6
by @oumfatima33
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*KOMAI TSANANI*
*By*
*KANSA'U* *BELLO*
*(OUM FATIMA)*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*PAGE 06*
*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*
"Kin santa ne?." Ya faɗa a dake yana kallon Atika dake kuka, sosai kwarjininsa yaso razanata don haka murya na rawa tace.
"E... Eh na... Na santa, ƙanwata ce." Kallonta yayi a tsanake kafin yace.
"Ok muje gidan naku."
"To." Ta faɗa kafin ta juya ta nufi hanyar gidan nasu. Ɗaya daga cikin yaran mai gari ne yayi ƙarfin halin matsawa kusa dashi yace.
"Malam waye kai da za'a kamaka kana lalata ƴar mutane sannan kuma don rashin kunya ka...." Wani kakkausan kallo mai firgitarwa daya jefa masa ya hana sa ƙarasa maganar da ya fara, sai ma jada baya da yayi a tsorace. Bin bayansa abokinsa yayi yana kiran sunansa akan ya dakata ya aje musu yarinyarsu suyi tafiyarsu tunda ga abinda mutane suka maida maganar daga taimako.
Rufa musu baya mutane suka yi ana ta ƙus ƙus ɗin abin da ya faru har ƙofar gidan Alhaji Zubairu Manomi, dakata wa yayi a waje ya kalli Atika yace.
"Je kice ana sallama da mai gidan." Da gudu ta shige cikin gidan tana ƙwala wa Alhaji kira.
"Wai Atika ba na haka ki irin wannan muguwar ɗabi'ar ba ta ƙwalla kiran sunan mutum tun daga waje ba, wai ma uban me aka yi kike wannan gudun kina huci." Alhaji daya fito daga ɗakinsa yake faɗa cikin mita yana hararar Atika.
"Alhaji wani mutum ne yake sallama da kai a waje." Ta faɗa tana nuna masa ƙofar gida.
"To wai kukan uban meye kike yi." Alhaji ya faɗa a ƙufule yana shirin doke mata baki.
"Alhaji Nanah ce gata can a hannunsa bata numfashi, kuma wai cewa aka yi... Cewa aka yi wai...." Ta kasa ƙarasa faɗar maganar Sabo da Mama data fito daga ɗakinta cikin sauri jin ta ambaci sunan Nanah.
"Me ya samu Nanah?." Mama ta faɗa tana kallon Atika. Kasa cewa komai tayi kawai sai ƙofar gida da take nuna wa, don haka Mama ta ɗauki hijabinta dake saman ƙyauren ɗakinta ta nufi ƙofar gidan. Shima Alhajin bin bayanta yayi don haka gaba ɗaya mutanen gidan suka rufa musu baya don ganin abinda ke faruwa.
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un! Me nake shirin gani haka ni Ramatu? Me ya samu Nanah? Bani yarinyata." Tayi maganar a ruɗe tana kallon mutumin dake tsaye ɗauke da Nanah bata numfashi.
"Kai wai miye ke faruwa a nan ne?." Alhaji Zubairu ya faɗa yana kallon tarin mutanen dake ƙofar gidan duk an zubawa baƙin Samari biyu ido.
"Kece Mahaifiyarta?." Matashin dake ɗauke da Nanah ya faɗa yana kallon Umma. Cikin sauri Umma tace.
"Ƙwarai nice Mahaifiyarta, me nene ya same ta?... Kayi min bayani mana!." Tayi masa tambayar cikin tashin hankali tana taɓa fuskar Nanah dake kallonsa. Miƙa mata Nanah yayi ta karɓa kafin ya juya ya kalli mutanen dake bayansu, cikin zafin zuciya ya shiga takawa zuwa inda Ilu ke tsaye yana raba ido ya damƙo wuyansa ya jefa gaban Umma kafin yace.
"Ina ɗayan tsinannen yake?." Yayi masa tambayar a tsawace yana shaƙe masa wuya. Cikin azaba Ilu ya shiga ƙoƙarin kwatar kansa. Kamar saukar aradu Umma taji ɗaya daga cikin mutanen dake wajen yana cewa.
"Ya zamu tsaya muna kallon mutumin nan yana raina mana hankali bayan Ilu ce mana yayi kama shi suka yi suna lalata da yarinya shine yayi wa Salmanu duka." Wani mugun jiri ne ya kwashi Umma har tana ƙoƙarin sakin Nanah dake hannunta sai da Alhaji ya tare ta ya amshe ta a hannunta. Kuka mai ƙarfi ta fashe dashi tana faɗin.
"Shike nan na shiga uku na lalace, ya kashe min yarinya marainiyar Alla bat...." Bata ƙarasa faɗar maganar ba ta zube ƙasa sumammiya. Hayaniya wuri ya kaure da ita kowa da abinda yake faɗa, sosai ransa yayi masifar ɓaci da abinda ke faruwa a wurin. So yake yayi wa Iyayen yarinyar bayanin abinda ya faru a samu a kula da yarinyar don a ceto rayuwarta, amma hakan ya gagara saboda gaba ɗaya ya lura mutanen nan basu da hankali. Ga tarin hayaniyar da ake tayi ta fara damunsa, ganin al'amarin na ƙara lalacewa yasa abokinsa matsawa kusa dashi yace.
"Mooh kazo mu bar wurin nan don Allah, shi yasa tun farko na hanaka shiga wurin nan." Kallo ɗaya ya masa ya ɗauke kai don baya jin zai iya magana a halin da yake ciki na ɓacin rai. Ƙoƙarin jan hannunsa Mus'ab yayi don su tafi aka riƙe hannun Mooh ɗin.
"Kuje ina bayan aika-ainar da kuka aikata? Ai daga nan wurin sai fadar mai gari don yace a taho daku." Yaron mai gari ya faɗa. Dafe kai Mus'ab yayi cikin takaicin abinda ke faruwa. Haka kawai daga taimako an zo ana ta raina musu hankali a wurin nan.
Umma kuwa ruwa aka zuba mata ta farka a zabure tana kuka ta nufi Nanah da aka zubawa ruwa itama ta farka tana ta zabura da surutai.
A ƙofar gida kuwa Mus'ab ne ke ƙoƙarin fahimtar da dogarin da aka aiko cewar sufa taimakon yarinyar suka yi saboda sun zo wucewa ne suka ji ihu shine suka je don ganin meke faruwa suka ga samari guda biyu na ƙoƙarin haiƙema yarinyar shine Mooh ya dake su ya taimake ta.
Wanda aka kira da Mooh kuwa kallo ɗaya ya yiwa ɗan aiken mai gari ya sakar masa hannu yana ja da baya.
"Let's go." Ya faɗa cikin dakakkiyar muryarsa mai cike da izza. Sai da suka bar wurin sannan wasu suka fara zagi da cika baki yayin da yaron mai gari ya tafi don sanar da mai gari abin da ya faru. Da haka kowa ya watse daga ƙofar gidan Alhaji Zubairu, cikin ƙanƙanin lokaci maganar ta zagaya ko ina cewar an kama agolar gidan Alhaji Zubairu tana lalata da baƙin nan ƴan bautar ƙasa.
A cikin gidan Alhaji Zubairu kuwa gaba ɗaya Matan gidan taruwa suka yi a kan Mama dake rungume da Nanah tana kuka tana ambatar sunan Salmanu kar ya cutar da ita. Maimakon su tausaya mata sai ma zagi da suke yi cewar ta janyo musu abin kunya abinda bai taɓa faruwa a gidan ba gashi nan agola ta janyo musu.
Sai da Alhaji ya tsawatar musu ya kori kowa kafin ko wacce ta nufi ɗakinta da yaranta suna mayar da yanda aka yi aka bar Mama na kukan baƙin ciki.
****** A ɓangaren su Mooh kuwa suna zuwa masauki ya shige ɗakinsa ya kwanta ya lumshe ido fuskar ƙaramar yarinyar da aka so wulaƙanta mata rayuwa tana dawo masa. A ɓangare ɗaya kuma ji yake dukan da ya yiwa yaron yayi kaɗan, kamata yayi ya karya ko wace gaɓa ta jikinsa ta yanda ba zai ƙara moruwa ba. Amma duk da haka ba zai ƙyale sa ba dole ne yasa hukuma su kama shi don a hukunta shi.
Ajiyar zuciya Mus'ab ya sauke kafin ya kalli Mooh dake kwance ya kumshe ido tamkar ba abinda ya aikata.
"Mooh ya kamata mu bar garin nan mutanen nan basu da kirki, ji sharrin da suka mana fa daga taimako. Sannan kuma ka san ba zasu bar maganar nan ba tunda mai gari ya aiko muje muka ƙi zuwa kasan dole gobe a neme mu. Mafita kawai mu shirya gobe mu bar garin nan, sai da nace kar muzo jahar nan amma ka dage sai mun zo. Gashi an kawo mu wannan ƙaddararren ƙauyen ji abinda ya faru daga taimako." Duk maganar nan da yake wanda ya kira da Mooh ko motsa wa bai yi ba daga inda yake bare ya buɗe ido ya kalli inda yake. Ransa ya fara ɓaci da wannan halin shariyar tasa don haka a ƙufule yace.
"Kai dai kana da muguwar matsala Wallahi, ya za'a yi in yi ta magana ka mayar sani wani sakarai?." Yanzun ma bai kulasa ba don haka rai a ɓace yace.
"Na san me zan yi." Wayarsa ya ɗauka yayi danne danne ya kara a kunne.
"Barka da dare Dady." Ya faɗa da girmamawa. Amsa masa aka yi daga can ɓangaren kafin ya shiga yi masa bayanin abinda ya faru. Shiru yayi yana sauraren maganar da ake masa daga can ɓangaren kafin ya miƙa masa wayar yace.
"Dady na son magana da kai." A hankali ya buɗe lumsassun idanunsa masu tsananin kyau ya zube su a saman fuskar Mus'ab yana masa kallon. 'meye kayi hakan.'
"Abinda ya kamata nayi Malam ka amshi waya kawai." Mus'ab ya faɗa yana harararsa. Wayar ya amsa ya ƙara a kunne yayi sallama cikin daddaɗar muryarsa wacce duk abin nan dake faruwa bai yi magana ba sai yanzu.
"Barka da dare Dady." Ya furta kalmomin a natse cike da tsari.
"Barka dai Muhammad, kana lafiya... Babu abinda suka yi maka dai ko?." Mahaifinsa ya furta cike da kulawa.
"Babu abinda ya same ni Dady ka kwantar da hankalinka." Ya faɗa a natse yana hararar Mus'ab dake kallonsa.
"Hankalina ba zai kwanta ba da zamanka a wannan yankin, dama ni kwata kwata hankali na bai kwanta da zamanka a yankin nan ba tun farko saboda rashin tsaro. Don haka maza ka dawo gida gobe ba buƙatar dole sai kayi service ɗin ma gaba ɗaya, wannan umarnina ne." Mahaifinsa ya faɗa daga can don ma kar ya musa masa.
"Ok Dady in sha Allah." Ya furta a taƙaice.
"Da kyau zan yi magana da Kwamishina ƴan sanda na jahar ayi muku Rakiya zuwa airport saboda tsaro." Dady ya faɗa kafin ya aje wayar. Kallon Mus'ab yayi yana jefa masa harara kafin yace.
"Matsoraci kawai, hankalinka ya kwanta, to ka shirya zuwa Kudu mu ƙarasa a can don dole sai mun kammala Service ɗin nan."
"Wah sai dai kaje kai kaɗai Allah kiyaye hanya ni kam babu inda zani." Mus'ab ya faɗa yana miƙewa don zuwa bayi ya watsa ruwa.
★★★
*Washe gari....*
Yanda Umma taga rana haka taga daren jiya saboda kuka da tashin hankalin halin da ƴarta ke ciki, addu'a ta riƙa yi mata sosai har ta samu tayi bacci sai dai baccin baya yin nisa take tashi a firgice. Alhamdulillah yau ta tashi da sauƙi don ta daina zaburar sai dai Kuka da take ta faman yi. Mama dake zaune saman abun salla tana lazumi ta juyo jin motsin Nanah ɗin. Tashi tayi taje inda take ta taimaka mata ta tashin zaune, sawun marin dake kwance raɗam a fuskarta ne yasa Mama share hawayen daya zubo mata ta riƙe hannunta tace.
"Kina ji, ki natsu kiyi min bayanin abinda ya faru." Hawayenta ta share cikin kuka sannan ta fara bawa Mama labarin abinda ya faru tun daga tahowarta gida har zuwa lokacin data suma ta daina gane komai.
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, Salmanu ɗan gidan mai gari fa kika ce Nanah?!." Mama tayi mata tambayar cikin ruɗanin data shiga.
"Amma suka ce Wani yaro ɗan bautar ƙasa ne aka kama shi shine ya musu duka?." Mama ta faɗa cikin mamaki.
"Allah Mama ƙarya suke Salmanu ne da Ilu suka ɗauke ni suka kai ni wurin yayi ta duka na yace wai ina masa wulaƙanci don haka sai ya wulaƙanta ni sai yaga ƙarshen girman kai, ina ta ƙoƙarin ƙwatar kaina ne naji wani ya shigo wurin ya ɗaga Salmanu ya fara dukansa, ni kuma daga nan ban san mai ya faru ba, tsoro nake ji sosai Mama!." Nanah ta faɗa tana rungume Mama ta fashe da wani kukan. Ƙara rungume ta Mama tayi tace.
"Kina nufin bai samu nasarar cin maki ba?."
"Ban sani ba Mama ya yaga min kayana yana ta son sai ya taɓa min..."
"Kinga ya isa haka yi shiru, muje kiyi wanka kiyi sallah gari ya fara waye wa." Mama ta faɗa tana tashi ta ɗauko mata zani ta ɗaura ta bata ƙaramin hijabi ta saka sannan ta fita ta juye ruwan zafin data ɗora lokacin data fita alwalar sallar asuba. Surka ruwan tayi yayi dai-dai ta ɗauka ta kai bayi sannan tazo ta kama hannun Nanah suka wuce tana jin Matan gidan da wasu daga cikin yara na binsu da kallo kafin ta jiyo muryar Indo na faɗin.
"Oh ni Indo Allah ya kawo mu zamanin da yarinya zata je tayi lalata ta dawo gida Uwa ta dafa mata ruwan wanka."
"Yo Indo kin manta daga bariki suka zo ai babu abinda ba zaki gani ba, ai mu dai kam Alhaji ya ɗauko mana mugun iri zai lalata mana zuri'ah." Barai dake hura hutar kokon safe da take sayarwa ta faɗa. Daga haka suka shige bayin ba tare data kula su ba.
Sai da ta duba Nanah sosai ta tabbatar da babu abinda ya sameta sannan ta sauke ajiyar zuciya ta taimaka mata tayi wanka suka fito tayi alwala suka wuce ɗaki.
"Maza ki shirya ina zuwa." Mama ta faɗa kafin ta fice a ɗakin don dama kunun da zasu karya dashi. Habaici matan gidan suka yi ta jefa mata har ta gaji tace.
"Duk wani mai nufi na da sharri in sha Allah bazai ci riba ba, kuma Alhamdulillah na gode wa Allah da yasa Salmanu bai samu nasarar wulaƙanta min rayuwar yarinya ba aka samu wanda ya taimake ta. Amma saboda rashin tsoron Allah shine suka juya maganar suna son masa sharri, kuma in sha Allah sai Allah ya tona masa asiri azzalumi, fasiƙi kawai!." Ta ƙare maganar cikin matsanancin ɓacin rai na tunawa da yanda yaso ratsa mutuncin marainiyar ƴarta. Salati Salmai Maman Aziza ta ɗauka tana faɗin sharri za'a yiwa Salmanu.
"Kar ki damu Babarmu, ai Salmanu da gatansa don haka babu wanda ya isa ya masa sharri ya zauna lafiya, yarinya taje tayi abinda ta saba saboda an kama su shine za'a yiwa masoyina sharri, to kuwa ta Allah bata mutum ba." Aziza ta faɗa cikin rashin kunya tana murguɗa baki. Girgiza kai kawai Mama tayi taci gaba da uzurin gabanta don Aziza ba sa'ar yinta bace, tana kammalawa kuma ta shige ɗaki tana jiyo duk magan-ganun da suke yi.
Kuka sosai ta samu Nanah nayi saboda duk abinda ke faruwa tana jinsu.
"Shike nan Mama kallon ƴar'iska za'a riƙa min, daman kowa baya son mu a garin nan Mama. Don Allah mu tafi mu koma gidanmu mu bar musu garin nan bana son sa!." Ta ƙare maganar cikin matsanancin kuka har tana shiɗewa. Itama Mama hawaye take share wa ta zauna kusa da ita ta shiga rarrashinta tana faɗa mata magana mai daɗi. Shigowar Sulaimanu ɗakin yasa suka daina maganar da suke yi sabo da shegen wayonsa......