9
by @oumfatima33
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*KOMAI TSANANI*
*By*
*KANSA'U* *BELLO*
*(OUM FATIMA)*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*PAGE 09*
*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*
Safiya ta ƙare maganar cike da mamakin yanda Nanah ke ƙin kula tarin masoyanta, don tun da tazo garin ko wane saurayi ke son ganin yayi soyayya da ita kasancewarta kyakykyawa masha Allah duk da cewa bata da wani girman jiki. Da mamaki Nanah ta kalli Safiya tace.
"Haba dai yanzu ke kina ganin ya dace in fara kula samari?." Tayi mata tambayar tana jiran amsar da zata bata. Cikin sauri Safiya tace.
"Me zai hana ke baki ga duk muna da samarinmu ba, kuma baki ga har ɗinkin sallah suke mana da saya mana kayan kwalliya ba. Amma ke kin tsaya har yanzu kan ki a tukunya, to Wallahi yarinya idan kika zauna ke zaki zama ƙarshe a cikinmu idan Sallah tazo don a shegen son kuɗin Babarsu Hasiya ba wani abin arziƙi zata maki ba duk irin kuɗin nan da kike tara mata kuwa." Safiya ta faɗan cikin son ta janyo hankalin Nanah ta amince da Habule don ya mata alƙawarin kyauta mai tsoka idan taci nasara ta amince da shi.
Girgiza kai Nanah tayi tace.
"Bana buƙatar abin hannun wani don Mama ta hana ni don haka kar ki ƙara min wannan maganar don Allah, ku wai ba kwa jin kunya a gan ku kun tsaya da saurayi ƴan ƙanana daku?." Nanah ta faɗa tana kallon Safiya.
"Wace kunyar zamu ji, to waɗan da basu kai mu bama zance suke yi bare mu. Ke kar fa ki raina mana wayo kice baki isa fara zance ba don garin da kika baro yara ƴan shekara goma ma wasu nada saurayi bare ke da za kiyi sha uku wanda nan da shekara biyu ma za'a iya aurar dake ki zauna daram har ki haihu a shekarar da aka yi auren." Safiya ta faɗa cikin jin haushin Nanah da shegen taurin kan ta.
Cikin sauri Nanah ta kalli Safiya jin tana mata maganar aure nan da shekara biyu har da haihuwa tace.
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un, gaskiya Safiya ki dai na min irin wannan maganar ni dai Mama ta hana ni." Takaici yasa Safiya kasa cewa komai sai dogon tsoki da taja ta ɗauki kwanon ƴar tsalarta tayi gaba tana mita. Da kallo Nanah tabi bayanta har ta ɓace ma ganinta kafin ta sauke ajiyar zuciya, ta rasa tunanin daya kamata tayi a wannan yanayin da take ciki. Ko kaɗan bata son wannan yawon tallar da take yi domin yana ƙoƙarin dakushe duk wani karsashinta na neman ilimi.
Sai dai hakan ya zame mata dole matuƙar tana zaune a gidan Kawu Basiru don in ma taƙi yi to abinda zata ci sai ya gagareta, tana son tafiya wurin Yaya Khalid kamar yanda Mama tace amma sai dai bata san taya zata tafi ita kaɗai ba. Koda ace kuwa ta gudu taje Kano to bata san unguwar da suke ba bare tayi tambaya. Nan ma data gane sabo da ƙaramin gari ne ana sauke ta a bakin titi tayi tambaya kamar yanda Mama ta sanar mata.
Da wannan tunanin a zuciyarta Amina ta dawo daga haɗo kwanukansu suka tattara suka wuce gida zuciyarta babu daɗi.
__________★
*Kano......*
A ɓangaren Khalid kuwa bai san duk abinda ke faruwa a can Gurjiya ba sakamakon makarantar daya ƙwallafa ma rai yana so, shi yasa ya mayar da kansa busy sosai yake aiki tuƙuru don ganin ya tara kuɗin da zasu ishe sa registration da sauran buƙatun da zai fara karatu awannan shekar mai zuwa. Wannan dalilin ne yasa kwata kwata bai samu damar zuwa duba Kakar tasu ba har Allah ya mata rasuwa bai sani ba, sakamakon bashi da lambar kowa shima babu mai tashi don bayan zuwan sa na ƙarshe ne ya samu ya sayi wayar tun da Alhaji Bala bai saya masa ba kamar yanda ya saya wa yaransa ba.
Alhamdulillah buƙatar sa ta biya domin kuwa lokacin daya buɗe bankin da yake tara kuɗin kuɗin daya samu sun bashi mamaki, don haka ba tare daya nemi shawarar kowa ba ya sayi form ɗin B.U.K ya fara neman admission da taimakon Baban abokinsa da suka gama secondary tare wan da shima bai samu fara karatun ba sai a wannan lokacin.
Alhamdulillah sun samu admission don haka babu ɓata lokaci ya biya kuɗin registration da komai sauran kuɗin ya ɗan sayi sabbin kayan da zai fara zuwa makaranta dasu ya ɓoye wasu sabo da sayen handouts da abin da ba za'a rasa ba. Sai da ya kammala komai sannan ya samu Alhaji Bala ya masa bayanin komai in da ya kama borin kunya ta hanyar rufe sa da faɗa.
"Wato haƙurin ne ba zaka iya ba har in samu damar da zan biya maka shine kaje kayi yin kan ka, baka san irin ƙoƙarin da nake yi ba wurin ganin na biya maka kuɗin makarantar nan ashe kai kana can kana yin kan ka... Wai ma a ina ka samu kuɗin da kayi hidimar makarantar dasu ne?." Alhaji Bala ya tambaya cikin borin kunya. Cike da ladabi Khalid ya duƙar da kansa yace.
"Kayi haƙuri Abba ba raina maka nayi ba, naga hidimar ta maka yawa ne shi yasa na yanke hukuncin tara ƴan kuɗaɗen da nake samu a kasuwa, to dasu ne nayi hidimar makarantar." Mamaki sosai ya kama Alhaji Bala na ganin yanda yaron ya tara kuɗin daya biya wa kansa kuɗin makaranta a ƴar buga-bugar da yake yi a kasuwa. Kallon sa yayi yace.
"To madallah Allah ya bada sa'a." Daga haka bai ƙara ba ya ɗauke kai yaci gaba da abin da yake yi. Godiya Khalid ya masa ya miƙe ya nufi cikin gidan don karɓar abincin daren sa.
Kai tsaye Kichen yaje ya duba inda Baba Laraba ke aje masa domin idan dai matan gidan ne zasu bashi abinci sai dai kar yaci. Cikin sa'a kuwa ya samu ta saka masa a wani ƙaramin flakes ta aje can lungu, don haka ya ɗauka ya wuce ɗakin da yake kwana ya zauna yaci.
★ Washe gari cikin farin ciki Khalid ya shirya ya fara zuwa makaranta sabo da zasu fara lectures, yaso yaje ya gano Kakarsa kafin a fara lectures ɗin amma bai samu dama ba don haka ya yanke hukuncin idan suka kammala zangon karatu na farko zai je ya duba su daga nan ya samo lambar da ake samun Mahaifiyarsa kafin ya samu damar zuwa can garin ya gano su ita da ƙanwarsa da ya san zuwa yanzu ta girma, wacce rabon daya ganta tun tana ƴar sheka uku.
______________
A can Gurjiya kuwa Baba Sahura ta ƙara ruɗewa da irin kuɗin da take samu da Nanah, don haka kullum take sake fitowa da sabon abin sana'a tana jibga mata ta mayar da yarinya kamar jaka bata da lokacin hutu. Ai kuwa ciki ƙan-ƙanen lokaci yarinya ta ƙara fita hayyacinta ta ƙara ramewa fiye da da, rashin samun wadatacciyar tsafta yasa farar fatarta tayi duhu. Gashin kanta da baya samun gyara tuni ya cukur-kuɗe kasancewarta mai cikar gashi kuma yana da ɗan ƙarfi, idan ka kalli Nanah sai ka zubar mata da tawayen tausayi domin ba zaka taɓa haɗa ta da Nanah dake samun gyara da kulawar data dace daga wurin Mahaifiyarta ba.
Ana haka ne kuma wata sabuwar rigima ta ɓullo daga wurin Inna Zulai Yayar Mahaifiyarta dake zaune a nan ita ma, garin irin kuɗin da Nanah ke tara ma Sahura da yanda ake fadar sa'ar yarinyar a wurin tallah yasa hassada ta kama Inna Zulai don haka tazo tace dole sai an bata ƴar ƴar'uwarta ta dawo hannunta don Sahura na ƙoƙarin kashe mata yarinya da wahala. Rikici sosai ya ɓarke tsakanin Inna Sahura da Inna Zulai don Inna Sahura tace babu wanda ya isa ya amshi yarinya a hannunta, tun da ba ita ta hana Inna Zulai daukarta a lokacin da Baba ta rasu ba. Sai yanzu da taga yarinya tana mata amfani shine baƙin ciki ya kama ta tazo ta tayar da rigima, to kuwa wallahi uban kuturu yayi kaɗan.
Kawu Basiru kuwa Matarsa ya goya ma baya kasancewar ita ce ke kula da gidan da sana'ar da take yi ɗin shi yasa baya mata musu, don haka aka nuna wa Inna Zulai fin ƙarfi aka hana ta ƴar.
Nanah kuwa baiwar Allah kuka tayi sosai ta roƙi Allah ya kawo mata ɗauki ya fitar da ita daga wannan tsaka mai wuyar da take cikinta.
Ana haka watan azumin Ramadan ya tsaya don haka ɗaukacin al'ummar musulmi ke farin ciki da zuwan watan lada, watan falala da gafara. Yayinda a ɓangaren Inna Sahura ke murna da zuwan watan samun kuɗinta sakamakon kayan sana'ar da take ƙara wa da kuma ciniki da yake ƙaruwa sosai fiye dana da. Kayan sana'ar safe data gama haɗawa sakamakon babu tabbacin za'a ga watan yau, dare suka bi suka dafa komai yayin da asuba ta tashi Nanah da ɗaya daga cikin yaranta suka fita ƙofar gida suna shelanta tallah. Dan da nan kuwa komai ya ƙare suka koma gida suma suka samu yi nasu sahur ɗin.
Gari na waye wa ta shirya ta shiga cikin garin Daura ta sayo su kayan haɗin jinja su baby mix's, Tiyara, dabino Suga da sauran kayan shan ruwa.
Haka da rana tsaka ta tashi Nanah ta kasa mata tallah tace ta zagaya kafin lokacin tallar yamma ya ƙarasa, tun dama can jikin Nanah baya son wahala ga azumi tana yi ga rana amma haka Sahura ta tura ta yawon tallah. Ai kuwa lokacin data dawo da ƙyar ta kawo kanta gida tana zuwa kuma ta zube zazzaɓi ya mata rijib.
Tashin hankalin Inna Sahura ba rashin lafiyar Nanah bane, a'a abincin data gama haɗa komai tana jiran yamma tayi Nanah ta ɗauka ta kai bakin titi kamar yanda aka saba shine damuwarta idan ta kwanta waye zai sayar mata dashi.
"Me nake gani haka ni Sahura, ai kuwa miƙewa zaki yi kisha magani ki ware ki ɗauki abincin nan ki sayar, don Wallahi babu mai ja min asara na dafa uban abinci kizo ki narke ba lafiya!." Inna Sahura ta faɗa tana ciro Naira hamsin a cikin lalitarta ta bawa Aliyu yaronta yaje ya sayo Paracetamol a bawa Nanah tasha ta miƙe kafin lokacin fita tallah.
Nanah na kwance a ɗakin Baba wanda suke kwana tare dasu Amina yaran Kawu Basiru Inna Sahura ta shigo ɗakin tana gyara ɗaurin zaninta wanda yayi baƙiƙƙirin da abin baƙin tukunya da abin gasara ne, kayan miya duka babu abinda babu a jiki.
"Tashi ƴar nan maza kizo kisha magani ki miƙe don ba zan yi asarar uban abincin dana ɗora ba. Ta faɗa tana miƙa mata kofin kunu data shigo mata dashi haɗi da magani. Cikin wahalar da take sha ta buɗe idonta da ƙyar tace.
"Baba azumi fa nake yi, kuma don Allah kiyi haƙuri yau ba zan iya zuwa tallah b..."
"Kamar ya ba zaki iya zuwa tallah ba? Uban wa kike so in ɗora ma wan can uban abincin dana dafa, wato kema baƙin cikin cinikin da kike min kike yi ko, to wallahi baki isa ba karya azumin zaki yi kisha magani tun da ba wajaba yayi a kan ki ba!." Inna Sahura ta tari numfashinta cike da masifa tana aje mata kofin kunun da magani ta kaɗa kai tayi gaba. Hawaye masu zafi na tausayin kanta ne suka zubo a saman kyakykyawar fuskarta, tana kallon Inna Sahura ta fice a ɗakin tana goranta mata a kan abincin da take bata da kuma kayan sallar da zata mata. Gab da zata ƙarasa ficewa ne ta jiyo muryarta tana faɗin.
"Idan kuma kika ce ba zaki min tallah ba sai dai ki tattara ki bar min gidana, in ma wurin Zulai ɗin zaki koma kije can ku ƙarata in dai Zulai ce babu abin da zata iya tsinana maki sab..." Bata ji ƙarshen abin da ta faɗa ba sakamakon ƙarasa ficewa da tayi a ɗakin. Kuka mai ƙarfi Nanah ta fashe dashi tana tunanin yan da rayuwa ta sake sauya mata da wata ƙaddarar mai cike da matsi da rashin mafita.
Bata son ta karya azuminta sabo da Mama tace idan ta san ba zata iya kai azumi ba kar ta ɗauka tun farko sabo da babu kyau karya azumi. Don haka ta lallaɓa ta miƙe ta fito tsakar gida tana kiran sunan Abdul Malik ƙaramin yaron Inna Sahura, saka shi tayi ya ɗebo mata ruwa a rijiya ya kai mata bayi tayi wanka ta ɗan samu ƙwarin jiki sannan ta shirya ta wuce wurin tallar cike da dauriya.
Dauriya sosai tayi wurin sayar da abincin har aka kira sallar magrib ta samu tasha ruwa kasancewar a can suke shan ruwa. Tana kammala shan ruwan ta riƙa kwara amai wanda ya galabaitar da ita sosai dole aka raka ta gida sai Safiya ce ta ƙarasa sayar mata da abincin da taimakon Amina.......