dogara Kuma shi zai mana maganin komai" ai ba tun yau aka fara ba wannan shine karo na Biyu.nidai abinda na sani Shine anyi na farko anyi na k'arshe Kuma wallahi zamu sa TSARO na musamman koma waye idan muka kama mutum wallahi Allah bazai tab'a jin Dad'i ba, Kuma Allah yay gaggawar tona asirin koma waye" ta fad'a tana kallan kowa. shakundum dai tana zaune kanta a k'asa kamar wata ta kirki kowa ya ansa Ameen d'in Hajiya inna ciki kuwa harda Shakundum.Mai martaba ya Kalli Hajiya inna ganin tayi shiru ya ce "Hajiya kin gama magana ni" Hajiya inna ta ce "na gama rankai Dad'e" Mai martaba ya juya Yana kallan kowa ya ce "To Alhamdulillah Tunda kowa yaji Mai muka fadi"? suka jin jina kai ya ce" kowa zai iya tafiya" nan suka Mik'e D'aya bayan D'aya suna fita daga falon har ya rage daga iya Mai martaba sai Hajiya inna. Mai martaba Yana kallan Hajiya inna Ya ce "jirgin naku na k'arfe 1 d'ayane ko? Hajiya inna ta ce "yanzu ma zan tafi muje mu shirya gara mu isa Abujan da wuri" Mai martaba ya Jin Jina kai ya ce "Babu damuwa bari yanzu za'a Kaiku air port na Kaduna bari na kimtsa na fito" Hajiya inna ta ce "Babu komai saika fito" daga haka ta Mai sallama ta fito Dan zuwa suma su shirya.


K'arfe 11 da mintuna suna Airport d'in Kaduna sultan ya tura gimbiya Aysha Dake zaune kan wheel chair bayan sunyi sallama da Mai martaba Anty Amina Kuma tana rik'e da Hannun Anam sai Hajiya inna Dake rik'e da Jakar ta ahaka suka nufi cikin air port d'in...


A kano Kuwa Suma dai su Ammie sun gama shirin su tsaf yanzu haka k'arfe biyu Saura suna cikin airport na kano.su su ukune kawai zasuyi tafiyar daga Ammie sai HUYAAM d'in sai Kuma Afeef suna nan tsaye aka fara boarding classes suka nufi cikin air port har suka Haura stairs d'in jirgin.suna shiga ciki Daman VIP session suke tunda nan suka biya,nan suka shiga Huyaam ta zauna kusa da Ammie sai Afeef da yake opposite d'insu Yana latsa wayarsa ahaka har matafiya suka gama shiga cikin jirgin ya tashi zuwa sararin samaniya......



#๐ŸŒนHUYAAM 
#๐ŸŒนLAMID'O 
#๐ŸŒนAZIZ CHIROMA 
#๐ŸŒนAFEEF 
#๐ŸŒนABDALLAH SHATTIMA 



Littafin HUYAAM na kud'i ne regular group akan naira 700 for VIP group Kuma 1k (1000) ku hanzarta ku biya ta wannan account d'in ๐Ÿ‘‡ 

2270127432 Naja'atu umar zenith bank 

Evidence of payment ๐Ÿ‘‡ 
***



*Yan Niger ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช_zaku iya biyan(500 CFR) a Yanzu before mu gama free page. idan muka gama Kuma zai koma(700 CFR) . for VIP Kuma (1000 CFR)MY NITA ๐Ÿ‘‡* 


***




***________โœ๏ธ