KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Ahmad bai tashi dawowa hayyacinsa ba saida ya iddasa komai ya gama samun nutsuwa, yana maida numfashi kamar wanda yayi tsere ya duqo gareta yana kallonta, amma sai komai nasa ya tsaya a take ganin Na'ima na wani irin jijjaga idanunta sun kafe, wani irin numfashi take fusga da kyar kamar ta shide qirjinta na wani irin hawa da sauqa...A firgice Ahmad ya dago ta yana fadin "Ya Allah.. Na'ima...Na'imaa" amma sai wani irin numfashi take kamar wadda ranta zai fita, a gigice ya sauqa daga gadon tareda daukan towel dinsa ya nufi falonsa da sauri ya dawo hannunsa da riqe da bottle water ya fara zuba mata ruwan a fuska, a tsorace yake fadin "Babe.... Na'ima...Look at me, Look at me" sai ta juyo da kanta tana kallonsa amma idanunta har sannan a kafe, dasauri ya kamo fuskanta yace "Breathe in..Breathe in pleaseee" dakyar ta gyada kai tareda bude bakinta taja numfashin dakyar, murya na rawa ya sake cewa "Breathe out, Breathe out again" nan ma ta fara qoqarin sake numfashin, tana damqe hannunsa dake cikin nata, haka ya kamota yana guiding nata yanda zata ja numfashin dan shine kadai solution a wannan lokacin, vividly gashinan Panic attack ta samu, haka ya rinqa mata har saida numfashinta ya fara daidai ta sannan ya miqe jiki na rawa ya dauki wayarsa dake bedside drawer sai kuma ya rasa me zeyi,  Hasbunallah...sai ya rasa ta ina zai fara ma, dan jinin da ya gani akan gadon ba qaramin firgitashi yayi ba, me ya ke faruwa ne? gashi shi ba likita ba balle ya san ta ina zai fara taimaka mata, da taimakon Allah anty Amnah tazo kansa nan yayi saurin buga mata kira yana kamo hannun Na'iman tareda damqewa tana jan numfashin da kyar, har zuciyarsa rawa take ganin yanda Na'ima ke kuka da numfashin a jejjere gashi Anty Amnah bata dauki waya ba sai yayi saurin nufan closet dinsa ya dawo hannunsa da wata babbar T-shirt dinsa ya fara dago Na'iman zai saka mata kawai tayi qara tana jijjaga kai a galabaice, da sauri ya ya maida ita ya kwantar yanajin da da hali shima kukan zeyi ganinta a galabaicen, kawai ya fara fadin "I'm sorry, kiyi hakuri, I'm sorry Na'eemah" kawai hakuri yake ta bata tana numfashin nan kuma Kiran Anty Amnah ya shigo wayan tasa yayi saurin dauka, kafin tace komai yace "I need your help" daga can Anty Amnah tace "Meya faru son?" A dan gigice ya fara magana "Na'eemah...tana numfashi da kyar...and i...i.." dasauri tace "Ahmad ka nutsu kaji, nutsu ka fadamin me ya sameta" ya shafa fuskansa a hargitse yace "Numfashinta yana breaking, please kizo yanzu, i need you" da sauri tace "i'm coming" da haka ya kashe wayan ya sake maida hankali gurin Na'ima da zuwa yanzu ta fara samun daidaiton numfashin sai kuka kuma da takeyi kamar ranta zai fita, ya duqa zai sake dago ta dan saka mata rigan sai ta turasa baya da dan sauran karfinta da ya rage, murya a shake tace "ka fita" cikin lallashi yace "Please ki bari in saka miki" ta kulle idonta tana numfashin a rarrabe tace "Banaso..ka fita" sai ta sake fashewa d wani kukan me karfi, kawai Ahmad ya hau gadon hankalinsa a tashe ya tsugunna kusa da itan tareda  kamo hannunta, ganin batace komai ba ya sashi samun kwarin gwiwan rungumota yana shafa bayanta, sunfi minti goma akan gadon tana wannan numfashin wani kiran daga security ya shigo wayan Ahmad ya miqa hannu ya dauka kafin suce komai yace "just let her in" ya kashe wayan tareda sauqa daga gadon ya sake komawa closet dinsa bai dade ba ya fito sanye da jallabiya sai ya qaraso gurin Na'ima ya fara gyara mata blanket din jikinta tana ta sauqe numfashi, da haka ya fita da sauri ya qarasa downstairs ya bude kofan, shigowa Anty Amnah tayi da sauri tace "Ina take?" yace "tana dakina" sai ta wucesa da saurinta ta nufi stairs riqe da babban jaka a hannunta shima ya rufa mata baya, shigansu dakin nasa Anty Amnah tayi sauri qarasawa gadon tana kiran sunan Na'iman, ganin yanda take kwantar numfashi da kyar itama sai da ta fara guiding dinta tayi numfashin sannan tayi saurin saka mata breather a hancinta tana matsa abun a nutse, Ahmad na tsaye yana kallonsu jiki babu qwari sai Anty Amnah ta kallesa tace "Bani ruwa, mai sanyi kuma" ya gyada kai ya fita, juyawa Anty Amnah tayi ta kalli Na'iman tace "Yauwa daughter, keep breathing" sai Na'ima ta ja numfashin sosai Anty tace "There....yauwa toh sakeshi a hankali" sai Na'ima ta sake numfashin asannu tana sake jan wanin Anty Amnah na guiding dinta, Ahmad ne yadawo hannunsa da ruwan sai Anty Amnah ta karba ta ajiye a gefenta sannan ta sake focusing kanta gurin Na'iman har sai da taga numfashin ya daidaita sannan ta cire mata breather din, kulle ido Na'ima tayi hawaye na fita daga idonta sai Anty Amnah ta bude ruwa ta miqo mata bakinta da nufin tasha, tana sha din Anty Amnah ta kalli Ahmad again tace "kawo mata riga ta saka, nan ma ya duqa ya miqa mata tashi dake yashe a qasan dakin ta karba ta fara kokarin sakawa Na'iman sai kuma taga taqi motsawa daga kwancen da take, dan sake kamota tayi sai Na'ima tayi stiff tana hawayen taqi barin position dinda take, sai Anty Amnah tafara dubanta dakyau, ahankali tace "Gyarawa zakiyi in saka miki rigan kinji" sai Na'ima ta fashe da kuka ta fara girgiza kai, nan kuma Anty Amnah ta fara yaye mata bargon tana duban ko wani abunne ya sameta a jikintan, Ahmad na ganin ta fara bude duvet din jikin Na'iman ya juya ya fice daga dakin, jiki babu qwari ya fita daga part din nasa gaba daya sai ya nufi kitchen din downstair direct ya bude fridge ya dauki bottle water, shan ruwan kawai yake a tsaye jikin kitchen island din amma kwata kwata baya cikin nutsuwarsa, sai kallon kofan kitchen din yake tunani iri iri aransa...Anty was more than shock da abunda ta gani a gadon, nan take ta maida bargon ta rufe Na'iman while ita kuma ta qara qarfin kukanta tana duqar da kai, cike da rarrashi Anty Amnah tace "Na'ima" kasa amsawa Na'iman tayi sai ta sake cewa "Daughter" nan ma kawai dan dagowa tayi ta kalli Antyn sai tace mata "Is this your first?" ahankali Na'ima ta gyada kai tana sauke idonta, sai Anty Amnah tace "Meya faru? Bakiyi ba a auren ki na baya?" murya a shaqe Na'ima tace "Ban taba yin wannan ba" sai kuma ta fashe da wani kukan tuna azaban da taji dazun, da sauri Anty Amnah takai hannunta baki cikin mamaki, sai kuma ta kamo hannun Na'iman ahankali tace "It's going to be alright kinji, bari nazo yanzunnan" sai Na'ima ta gyada kai kawai har sannan ta kasa kallonta, da haka Anty Amnah ta miqe ta fita daga dakin, ganin babu Ahmad a falon yasa ta sauqa qasa ranta a dan bace, nan ma bata gansa ba ta kwala kiran sunan sa, sai tajiyo takunsa daga corridor'n ya fito yana kallonta, rai abace tace "She had panic attack, you could've killed her Ahmad" ahankali yace "I'm sorry please" tace "Kuma kasan matarka virgin ce, kaje mata da wannan qarfin Ahmad, what were you even thinking?" 
Qamewa Ahmad yayi a gurin atake ya shiga shock yana kallon Antyn tasa, itama tana kallonsa tace "Don't look at me like that, kana nufin baka sani ba kome?" har sannan ya kasa magana, ganin yanda ya shiga shock din yasa Antyn cewa "Muje kitchen kabani gishiri, sannan kazo mukaita asibiti yanzun nan, numfashinta bai gama tsayuwa ba kuma sai na dubata" sai sannan ya bude baki a hankali yace "Anty Bansani ba" tace "Toh amsanka yana gurin matarka, muje ka bani abunda nake nema yanzun ka tayani mukaita asibitin" da haka ta nufi kitchen din yabi bayanta a jikinsa sanyi qalau, da suka koma dakinsa sai ya rinqa kallon Na'iman kamar wanda yau yafara ganinta, yama rasa me yakeji a wannan lokacin game da ita, Anty Amnah tace masa "Zo ka daukamin ita muje toilet" sai ya tako jiki babu laka ya fara nannade Na'iman cikin duvet din yana kokarin daukanta, Na'ima ta damqe idonta har ya dauketan ya wuce da ita toilet din Anty Amnah na biye dasu a baya, bai sauqeta ba har sai da Anty Amnah ta hada mata ruwan mai dumin daya kamata sannan ta tace ya saka ta cikin bath din a haka kar ya cire duvet din, hakan ya saka ta dan dama beyi nufin ya cire mata duvet din ba tun farko, aikuwa tsam Na'ima ta miqe tsaye jikinta na rawa ta dafasa, kuka take tana girgiza kai jin yanda ruwan ya shigeta, Ahmad ba kunya ya rugumeta da sauri sai ya kalli Anty ahankali yace "Anty sai ta shiga ne?, it's hurting her" Anty Amnah ta banka masa harara tace "fita daga toilet dinnan, kaida kayin bakasan it'll hurt her ba sai ni da zan mata maganin, zo ka ficemin daga bandakin nan" da haka ta riqo Na'iman tace "Daughter this is the only way da zaki samu sauqi kinji, i promise zaki daina Jin zafin once kika samu seconds aciki kinji" sai Na'ima ta gyada, har sannan Ahmad ya kasa saketa sai Anty tace "Ka saketa ka bamu guri" sai ya sake jikin Na'iman ya juya ya fita cikin sanyin jiki, haka Na'ima ta shiga ruwan nan duk yanda takejinsa ajikinta Anty na taimaka mata har sai da ta samu sauqin radadin da takejin, wani irin haushin kanta ma takeji da ta yarda Ahmad ya mata hakan tun farko, tunaninta daya a wannan lokacin shine kuma anyi na farko anyi na qarshe.....
Fitowan su daga toilet suka samu Ahmad ya dauko mata wata doguwar rigan da hijab harda lingeries daga can dakinta, nan Anty Amnah ta zaunar da ita a bakin gadon tana dingisawa ahankali sai ta taimaka mata ta saka su har lokacin kuma bata bar hawaye ba, saida ta gama kintsawan sannan Anty tace su tafi Asibitin, aikuwa Ahmad ya duqo ya sake daukar abarsa suka fita gaba dayansa tana jikinsa, a back seat na motarsa ya kwantar da ita sannan Anty Amnah ta shiga itama sai ya zagaya shi ya shiga gaban suka tafi ahakan, a asibitin ma Na'ima na dinqisawa ya nemi daukanta tayi saurin kwacewa sai Anty Amnah ta riqeta suka shiga ahakan yana biye dasu, nan office din Anty Amnah ta kwantar da Na'iman, ta juya ta kalli Ahmad dake tsaye ya musu baqe baqe, sai taji dariya na zuwa mata kawai tayi murmushi tace "Kadan bamu guri son in dubata" sai ya gyada kai ya fitan, Anty Amnah na tsaye akanta tace "daughter kin taba samu matsalan numfashin ne abaya" Na'ima ta bude idonta dake rufe tana tuno bayan da yanda take samun shigen hakan amma ba wai yakai wannan din ba, share hawayenta tayi ahankali tace "be kai haka ba" sai Anty Amnah tace "Sannu kinji, in sha Allah ze daina, bari na duba miki ciwon yanzu" sai Na'ima ta damqe idonta cike da kunya ganin abunda Antyn ke shirin yi, aikuwa Na'ima tasha kuka jin yanda anty Amnah ke hade gurin da allurai alamun dinki ake mata ma, gashi bawai an kashe gurin bane gaba daya, wiwi ta rinqa kuka tanajin haushin Ahmad kamar da duk abunda ya shafesa, Anty Amnah sai tausanta take tana fada mata saita mata hakan zata samu lafiya, sai da ta tabbatar ta mata abunda ya kamata sannan ta kira nurses suka dauketa a wani gadon suka fice da ita tana bin bayansu, a bakin office suka ga Ahmad har sannan yana tsaye, ganinsu yasashi tahowa sai Na'ima ta rufe idonta dan batason ganinsa ma, sai da ta samu nutsuwa a dakin hutun sannan Anty Amnah ta mata alluran da ya kamata tareda qarin ruwa duk Ahmad na zaune a kujerar jikin gadon, Na'ima kuwa ta rufe ido har sannan, Anty Amnah na kallonsa tace "Bari ta samu baccin yanzu nima bari naje nayi sallah sai in dubo ko yarinyar can ta tashi itama" gyada kai Ahmad yayi shima ya miqe zai shiga nan toilet din dake dakin dan yin alwala.....Anty Amnah bata tashi zuwa dakin da Lailan ke kwance ba saida tayi sallah sannan ta fita daga office dinta zuwa can, shiganta ta samu su Mummy Murja da Ummi ne suke zazzaune a jikin gadon Lailan sannan Mamma, Anty da Fatima kuma suna zaune a waiting lounge na dakin, Mummy na ganinta tace "Amnah dazu murja taje duboki baki dauki kira ba kuma bakya nan, naga kamar numfashin nata har yanzu yana mata nauyi wani lokacin" sai Anty Amnah ta qaraso bakin gadon tana duban Lailan tace "Da hakan zai daidaita in sha Allah, sai ahankali daman" sai da tagama monitoring Lailan sannan ta nufi gun su Mamma dake zaune a sofas masu laushi na dakin, zama tayi sannan suka fara gaisawa, Mamma tace "sannu Amnah, ya hidima" tace "Alhamdulillah" da haka ta jawo food flask dinda suka taho dashi din ta zuba abinci a plate tafara ci a nutse, Mummy ce ta tambayeta "Su Ahmad sun dawo ne, akwai maganin da nake so ya karbo mata tasha, mun aika pharmacyn ku na cikin asibitin wai ya qare" hankali kwance Anty Amnah takai spoon din abincinta baki tace "Ahmad na gurin matarsa shima, just few rooms away" duk mutanen dakin suka kalleta idonta na kan plate dinta, Anty tace "Meya faru kuma?" sai ta ajiye plate din ta dago tana kallonsu da murmushi a fuskarta tace "Ashe matarsa budurwa ce tun fil azal ba'a sani ba" sai kowa yayi stiff adakin sai Mummy tace "Amnah bansan yaushe kika koma babbar maqaryaciya ba yanzu" rai abace Amnah tace "Meyasa zan muku qaryan, wani abun zai qara min ne ko wani abun zaku bani, kinga kidaina fadamin duk maganan da tazo bakinki banason haka" jiki na tsuma Mummy tace "to in ba qaryan kike ba tayaya matar da ta shekara kusan shida a gidan wani zakice wai ta kasance budurwa, shi tsohon mijin nata mahaukaci ne ko me?" anty Amnah tace "Wannan kuma mun barwa Allah sani, amma kinganni nan da hannuna na dinketa yanzu a asibitin nan, can gidansu naje da kuka aika ba'a samenin ba dazu, kinsan dai kuma nasan aikina ko?" Anty tafara tafa hannu da mamaki tace "Wannan yarinya dai cike take da abubuwan al'ajabi" Anty Amnah na murmushi tace "ikon Allah ba" Murja dasu Ummi babu bakin magana dan sunsan halin Anty Amnah na rashin daukan raini, Laila kam daskarewa tayi azaune kan gadon, wani irin tururi ke taso mata tun daga qasan zuciyarta, miqewa Mamma tayi duk suka kalleta sai ta ce da Amnah "Inane dakin" sai Anty Amnah ta miqe itama tace "Muje in kaiku" da haka su Fatima da Antyn suka miqe suka bi bayansu, nan Laila ta fashe da wani kukan me qarfi sai Mummy da murja sukayi saurin kamo hannunta dan sun rasa ma me zasu ce.....shigansu dakin suka samu Ahmad na duqe daf da Na'iman kamar me fada mata wani abun, ita kuma ta dan juya kanta idanunta a rufe, jin shigowar mutane yasa shi dagowa yana kallon bakin kofan sai ya miqe idonsa a duqe ya kasa kallon Mamma da ta shigo, qarasowa sukayi idonsu na kan Na'iman da kana ganinta kasan ba lafiya, ga fuskan ta nan tayi ja kuma alamun kukan da tasha, Anty ce ta fara fadin "sannu Na'ima" jin muryansu yasa taji kamar qasa ta tsage ta shige sai tayi luf kamar me bacci a juyen, Anty Amnah ta qarasa tana kallonta, sanin ba bacci take ba sai kawai tayi murmushi tace "ai inaga tayi bacci ma" anutse Ahmad ya nufi kofa zai fita duk suna kallonsa, sai Fatima tace "Ina wuni Yaya" kansa a gaba ya amsa da "Lafiya" kawai ya fice, bin bayansa Anty Amnah tayi ta fitan dan tanason ta kira Mami itama....