KOMAI TSANANI

21

by @oumfatima33

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    *KOMAI TSANANI* 

             *By*

         *KANSA'U* *BELLO* 
    
   *(OUM FATIMA)* 
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


   *PAGE 021* 


 *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*



★★★

 *Washe gari....* 


 Washe gari ta kama ranar da za'a yi kamu da walima gobe juma'a kuma a ɗaura aure shike nan an kammala biki a nan sai kuma dinner da za'a yi bayan an kai amare. Nanah tana cikin farin ciki sosai domin kuwa a ranar su Yaya Khalid suka zo tare dasu Farooq.

   Lokacin daya shigo tana zaune a sashen Mamu ta tsare ta da farfesun kayan ciki data saka mai aikinta tayi wa Nanah musamman, sai mita take a kan ramar Nanah tana faɗin zata saka Ridwan ya kai mata ita asibiti a duba ta wannan ramar bata lafiya bace.

   "To ina dalili yarinyar tamkar ƴar tsana har wani lanƙwashewa take tsabar rama an bar yarinya ba'a kula da ita ina kuwa zan lamunci hakan, maza za ki yi ki cinye duka har romon kafin Asabe ta kammala dama maki kunun da tace yana cire rama." Mamu ce ke wannan mitar yayin da Baba Asabe mai aikinta ke Kichen tana musu dariya, don Nanah har da hawayenta a kan ita ta ƙoshi da farfesun amma Hajiya Mamu ta
 dage sai ta cinye sa.

   Sallamar da Khalid yayi ya shigo ita ce ta ceci Nanah daga hannun Mamu ta miƙe da gudu ta nufi in da yake ta riƙe hannunsa tana matse hawaye. Murmushi Khalid ya saki yana faɗin.

   "Kin cika shagwaɓa Nanah, baki san cewa kin fara girma ba." Ya faɗa yana kama hannunta suka ƙara sa in da Mamu take zaune tana mitar cewa.

   "Ka bari kawai ɗan nan ai ni ban taɓa ganin sakaliyar yarinya irin wannan ba, na rasa wani irin raino ne Ramatu tayi mata. Ace yarinya ba zata buɗe ciki taci abinci ba, yo ba dole ta riƙa figewa ba tamkar wata kazar mayu." Dariya sosai Khalid ya saki yana faɗin.

   "Ai kau dai Mamu kin ganta nima haka nake fama da ita tun da ta dawo hannuna." Ita dai Nanah lafewa tayi a gefen Khalid tana sauke ajiyar zuciya. Gaishe da Mamu Khalid yayi ta amsa da kulawa tana cewa.

   "Idonka kenan Khalid rabon ka da nan kusan shekara biyu kenan ka ɓoye a Kano?." Murmushi Khalid yayi yana sosa ƙeya yace.

   "Ayi haƙuri Mamu abubuwan ne suke min yawa ga karatu ga kasuwa kuma." Ya faɗa yana bawa Nanah chocolate ɗin daya zo mata dashi.

   "Masha Allah an fara karatun kenan.?" Mamu ta faɗa.

   "Eh na samu na fara yanzu haka ina shekara ta biyu ne."

  "Masha Allah, Allah yayi albarka, amma nace ba tare zaku kammala dasu Farooqu ba?... Kamar haka naji Abban naku ya sanar wa Dadyn naku lokacin daya masa maganar kuɗin makarantar naku." Shiru Khalid yayi yana mamakin halin Abba, wato kenan lokacin da zai saka su Farooq makaranta Dasu ne ya biya musu kuɗin registration ɗin har da shi amma bawan Allahn nan yaƙi biya masa ya bar shi yana ta faɗi-tashin yanda zai samu ya saka kansa da kansa, ya saka iya nasa yaran shi ya kawo masa ƙabli da ba'adin bashi da halin da zai iya ɗaukar nauyin karatunsu su duka.

     Shirun da yayi ne bai ce komai ba ya bawa Mamu amsa don haka ta girgiza kai kawai tana mamakin halin Balarabe.


**** Misalin ƙarfe 5 na yanma aka fara gudanar da kamu shima dai a cikin hole ɗin gidan aka gabatar wan da ya ƙawatu sosai, yau ma Anisa ce ta bawa Nanah kayan data saka don tun jiya ta sanar da Ammy aka kawo mata duka ɗinkunan da zata saka da bikin ita ma, hakan ba ƙaramin ƙona ran yaran Alhaji Bala yayi ba don suna ganin Nanah bata kai matsayin data samu ba a gidan Dadyn. Ƙarfe 6:30pm aka tashi daga taron, a dai-dai lokacin ne wata kyakykyawar mota mai daukar ido ta tsaya a harabar wurin. Gaba ɗaya idon mutanen dake fitowa daga wurin taron ya koma kan kyakykyawar motar data tsaya ɗin. Kamar mutumin dake cikin motar ya san fitowarsa ake jira yayi zaman sa abinsa yaƙi fitowa.

   An ɓata mintuna kusan uku kafin aka buɗe gidan gaba, wani matashi ne ya fara fitowa a motar ya tsaya yana ƙare wa harabar kallo.

   "Ya Haidar?." Anisa ta faɗa fuskarta cike da mamaki kafin ta kama hannun Nanah tana cewa.

   "Zo muje ku gaisa da Ya Haidar ɗina." Nanah bata yi musu ba suka nufi wurin da motar ta tsaya dai-dai lokacin kuma wani kyakykyawan matashin ya fito daga ɗayan side ɗin mai zaman banza.

   "Lah! Ya Ammar?." Anisa ta kuma faɗa fuskarta na ƙara washe wa, saurin tafiyar ta ƙara suka isa in da suke a tsaye.

   "Ya Ammar sannu da zuwa." Ta faɗa cike da murna tana ƙara matsawa kusa da Ammar ɗin kasancewar akwai shaƙuwa a tsakaninsu. Ammar da tun da suka doso wurin idanunsa suka sauka saman fuskar kyakykyawar matashiyar dake tare da Anisa, wani irin harbawa yaji zuciyarsa tayi a cikin ƙirjinsa da mugun gudu har sai da ya lumshe ido, kallo ya kafe fuskarta da shi yana jin wani irin yanayi mai nauyi a cikin zuciyarsa a game da yarinyar wan da bai taɓa jinsa ba a tarihin rayuwarsa.

   "Ya Ammar?." Anisa ta kuma faɗa tana riƙo hannunsa ganin yanda yayi tamkar bai ganta ba, wayancewa yayi ya dawo da kallonsa saman fuskarta yana sake mata murmushi a hankali ya furta.

   "Autar Ammy ya kike?." Ya faɗa yana ƙara kallon fuskar yarinyar. Cike da farin cikin ganinsa tace.

   "Ina lafiya Ya Ammar, ka dawo lafiya, ya hanya?." Ta faɗa duka a tare.

   "Alhamdulillah." Ya faɗa yana sake mata murmushi yayin da hankalinsa gaba ɗaya yake kan yarinyar data buɗe baki a natse ta gaishe su su biyun da siririyar muryarta. Sai a lokacin Anisa ta juya gun Ya Haidar tace.

   "Barka da yanma Ya Haidar." Harara ya zuba mata yace.

   "Sai yanzu kika ganni bayan idonki ya rufe a kan Yayanki." Murmushi ta saki tana riƙe hannunsa tace.

   "I'm sorry Ya Haidar Allah nayi missing Ya Ammar ne kai kuma koda yaushe ina ganin ka ai shi yasa, saura Hammanah shima na san yana hanya." Ta faɗa cike da ɗoki. Kallon Nanah yayi da kanta ke ƙasa yace.

   "Baƙuwa kika yi ne?." Haidar yayi mata tambayar dake cikin zuciyar Ammar tun ɗazu ya kasa furtawa.

   "Lah Sister ɗina ce ƴar wajen Uncle Khamis Allah ya masa rahama, sunanta Nanah a gidan Abban Kano take zaune ita da Ya Khalid." Anisa ta faɗa tana riƙo hannun Nanah.

   "Masha Allah." Ammar da Haidar suka furta a tare, dai-dai lokacin ne kuma sauran yaran gidan suka riƙa zuwa suna gaisawa da Ammar wan da dawowarsa kenan daga India in da yake karatu, saukarsa kenan Haidar yaje ya ɗauko sa a airport. Suna ƙoƙarin shige wa ne Mabaruka ta iso wurin da sauri don lokacin da Ammar ɗin ya fito a mota ita tana wurin da aka yi kamun suna ɗaukar hotuna ana ta iya yi sunƙi fitowa. Nawal ce ta koma da sauri ta sanar mata cewar ga Ammar ya dawo, da gudu ta fito sai da ta kusa zuwa ta dai-daita tafiyarta ta ƙara so inda suke ƙoƙarin shigewa Haidar yana riƙe da ƙaramar kyakykyawar jakarsa ta matafiya.

   "Sannu da zuwa Ya Ammar!." Mabaruka ta faɗa da sauri tana sauke numfashi sabo da gudun da tayi don kar ya shige ba tare data gan shi ba. Dakata wa yayi daga wucewar da yake ƙoƙarin yi sashen su ya juyo don ganin wace wannan take ƙwala masa kira. Ido suka haɗa da Mabaruka wacce ke ta sakar masa murmushi kamar wata sokuwa, a zuciyarsa ya raya cewar.

   'wannan kanta ƙalau kuwa?.' yayin da a zahiri ya ƙara haɗe ransa yace.

  "Yauwa." A taƙaice yayi wucewar sa. Kallon kallo mutanen wajen suka shiga yi sai kuma su kalli Mabaruka da tayi tsamo tsamo kunya duk ta kamata. Murmushi Anisa ta saki ƙasa-ƙasa ta furta.

   "Lallai kina da aiki yarinya in dai Ya Ammar ne." Tayi maganar sannan ta juya ta kalli Nanah ta sakar mata murmushi tace.

   "Let's go Sis." Murmushin ta mayar mata suka wuce ɓangaren Mamu. Wani mugun tsoki Mabaruka ta saki lokacin dasu Nanah suka yi musu nisa, a ƙufule ta kalli Nawal dake kusa da ita tace.

   "Wai baki lura da kan baƙauyiyar yarinyar can ya fara girma ba sabo da ta samu shiga a wurin Mamu da waccen mara mutuncin yarinyar!." Ta ƙare? maganar rai a matuƙar ɓace da takaicin yan da Ammar ya yarfa ta da kuma murmushin rainin wayo da taga Anisa na mata."

   "Ai ki bari kawai Ya Mabaruka na matsu mu koma Kano taci uwar ubanta, shegiya mai kama da aljanu!." Nawal ta faɗa cike da hassadar Nanah. Ƙwaffa Mabaruka taja suka shige jiki ba ƙwari.


****** A ɓangaren Ammar kuwa tun da ya ɗora ido a kan yarinyar tayi masa tsaye a cikin zuciya, gata dai yarinya ƙarama don baya tunanin ta wuce 15 years amma yanda yake jinta a zuciyarsa bai taɓa jin irin hakan ba a kan ko wace ƴa Mace ba. Kai tsaye ɓangaren Iyayensa ya fara zuwa in da suka tare da da murna, bayan sun gaisa ya wuce ɗakinsa ya samu yayi wanka da salla yaci abinci kafin ya kwanta sabo da a gajiye yake ba zai iya fita ko ina ba. Wayarsa ya ɗauka yana duba saƙonni ta email ɗinsa, saƙonnin Whatsapp ne suka yi ta shigowa bai bi ta kansu ba. Sai da ya kammala abin da yake kafin ya shiga Whatsapp ɗin ya fara duba saƙonni masu amfani yana yin reply, har zai fita kuma sai ya fasa ya shiga ɓangaren Status ya fara duba wa. Sunan Little Sis ya gani Anisa kenan ta ɗaura sabon update don haka kansa tsaye ya shiga ya fara duba wa, hotunan su ne ita da Nanah na jiya da suka ɗauka a wurin Mother's day da kuma na yau ta ɗora. Sun yi matuƙar kyau wanda bai san lokacin da yayi zooming face ɗin Nanah ba ya zuba mata ido yana jin zuciyarsa na motsa wa. Ya jima yana kallon hotunan kafin yayi saving ɗin su duka ya adana su a wuri na musamman.

   A daren kasa daina kallon hotunan yayi har sai da bacci ya ɗauke sa wayar nanhannunsa.....


  
  (Asuba ta gari Ya Ammar amma fa ina da ? A kan ka... What do you mean ɗinka ne?)