KOMAI TSANANI

18

by @oumfatima33

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    *KOMAI TSANANI* 

             *By*

         *KANSA'U* *BELLO* 
    
   *(OUM FATIMA)* 
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


   *PAGE 018* 


 *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*



     "Ki dai bi a hankali don kin san Ya Ammar shima baya son rawar kai don shida Boss ɗin duk kanwar ja ce wurin tsare gida." Nawal dake kusa da ita ta faɗa.

   "Uban wa ya kasa dake da zaki ɗauka ƴar baƙin ciki?." Mabaruka ta faɗa tana kai ma Nawal duka, cikin sauri Nawal ta kauce tana murguɗa mata baki da cewar.

   "Allah ba zaki dake ni ba, ai gaskiya na faɗa keda Ya Yusrah duk ƴan wahala ne gara ma tun wuri ku kama kan ku don ban ga alamar zaku samu shiga a in da kuka ƙwallafa ran ba." Bata ƙarasa faɗar abin da tayi niya ba Yusrah ta kai ma bakinta duka, dai-dai lokacin da motocin suka tsaya a in da ake ajiye motoci. Sai da Nawal ta tabbatar ta fita daga motar kafin tace.

   "Na faɗa ɗin wahalar banza kuke yi, kuma Allah ya isa ban yafe dukan da kika yi min ba." Tana kammala faɗa ta ruga da gudu wurin motar su Abba da suka fito suma.

    "Toh!! Toh!!! Sarkin tsokana wa kika tsokano kike gudu haka?." Abba ya faɗa yana kallon Nawal.

    "To ba Ya Yusrah bace zata dake ni." Ta faɗa tana tura baki cike da taɓara irin ta yaran da ba'a kwaɓa.

    "A kan me zata dake ki, ita waye ya dake ta?." Abba ya faɗa yana riƙe hannun Nawal ɗin dake ƙara narke wa, dai-dai lokacin Yusrah ta ƙaraso a fusace tana son kai wa Nawal duka Abba ya dakatar da ita.

   "To Abba kace ta fita a sabgata." Yusrah ta faɗa tana ɓata rai.

   "Shike nan naji zan mata magana." Abba ya faɗa dai-dai lokacin da ma'aikatan dake tsaron second gate suka ƙaraso suka fara ɗibar kayansu zuwa ɓangaren Mamu dake ta dama, gaba ɗayansu can suka nufa domin idan sun zo a can suke sauka dama. Da fara'a Mamu ta tare su tana musu maraba lale yayinda yaran ke zuwa ɗaya bayan ɗaya suna rungume ta, Nanah dake gefe a raɓe riƙe da ƙaramar jakar Mumy Mamu ta zuba ma ido. 

   "Wa nake gani haka da fuskar Khamis?." Ta faɗa tana tsare ta da kallo.

   "Murmushi Abba yayi cike da son gwaninta yace.

   "Mai sunan ki ce Maryama, ai ita Uwar ta maidota gidana yanzu duk su biyun nake riƙewa." Ya ƙare maganar yana sakin murmushi tamkar wan da yake riƙe ta tsakani da Allah.

   "Masha Allah takwara ta ta girma, amma shine ka kasa sanar dani Balarabe?." Mamu ta faɗa tana kallon Abba. Sosa ƙeya yayi yace.

   "Kiyi haƙuri Mamu dama bari nayi idan muka zo sai ki ganta." Bata bashi amsa ba sai Nanah da take kallo wacce ta fahimci cewa a ɗarare take ta kasa sake jikinta tamkar sauran yaran da wasu tuni sun wuce ɗakin da suke sauka idan sun zo.

    "Zo nan takwara." Ta faɗa tana miƙa mata hannu. A hankali ta shiga takawa zuwa gaban Mamu ta tsuguna ta shiga gaisheta ta, da fara'a sosai Mamu ta amsa ta kamata ta zaunar da ita kusa da ita sannan ta ɗago suka gaisa dasu Mamy kafin ta saka mai aikinta ta nuna musu ɗakunan da kowa zai shiga ya samu ya watsa ruwa suyi salla kafin su fito cin abinci. Zaune kawai Nanah tayi ta kasa bin kowa a cikin yaran har Mamu ta fahimci hakan, don haka da kanta ta kama hannunta suka haura sama inda bedroom ɗinta yake. Suna tafiya Mamu ke mata tambayoyi tana amsa mata.

   Koda suka shiga sosai Nanah ta tsaya kallon ɗakin sabo da yanda ya tsaru tamkar ba na tsohuwa ba, bayi Mamu ta nuna mata tace.

   "Shiga kiyi wanka ki fito kiyi sallah kafin a kammala shirya maku abinci."

   "To." Kawai ta faɗa tana wuce wa in da aka nuna mata, da kallo Mamu ta bita tana jin soyayyar yarinyar a cikin zuciyarta. Yayin da kewar rashin ɗanta ke dawo mata sabuwa, a kallo ɗaya ta fahimci yarinyar bata cikin wal-wala sannan kuma bata da sake wa kamar mai jin tsoro mutane.

   Nanah kuwa koda ta shiga bathroom ɗin Mamu kasa taɓa komai tayi sabo da bata san yanda ake amfani da abubuwan ba, don haka ta fito jiki a sanyaye ta kasa magana.

    "Ya aka yine takwara... Me yasa baki yi wankan ba?." Mamu ta tambaye ta, duƙar da kai tayi tace.

    "Dama bucket nake nema zan ɗibo ruwan wankan." Murmushi Mamu tayi don yanzu ta fahimci abin da ya hana ta yin wankan, don haka ta miƙe ta kama hannunta zuwa bathroom ɗin ta haɗa mata komai ta kuma nuna mata yan da zata yi amfani da shi. Kasancewar tana da sharp brain yasa ta ɗauke komai nan take don haka tayi wanka da alwala ta fito.

   Nihal ta samu zaune a saman bed side loca inda ta bita da kallon ƙurulla tana taɓe baki tace.

   "Eh lallai ƴar ƙauye an samu shiga a wurin Mamu, har da yin wanka a bathroom ɗinta lallai kam!." A kunnen Mamu da shigowarta kenan magan-ganun Nihal ɗin suka sauka.

    "Me yasa kike irin haka ne Nihal ba ƴar'iwarki bace kike hantarta, kar na sake ji." Ta faɗa fuska a haɗe kasancewarta tsayayyar Mace da bata ɗaukar raini a wurin jikoki. Baki ta zumɓura ta miƙe ta fice a ɗakin.

   "Ja'irar yarinya gaba ɗaya su Zuhura sun saki yara ba kwaɓa suna rashin mutunci, to ni ba zan ɗauki rashin kunyarku ba ubanku zaku ci." Mamu ke wannan mitar kafin ta kalli Nanah dake tsaye tace.

   "Wuce kije ki ɗauko kayanki ki shirya ki fita cin abinci." 

   "To." Ta faɗa tana gyara hijabinta ta sauka ƙasa zuwa ɗakin da taga an shigar da jakun-kunansu, ɗaki biyu ne aka bawa yaran su Nihal, Nawal, Maimoon, Salma da Nanah aka basu nasu da ban. Sai na ƴanmatan Yusrah da Mabaruka nasu da ban suma, Iyayensu ma kowa da nata ɗakin don akwai wadatar ɗakuna a ɓangaren.

   Tana shiga ɗakin duk suka zubo mata ido suna kallonta da alama Nihal ta sanar dasu abin da ya faru a ɗakin Mamu, tana jin suna faɗa mata baƙar magana amma taƙi kulasu ta nufi in da jakarta take ta ɗauka ta fice a ɗakin.

   "Daga can kar ki dawo don bama buƙatar haɗa ɗaki ɗaya dake." Salman ta faɗa tana harararta, bata ko kalli in da take ba tayi tafiyarta don itama ba buƙatar zama a cikin sun take yi ba. Tana zuwa ta ɗauki doguwar rigar wani material irin mai mayafin nan ta saka ta shiga rama sallolin da suka same su a hanya kafin tayi zaman addu'a.


***** Ƙarfe 8:00pm kowa ya hallara a dinning don yin dinner tare, a nan ne Mamu take tambayar Abba a kan Nanah yana bata amsa. Bayan sun kammala kowa ya shige ya kwanta sabo da akwai gajiyar tafiya a jikinsu, sai dai wasu daga cikin ƴanmatan duk sun shiga cikin gidan musamman ɓangaren Alhaji Ridwan in da a can ne amaryar take. Nanah kuwa a ɗakin Mamu tayi kwanciyarta hankali kwance babu mai zaginta ko yi mata gori.


★ Washe gari....

 Washe gari bayan kowa ya tashi ya shirya suka haɗu a dinning room suka yi breakfast gaba ɗaya har da Alhaji Ridwan da yazo gaishe da Mamu, ya gaisa da ɗan'uwansa da iyalansa. Su Hajiya Zuhura duk ɓangaren Alhaji Ridwan suka wuce sabo da tuni gida ya ɗauki harama domin ƴanmata biyar za'a aurar a Mai ƙusa mansion ɗin.

***** Kamar yanda nayi bayani a baya mai ƙusa family a halin yanzu gaba ɗaya suna rayuwa ne a mai ƙusa mansion mallakin Alhaji Ridwan Muhammad Ali mai ƙusa. Shine ya fara tarewa a Abuja lokacin daya dawo daga karatunsa a kasar China, in da ya buɗe babban companynsa da ake shigo da ƙarafa daga ƙasashe. Aurensa na farko ya auri Matarsa Hajiya Raliya wacce suka haɗu a China lokacin da yake haɗa master's ɗinsa, a can suka ƙulla soyayya har ta kai su ga aure. Wan da kwata-kwata Inno bata so hakan ba. Domin kuwa tun da ta ga Allah ya ɗaga Alhaji Ridwan ɗin fiye da nata ƴaƴan sai abin yake mata ciwo sosai, baƙin ciki da hassada suka taso ta a gaba. Sai dai da yake gwana ce wurin iya ɓoye abu sai ba wan da ya san da hakan a cikin zuciyarta sai wan da ya san ainahinta.

   Tun daga lokacin ta fara ƙoƙarin gani ta bashi wata matar daga gefenta wacce zata riƙe ta a matsayin makamin yaƙinta, burinta bai samu cika ba har Hajiya Raliya ta haifi ɗanta na farko wanda yaci sunan Mahaifinsa Muhammad. Bayan shekara huɗu ta ƙara haihuwar Namiji aka saka masa Aliyu sunan mahaifin Alhaji Muhammad, sai a lokacin ne Inno ta samu nasarar haɗa Alhaji Ridwan aure da ƴar Aminiyarta Hajiya Turai mai suna Badariyya, sai da suka haɗa da asiri da ƙulle-ƙulle kafin hakan ya kasance don da farko da tayi masa maganar bai amince ba. Hajiya Raliya bata wani tayar da hankalinta ba kasancewarta wayayyiyar Mace mai Class wacce ta san kanta, ba wai don bata kishin Mijinta bane a'a sai don ilimin zamani dana addini daya ratsata. Hakan yasa take tafiyar da tsaftataccen kishi irin wanda addini ya koyar damu da kuma gogewar da take da ita.

   Bayan Muhammad da haidar Hajiya Raliya ta sake haifar yara Mata guda biyu Aimana da Anisa wanda a kwai tazara sosai tsakanin Aimana da Anisa don har ta cire rai ma, saboda sai da ta shekara shida kafin ta samu wani rabon. Yayin da Matarsa ta biyu Hajiya Badariyya ta haifi yara biyar duk Mata wan da baƙin cikin hakan ya tsaye a zuciyarta data Mahaifiyarta har da Uwar ɗakinta Inno data haɗa auren. A halin yanzu Alhaji Ridwan nada yara tara kenan, Hajiya Raliya da suke kira da Ammy tana da huɗu yayin da Hajiya Badariyya da suke kira Mommy keda biyar. Babbar ƴarta A'isha da taci sunan Yayar Dady ƴar Inno ta biyu suna kiranta da Aysha, sai ta biyun Amani, sai ta ukun Farhat, Ruƙayya sai Auta Saima.

   Cikin ƙanƙanin lokaci Dady ya ƙara bunƙasa sunansa ya shiga cikin jerin manyan ƴan kasuwa, yayinda Companynsa ya rinƙa samun rassa tako ina mai ƙusa industry ya kafu. A lokacin ne ya fara ginin tafkeken mansion ɗinsa a babbar unguwa ta manyan masu kuɗi, gini ne ake yi unguwa guda domin kuwa gidaje goma aka gina a ciki wan da ko wanne tsari ne mai matuƙar ƙayatarwa.

   Lokacin da ginin ya kammala ya tattaro gaba ɗaya ahalinsa dake Kaduna ya dawo dasu nan Abuja ya bawa kowa ɓangaren daya dace da iyalansa.

***** A ɓangaren Inno bayan Mudansir wanda a yanzu yake amsa sunan Alhaji Mudansir, Matarsa ɗaya har yanzu da yaransa biyar. Babba ɗansa shine Ammar wan da suke da kyakykyawar alaƙa da Muhammad a kaf Familyn domin jininsu yazo ɗaya don haka akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu duk da cewar Muhammad ɗin ya girmi Ammar ɗin da kusan shekara huɗu. Bayan Ammar akwai Muhusin, sai Aliya, Khadijah, da Zainab.

   Sai Ummah A'isha ita ce ƴarta ta biyu wacce take aure a can Kaduna itama da nata Iyalan, bayan Ummah A'isha ta haifi Buhari wan da shima yake rayuwa a cikin Mansion ɗin da Matansa biyu da yara Uku wan da ya haifa da amaryarsa sakamakon Uwar gidan da bata haihuwa. Bayan shi sai Yahaya wanda shima yana zaune a cikin Mansion ɗin da matarsa ɗaya da yaransa biyu. Waɗan nan sune iyalan mai ƙusa dake rayuwa a wuri ɗaya a halin yanzu bayan rasuwar Alhaji Ali da matarsa Inna wan da sune suka kafa zuri'ar.

***** A ɓangaren Alhaji Ridwan zai aurar da yara uku Mata ɗakin Hajiya Raliya (Ammy) zata aurar da Aimana, a ɗakin Hajiya Badariyya (Mommy) zata aurar da guda biyu Aysha da Amani. Sai ɓangaren Alhaji Mudansir (Abba) zai bayar da Aliya da Khadija. Waɗan nan sune ƴanmata biyar da za'a sha shagalin bikinsu a familyn mai ƙusa.

******* A ɓangaren Nanah koda ta kammala breakfast ɗakin Mamu ta koma tayi zamanta don bata son abinda zai haɗa ta dasu Nawal su wulaƙanta ta kamar yanda suka saba, tun da ta samu Mamu ta jata a jiki shike nan ta samu mafaka. Tun tana ɗari-ɗari da Mamu har ta fara sake jiki da ita, domin kuwa sosai Mamu ta jata a jiki musamman data fahimci kamar tana tsoron mutane.

   Zama take yi tayi ta janta da hira tana bata labarin Abbanta wanda sosai Nanah ke jin daɗin hakan, a hankali cikin hikima da dabara take tambayarta yanda ta gudanar da rayuwar ta a baya. Sosai Nanah ta saki jiki ta bawa Mamu labarin rayuwarta a Cigama da dalilin dawowarta gidan su Mama da irin rayuwar da tayi a can har zuwan Yaya Khalid ya tafi da ita Kano. Sai dai ta kasa sakin jiki ta faɗa mata irin zaman da suke yi a gidan wan Mahaifin nasu, ita da kanta ta fahimci ba daɗin zaman suke ji a can ɗin ba sabo da ta san halin Matan ɗan nata da yaransu ba kirki ne suka cika ba......

OUM FATIMA 

***