4
by @oumfatima33
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*KOMAI TSANANI*
*By*
*KANSA'U* *BELLO*
*(OUM FATIMA)*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*PAGE 04*
*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*
A halin da ake ciki yanzu tuni an fara aurar da sa'o'inta dake gidan, don itama Manniru Alhaji yake son yi musu haɗin gida. Mannirun da yake ɗaya daga cikin tuzuran ƙauyen domin kuwa sa'anninsa har da mai yara huɗu, sai dai koda Alhaji ya shawarce sa da maganar ƙiyawa yayi ya nuna sam bai amince ba. Kai tsaye ya kalli Alhajin yace masa.
"Allah ya kiyaye me zan yi da wannan abar, duk tarin ƴanmatan dake garin na in rasa wacce zan aura sai wannan langa-langar yarinyar mai kama da kamun mayu, da wasu ƙwala-ƙwalan idanunta tamkar zata cinye mutum dasu. Haba Alhaji Allah ya kyauta ace duk daɗewar da nayi ban yi aure ba kuma sai in ƙare da wannan kwanan gida yinin asibitin, wannan ai dare ɗaya xan kakkaryata azo kuma ana tuhuma ta da laifi, kai!! ina!!! Ba zai yiwu ba, a kai kasuwa." Duk da cewa magan-ganun da Manniru yayi amfani dasu sun matuƙar ƙona ran Mama, sai dai ƙin amincewar tasa ya mata daɗi bata shirya aurar da Nanah a wannan lokacin ba. Taci buri sosai a kanta ita da ɗan'uwanta da bata san a halin da yake ciki a yanzu ba tsawon shekara kusan bakwai kenan.
A ɓangaren Nanah kuwa da taji abinda ya faɗa ɗin tayi kuka sosai, ta rasa wace irin tsana Baba Manniru yayi mata da har zai furta irin waɗan nan magan-ganun a kanta. Ji tayi itama ta ƙara tsanarsa sosai a cikin ranta.
Rashin amincewar Alhaji yasa Nanah bata shiga secondary ba a shekarar data gama primary har abokan karatun ta suka wuce suka barta, yayin da da yawa daga cikin ƙawayenta ake ta aurar dasu.
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*KANO...*
Matashin saurayi ne ɗan kimanin shekaru goma sha takwas ya sauka daga saman mashin ɗin daya tsaya dai-dai ƙofar wani gida. Ɗari biyu ya fito da ita ya miƙa masa sannan ya tunkari gate ɗin gidan dake gabansa, cike da natsuwa ya tura ƙaramar ƙofa ya shiga hannunsa riƙe da babbar laidar dake ɗauke da kayan miya da ya amso daga kasuwa.
Gidane ne irin na masu matsakaicin ƙarfi wato masu rufin asiri sosai sai dai ba za'a kira su da masu kuɗi sosai ba, mai gidan Alhaji Bala (Yayan Malam Khamis wato Mahaifin su Nanah) yana da rufin asiri dai-dai gwargwado domin kuwa sana'ar sayar da yadika yake yi a Kasuwa. Kuma Alhamdulillah asirinsa a rufe yake.
Yana da Matan aure guda biyu da yara tara, Matarsa ta farko ita keda yara shida amarya nada uku. Sai Khalid ɗan wajen marigayi Malam Khamis da yake riƙo wanda bashi da takamai-man Uwar riƙo a gidan haka yake walagigi a cikin yara. Tsawon shekaru kusan bakwai haka ya rayu tamkar wani almajirin gida don duk wata wahalar aiki da aike shi ke yinta, kuma a ƙarshe abinci ma sai rabonsa ya rantse yake samun sa.
Amma kasancewarsa yaro mai tsananin haƙuri da ladabi da biyayya yasa ya iya jure komai ya rayu a haka. Damuwarsa ɗaya ce wacce yake kwana da ita yana tashi itace na rashin sanin halin da Mahaifiyarsa da ƙanwarsa suke ciki na tsawon shekaru bakwai. Duk lokacin daya samu hutun Makaranta ya roƙi. Abba (Alhaji Bala) zuwa can Daura yayi hutu, ba don komai yake son zuwan ba sai don ko zai samu labarin halin da suke ciki. Kullum kuma idan yaje labarin baya sauyawa akan tana gidan Mijinta tana zamanta lafiya.
Duk yanda yayi a kan wani yaje ya duba su abin ya gagara, dama ba wasu tsayayyu masu kula da ita gareta ba. Mahaifiyarta kaɗai ta rage mata kuma tsufa ya kamata sosai, sai ƴan'uwanta guda uku Mata biyu Namiji ɗaya.
Duka Matan suna gidajensu da nasu Iyalan, Namijin shima yana da nasa iyalin kuma rayuwa ce suke irin ta kowa yayi ta kansa domin babu wani mai ƙarfi a cikinsu. Daɗin daɗawa kuma basu wani damu da taimakon juna ba, yana ɗaya daga cikin dalilin daya sa Yayanta ya takura mata ya aura mata Alhaji Zubairu saboda ba zai iya riƙe ta ita da ƴaranta ba.
Wannan kenan...
Cikin natsuwarsa yayi sallama a faffaɗan tsakar gidan nasu mai ɗauke da ɓangare biyu, na farko shine na mai gidan. Sai ɗayan shine na Matan gidan da Yaransu, ko wace Mace nada babban Palonta mai ɗauke da bed room ɗinta dana yaranta Mata. Yara Maza kuwa suna a Boys quarter's ne, ciki har da Khalid.
Kai tsaye ɓangaren Uwar gidan ya nufa mai suna Hajiya Zuhura, sallama yayi kusan sau biyar kafin aka bashi izinin shiga. A palo ya sameta zaune saman kujera tana danna waya sai yarinyarta mai suna Yusrah zaune a gefenta tana kallo a waya. Har ƙasa ya tsuguna ya gaisheta yayinda tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kai tana amsa masa cikin halin ko in kula.
"Mumy ga kayan miya Abba yace a kawo." Ya faɗa cikin girmamawa. Laidar hannunsa ta kalla ta ɗauke kai ta mayar kan wayarta sannan tace.
"Ka kaiwa Larai tana Kichen, kace tayi maza ta gyara su."
"To Mumy." Ya faɗa yana miƙewa ya nufi ƙofa. Har ya saka ƙafarsa Yusrah ta ƙwala masa kira tamkar wani yaronta, duk da cewar ta girme sa don zata iya bashi shekara biyu. Juyowa yayi ya kalleta yana jiran jin abinda zata faɗa.
"Ka ɗauko min ruwa mai sanyi a fridge." Tsaye yayi yana kallon yanda take bashi umarni ciki isa.
"Ko baza ka ɗauko mata bane? Bafa na son rashin mutunci don naga kwanakin nan idonka yayi tsauri, to kar ka manta cewar zaman cin arziƙi kake yi a gidan nan." Hajiya Zuhura ta faɗa cike da takaicin zaman yaron a gidan tamkar wanda ya tare mata wani abin.
Ta manta cewar shima ɗane a gidan domin da Alhaji Bala da Malam Khamis Uwa ɗaya Uba ɗaya suke, don haka Alhaji Bala shike da ikon riƙe yaransa bayan ransa.
Cikin sanyi jiki ya aje laidar hannunsa ya nufi inda fridge yake ya ɗauko ruwan ya kawo mata, harara ta jefa masa kafin ta warci ruwan tana sakin tsoki. Bai ko kula taba ya juya ya ɗauki laidar kayan miya ya fice yana jin takaici ƙasƙancin da ake nuna masa a gidan Yayan Mahaifinsa.
Kichen ɗin yaje inda ya samu Larai tana ta aikin ɗaura girkin rana, jiki a sanyaye ya gaisheta tare da bata saƙon ya juya ya fice, da kallon tausayi Larai ta bishi tana masa addu'ar dacewa da nasara a rayuwarsa. Sosai take ƙaunar yaron tun lokacin da riƙon sa ya dawo gidan, yaro ne mai sanyin hali da girmama na gaba da shi. Rashin girmama mutane da wulaƙanta wanda suka fi ɗabi'ar yaran gidan ce kasancewar Iyayensu Mata basu damu dasu tsawatar musu ba idan suna rashin kirki wa mutane, mai gidan kansa yana da matuƙar son yaransa shi yasa bai cika tsawatar musu ba. Shi yasa suke abinda suka ga dama a cikin gidan don babu mai ce musu don me.
Kaf a yaran gidan Khalid shi kaɗai ne yake girmamata a matsayinta na mai aikin gida, wannan dalilin ne yasa take jinsa a zuciyarta. Har abinci take ɗiba ta ɓoye masa idan ta kammala, domin idan ta riga ta gabatarwa mai yin girki sai rabonsa ya rantse yake samu.
Yana fitowa ya tare ɗan sahu ya koma Kasuwa don tunda ya kammala secondary yake bin Abba shago yake taimaka masa da wasu abubuwan, duk da cewa Abban yana da yaran dake kula masa da shagunansa dake cikin kasuwar. Tare suka kammala makaranta da Abdallah da Rafeeq waɗanda suke sa'o'insa ne, kuma su tuni Mahaifinsu ya sama musu makaranta sunci gaba da karatu inda shi kuma yace ya bari sai wata shekarar saboda kashe kuɗin zai masa yawa idan ya haɗa da shi.
Yayi kuka sosai a lokacin saboda ba ƙaramin ƙwallafa rai yayi a karatu ba, don shi kaɗai ne yake gani a matsayin hanyar da zai bi wacce zata sa ya tsaya da kansa har ya tsayawa Mahaifiyarsa da ƙanwarsa. Tun daga lokacin ya fara ƴan buga-bugarsa a cikin kasuwa yake tara abinda yake samu a cikin asusun daya siya da niyar idan suka taru zai yiwa kansa hidimar Makaranta don ya lura Abban bashi da niyar saka shi tunda su Rafeeq a yanzu suna cikin shekara ta biyu ne. Kuma ba wai don bashi da halin biya masa kuɗin bane kawai bashi da niyya ne.
_______________________
A Cigama kuwa rayuwa tayi matuƙar yiwa Mama da Nana zafi domin kuwa babu abinda ya sauya na daga irin wulaƙanci da tuggu da kishiyoyi ke haɗa mata, gashi sun samu ɗaurin ƙugu a wurin Iya shi yasa suke mata abinda suka ga dama. Alhaji kuwa yana yin magana Iya zata zage shi tas a gaban Matansa da yara, wannan dalilin yasa yanzu ko tsakar gida Mama bata fitowa kullum tana ɗaki. Idan kaga ta fito to wani abu zata yi kuma tana kammalawa zata koma ɗaki.
Ta daina kula su akan duk abinda suke mata ko ɗaga kai ta kalle su bata yi, wanda hakan yake ƙona musu rai sosai don sun fi son ta tanka su samu damar da zasu mata abinda suka ga dama. Nanah kuwa gaba ɗaya yaran gidan sun tsangwame ta idan ka cire Atika wacce tasu tazo ɗaya, bata isa shiga cikin ƙawaye ba in dai dasu to sai sun tozarta ta da kiranta da agola, mayya da sauran su. Haka zasu saka yara suyi ta mata ihu da dariya, sai dai tayi kukanta ta share ta koma gida. Ƙarshe dai Mama hana ta fita tayi idan ba da wani dalili ba, so take Alhaji ya amince ta sakata a makarantar secondary taci gaba da karatunta kafin ta samu damar da zata rabata da garin taje inda zata samu damar ci gaba da karatunta cikin kwanciyar hankali.
Duk cewa inda take son turata ɗin ma ba wani gata zata samu ba amma ya fiye mata nan, saboda koba komai can ɗin suna da ilimi da waye wa.
Gobe ta kama ranar da mutanen garin ke gudanar da al'adar bikin binne doya wanda suke yi idan an gama noman doya. Ko wane gida zai bayar da doya ɗaya idan aka tara sai a haɗu ƴanmata da Samari, manya da yara a tafi bayan gari a haƙa rami mai faɗi 4 corner sai ayi wani ƙarami a cikinsa ma'ana ciki da palo tamkar dai ginin ƙabari, sai a zuba doyar a can ciki a shirya itace a kunna wuta sannan a ƙara shirya wasu itace a sama a tsai-tsaye a haɗa kawunansu sai a kwaɓa ƙasa a yaɓe sai a bata lokacin da zata gama dahuwa.
Da zarar ta kammala dahuwa sai a saka manyan itace ayi ta duka har sai an rushe duka wannan ƙasar da itacen da aka yaɓe sannan sai a tone doyar, ayi ta ɓarewa ana yanka wa ana raba wa kowa dake wurin, inda za'a yi ta dangwala wa da yaji ana ci. Hatta waɗan da ke gidajensu ma ana aika musu. To daga nan ne kuma ko wane saurayi zai ja budurwarsa su koma gefe suna ci suna hira abinsu, yara kuma suyi ta wasan su kamar dai yanda aka saba.
(Wannan al'ada ce da ake yi a wasu ƙauyuka musamman guraren da suke noma, zaka ga duk abinda aka gama nomansa anayin wannan al'adar irin su gero ana ce masa ACI GERO wasu suyi tuwon ruwa (sindilƙe) wasu suyi ɗanmalele wasu waina. Kamar waken suya shima ko wane gida zasu yi awara, za kuga wasu ƴanmatan na fita ƙofar gida su soya ana rabawa samari da abokan arziki, musamman in an samu amfani da yawa za'a saka rana da kowa za'a dafa a gidansa yara su fita wasa, ƴanmata su kaiwa samari da dai sauransu.
A wannan karon noman doya aka kammala kuma gobe ne zasu gudanar da al'adar don haka manya da yara, samari da ƴanmata suke ta farin ciki domin abin akwai ƙayatarwa.
A ɓangaren Nana ma ba'a barta a baya ba murna take sosai saboda tana son irin waɗan nan al'adun suna matuƙar burgeta. Sai dai da ta san cewa ranar goben a gare ta rana ce da zata buɗe mata sabon shafin ƙaddara wanda zai ƙara jefa rayuwarsu cikin takura da baƙin ciki fiye da wanda suke a cikinsa ita da Mahaifiyarta da ba tayi farin cikin zuwan ranar ba bare ta kai kanta inda ƙaddara ke jiranta, sai dai ƴan magana suka ce wai ƘADDARA TA RIGA FATA.......