“SANADIN ƘADDARATA”

Page-56

by @zahratulqalam51

*FASAHA WRITER'S ASSOCIATION*
     (*F.W.A)*©✍️
     ⭐⭐⭐

Ƙungiya masu aiki cikin salon hikima da fasaha gurin juya tunanin al-umma, kaifin alƙalumansu ya zarta takobi ©✍
___________________________________________________



بسم الله الرحمن الرحيم.
اللهم صلي وسلم على نبينا محمد. 




❁ 𝐒𝐀𝐍𝐀𝐃𝐈𝐍 Ƙ𝐀𝐃𝐃𝐀𝐑𝐀𝐓𝐀 ❁ 



Free book📓



By: _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_




Page5️⃣6️⃣





Mamaki ya gama bayyana akan fiskarta, me wannan numbern ya ke yi a cikin wayar Ayusha? Ta tambayi kanta. Zuciyarta ce ta ce da ita ta ɗauka kawai ta ji me yasa ya kira wannan layin? Amma kuma ai numbern da saving, ko kuma ƙila ma kawai suna gaisawa ne. Ba ta ƙi ɗaukar shawar Zuciyarta ba, ta ɗaga wayar ta kara a kunnenta.

SUNUSI.

Tun da abubuwa su ka kan-kama musu shi da Ayusha, ya yi ta sa'idon ganin alert ɗin kuɗin da ta yi masa alƙawari, amma shiru ka ke ji wai shirwa ya yi ƙwai, ko ya kirata ba ta ɗagawa. Ƙarshe ma gaggaya masa magan-ganu ta yi cewa, ba za ta ba shi ko sisi ba, idan ya isa ya ƙwata, kuma kada ya sake ya takurawa rayuwarta, idan ba haka ba to ta san hanyar da za ta bi don tona masa asiri a wurin Asma'u da dangi ma, sannan a fasa aurensa da ya shirya, ita kuma ta ɓoye na ta asirin ba tare da kowa ya sani ba, kuma bai da hujjar da zai ce har da ita a ciki.

Wannan maganar ta rura wuta a zuciyar Sunusi sosai, don haka yau ya sa a ransa idan har Ayusha ba ta ɗaga wayarsa ba, to zai aiwatar mata shirin da ya ke da shi akanta, ba ta san waye shi ba ne shiyasa.

Wayar tana ringing amma ba'a ɗaga ba, hakan yasa ya ja wata ƙwafa yana giɗa kai idonsa kan wayar, kawai kuma sai ya ga alamar an ɗaga. Da saura yasa a kunne cikin ɓacin rai ya fara magana da cewa.

"Sai yau ki ka ga damar ɗaga min waya? Ke Ayusha You should listen to me carefully! Kar ki ga don ina binki ki maidani kamar bawanki fa, to wallahi ki gane ni ba wanda za ki yiwa hakan ba ne, wato ke kin samu na magance miki matsalarki shine za ki nuna min halin 'yan iska? Wato baki ɗaya zuciya biyu ko?" Ya saki ƙwafa ya ɗaura da cewa.

"Wawuyar nan Asma'u za ta aureni, kuma har yanzu ba ta san gaskiya ba, sannan ita wancan shashashar Nuriyyah mun gama da babinta, kuma kin san da ba da ni ki ka shirya komai ba da baza ki yi nasara ba! Nine silar da yau aka amince miki za ki auri Abban, don da ban sauya kalamai ranar ba cikin hikima, da duk wannan nasarorin ba za su samu ba, saboda haka! Idan ki ka ce za ki tona min asiri kamar yadda ki ka faɗa a baya, to ki sani har da kanki za ki yiwa! Kin san me? Ban ga laifinki ba, don baki san waye Sunusi ba, to ki bi a hankali!".

Budurwarsa Billy da ke gefensa ne ta amshe wayar tana faɗin, "Billy budurwa kuma matar da Sunusi zai aura ta ke magana, na san ba ki san ni ba, to ki ji ni da kunnenki na basira, ki gaggauta tura mana kuɗaɗen da ki ka yi mana alƙawari, idan ba haka ba, za mu yi maganinki cikin sauƙi, kada ki ga don ke 'yar masu kuɗi ce ki ce kin fi ƙarfinmu, to wallahi ba abun da ya damem..." ba ta kai ga ƙare zancen ba wayar ya katse.

Ta juya ta kalli Sunusi da ya miƙe daga zaunen da ya ke a ƙufule ya ce, "shigeyar kashe wayar ta yi? Lallai ta ɗebo ruwan dafa kanta, wallahi sai na bambance mata aya da tsakuwa, sai na sa ta ta ijje ƙwarya a gurbinsa tabbas!" Ya faɗi fiskarsa ya cika da alwashi mugunta, "zuwa yaushe?" Cewar Billy, ya amsa mata da, "tomorrow!" Murmushin mugunta itama ta yi suna kallon juna.....

Nusaiba

Ita da Iya Mairo, yau ma sake dirzar hanya su ka yi har su ka iso gidan boka, kamar yadda su ka sha yi a baya, sai dai suna tsoron jin furucin da su ka ji a duk lokacin da su ka zo, "muma ba mu san abu. Da ya hanashi dawowa ba, amma dama cewa ya yi zai daɗe" wannan shine kalaman da mutane ke sanar da su a wurin idan sun je.

Kallon wani mutum da su ka yi a wurin, yasa su ka gaishesa sannan su ka tambayesa bokan nan, buɗan bakin mutumin sai cewa ya yi, "bayin Allah daga ina ku ke haka? Ba ku ji labarin abun da ya faru da bokan ba ne?" Sai da Nusaiba ta juya ta kalli mahaifiyarta cikin tsoro sannan su ka juyo suna ƙara kallon mutumin don ya yi musu ƙarin bayani.

"Bawon Allah me ka ke nufi?" Cewar Mairo, mutumin ya ce, "hmm, mun samu labarin ya samu hatsari a hanyarsa ta dawowa, kuma ana raɗe-raɗin haƙƙin mutane ne ya bi sa, domin ba ƙaramin cutar da al'ummar Annabi ya ke ba a silar bokancin nan na sa, ance ma ko gawarsa ba a iya ganewa ba, saboda yadda namansa ya ragargaje kamar markaɗaɗɗen tumatiri, sannan...".

"Haba bawan Allah! Irin wannan jawabi haka ya isa mana, kwatancen gawan mutum ka ke ƙoƙarin haɗawa da tumatir? Haba da me za mu ji?" Cewar Nusaiba kamar ta fasa ihu, "bayin Allah à dai ji tsoron Allah wallahi, idan ba haka ba kuma za ku bi sawun bokan na ku, don ba hanyar arziƙi ku ke bi ba, ai na sha ganin wannan tana zuwa wurinsa" mutumin ya faɗi yana nuna Mairo, da idanuwa su ka raina fata, zuciyarta sai bugu ya ke yi da jin wannan lukutar masifar.

"Kuma ku sani Allah yana ganinku, shi dai boka ya yi mummunan ƙarshe, ku kuma ya rage na ku" ya kuma cewa ya juya ya aza icchensa aka yana wucewa. Haushin da ya mamayeta ta kwasa ta juya ta fara tafiya ko kallon inda Nusaiba ta ke ba ta yi ba. Ita ko Nusaiba da ta saki baki bisa kalaman mutumin, ta bi bayan mahaifiyarta cike da fargaba.

Tafiya su ka yi mai nisa har su ka hayo kan titi ba tare da sun yi magana a tsakaninsu ba. Sai yanzu Nusaiba ta buɗi baki tana cewa, "Iya na shiga uku! Yanzu shikenan na rasa Faruq kenan, boka ya mutu burina ma ya mutu Iya? Wayyo ni ina zan sa kaina? Sai da na ce miki mu canza wani boka tun kafin lokaci ya yi mana ƙwalele, amma ki ka ce mu cigaba da jiransa zai dawo, har da cewa na kwantar da hankalina, yanzu ga shi ashe ya ma mutu ya barmu da tashin hankali, tsawon wannan lokacin zuwan da mu ke yi ya tafi a banza".

Mairo da ta gaji da jin kalaman 'yarta dama ita ta riga da ta shiga tashin hankalisosai u, cikin ɓacin rai ta juyo ta kalleta haɗi da sa hannu ta janyota baya tana cewa, "ki min shiru ni kin isheni da sababi! Ke kanki kawai ki ka sani kina magana akan Faruq Faruq, bayan tun da na turaki gidansa ki farauto mana dukiya ya gagareki, gashi shikenan yanzu ba mu ga tsuntsu kuma ba mu ga tarko, mun yi biyu babu. To ki sani ke abunki ma da sauƙi ne, ni nawa ne kacokan matsalata, ke ba ki ga mahaifinki ya daɗe da sauya min ba? Bare yanzu da na samu labarin mutuwar boka shikenan nima shirina na shekaru aru-aru ya tafi a banza, yanzu da na koma ubanki rabuwa zai yi da ni Nusaiba!".

Da tsananin mamaki Nusaiba ta ke kallon Mairo da ke fitar da hawaye ta ce, "Iya wai kema da magani ki ka riƙe Babanmu?", "to dama idan ba da magani ba zai rinƙa yi min biyayya haka ne? Ko kuma zai rinƙa yarda da amincewa da ni aduk maganar da na zartar?" Faɗin Mairo.

Nusaiba cikin tashin hankali ta ce, "Na shiga Uku!" "Ba ke ki ka shiga uku ba Nusaiba ni ce na shiga uku, dama boka ya faɗa, duk ranar da na riski labarin mutuwarsa to ɗaya ya ke da nawa mutuwar auren, da kuma shiga mummunar wahalar rayuwa" cewar Mairo tana fashewa da kuka, itama Nusaiba kukan ta fara yi.

"Da à ce tun da ki ka auri Faruq kina yin duk abun da na ce miki, da yanzu muna da dukiyar da ko da ankoreni zan samu masauki a ciki, amma ke ki ka rinƙa baza pakasitinki yadda ki ke so kawai don kin samu guri" Mairo ta kuma yin maganar ba ta daina kukan ta ƙare min ba.

Ƙarar mota da su ka ji ne yasa su saurin ɗaga kai haɗi da zare ido suna kallon ya durfanosu, gashi su ba ma su san yaushe su ka hayo tsakiyar titi ba, ihu su ka fara yi haɗi da ɗaɗɗage hannaye sunawa motar alama da ya dakata, shi ko mai tuƙin motar kamar baya gani sai zuba gudu ya ke abunsa. Ƙara rafka ihu su ka yi sosai suna niyyar kaucewa, amma sai dai kash haƙansu ba ta cimma ruwa ba!......

ASMA'U.

Tun bayan da ta amsa wayar, kafin ta kaiga yin magana ta fara jin zafafan kalaman da Sunusi ke furzowa daga cikin bakinsa, ƙamewa ta yi ko motsi ƙwaƙƙara ta kasa yi, sai kyarma da hannunta ya fara yi tana ƙoƙarin sakin wayar ƙasa.

Ayusha kuwa sai da driver ya fice da ita waje, ta sa hannu a jakar za ta ɗauki wayarta ta gane ashe ta manta shi a cikin falon Hajiya Kaka, don haka ta cewa driver ya tsaya sannan ta fita ta nufi zuwa ɗaukar wayarta.

Asma'u, a yanzu gaba ɗaya jikinta ya ɗau wannan karkarwan, numfashinta ya fara yin sama da ƙasa cikin tashin hankali, ta ciki kuwa zuciyarta na bugawa musamman bayan ta ji muryar wata budurwa da ta kira kanta da Billy, wanda ta ji sunan a bakin Nuriyyah ranar da ta sanar da ita cewa Sunusi ba mutumin kirki ba ne.

Kasa ƙarashe sauraron kalaman ta yi ta katse kiran da hanzari haɗi da jefar da wayar akan kujera, ta rasa ma me za ta yi yanzu, har ta nufi ƙofar fita, sai kuma ta dakata, sannan ta nufi ɗakin Hajiya Kaka.

Bayan Ayusha ta shigo falon inda ta ijje wayarta ta nufa, amma da mamakinta baya kan kujerar da ta zauna akai, ɗage kafaɗa ta yi alamar ba wani abu ba ne sannan ta ɗaga wayar haɗi da shan ruwan da ta gani wanda ta san wanda Asma'u ta kawo ne, tana sha ta fice daga falon.

Ko da Asma'u ta shiga ɗakin Hajiya Kaka ba ta taddata ba da alamu tana toilet, kwatsam ta tuna Abba ya dawo, don haka ta nufi ɗakinsa à ruɗe, da zafi-zafi ta ke bubbuga ƙofar ɗakin tana kiran sunansa, "yaya Abba, yaya Abba!!" Da sauri ya miƙe daga kwancen da ya yi yana sauke numfashi, don ko kayan jikinsa bai iya canzawa ba, saboda yau yanayinsa ya fi na kullum.

_ni kuwa na ce da saura dai bari Asma'u ta shigo ta zuba zance tukunna_

Zuwa ya yi ya buɗe ƙofar yana kallonta cikin tsananin mamaki ya ke bin ƙanwar ta sa da kallo. Ita dai tana shigowa ta fashe da kuka sosai har da durƙusawa, gaba ɗaya ta ta da masa hankali, ya yi saurin yin ƙasa yana dafa ta a hankali ya furta, "my Si, what's happened?" Ta Ɗaga idanuwanta da su ke shaɓe-shaɓe da hawaye ta dire su akan fiskar Abba, baki na rawa ta ce.

"Ya...yaya, mun aikata kuskure, mun... mun aikata babban kuskure!" Tana faɗi ta kuma sa kuka, gaban Abba ya faɗi da jin wannan furucin, sai dai har yanzu bai fahimci komai ba. Ganin ta kasa ba sa amsa yasa shi sa hannu ya ɗagata ya zaunar da ita kan kujera, sannan ya ɗauki ruwa ya zuba a kofi ya miƙa mata cikin kulawa, a hankali ta sa hannu ta amsa tana sheshsheƙa, ta sha kaɗan sannan ya mayar kan table.

Ya zauna a gefenta cikin kulawa ya ce, "ki natsu me kyau my Si, ki sanar da ni me ya faru? Me yasa ki ke kuka? Sannan wani kuskure ki ke magana akai?" "Kuskure akan koran Nuriyyah da mu ka yi, ashe... ashe duk abun da ta faɗa gas... gaskiya ne yaya Abba" ta faɗi tana fitar da wasu hawaye. Abba da zuciyarsa ta fara bugawa tun da Asma'u ta kawo maganar Nuriyyah ya ce. "Me ki ke cewa? Abun da ta faɗa gaskiya ne? Wani gaskiya? Ban... Ban fahimta ba".

Asma'u cikin rarraunar murya ta ce, "ashe gaskiya ta faɗi akan halin Sunusi, 'yar uwata ba ta aikata laifi ba!". Shi kuwa Abba cikin wani irin sauri ya miƙe sama, ya zare ido cikin ransa na yin wasu irin luguden buguwa da ƙarfi, cikin sassarfa ya iya fitar da cewa, "wa...who told you?! Sann... sannan waye ya aikata?" "Sunusi ne ya kira wayar Ayusha, ko da na ɗaga kunnuwana su ka jiye min komai" nan ta sanar da shi abun da ta ji ta kai ƙarshe tana fashewa da matsanancin kuka.

Ƙamewa Abba ya yi yana jin wani irin yanayi na tashin hankali ƙarara yana sake ziyartar zuciyarsa, bai san lokacin da ya yi baya haɗi da sakin jiki ya zauna akan gadonsa ba, Asma'u ta matso kusa da shi tana cewa, "duk kalaman da ta faɗa min akan Sunusi gaskiya ne, maganar binsa don su aikata alfasha sharri ne, kuma Ayusha da shi ne su ka aikata hakan".

Abba ya Miƙe idanuwansa sun gama rikiɗewa sun yi jazir da su, "kenan... maganar poison ma ƙar... ƙarya ce, duk haɗawa aka yi?" Asma'u ta yi shiru tana jin maganar Abba da ya yi sa cike da nazari, sannan ta ce, "yaya Abba, idan kuwa haka ne, kenan Ayu...Ayusha da Sunusi ne su ka aikatawa Momy?!".

Numfashi mai ƙara Abba ya sauke, Asma'u ta dafa shi da sauri tana faɗin, "mu sanar da su Momy gaskiyar komai, yanzu zan je insanar da su!" ta yi maganar tana share hawayenta bakinta na rawa ta nufi hanyar fita, "dakata!" Furucin Abba ya tsayar da ita, ta juyo tana kallonsa. A hankali cikin dauriya ya ƙaraso gabanta ya ce, "My Si, kar ki sanar da su Momy yanzu!". 

"Sai zuwa yaushe kenan? Yakamata kowa ya san asalin abun da ya faru, 'yar-uwata ba ita ke da laifi ba, sannan wanda na ke so, na ke nunawa ƙauna ta haƙiƙa, shi... shine wanda ya ke son cutar da ni" ta faɗi wani kuka na zuwar mata sabo, tana jin ciwo ya ranta, rungumarta Abba ya yi yana rintse idanuwansa, don shima ƙwallar ta fara taruwa a ciki.

"Ki daina kuka ƙanwata, ni zan san abun da zan yi!!" Ya faɗi zuciyarsa na wani irin tafarfasa mai zafi da ƙuna, haɗi da ɓacin rai sosai.


Last page
___________________________________________________

Hmmm, akwai me magana ne🥺😁?

To su kuma su Nusaiba da Iya, ƙaƙa ya faru da su?.

Mu kasance a next don jin me zai faru?




 _*🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️*_