Love that binds us

EPILOGUE

by @theroughpages

Shekaru sun ja.


Ba tare da hayaniya ba. Ba tare da gaggawa ba. Kamar yadda soyayyarsu ta fara—a hankali.


Gidan ya cika da hasken yamma, rana tana shirin faɗuwa, tana zuba launin zinariya a ko'ina. Salma ta tsaya a gaban tagar falo, tana kallon yadda iska ke motsa labule. A hannunta akwai kofin shayi, amma ba ta sha ba. Tana jin nauyin lokaci, irin wanda ke zo da tunani mai zurfi.


"Mommy," ƙaramin murya ta kira daga bayan ta.


Ta juya da murmushi. "Yes, habibti?"


Yarinya mai idanu kamar na Ahmad, gashi kamar na Salma, ta zo da gudu ta rungume ƙafarta. "Daddy said you're daydreaming again."


Salma ta yi dariya. "Daddy ɗinki yana yawan faɗin gaskiya."


Ta ɗauki yarinyar ta rungume ta, ta sumbaci goshinta. A cikin gidan, akwai sautin dariya—na yaro, na natsuwa, na rayuwa da aka gina da haƙuri.


Ahmad ya shigo daga waje, yana cire agogon hannunsa. Ya tsaya na ɗan lokaci yana kallon su biyu, idanuwansa cike da nutsuwa. Wannan hoton—matarsa da 'yarsu—ya zama abin da zuciyarsa ta daɗe tana nema.


"You're home early," Salma ta faɗa.


"I wanted to beat the sunset," ya ce, yana murmushi.


Sun zauna tare daga baya, yaran suna wasa kusa da su. Ba su magana da yawa. Ba su buƙatar hakan. Kowane shiru yana ɗauke da fahimta.


Salma ta jingina kanta a kafadarsa. "Do you remember," ta fara, "how scared I was in the beginning?"


Ya yi murmushi kaɗan. "I remember."


"I didn't think I could ever feel this safe," ta ce. "I thought love was loud. Painful. Demanding."


"And now?" ya tambaya.


"Now I know it's quiet. Steady. Kind."


Ya riƙe hannunta. "That's the love I wanted to give you."


Dare ya sauka. Bayan sun kwantar da yaran, sun fita baranda. Sama cike da taurari, iska mai sanyi tana zagayawa. Ahmad ya kawo mata tsohuwar blanket ya lullube ta.


"You still get cold easily," ya ce.


"And you still remember," ta amsa.


Ya zauna kusa da ita, yana kallon sama. "Sometimes I think about how close we were to missing this."


Salma ta kalle shi. "But we didn't."


"No," ya ce. "We chose to stay."


Ta ɗora kanta a kafadarsa. A zuciyarta, ta sake jin kalmar nan—stay—amma yanzu tana nufin har abada.


Wani lokaci daga baya, sun tsaya a gaban madubi a ɗakin su. Salma tana shirin fita, Ahmad yana gyara rigarsa.


"You look beautiful," ya ce, kamar yadda ya saba.


Ta kalle shi ta murmusa. "You still say that like it's the first time."


"It still feels like the first time."


Sun fita tare. A mota, shiru mai daɗi ya cika sararin. Hannayensu suna haɗe.


Lokacin da suka isa wurin taro—wurin da suka fara haduwa a matsayin ma'aurata bayan aure—Salma ta tsaya na ɗan lokaci.


"This place," ta faɗa, "used to scare me."


"Does it still?" ya tambaya.


Ta girgiza kai. "No. It reminds me of how far we've come."


Ahmad ya riƙe hannunta da ƙarfi. "Every version of you was worth waiting for."


Ta ɗaga kai ta kalle shi, idanuwanta suna ɗauke da hawaye masu daɗi. "And every act of patience you gave me... I carry it with me."


A ƙarshen daren, sun dawo gida. Gidan ya yi shiru, amma zuciyarsu cike take. Sun kwanta tare, kamar yadda suka saba, jikinsu yana kusa, zuciyarsu a buɗe.


Salma ta ɗan matsa kusa. "If I had to do it all again," ta faɗa a hankali, "the fear, the doubt, the waiting... I'd still choose you."


Ahmad ya matse ta a jikinsa. "In every lifetime."


Fitilar ɗakin ta kashe. Amma soyayyarsu ba ta buƙatar haske don ta gani.


Domin a ƙarshe, wannan ba labarin aure ba ne kawai.

Labari ne na zaɓi.

Na haƙuri.

Na soyayya da ta girma cikin shiru har ta zama gida.


Kuma a wannan gidan—

zuciyarsu ta huta.


"Love didn't rush them — it waited, healed, and stayed."