19
by @oumfatima33
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*KOMAI TSANANI*
*By*
*KANSA'U* *BELLO*
*(OUM FATIMA)*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*PAGE 019*
*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*
Mamu sai da ta share hawaye sabo da tausayin irin rayuwar da jikarta tayi alhalin tana raye cikin jin daɗi da wal-wala, ji tayi sam basu kyauta wa Khamis ba don da ace zai dawo ya ga yanda suka kasa kula wa da amanar daya bar musu ba ƙaramar kunya zasu jiba. Amma yanzu komai yazo ƙarshe in sha Allah zata ɗauki matakin daya dace, zata yi ƙoƙarin gyara kuskuren da suka yi.
Yau za'a gudanar da Mother's day a cikin katafaren hole ɗin taron dake cikin Mansion ɗin, ƙarfe 5 na yanma za'a fara gudanar da taron don haka tun bayan sallar Azahar masu decorations suka zo suka ƙayata wurin yayi matuƙar kyau. Duk abin nan da ake Nanah na ɗakin Mamu abinta ta ɗauki wayarta tana ta danne dannenta, yayin da sauran yaran gaba ɗaya duk sun bazama cikin gidan kowa ya haɗe da wan da tasu tazo ɗaya.
Bayan sallar la'asar Nana na kwance saman gadon Mamu tana karanta littafin azkhar wata kyakykyawar budurwa ta shigo ɗakin da sallama tana ƙwala kiran suna Mamu.
"Bata nan ta sauka ƙasa." Nanah ta faɗa da siririyar muryarta wacce ta janyo hankalin Anisa gareta.
"Masha Allah." Ta furta lokacin data ɗaura idona a kan kyakykyawar matashiyar yarinyar dake kwance saman gado tana karanta littafin azkhar ɗin Mamu data ɗauka. Sosai yarinyar ta burgeta ganinta kyakykyawa Masha Allah, gata da manyan idanu farare ƙal masu ɗaukar hankali don lokacin data kalleta dasu har wani maiƙo-maiƙo ta gani kwance a cikin su. Cikin natsuwa ta shiga ƙaraso wa in da take tana kallonta.
"Wacece ke?." Tayi mata tambayar tana ƙara zuba mata ido. Tashi zaune Nanah tayi tana gyara wuyan rigarta daya ɗan zame ta kalli Anisa tace.
"Sunana Maryam ana ce min Nanah."
"Nice name, wurin granny kika zo?." Anisa ta faɗa tana kallon ta. Nanah na ƙoƙarin bata amsa Mamu ta shigo ɗakin da sallama. Ganin Anisa zaune kusa da Nanah yasa tace.
"Yauwa Anisa gara da kika zo, dama yanzu nake neman wanda zan haÉ—a da wannan mai tsoron mutanen."
"Granny wacece ita?." Anisa ta mayar da tambayar kan Mamu.
"Ćłar'uwarki ce Ć´ar waje Kawunku Khamis daya rasu." Mamu ta bata amsa.
"Lah dama ita ce wannan kike bamu labari, amma me yasa bata taɓa zuwa ba ita?." Anisa ta faɗa cikin farin cikin jin cewa ƴar'uwarta ce don haka kawai jininta ya haɗu da yarinyar.
"Mamanta ta tafi da ita wani gari mai nisa shi yasa baku santa ba." Mamu ta bata amsa a taƙaice.
"Tana da kyau sosai Mamu." Nisa ta faɗa sannan ta miƙawa Nanah hannu tace.
"Sunana Anisa, zamu iya zama friends?." Murmushi Nanah tayi mata wanda ya loɓa kyakykyawan dimple ɗinta dake duka kumatunta ta gyaɗa mata kai.
"Kina da kyau sosai Kamar Hammanah shima yana da irin naki." Anisa ta faÉ—a tana saka yatsarta a kumatun Nanah Murmushi Nanah ta kuma yi mata bata ce komai ba.
"Wai ke bakya magana ne?." Anisa ta faÉ—a kasancewarta mai surutu sosai.
"Ina yi mana Nanah ta bata amsa a hankali.
"Kin ganta nan tun da suka zo take zaune a É—aki tamkar mai jin tsoron mutane." Cewar Mamu.
"Shike nan yanzu kizo muje É—akina mu shirya a akwai event da za'a yi yau a gidan." Cewar Anisa tana kama hannun Nanah.
"Bari na É—auki kayana to." Nana ta faÉ—a.
"Ok." ta faÉ—a tana sakin hannunta, school bag É—inta data zubo kayanta a ciki ta buÉ—e ta fito da sabon É—inkinta a cikin wanda Yaya Khalid ya mata.
"Kinga ki bar waɗan nan akwai anko da Ammy tayi min Tailor ɗin ya ɗinka yayi min kaɗan aka sake wani na san zai yi maki." Anisa ta faɗa tana riƙe hannunta suka fice, da kallo Mamu tabi su tana murmushi, sosai taji daɗin yanda Anisa ta jata suka tafi ko ba komai zata saki jiki ta.
Kai tsaye ɓangaren Hajiya Raliya suka nufa tare da Anisa, har ɗakin Ammy ta kaita suka gaisa take mata bayanin wacece ita. Da fara'a sosai Ammy ta amsa mata suka wuce ɗakin Anisa kasancewar Ammyn na tare da ƙawayenta da suka fara taruwa domin gudanar da Mother's day ɗin. Suna zuwa mai make up ɗin da Anisa ta ɗauko ta kira ta a waya ta sanar da ita isowarta, mai aikinsu ta bawa umarnin zuwa ta shigo da ita sannan ta kalli Nanah tace.
"Sis ga bathroom ki shiga ki fara yin wanka lokaci ya fara tafiya, don yanzu an kusa kammala yiwa Aunty Aimana make up na san." Bata yi musu ba duk da cewar tayi wanka a ɗakin Mamu ɗazu, bathroom ɗin ta shiga wanda ta ɓata lokaci wurin ƙare masa kallo da mamakin yanda aka tsara shi tamkar wani wurin kwalliya ba bayi ba. Kasancewar Mamu ta koya mata yanda ake amfani da abubuwan yasa kanta bai kulle ba tayi wankan tayi alwala ta fito tana goge gashi ta data wanke sabo da yana ɗan damunta.
"Masha Allah kina da gashi sosai Sis, amma sai dai ba kaya gyara shi kin bar shi ya sarƙe, yanzu dai lokaci ya ƙure ki ɗan taimaka mata a gyara shi kafin gobe da safe muje ayi masa abinda ya dace." Anisa ta ƙare maganar da bawa mai make up ɗin umarni kafin ta shige bathroom ɗin don yin wankan ita ma.
Budurwar data É—auko don yi mata make up hair dryer ta É—auko ta busar da gashin Nanah ta shafa mata mayukan gashi masu kyau ta daure mata shi sabo da babu lokacin da za'a yi stretching É—in sa.
"Kina buƙatar make up ne?." Ta tanbayi Nanah dai-dai lokacin da Anisa ta fito daga bathroom.
"A'a bana son kwalliya ni dai." Ta bata amsa a taƙaice. Kallon ta Anisa tayi da murmushi tace.
"No Sis ki bari ayi light zata yi maki kyau sosai." Ba don tana so ba ta bari aka yi mata light make up iya powder kwalli da lips gloss. Wani irin sihirtaccen kyau tayi wan da ya sa mai make up É—in da Anisa kasa daina kallonta.
Lokacin data saka atamfar ankon ɗinkin doguwar riga T buba sai ya zama kamar dama ita aka ɗinka ma kayan kasancewata doguwa kuma marar jiki, atamfar tayi matuƙar yi mata kyau kasancewarta mai duhu sai ta haska farar fatarta. Sassauƙan ɗauri ta soke mata wan da ya zauna ɗas a saman kyakykyawar fuskarta yayi mata kyau, sarƙa da ɗankunne da siririn agogo Anisa ta bata ta saka ta bata ƙaramin mayafin daya shiga da atamfar ta ɗora shi saman kanta tayi mata irin yafin da ake kira da Akuya style sabo da yanayin ɗinkin jikinta. Subhanallah idan kaga yanda Nanah ta sauya gaba ɗaya kai ba zaka taɓa cewa ita ce wannan wacce tayi rayuwa a ƙauye cikin wahala ba.
Tayi wani shahararren kyawu irin wanda ba zaka iya É—auke ido a kanta ba idan ka kalle ta.
"Kai Sis kar fa ki cinye taron yau ɗin nan don yan da kika yi kyan nan bana tunanin akwai wanda zai doke ki." Anisa ta faɗa tana murmushi lokacin da aka kammala shirya Nanah. Tattausan murmushi ta saki wanda ya ƙawata fuskarta dai-dai lokacin da mai make up ɗin ta haska ta d Camera, sai hoton ya zama na musamman yayi bala'in kyau.
Kasancewar lokaci ya ƙure don tuni an fara gudanar da taron sabo da Ammy ta kira Anisa a waya don jin inda ta tsaya yasa aka yi maza aka shirya Anisa itama cikin irin atamfar Nanah wacce ba ƙaramin kuɗi aka zuba wurin sayar ta ba. Tayi matuƙar kyau itama kasancewarta kyakykyawar, hotuna aka yi musu kafin ta sallami mai make up ɗin ta bawa Nanah plat shoes da bag mai kyau suka fice sunanta baza ƙamshi.
Lokacin da suka isa Hole ɗin da ake gudanar da taron tuni shagali ya fara kan-kama amare suna zaune a wurin da ka tanadar musu, haka ma Iyaye da ƴan'uwa sai Mc dake gudanar da taron. Wurin su Ammy suka fara zuwa suka gaishe su kafin suka nufi wurin amaren wan da a nan ne Nanah taga Aunty Aimanan Anisa suna matuƙar kama da juna.
A nan suka haɗe da sauran ƴanmatan gidan wan da a nan Nanah taga su Nawal, su Ya Yusrah anci kwalliya ana ta iya yi, baki da hanci suka saki suna kallon Nanah don da farko basu gane ta ba kasancewar sun ganta da ankon ƴan gidan. Kai gaba ɗaya ma shigar dake jikinta babu abinda ya dace da nata, don haka nan take baƙin ciki da hassada ya motsa. Nihal ta fara zuwa in da suke tsaye da Anisa tana gaisawa da ƙawayenta da suka zo mata.
"Hi sis." Ta faɗa tana taɓo Anisa. Juyowa tayi ta kalle ta tace.
"Hi ya kike." Ta juya ga ƙawayenta. Haushi ya kamata don a ganinta Anisa ta wulaƙanta ta a gaban Nanah, don haka cike da jin haushi ta juyo wurin Nanah ta ƙare mata kallo a wulaƙance tace.
"Ita kuma wanan baƙauyiyar yarinyar waye ya bata aron kaya har ta samu damar shiga cikin mutane take wani jiji da kai gaka?." Tayi tambayar cike da rainin wayo wan da ya janyo hankalin su Anisa dake kusa dasu, dariya Nawal ta sheƙe da ita tace.
"Shish-shigi mana daga zuwa an fara maƙalewa ƴan gida ana aron kaya don ayi ƙarya, sai dai kuma a banza don baki ganta ba kayan da ban ita da ban don ba saba saka wa aka yi ba." Ta ƙare maganar cike da hassada don ko ita kanta ta san ƙarya ta faɗa. Mabaruka zata yi magana Anisa ta ɗaga mata hannu rai a ɓace tace.
"Ya isa haka dan Allah, waye yace aro tayi aka bata, ai itama ƴar gida ce kamar yanda kuke jin kuna da matsayi a gidan nan itama haka ne sabo da abu ɗaya ya haɗa mu. Sannan maganar cewa kaya da ban ita da ban wannan ƙarya ne kowa ya kalle ta ya san ita ɗin mai kyau ce kuma kaya sun dace da ita sai dai mahassadi!." Ta ƙare maganar rai ɓace tana makawa Nihal harara sabo da bata son wulaƙanci, ita dama can yaran basu yi mata ba sabo da sun cika rawar kan tsiya da shegen son nuna su wasu ne.
"Sis ku muje don Allah kar raina yafi haka ɓaci a wurin nan." Anisa ta kuma faɗa tana kama hannun Nanah suka wuce suka bar su Yusrah da baki a sake, baƙin ciki tamkar zai kashe su don ganin yan da Nanah ta samu shiga daga zuwanta ace har ta samu shiga a wurin Anisa wan da su da suka jima suna neman hakan basu samu ba, musamman Yusrah dake haukar son Muhammad take neman kusanci da ƴan'uwansa tako wane hali.
Wani wurin da ban suka samu suka zauna suna hirar su yayin da biki ke ci gaba da gudana, koda aka kira amare fili Iyayensu Mata na musu liki duk miƙewa suka yi suna ɗauka a waya bayan photo grapher dake aikinsa. Lokacin da aka buƙaci ƙannen amare a fili Anisa ta kama hannun Nanah suka je wurin Ammy ta basu bundle ɗin 1k sabbi kowa guda ɗaya suka je suka yi liƙi wan da baƙin cikin hakan ya kama su Yusrah, ganin hakan yasa suka je suka matsawa iyayensu suma suka basu kuɗin suka shiga suka yi liƙin don dai kar su zama ƴan kallo.
Sai da aka kira sallar magrib kafin aka tashi a wurin taron cike da murna, har first gate Anisa da Nanah suka raka ƙawayen Anisa da suke ta jan Nanah da hira don yarinyar tayi musu kyau sosai suna don ta haɗe dasu. A ɓangaren Nanah kuwa ta kasa sake jiki sabo da rashin sabo da hakan, don ta saba da kyara da hantara daga wurin mutane bata saba da janta a jiki da nuna mata soyayya irin haka ba. A hanyar su ta koma wa ne Anisa ke bawa Nanah labarin Hammanta take sanar mata cewar gobe zai dawo daga London a can yake yin master's ɗinsa yama kusa kammala wa. Ita dai Nanah zata so taga wannan Yayan nata da ake ta zuzutawa, kamar Anisa ta shiga zuciyar Nanah tace.
"Ai gobe muna da manyan baƙi domin basawan gidan zasu dawo Hammanah da Ya Ammar, kin san kaf a gidan nan an fi jin tsoronsu fiye da kowa, sabo da basa wasa da yara a kwai tsare gida musamman Hammanah. Amma fa duk da haka yana da kirki sosai sannan kuma yana matuƙar ji dani. Ammy ta taɓa bani labarin cewar lokacin da yana ƙaramin yaro yana da fara'a sosai tun da wani tsau-tsayi ya samu Aunty Amirah yayi sanadin rasuwarta shike nan ya sauya ya daina dariya da fara'a ya zama fuskarsa kullum a haka!." Ta ƙare maganar fuskarta na sauyawa da alamar damuwa.
"Wacece Aunty Amirah?." Nanah ta samu kanta da tambayar Anisa dai-dai lokacin da suka shiga cikin É—akin Anisa. Maimakon ta bata amsa sai cewa tayi.
"Kin ga lokacin sallah zai wuce ki bari wani lokacin zan baki labari duk da dai nima labarin aka bani ban santa ba a zahiri sabo da lokacin da abin ya faru ba'a haife ni ba in ji Ammy. Anisa ta faÉ—a tana shigewa bayi sabo da fitsarin É—aya matse ta.
A ɓangaren Nanah kuwa haka kawai maganar ta tsaye mata a rai taji tana son jin labarin wan da ake kira da Muhammad ɗin nan duk da cewa bata taɓa ganinsa ba......