Kuncin zuci
by @bintuuu
Da asuba Ahmad ya riga Na'ima tashi dalilin jiyo kiran sallah da yayi, a sannu ya bude idanunsa da suke cike da bacci ya juya gefen Na'ima dake baccinta hankali kwance, dan tsayawa kallonta yayi sai ya kai hannu yana gyara mata gashinta da ya rufe mata fuska dan tuni hulan tayi nata guri, dan motsa fuskanta tayi sai ta juya masa baya tana qara shigewa cikin duvet duk acikin baccin, murmushi yayi yana kallonta sai ya yaye duvet din jikinsa ya miqe ahankali zuwa bayi, bayan yayi alwala ya fito sai ya ganta zaune bakin gadon tana daure gashinta, qarasowa yayi gareta yace "zanje masjid" ta gyada kai bata kallesa ba, da haka ya nufi closet dinsa sannan ya fito sanye da jallabiya ya fita, Bayan sunyi sallah a masallacin dake cikin Estate din wanda ya kasance babu nisa da gidan Ahmad din sai ya tsaya suka gaisa da wani maqocinsa wanda ya kasance matashi shima amma zai iya fin Ahmad din a shekaru, tare suka fito kowannensu ya dauki hanyan gidansa, da ya shiga sai ya nufi part din Na'ima tuna wayoyinsa suna dakinta jiya ya bari, anan dakinta ya sameta zaune kan sallaya alamun tayi nata sallahn itama, hannunta da tasbaha tana azkhar, zama yayi a kusa da ita har ta gama sannan ta juyo ahankali tace "Ina kwana" ya amsa da "Lafiya Baby Na'eemah, kin tashi lafiya" sai tayi murmushi tace "Alhamdulillah" sai ya miqe ya kamo hannunta yace "Zo muyi bacci" bata daina murmushin ba ta gyada masa kai, sai ya jata zuwa gadon ta hau shima yabi bayanta sannan ya gyara musu duvet din, rungumota yayi a qirjinsa amma bai kai ga rufe idonsa ba yaji dayar wayarsa da bakowa ke da line ba tayi qara, miqa hannu yayi sai yaga message din Adam kamar haka "We're in windscare Hospital, you need to come right now" sai Ahmad ya dan hade gira in confusion bayan ya gama karanta message din, 'windscare'? asibitin Anty Amnah kenan?, fita yayi daga kan saqon nan yaga wasu saqon da wata baquwar number wanda tun daren jiya aka turo masa saqon ma bai lura ba, shiga yayi ya karanta sai ya dan miqe zaune bayan ya gama karanta content na text din, Na'ima dake gefensa sai kallonsa take, qura ido yayi kan screen din wayan yanajin ransa na baci, saqo ne da openly ya gane who sends it, be kai ga kiran Adam ba sai ga kiran Baba ya shigo, yana dauka ya gaishesa, bayan Baban ya amsa sai yace "Adam ya kira ka?" anutse ya amsa da "Naga saqonsa" sai Baba ya kuma cewa "toh ka samomu a Windscare yanzun nan" da hanzari Ahmad ya amsa da "Toh" sannan Baba ya kashe wayan, juyawa gurin Na'ima yayi yace "Babe zan dan fita kinji" ahankali tace "Lafiya?" sai ya duqo yayi kissing goshinta yace "Babu komai zanje dubiya ne tareda Baba" gyada kai tayi kawai sai ya miqe tareda gyara mata duvet din yace "Kiyi bacci sosai kinji" ta sake gyada kai tana kallonsa da haka ya juya ya fita daga dakin nata, asannu ta sake gyara kwanciyanta tana kallon kofan dakin duk da ya fitan...
Sai da Ahmad ya yayi changing into qananun kaya sannan ya fita compound da saurinsa ya nufi parking space ya shiga motarsa, Jin tashin motansa yasa security daya yabude masa gates da hanzari, sai da yazo daidai fita yayi rolling glass dinsa ya sake ce musu "ku kula sosai fa" da sauri suka amsa da "toh yallabai" "Adawo lafiya" da haka Ahmad ya gyada kai sannan ya ja motarsa ya dauki hanyar Asibitin da ya kasance distance din 20 minutes ne tsakaninsu, in ma mota tayi gudu zai kasance 16-17 minutes ne saboda unguwar da gidansa yake tafi kusa da Asibitin, tafiya yake yana tunanin text din da ta tura masa, yana fatan Allah yasa ba wani shit din tayi ba dan jikinsa yayi sanyi da kalaman da suke rubuce cikin content din, yana wannan tunanin ya isa, direct ya kira Adam yana dagawa ya fada masa suna emergency ya karaso, jin haka yasa zuciyarsa tadan buga kadan, cike da sanyin jiki ya shiga Hospital din yana tafiya da dan saurinsa, yana shiga corridorn da zai kai mutum direct emergency din ya hango duk manyan familyn nasa a tsattsaye wasu kuma suna zaune, Ahmad ji yayi jikinsa ya mutu amma yayi qarfin halin qarasawa sai duk suka dago kai suna kallonsa, da sauri Mummy ta qaraso gurinsa tana kuka ta fara dukansa a qirjins tana fadin "Wallahi in 'yata ta mutu kaine, wallahi inta mutu bazan yafe maka ba" sai Abba yace "Stop this please, ba abunda yakamata muyi yanzu ba kenan" Daddy dake tsaye rai abace yace "It's his fault" sai ya juya yana kallon Ahmad dake tsaye a gurin, rai abace ya gyara glass din fuskarsa yace "Ahmad me kayiwa 'yata? wallahi in wani abu ya sameta sai ka gamu da fushi na" sai lokacin Baba ya sauqe numfashi zeyi magana sai ga Anty Amnah ta bude glass door din gurin tareda wasu doctors abayanta, jikinta sanye cikin doctor's coat da face mask ta qaraso gurin 'yan'uwan nata sai duk hankali ya koma kansu, mummy tace "Amnah kicemin ta farka Dan Allah" sai ta amsa da "She's fine, in Sha Allah muna sa ran zata farka nan bada jimawa ba, zanyi referring nata dakin hutu yanzu ma zuwa anjima zaku iya ganinta" da sauri Mummy ta sauqe numfashi tana hawaye sai murja suka fashe da kuka itada su Ummi, Mamma da Mami daman guri suka samu suka zaune tun shigowarsu gurin sai sannan suka miqe, ba'afi second 20 ba wasu nurses suka fito da Laila kwance akan qaramin gado suna turata tana bacci hancinta maqale da breather, duk sai da kowa yayi stiff agurin kallon yanda take kwance kamar matacciya, Ahmad ya qura mata ido ganin yanda ta zama so pale, su Mummy ne suka bi bayanta da sauri zuwa dakin da za'a kaita, Anan cikin asibiti kowa yakai har qarfe 10 na safen suna jiran tashinta but sai 10:30 ta farka, sai nurses suka kira Anty Amnah da wani likitan shima sukaje dubota, suna shiga Anty Amnah ta qarasa gadon tace "Sannu daughter, it's going to be Okay kinji" ta qarasa magana tana examining ventilator din gefen gadon, rufe Ido Laila tayi batace komai ba saida Anty Amnah sukaga komai nata ya daidaita harda numfashin sannan suka zare mata ventilatorn suka bar 'yan'uwan suka shigo dakin, duk sannu suka rinqa mata Daddy ya riqo hannunta sai ta fara kuka, dasauri yace "kiyi shiru kinji princess, it's going to be Alright" sai Laila ta gyada kai amma tana hango Ahmad dake tsaye can bakin kofa nan kuma ta fara wani kukan tana kallonsa, duk sai aka juya ana kallon inda take gani, gani sukayi Ahmad ya juya zai fita sai Mummy tace "baka da imani Ahmad, kai ko nauyin 'yan'uwatakan dake tsakaninku bakaji" confusedly Baba yace "Menene ke faruwa?" Mummy tace "Jiya agabana ta kirasa, wallahi ko ni aka fadawa wannan kalaman da ya fada mata sai naji ciwo" Laila na kuka tace "Baba shi ya min alqawari tun ba yau ba zai aureni tun ba yau ba, da ya fadamin zeyi aure inyi hakuri inyarda ya aureni a ta biyu..." Kawai ta fashe da kuka duk ana kallonta, kasa fita Ahmad yayi daga dakin sai ya juyo gaba daya yana kallonta, tana kukan sai Baba yace "Muna jinki daughter, karki ji komai kinji, fada mana meya faru" sai ta share idonta tace "Jiya dana kirasa sai yace min shi ya fasa, kar in sake kiransa kuma wai......" nan ma ta fara wani kukan, sai Abba yace "Shine kikasha pills Laila?" Mummy zatayi magana Baba ya dakatar da ita yace da Laila "Yi hakuri daughter, zan yi magana dashi, be kyauta ba tunda ya miki alqawarin aure kuma ya saba, yanzu ki daina kukan nan kinji" sai ta fara share hawayenta duk ana kallonta a dakin, more especially su Mami da Mamma da abun ya dakesu sosai, Daddy ne ya gyara mata blanket yace "Yi bacci princess, it's going to be alright" Laila ta gyada kai tana hango yanda Ahmad ya daskare yana kallonta shi dasu Adam da Faruk, Baba ne yace abata guri tayi bacci sai duk mutan dakin suka nufi kofa suka fice, Ahmad was lost of word har lokacin haka ya fita corridor din sai kuma akayi sa'a babu wanda ya tada maganan da suka fito din, asannu ya nemi guri kan daya daga cikin waiting chairs na hospital din yanajin ransa na baci kuma, He thought she attempt the suicide out of her love for him wanda har hakan yasa jikinsa ya fara sanyi, but to think that she did it to frame him into marrying her shine babban abun takaicin, to think that zai auri irin wannan macen ma is disgusting..
Na'ima bata tashi ba sai around 8:30 na safen, ahankali ta miqe zaune akan gadon tayi miqa sannan ta sauqa tana gyara zaman hulanta, idonta ne yakai gurin balcony sai ta nufi wajen tareda jan makeken glass din wajen ta bude, wani irin iska me dadine taji yana buganta a gurin,tarinqa kallon gine ginen cokin Estate din and beyond, sai da ta sha tsayuwanta a gurin sannan ta koma daki ta shiga wanka, zuwa 9:30 tagama shirinta cikin wata atamfa maroon color mai masifar kyau data haska ta sosai, sai da ta gama shiryawa ta kawo simple jelwery ta saka sannan ta fita daga dakin, as tana sauqe a stairs tana bin farin babban falon da kallo, everywhere neat and quite, ji tayi zuciyarta na melting ganin dagasken irin interior din office din Ahmad dinne, ita mamakinta ma shine ta yanda bai manta ba har zuwa wannan lokacin, da wannan tunanin ta qarasa kitchen ta fara preparing breakfast mai rai da lafiya, saida ta kusan qarasawa taji bugun kofa da hanzarinta ta nufin falon ta bude sai tayi Ido biyu da Nafisa, dan ihu suka fara tareda rungume juna suna murna, sai Nafisa tace "Securities dinkun nan babu mutunci a lamarinsu, kinsan sai da na kira Yaya sannan ya musu magana suka barni na shigo" Na'ima tace "Sorry" tace "A'a ai aikinsu ne, inata kiran wayan ki ma no answer" sai Na'ima tace "Tana upstairs, sorry sis" da haka ta ja hannunta suka shiga falon, Nafisa ta zube a kujera tace "Jiya a dakinki na kwana" dan murmushi Na'ima tayi tace "Toh ki kwana anan yau kawai" dasauri Nafee ta hangame baki "Ahhh, yanzu ma nasan Yaya sunje dubiya ne asibiti har dasu Mamin shiyasa nazo" Na'ima tace "Lafiya kuwa? Meya faru?" ta amsa da "Laila ce tasha pills yau da asuba, haukan ya motsa kuma duk ganin Daddy ya dawo jiya ne shiyasa" sanyi jikin Na'ima yayi sai ta budi baki ahankali tace "Allah ya bata lafiya" Nafisa ta amsa da "Amin" sannan ta jawo dan babban jakan dake gefenta ta bude ta fara ciro gadgets din Na'iman da ta bari can gidan, tana cirowan tace "Banga dayan qaramin iphad dinki ba sai babban nasamu" ta qarasa magana tareda miqa wa Na'iman su Laptop da iphad dinta, karba Na'ima tayi tace "Muje kici abinci saura kadan" da haka suka miqe Na'ima ta ajiye kayan anan kan kujera suka tafi kitchen, nan Nafisan ta taya Na'ima suka girka har lunch sannan suka zuba kowanne cikin coolers, basu suka gama ba sai sha biyu saura, da suka gama jera komai a dining area sai suka debi nasu suka zauna nan kan kujerun da suke jikin kitchen island suka fara cin abincin, Hira sukeyi hankali kwance sunacin abincin sai Nafisa tace "Umar ya kirani jiya wai zaizo dai, I'm so confused Bobo, yana daga cikin dalilin da yasa nazo ma kiban shawara" Na'ima na kallonta tace "I thought kince baya making effort a relationship din naku Nafee" sai tace "Yes but...i..." qura mata Ido Na'iman tayi tana jiran jin me zata ce, ganin ta kasa cewa komai yasa ta cewa "In tambayeki?" ta gyada kai sai Na'ima tace "Is Lamin making effort on you?" Nafisa ta gyada kai sai ta sake tambayata "Da shi da Umar wayafi treating dinki softly da kuma nuna miki qauna?" ta amsa da "Lamin, even though bamu dade tare ba amma bamu taba fada ba, I feel like yafi understanding dina da kuma understanding inda na dosa, yana saurarena sosai ba kamar Umar ba, it's just that na kasa mantawa da Umar ne sis" Na'ima ta sauqe numfashi tace "Nafee abun nan a fili yake, qualities din Lamin da kika qirgomin su kadai sun isa su nuna wayafi cancanta" Nafisa tace "kinsan zuciya, jiya da ya kirani yana bani hakuri sai narasa meyasa zuciyata ta sauqo akansa" Murmushi Na'ima tayi tace "Kiyi addu'an mafi alkhairy acikinsu sis but honestly speaking, I'm rooting for you and Lamin" shiru Nafisa tayi tana wasa da cokalin hannunta sai Na'ima ta sake cewa "Nafee soyayyar Namijin da zai soka yaso halinka ma daban yake, you and Umar are not compatible tun farko, ke kinyi gabas shi yayi yamma, you're only obsessed with each other but can't stand each other, kiyi tunani dan Allah" sai Na'ima ta amsa da "in sha Allah" sannan suka cigaba da cin abincin, sai da suka gama Nafisa ta jasu sama suka fara touring gidan gaba dayansa amma banda part din Ahmad, Na'ima ji tayi zuciyarta na sanyi duk inda suka shiga dalilin ganin kyawun gidan da yanda Ahmad ya tsara komai to her taste, da sukaje closet dinta Nafisa tana sake yi mata arranging jewelries dinta sai taga wata sarqa da akayi engraving sunanta ajiki ta miqa hannu ta dauka tana murmushi nan Nafisa ta sake dauko wata sarqan tace "Bobo kiga wannan ma" Na'ima ta miqa hannu ta karba nan taga shikuma ansaka "A&N" ajiki, murmushin ta ne ya fadada tana kallon letters din zuciyarta na melting, cire sarqan wuyanta tayi sai ta saka wannan din Nafisa na kallonta tana murmushi itama...