KOMAI TSANANI

17

by @oumfatima33

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    *KOMAI TSANANI* 

             *By*

         *KANSA'U* *BELLO* 
    
   *(OUM FATIMA)* 
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


   *PAGE 017* 


 *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*





        Sai dai bayan barin Mamu ƙasar sai Alhaji Bala yayi duk yan da yayi ya karɓe kuɗin hannun Mama da sunan shi zai ci gaba da kulawa da amanar ɗan'uwansa, kuma a matsayinta na Mace bai kamata ta riƙe kuɗi masu yawa irin wannan ba sabo da za'a iya shigowa a kashe su a kwashe kuɗin a banza. Da wannan daɗin bakin ya amshe kuɗi yaje yayi abin da yaga dama dasu, sai dai idan tana buƙata ta kira shi ta tambaye shi sai ya bata ɗan abin da bai taka kara ya karya ba.

   Kayan abincin ma bai bar mata ba haka ya rika ɗauka yana kaiwa gidansa duk da cewa yafi ƙarfinsu amma haɗama irin tasa ya kasa ɗauke ido a kan su. Kafin kwana arba'in rayuwar Mama da yaranta ta fara sauya wa, domin kuwa abinci ya ƙare gashi yanzu ko ta tambayi Alhaji Bala kuɗi sai ya kawo mata uzurin cewar babu ciniki yanzu a kasuwa waye waye da sauransu ya ɗauki dubu ɗaya ko biyu ya bata, rayuwa ta fara musu tsanani har abinda zasu ci yazo ya fara gagararsu, tuni aka koro Khalid daga makarantar da yake yi sabo da rashin biyan kuɗin makaranta. Koda ta samu Alhaji Bala da maganar faɗa ya rufe ta dashi kan cewar bata da godiyar Allah, ganin da Mama tayi cewa idan taci gaba da zama a haka zasu cutu ita da yaranta yasa ta yanke shawarar komawa gidan Iyayenta.

   Hakan yasa taje ta samu Alhaji Bala da maganar inda ya nuna amincewarsa a kan hakan yace bai kamata dama taci gaba da zama ita kaɗai ba tun da tana da ƙuruciyarta, sai dai koda ta masa maganar gadon yara sai ya rufe ido ya nuna sam shine ya dace ya kula musu da dukiyarsu, don haka ma ba zata tafi da Khalid ba zata barshi a hannunsa yaci gaba da karatunsa. Babu yanda ta iya haka ta bar Khalid ta ɗauki Nanah ta tafi da ita, taso ace sun haɗu da Mamu kafin ta tafi amma sai dai shiru har yanzu Mamu bata dawo ba. A bakin Iyalan Alhaji Bala take jin cewar Mamu ta wuce Umara zata huta a can ba yanzu zata dawo ba.

   Haka ta tafi ta bar Khalid da gadonsu a hannun Alhaji Bala ba don taji gamuwar zasu kasance cikin aminci ba, sai don ta san koda ta tayar da rigima bata da mai tsaya mata. Bata da Mahaifi sai Mahaifiya ita kuma ta tsufa sosai babu abinda zata iya, sai ƴan'uwa guda biyu Namiji da Mace suma babu abin da zasu iya mata domin babu mai ƙarfi a cikinsu. Sai waɗan da suke ƴan'uba wan da basa wani shiri sosai daman, kuma koda ace ta karɓi gadon nasu ta tafi dashi a can ɗin ba tsira zai yi ba a hannun ɗan'uwanta da baya sana'ar komai sai zaman kashe wando ya sakar wa Matarsa ragamar kula da gidansa. Wannan yasa bata da wani zaɓin dole ta haƙura ta bar wa Alhaji Bala da tunanin duk lokacin da Khalid ya girma ya mallaki hankalinsa zai karɓe haƙkinsu dake hannun wan mahaifinsu.

 

***** Ta koma gidansu tare da marainiyar ƴarta cike da kewar babban ɗanta da kuma Mahaifinsu da baya raye, da farko ƴanuwanta sun karɓeta hannu biyu suna kyautata mata. Sai dai zaman bai je ko ina ba suka fara gajiya wa da ita, ganin zaman ba zai mata ba yasa ta fara ƴar sana'ar ƙulla kayan miya tana sayar wa a cikin gidan. Ɗan abin da ta samu take haɗawa tana sama musu abinci ita da Mahaifiyarta da ƴarta. Lokacin data kammala takabarta ne ɗan'uwan Mahaifiyarta dake Cigama ya kawo musu ziyara, koda ya samu labarin mutuwar Mijinta ya mata gaisuwa. Sai dai a nan take yayi tunanin damar mallakar ta ta sake dawo masa a karo na biyu sakamakon ya sota tun tana budurwa, bai yi ƙasa a gwiwa ba ya shaida wa Baba Mahaifiyarta da Yayanta Basiru yana son aurenta idan ta amince.

   Ƙin amincewa tayi sabo da bata son sa, sannan ko ba wannan ba bata shirya sake wani auren ba a halin yanzu. Sai dai Alhaji Zubairu bai tsagaita ba sai da ya san yanda yayi ya saye zuciyar Baba data ƴan'uwanta yasa suka tursasata ta aure shi da daɗin bakin zai kula da Nanah tamkar ƴar daya haifa a cikinsa, cewa yayi har Khalid ɗin ma idan tana so ta ɗauko sa zai haɗa ya riƙe mata amana. 

   An yi auren ba don tana so ba sai don tayi wa Mahaifiyarta biyayya a wannan karon, don haka aka ɗaura aure bayan sati ɗaya suka wuce tare da Nanah da rakiyar ƴar'uwarta.

  Wannan ne silar zuwan Mama da Nanah garin Cigama da duk abinda ya faru a can...


***** A ɓangaren Mamu kuwa koda ta kammala hutunta ta dawo gida, Alhaji Ridwan ya shawo kanta ta yarda zata koma Abuja da zama domin aci gaba da kula da lafiyarta a can kamar yan da Doctor ya bayar da shawara. Sai dai ta dawo gida domin taga halin da su Mama ke ciki kuma a samu matsaya a kan in da zasu ci gaba da zama don kula da amanar ɗanta. Sai dai koda ta dawo ta tarar bata nan ta tambayi Alhaji Bala sai ya sanar da ita cewa tace ba zata iya zama ba ta tafi gidansu sabo da aure zata yi, ta tafi da Nanah amma Khalid yana hannunsa kuma zai riƙe sa amana kamar ɗan daya haifa da cikinsa. Ta ji babu daɗi a kan tafiyar Mama sai dai kuma idan an duba itama tana da gaskiya don ba wuce auren tayi ba sannan kuma ta gamsu da bayanin Alhaji Bala na riƙe Khalid domin shike da haƙƙin yin hakan. Da wannan Mamu ta tattara ta koma Abuja da zama cikin MAI ƘUSA MAIMSION mallakin ɗanta, inda aka ware mata ɓangarenta da ban aka zuba mata komai na jin daɗin rayuwa.

***** Ran Inno yayi matuƙar ɓaci da dawowar Mamu cikin mai ƙusa mansion, domin ada ita ce ita ce ke juya gidan. Yanzu da asalin Uwar mai gidan ta dawo da zama sai kishi ya ƙara kamata bayan kishin dake tsakaninsu na tun can. Abu na biyu dake ɗaga mata hankali shine kar Alhaji Muhammad mijinta da a yanzu ake kira da (Alhaji Baba) yayi tunanin mayar da aurensu idan yana ganinta a kusa tun da yanzu bata da aure. Haka tana ji tana gani Mamu ta dawo rayuwa a cikinsu a karo na biyu da matsayi mai girma, domin kuwa irin gyaran da aka yiwa ɓangarenta kaɗai ya isa ya shaida wa mutum matsayin wacce zata zauna....

 *Wannan kenan, yanzu* *zamu koma ainahin* *labarin wanda a ciki zaku ƙarasa fahimtar duk abinda ya shige muku duhu....*



   Yau ta kasance ranar da mutanen gidan Alhaji Bala zasu wuce Abuja domin halartar bikin ƴar Dadyn Abuja da za'a yi, gaba ɗaya kowa yana cikin farin ciki sabo da suna son zuwa gidan Dadyn Abuja domin gidan ya haɗu ba kaɗan ba. Sannan kuma kowa abin da yaga dama yake yi a gidan, a ɓangaren ƴanmatan kuwa suna murna ne sabo da zaratan samarin yaran Dadyn Abuja da suke da matuƙar kyau da kwarjini, uwa Uba kuma suna da ƴaƴan banki wanda sune suka fi ruɗar ƴanmatan zamanin nan, musamman babban ɗansa Muhammad wan da yaran gidan suke kira da Boss don a halin yanzu ya gawurta a harkar kasuwanci da manyan mutane daga ƙasashe da sassan Nigeria. Kuma shine wanda Yusrah ta mato a kan sa.

   Kasancewar gaɓa ɗaya gidan zasu wuce yasa Alhaji Bala yace da Nanah ta shirya itama a tafi da ita domin ba su yiwu ba a barta ita kaɗai a gidan, Khalid da wasu daga cikin samarin su sai ya gobe ɗaurin aure zasu tafi sabo da akwai masu jarabawa a makaranta. Khalid yayi ƙoƙari ya ɗinka ma Nanah sababbin kaya kala biyu bayan guda ɗaya da Abba ya musu gaba ɗaya ita da yaran, wannan yasa bata da matsalar kayan da zata saka duk da dai su Nawal na nuna mata cewar bata isa ta shiga cikinsu ba sai dai ta bisu a matsayin mai yi musu hidima.

   Tafiyar safe suka yi kasancewar tafiyar Mota ce, motar Alhaji ita matan gidan suka shiga da wasu daga cikin yaran. Sai wacce ake kai yara makaranta wacce su Nanah ke ciki da driver na jansu, sun tafi cikin farin ciki saɓanin Nanah da jikinta ke a sanyaye sabo da yan da suke tsangamarta da kuma tunanin kalar tarbar da zata samu a can ɗin don ta gama camfa kanta akan cewar duk gidan da zata je sai mutaten gidan sun tsane ta.


   ***** Bayan doguwar tafiyar da suka yi sun isa garin Abuja cikin aminci in da kai tsaye suka nufi babbar unguwar da a can ne mai ƙusa mansion yake mallakin Alhaji Ridwan Muhammad Ali mai ƙusa shararren ɗan kasuwar daya shahara a harkar shigo da ƙarafuna da sarrafa su. Tun da suka shiga garin Nanah ta buɗe ido tana kallon sabuwar duniyar da bata taɓa ganinta a zahiri ba sai a cikin kallo take gani. Sosai ta buɗe ido tana kashe ƙwarƙwatar idonta, yayin da su Nihal ke taɓo juna suna nuna ta sai su ƙyal-ƙyale da dariya.

   "Yau fa ba sabon ba ƙatuwar ƙauye ta shigo Abuja an sake baki da hanci ana ta zuba ƙauyanci." Cewar Mabaruka tana kwashe wa da dariya. Kallon in da take Yusrah tayi ta taɓe baki tace.

   "Saura muje gidan kije kiyi ta wannan shegen ƙauyancin naki ki zubar mana da Class a wurin Classic babes ɗin dake gidan." Ta ƙare maganar tana maka mata harara.

   "Kema Sis ai bata isa ta shiga cikinmu ba bace bare ta samu damar zubar mana da Class ɗin, ai bata wuce matsayin mai mana aiki ba." Cewar Mabaruka cikin isa da tinƙaho. Dariya su Nawal suka riƙa mata suna nuna ta wan da hakan yasa ta tsargu sosai tayi tsamo a cikinsu tamkar marayan ɗan tsako a cikin masu Uwa.
 
   A haka suka ƙaraso ainahin unguwar da mai ƙusa mansion yake wacce tun daga tsaron dake bakin gate ɗin shiga unguwar kaɗai ya isa ya shaida maka cewar ba ƙananan mutane bane ke rayuwa a cikinta. Shimfiɗaɗɗiyar kwalta ce wacce take a tsaftace tamkar babu mai takawa ta mamaye illahirin street ɗin, manya manyan gidaje ne irin waɗan da Nanah bata taɓa gani ba ko a mafarki. Kai ita fa ba don taji suna cewa a cikin Nigeria Abujan take ba to da sai tace wata ƙasar ce suka je sabo da kyawuda tsaruwar garin.

    Daidai bakin wani tafkeken gate suka tsaya wan da security ke tsaron sa.

 *MAI ƘUSA* *MANSION.* Shine sunan da aka rubuta a jikin wani kyakykyawan bord da wani kalar rubutu tamkar da ruwan zinare aka yi shi sabo da yanda yake ɗaukar ido. Kasancewar securities ɗin sun san motocin Alhaji Bala yasa aka barsu suka wuce kai tsaye.

   "Alhamdulillah Allah kasa da my Bobo zan fara yin tozali." Mabaruka ta faɗa tana lumshe ido haɗi da rungume hannayenta a ƙirji......


 Barkammu da dare da fatan kowa yayi weekend lafiya, ayi haƙuri da wannan ba yawa bana jin daɗi ne ina fama da mura. Waɗan da suka tun-tuɓe ni a Facebook da Whatsapp don jin ko lafiya ina godiya sosai Alhaji ya bar zumunci.