ƘWAI BIYU

Chapter Ten

by @thehealerspen654

GARGADI❗️❗️❗️

Labarin 'ƘWAI BIYU' taska ce daga fasahar Khadija Aliyu Ibrahim. Kuma kyauta ne.

Satar rubutu ba nishadi ba ne, cin amana ne ga marubuciya da kuma kokarin toshe hasken hazakarta. 

Idan ka ga wannan rubutu ba tare da sunana ko link ba, ka sani ba daga gare ni yake ba.

Sannan duk wanda muka kama da wannan laifin zai fuskanci fushin hukuma.

Saboda haka a kiyaye.

https://www.arewapen.com/book?id=6973796cb4ed2df0424e19cf

WhatsApp channel 👇

***


           From the writer of
           'NI DA KANNENA'  

        "بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْم"       

             'ƘWAI BIYU'
          CHAPTER TEN 

Yana zaune akan gadonsa sanye da wasu kayan bacci farare idon sa ƙyar akan katuwar TV da take malale a jikin bango, hawaye ne kawai suke zirya a idonsa, duk wani motsi da take yi ƙara ɗaga masa hankali yayi.

Hakan ya sanya ya fara nadamar video da ya saka aka turo masa. Video ya ƙunshi duk wani gurmi da aka tafka da Radiya lab din su sati guda da suka wuce. 

Bai san tsautsayin da ya saka yace a tura masa ba. Shi a tunaninsa abinda ta aikata zai saka ya fitar da ita acikin zuciyar sa cikin sauki. Sai dai kash, sake hura wutar abinda yake ji a ransa yayi ninki dubu.

Hannun sa ya saka ya share hawayen da suke zubo masa, sannan ya dauki remote ya kashe TV. ya rasa me yake damunsa acikin sati guda nan, baya taɓa samun sukuni idan bai kalli video Radiya ba, a hakan ma maimakon ya samu sauƙi kullum abin nasa ƙaruwa yake yi.

Miƙewa yayi cikin hanzari ya nufi banɗakinsa ya ɗauro alwala ya shimfiɗa sallaya, ya gabatar da sallah raka'a biyu, ya ɗaga hannunsa zai fara addu'a, take ya sake jin wani kuka mai ƙarfi yase ƙwace masa.

Hakan ya saka ya kifa kansa kawai akan daddumar ya ci gaba da kukan mai tsananin ƙarfi tare da ambaton: 

"Astagfirullah!...Astagfirullah ya Rabbi, ya Allah ka yafe min bana nufin shiga hurumin ka...ban aikata hakan da gayya ba.

Ya Allah ka yafe min...ya Allah ja cire min ita zuciyata...ya Ubangiji na rasa yadda zanyi nafi karfin zuciyata, Allah ka sauƙaƙa min Astagfirullah! Allah na tuba..."

Abinda yayi ta ambato kenan har ya samu zuciyarsa ta yi sanyi, sannan ya miƙe ya fara shirin kwanciya,  ba don zai iya yin bacci ba, a'a saboda ya samu ya huta.

Saboda a duk lokacin da dare yayi damuwarsa ƙara nunkuwa take yi, saboda wani matsanancin kishi da yake turnuƙe zuciyarsa.

Zuciyarsa tana raya masa cewar: "tana can tare da wanda take so, suna rayuwar auren su cikin farin ciki, wataƙila ma suna raya wannan daren."

Wannan tunanin ne a kullum yake hana shi bacci. Duk ya rame idon sa yayi ciki duk da daman yana cikin damuwa a baya kuma yana kokarin ɓoye damuwarsa.

Amma wanna karon ya kasa sarrafa kansa, shiyasa ya gwammace ya killace kansa a ɓangarensa domin ya ƙauracewa duk wasu tambayoyi da tuhuma daga Ammey da kuma Sauban.

Yana kwance kansa yana kallon sama, da zarar bacci ya fara daukar sa, sai zuciyar sa ta farkar dashi da faɗin "tana can tare da wani ba kai ba."

Hakan ya saka yake kasa rufe idonsa saboda a tunaninsa rashin yin baccin shi zai saka ya sami salama.

Amma daga bisani idan yaji wannan yanayin sunan Ubangiji yake kira tare da ambaton "Astagfirullah." 

Wannan ya saka ya samu sauƙi, sai misalin ƙarfe uku na dare sannan bacci ya ɗauke shi.

Misalin ƙarfe goma da rabi na safe Sauban yana zaune a gefen gadon Sultan yana ƙare masa kallo, fuskarsa cike da tausayin rabin jikin nasa. 

Ya tabbatarwa da kansa cewa Sultan yana cikin damuwa, amma ƙarfin hali irin nasa ya saka yake ɓoyewa, musamman keɓe kansa da yayi, baya son shiga cikin mutane, sannan ga ramewar da yayi ya daɗa tabbatar da hakan.

Cikin baccin sa yaji alamar ana kallonsa, hakan ya saka ya motsa tare da buɗe idonsa yana salati. Ga mamakinsa yaga Sauban a zaune yana kallonsa.

Zumbur! ya miƙe zaune, saboda yadda yaga rana ta fito sosai, ya kama kansa a daidai lokacin da ya kalli agogon da yake kan side drawer yana mamakin yadda akayi bai ji alarm ba. 

A hankali ya mayar da hankalinsa kan Sauban yace:

"Kai kashe min alarm ko?"

Murmushi yayi sannan yace:

"Kana buƙatar kayi bacci sosai."

"Who told you!" Ya katse shi da sauri.

Murmushin yaƙe Sauban ya sake yi, sannan yace: 

" I feel it..and nasan ka ɗauki hutu baka zuwa office."

Wani gajeren tsaki Sultan yaja ya miƙe yana ƙoƙarin nuna babu abinda yake damunsa sannan ya nufi banɗaki. 

Murmushi Sauban ya sake yi sannan yace:

 "Ina jiran ka zamuyi breakfast."

Jinjina kansa kawai yayi ya shige banɗakin.

Suna zaune akan dinning suna karyawa, Sauban ya ƙura masa ido. Ya lura kawai tura abincin yake yi ba don yana so ba, saboda yasan yana wajen. Wannan ne dalilin da ya saka yazo saboda ya tabbatarwa da kansa in dai yana wajen ko baya so zaici abinci.

Cike da ƙuluwa Sultan ya kalle shi yace:

"Wai waye ya hana ka kayi breakfast a gidanka?"

"Excuse me!" Abinda Sauban ya faɗa kenan cike da mamaki.

"You know what? ka dinga breakfast a gidanka ka daina zuwa kana takuramin please!"

Murmushi Sauban ya sake yi sannan yace: 

"Har yaushe kayi wayon da zaka fara ɓoye min abinda yake damun ka Sultan?" 

Ya faɗa yana kafe shi da ido.

Cikin sauri Sultan ya ɗago ya kalle shi yace:

"I don't understand. I'm asking about why you didn't have breakfast in your home, and you're switching in to rubbish...."

"It's because I want you to eat." Ya katse shi.

Cike da ɓacin rai Sultan ya miƙe ya bar dinning ɗin ya nufi parlour ya kunna PSP Game a TV. A hankali Sauban ya ƙaraso shima ya dauki ɗaya thumstick ɗin suka fara gwabza wasan.

Yanayin yadda Sultan yake game ɗin cike da ɓacin rai ya saka Sauban ya ajiye thumstick ɗin ya dafa kafaɗarsa yace:

"You need to stop all this. I know you love her, and I will do anything to...."

"What on earth are you talking about?" Sultan ya katse shi cikin tsawa tare da buga thumstick ɗin hannunsa a ƙasa ya tarwatse.

Sannan ya sake kallonsa ransa a ɓace yace:

"Idan ka sake yi min magana akan yarinyar nan I'll cut you off."

Ya miƙe da niyyar tafiya, Sauban ya finciko hannunsa cike da tsananin ɓacin rai yace:

"So what if you cut me off? 

Zan fasa rayuwa ne? 

Ko zan fasa jin daɗin rayuwa? 

Na faɗa kana son ta shashasha mai burga akan rashin gaskiya."

Cike da mamaki Sultan ya kalle shi yace:

"Ni ka cewa shashasha Sauban?"

"Yes I told you shashasha ne kai, nonsense. 

Duk motsin ka ina sane dashi. Baka son ta ka saka aka tura maka videos ɗinta kullum sai ka gani? 

Baka son ta kake kulle kanka kake kuka da idon ka? 

Baka son ta kake kasa yin bacci, kake kasa cin abinci? 

Baka son ta zaka saka a kulle laboratory da ka daɗe kana jiran sakamako daga gare shi? 

To bari kaji in fada maka abinda ka kasa ganewa; tunda har ka saka aka rufe lab ɗinnan, zuciyarka tana faɗa maka cewar ta gama samun abinda take nema, ƙwaƙwalwarka ce take yaudarar ka...?

"You're spying at me?" Sultan ya katse shi tare da cakumo kwalar rigarsa, shima ya cakumi tasa. 

A dai dai wannan lokacin Ammey ta ƙaraso da sauri sakamakon ɗaya daga cikin masu aikin gidan taje ta sanar mata. 

Da sauri ta fara ƙoƙarin shiga tsakanin su. Kallon kallo kawai suke yiwa juna, sai huci suke yi kamar wasu zakuna. 

Duk ƙoƙarin da tayi don ta ɓanɓare hannunsu daga shaƙar da suka yi wa juna ta kasa. Hakan ya saka ta fashe da kuka tana faɗin:

"Ku kashe junan ku to nima baƙin cikin ku sai ya kashe ni..."

Hakan ya saka suka fara sassautawa, Sauban ya saki wuyan Sultan shima ya saki masa. Sannan Ya kalle shi yace: 

"Idiot!" 

Ya nufi hanyar fita.

Cikin zafin nama Sultan ya sake zabura zai bi bayansa, da sauri Ammey ta riƙe shi, ya juyo ya kalle ta hankalinsa a tashe yace: 

"Ammey he insult me....he called me idiot nonsense a gabanki kuma kina ji...?"

Gam! ta riƙe shi a jikinta. Tana kuka saboda rabon da taga sunyi faɗa irin wannan tun suna secondary school. 

Wannan ya saka hankalinta ya tashi, saboda basa ɓatatawa junansu rai, a duk lokacin da ɗaya yayi fushi, to ɗayan sauka yake yi.

Amma yau gabaɗayansu sunyi fushi, banda Allah ya kawo ta da wuri ta tabbatar da sun dinga jefe jefe kenan sai sun tarwatsa duk abinda yake parlour tare da jiwa junansu rauni.

Wani irin huci taji Sultan yana yi, zuciyarsa tana bugawa sauri. Hakan yayi matuƙar ɗaga mata hankali.

A hankali ta jawo hannunsa ta zaunar dashi akan kujera, ta saka aka kawo mata ruwan sanyi a kofi ta kai masa bakinsa ya kawar da kansa yana wani irin huci. 

Da ƙyar ta lallaɓashi yasha ta fara yi masa nasiha a nutse:

"Sultan kai ne baka da gaskiya tun da Sauban yayi fushi kai ne mai laifin. Babu wanda ban san halinsa ba acikin ku, saboda haka ka neme shi ka bashi haƙuri."

Cikin sauri ya juyo ya kalle ta bai san lokacin da hawaye suka fara zubo masa a idonsa ba yace:

"Ammey he's always stand for me...meyasa yau zai min haka....ya sani bazan iya jure rashinsa ba..."

"Yana matukukar ƙoƙarinsa akanka domin ya cika umarnin mahaifinku, bai cancanci abinda kayi masa ba, duk da bana shiga sabgar ku, ban san me ya haɗa ku ba, amma ka bawa ɗan uwanka haƙuri Sultan."

Jinjina mata kai yayi tare da kwantawa akan cinyar ta, zuciyarsa tana yi masa raɗaɗi akan yau shi Sauban ya kira da shashasha kuma idiot.

A ɓangaren Sauban, shima yana isa gida ya nufi apartment ɗinsa da sauri. Cikin zafin nama Zainab tabi bayansa, amma kafin ta ƙarasa tuni ya rufe ƙofar.

Cike da tashin hankali ta fara ƙwanƙwasa ƙofar bedroom ɗinsa, amma sam bai buɗe ba. A ƙalla ta kai mintuna goma sha biyar a tsaye tana abu ɗaya, sai daga bisani ta jiyo muryarsa cikin ƙaraji yace mata: 

"Leave me alone!"

Cikin razani ta sakko ƙasa ta ɗauki wayarta ta fara kiran layin Ammey. Cike da tashin hankali ta fara tambayarta abinda ya faru saboda kafin ya fita ya sanar mata da cewar gida zai je. 

Cikin hikima Ammey ta kwantar mata da hankali, sannan tace mata sun samu saɓani ne da ɗan uwansa. Saboda haka abu mafi sauƙi ta ɗan bashi waje ya sarara, idan suna wannan yanayin duk wanda ya shiga to komai zai iya faruwa dashi.

Hakan ya saka ta ɗan kwantar da hankalinta ta nemi waje ta kama kanta, saboda gudun matsala, saboda sarai tasan halin mijinta da zuciya musamman idan abun ya shafi rabin jikinsa Sultan.

***        

•••••••••••••••••••••••••••

Yana ta zirya tare da kai kawo acikin bedroom ɗinsa. Kansa ya ɗauki zafi, zuciyarsa sai bugawa take yi kamar zata fito sarari, ya rasa wacce damuwar zai saka a gaba.

Tsananin wutar kishin da take ruruwa a zuciyarsa na Radiya, kokuwa rikicin da ya gudana ɗazu tsakaninsa da ɗan uwansa akan rashin gaskiyar sa, saboda ya sani sarai Sauban ya fishi gaskiya amma ƙi faɗinsa ya saka ya danne hakan.

Fitowa yayi balcony da yake bedroom ɗinsa ya iske ana tafka ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, ga tsawa da cida da take tashi.

Hakan ya saka ya dawo ya zauna a gefen gadonsa, ya kalli agogon da yake maƙale a bangon dakin yaga sha biyu saura mintuna 25 na dare. 

Ya tabbatarwa da kansa cewar ko da ya kwanta ba zai taɓa yin bacci ba. Wannan al'adar su ce duk ranar da suka samu saɓani babu wanda yake iya yin bacci. 

Hakan ya saka ya miƙe ya cire kayan baccin da suke jikinsa ya ɗakko wandon joggers ash color ya saka, tare da wata farar T-shirt, sannan ya ɗora rigar sanyi mai haɗe da hula (hoddie) ya saka p-cap ya ƙara da hular rigar, ya saka safa tare da running sneakers, sannan ya fito tare da sakkowa ya nufi waje.

Duk da tsananin ruwan saman da akeyi ko a jikinsa, haka ya buɗe ƙofar apartment dinsa ransa a bace kamar mayunwacin zaki ya nufi main gate.

Ganin hakan ya ɗaga hankalin securities ɗin gidan da suke gadin lafiyarsa. Musamman da suka ga ya nufi gate ɗin fita da kafa ba tare da ya nemi mota ba.

Saboda sun sani ko da sunyi ƙoƙarin dakatar da shi a wannan yanayin ba zai taɓa tsayawa ba, hakan ya saka kawai suka fara kokarin bin bayansa.

Cikin zafin nama yake tafiya, ga mugun ruwan saman da ake tafkawa, am a haka ya fice daga gidan ya ɗauki hanya ya fara tafiya a ƙafa.

Hannayensa cikin aljihun rigar sanyin, fuskarsa ta ƙule acikin hular rigar sanyin, sannan p-cap ɗin da ya saka ta daɗa ɓatar da kamanninsa.

Haka ya dinga tafiya cikin zafin nama da taƙama, securities suna bin sa a baya. Ba tare da sun san in da ya dosa ba.

Sai da yayi aƙalla tafiyar mintuna talatin, sannan ya iso wani katafaren gida mai hawa uku, kafin ya kai ga kwakwasa gate ɗin tuni aka buɗe masa ƙofar ya shige cike da taƙama, kai tsaye ya nufi cikin gidan, securities ɗin sa suka sake bin bayansa.

Sauban yana tsaye a balcony da yake bedroom ɗinsa yana ta kai kawo yana kallon gate ɗin shigowa, hankalinsa a tashe ya kasa kwanciya zuciyarsa sam babu daɗi.

Kamar da wasa ya hango shigowar Sultan, tsayawa yayi daga sama yana kallon sa. Haka shima ya ɗaga kansa yana kallon sa tare da sauke hular rigar sanyin nasa

Sun kai a ƙalla mintuna biyu zuwa uku a haka babu wanda ya motsa. Sultan yana tsaye yaki shiga cikin gidan, duk da tsananin ruwan saman da ake tafkawa yana tsaye ya ɗaga kansa yana ƙurawa Sauban kallo.

Ganin hakan ya saka Sauban ya motsa saboda ya tabbatarwa da kansa abinda Sultan yake nufi. Hakan ya saka ya sakko ya nufo ƙofar shiga wani keɓaɓɓen ɓangare a gidan, ya buɗe ƙofar ya tsaya yana jiran ya ƙaraso.

Maimakon Sultan ya ƙaraso, amma ya tsaya ya sake ƙurawa Sauban kallo. Hakan ya saka shima Sauban ya tsaya ya ƙura masa ido, wannan karon ma ya tabbatar da abinda Sultan yake nufi.

Ajiyar zuciya yayi,  sannan yaja wani dogon tsaki rai a ɓace ya nufo in da yake ya kama hannunsa suka shiga cikin parlour.

Suna zaune gabaɗayansu sai huci suke yi,  Sauban ne ya fara ɗagowa ya kalli Sultan yaga yadda ruwa yake ɗiga daga jikinsa ko ta ina. 

Hakan ya saka ya miƙe ya sake kamo hannunsa domin ya raka shi bedroom ya canja kayan jikinsa, amma da mamakinsa wannan karon Sultan yaƙi motsawa.

Ba tare da ya juyo ba ya sake jan hannun sa, amma bai ji alamar zai motsa ba. Hakan yasa yace: 

"You need to freshen up, you know you have an allergy to rain."

"I'm sorry!"

Abinda Sultan ya furta kenan, hakan ya saka Sauban ya juyo ya kalle shi. Hawaye yaga suna kwarara a fuskarsa ba ƙaƙƙautawa.

Hakan ya saka jikinsa yayi sanyi, ya juyo da niyyar yayi masa magana, ba tare da ɓata lokaci ba Sultan ya durƙushe a akan gwiwoyinsa tare da riƙe hannun Sauban da hannu biyu ya fara roƙon sa kamar ƙaramin yaro.

"Please Sauban...I can't hold on without you, I can't. Ka fini gaskiya ina son ta..na kasa jurewa, zuciyata ta na ƙoƙarin ta jefa ni a halaka tana ƙoƙarin ta saka na shiga hurumi Ubangiji Sauban. 

Tun lokacin da na ɗora idona akan hotonta na kasa samun sukuni, tun lokacin da na fahimci tana da aure kishi ya hana ni sukuni I barely to sleep. I feel like she's with her love one...may be they are making love...or something else.

Zuciyata tana nuna min kamar wani ya ƙwace min abin da yake nawa ne, na kasa yarda nine nake nema na shiga hurumin wani. Sauban zuciyata tana nema ta halakani...."

"Zuciyar ka tana kan daidai matuƙar ka tsaya ka saurari abinda zan faɗa maka game da ita Sultan." Ya katse shi.

Sannan yacigaba da magana:

"Zuciyar ka bazata taɓa halakar da kai ba akan Radiya you're the right one, she's yours, keep claming her, and I'll prove it."

Cike da mamaki Sultan ya miƙe tsaye yana kallon Sauban sannan ya bude bakin sa zaiyi magana Sauban ya katse shi da cewar:

"Matuƙar ina raye kuma ina numfashi kuma Ubangiji ya kaddara, to sai ka rayu da Radiya na har abada, ka kwantar da hankalinka ka fara lissafin ranar ɗaura aurenku daga yau."

Sannan ya kama hannun sa suka yi sama ya buɗe masa banɗaki ya shiga. 

Sultan kallon mamaki kawai yake bin Sauban dashi. Duk da ya san Sauban bai taɓa yi masa ƙarya ba musamman akan al'amari irin wannan, amma tabbas yana matuƙar mamakin yadda wannan al'amarin zai kasance. 

Kafin ya fito Sauban ya buɗe wardrobe ya ɗakko masa kayan da zai canja ya ajiye a gefen gado, sannan ya zauna yana jiran fitowar sa.

Kasancewar shaƙuwar su tayi yawa ya saka kowanne cikin su sai da yayi ɓangare guda na musamman acikin gidansa wanda nasu ne su biyu suke zama da zarar daya yazo, babu abinda babu aciki na buƙata. Yadda yake a gidan Sauban haka yake a gidan Sultan babu bambanci.

Da Sultan ya fito daga wanka ya canja kayansa anan ne Sauban ya zayyana masa duk wata makamar da ya samu akan binciken da yayi akan Radiya, da mijinta, sannan  kuma ya tabbar masa da cewar zasuyi nasara In shaa Allahu.

Hakan ya jefa gabaɗayansu acikin farin ciki. Suka yi ta hirar zumunci, sannan suka miƙe suka shiga kitchen tare suka girka abinda zasu ci.

 Kasancewar babu wanda ya saka wani abu acikinsa tun bayan rikicin su, sai da dare ya tsala sannan suka kwanta bacci...



          Written by: 
     Khadija Aliyu Ibrahim 
      (The Healer's Pen)
         *** 




Read our free Books 👇

https://www.arewapen.com/book?id=6973a231b4ed2df0425189c7

Whattpad 👇

***