BAFULATANA🐄

Chapter 7

by @zmchubado

*BAFULATANA*

ZM~CHUBAƊO

         07

"Ni ɗane ga Abdulwahab Abdullah mu uku  Mahaifinmu ya haifa, ni ne babba sai Fadilah Sannan zainab, ni kaɗaine Namiji kuma wanda ke jan ragamar kamfanoninsa dake nan gida Nigeria harma dana ƙasashen waje."

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ƙara da cewa

"mahaifina Haifaffan Garin kano ne cikin unguwar Hotoro, Su biyu ne kacal a gurin iyayensu da shi da ƙanwarsa Asma'u muna kiranta da Mama. Mahaifinsu Shahararren ɗan kasuwa ne sosai, wanda ya kasance a garin na kano ana matiƙar jidashi a ɓangaren kasuwanci, ya Rasu ya bar duniya a lokacin da Mahaifina ya ke dabda kammala karatunsa na Scondry school, a lokacin ita kuma ƙanwar mahaifina Asma'u take dabda shiga sas 2. Bayan Rasuwar kakana ba jimawa Itama mahaifiyarsu ta bishi sakamakon Ciwon zuciya, bayan Rasuwar Hajiya da kimanin shekara 2 Mahaifina ya fara tasowa sosai a ɓangaren Kasuwanci,cikin ƙanƙanin lokaci Sunansa ya zarta na Mahaifinsa shahara, bayan Asma'u tayi Aure ne ta buƙaci da A raba musu gado a bawa kowa nasa.

Sosai Mahaifina ya nuna mata rashin dacewar hakan amma sam taƙi fahimta dole ya amince da abinda tazo dashi ɗin kuma ya kai maganar kotun Musulunci dake Kano aka raba musu gadon, bayan an Raba musu gado Asma'u ta fara business da kuɗaɗenta se dai bata ɗauki lokaci me tsaho ba jarin nata ya karye, shiko Mahaifina tamkar ana ƙara ɗagashi haka dukiyar ta dinga haɓaka cikin ikon Allah da Albarkasa.

Da wannan damar mahaifina ya yi amfani ya ƙara bata wani babban jarin daya ninka nata, ta ƙara zuba kuɗin a cikin kasuwancinta, cikin ikon Allah itama nata kasuwancin ya kafu da ƙafarsa, familymƴ muan da wata tawaya ta tashin haihuwa da yawa, wannan ya sa bamu da yawa sosai amma dai akwai kyakkyawr mu'amila a tsakanin mu kuma muna son junan mu sosai." Ko da Muzaffar yazo nan a zancensa se ya ɗaga kai ya kalli Baffah ya ce,"wannan shine tarihina a taƙaice."

Tun da ya fara magana Baffah ya yi masa zuru da idanu yana kallonsa, cikin Rashin gamsuwa ya ce"har yanzu yaro baka sanar dani abinda nake son ji a tareda kai ba, kana so ka gaya min cewar dama ba Sunan ka muhammad Ali ba kamar yanda ka gayamin a baya ba? Amma me ya sa ka zaɓi yaudarata bayan ni da zuciya ɗaya na zauna da kai?"

Jikin Muzaffar ba ƙaramin sanyi ya yi da jin kalaman Baffah ba, gabaɗaya sai ya ji bai kyauta ba da ya yi masa ƙarya, a hankali ya ya ce,"don Allah Baffah kayi haƙuri karka ka ga laifin pls, ni mutum ne me mu'amala da mutane kala-kala kuma wanda ake farautar Rayuwarsa ta ɓangarori da dama, banyi maka haka da wata manufa ba sai don na kare kai na."

"A'a yaro sam ba laifi kayi ba amma da aka ɗauki lokaci muna tare sai ka gaya mana gaskiya, amma ba kayi haka ba sai ka ɓoye mana kaci gaba da cutar da yardan mu a kanka."

"Don Allah Baffah daina faɗar haka pls, wllh ba da nufi nayi ba amma tabbas na san ban kyauta maka ba amma ina da yaƙini akan zaka Fahimceni, bayan haka kuma zaka yafe mini laifina na ɓoye maka Asalina da nayi."

Ajiyar zuciya Baffah yayi sannan yace "Shikenan na karɓi Uzirinka sannan innai maka fatan Alheri a Rayuwark ta gaba, amma kafin ka tafi zan baka wata babbar gudunmawa wadda nake da tabbacin  zata taimakeka da izinin Allah, ko wani irin yanayi zaka shiga a nan gaba." Baffah ya faɗi haka a lokacin da yake miƙawa Muzaffar wani jiƙo dake cikin ƙaramin ƙoƙo ya shanye.

Sai da ya shanye tass sannan ya kalleshi ya ce "Baffah wannan maganin na menene ?"

Moddibo ya kalleshi ya ce "maganin tsarin jiki ne da na gajeshi a gurin mahaifina wanda ya gargaɗeni akan kan  kar in badashi ga kowa sai wanda naji zuciyata ta Amince dashi, har A raina nakejin na yarda da kai shiyasa ma na baka wannan dafa'in namu na gado wanda nakeda tabbacin za kaga amfaninsa a gaba koda bana raye. ni dai nasihata a gareka shine ka riƙe Gaskiya da amana karka taɓa bari zuciyarka ta ruɗeka ka cutar da wanda yayarda da kai duk rintsi."

Sosai jikinsa yay sanyi da kalaman Baffah dan haka muzaffar ya jashi jikinsa ya Rungumeshi yanajin wani abu mai kama da kewa yana mamayar zuciyarsa kamada yanayi na kewa.

Zare jikinsa ya yi daga na muzaffar sannan ya ɗau Boron Maganinsa ya yi waje ba tareda ya ce dashi ƙala ba, shima muzaffar ɗin fita ya yi, se da ya ɗauki lokaci me tsayi sannan ya koma cikin gidan a ciki suka haɗu da Rabe tana ƙoƙarin shiga ɗakin Baffah, bin bayanta yayi shima suka shiga ɗakin tare.

Yana shiga ya nemi guri ya zauna itama zaman tayi, tun da ta zauna take kallon sa tun be lura ba har ya fahimci irin kallon da take masa, amma se ya share sabda yasan in dai ya kalleta dena kallon sa za tayi, shi kuma hakanan sai yaji a ransa baya so ta dena kallonsa sam.

Ta jima tana aikin kallon sa sannan ya dago a nitse idanunsu ya sarƙe cikin na juna kashe, kashe mata ido ɗaya yayi ba shiri
tayi ƙasa da idanunta sbda wata irin kunya ya baya. Uwa ubakuma ga wani irin kwarjini da taji ya yi mata.
Abine ya bashi dariya don haka ya murmusa sosai sannan ya ce,"Ohmg yau na kama Fulani Girl tana  kallona da alama you want to say something ko? oya say it pls." Ya faɗa yana wani kallonta in a romantic way ba tareda ya san yana yi ba.

Kasa ɗagowa tayi hakanan sai taji tanajin kunyarsa dukda irin damuwar dake Ranta akan tafiyarsa, gabaɗaya sai yanayinta ya canza ta koma asalin miskilarta kafin zuwansa garin, kamar me koyon magana ta buɗe baki ta ce "meyasa zaka tafi yanzu bayan mun saba da kai?" tayi maganar idanunta suna cikowa da ƙwallah

Shiru ya yi yana kallonta ganin hawaye a kwance cikin idanunta yasa ya kalli gefanta ya ce,"saboda inaso naje gidan naga iyayena na san sina cikin damuwar rashina a kusa dasu." ya yi maganar a sanyaye  fuskarsa na sauyawa.

"Na san zasu damu saboda basa ganinka da kaɗo, na tabbata muma irin damuwar da zamu shiga kenan idan ka tafi ka barmu." Rabe ta faɗi hakan hawaye dake cikin idanunta suka zibo.

Kasa cewa komai ya yi hakan yasa ta ƙara kallonshi ta ce,"meyasa ka ɓoye mini sunanka na gaskiya?"

Kasa kallonta ya yi ya ce "saboda lokacin da ya kamata ku sani ne beyi ba."

Kallonsa kawai takeyi a ranta tana mamakin halinsa, yanzun nan ze sake da kai har kuyi hira amma lokaci guda se ya gimtse kamar bashi ba, taɓe baki tayi tace "inaso ka gaya mini sunan da ba kaso a sani ɗin!"

A taƙaice ya ce "Muzaffar Abdulwahab."

Wara manyan idanunta tayi ta ce,"Sunanka wani iri ba irin namu bane, yana da tsayi sosai zan  kiranka da Zafar kawai."

Sai a lokacin ya kalleta data kai ƙarshen maganar ya ce,"yanda kika so."

Ba ta sake cewa komai ba tayi shiru sai kallonsa kawai takeyi, wanda hakan ya alamta nasa cewa bata cikin yanayi me daɗi.

Jikinsa a mace ya kalleta sika haɗa ido ya ce,"wllh ki daina sa damuwa a ranki saboda zan tafi gida, ba nace miki idan na tafi zan dawo ba?"

Haɗe fafunta tayi sannan ta kifa kanta akai ta fashe da kuka sosai, al'amarin da ya ƙara ɗaga masa hankali kenan ya matsa  kusa da ita, hannu ya ɗaga kai ɗora a bayanta sai kuma ya fasa. 

Shirune ya ratsa bukkar baka jin komai sai sautin kukanta dake tashi cikin siririyar muryarta wadda ba ta fita sosai, gyara zamanaa ya yi sannan ya rage sautin muryarsa cikin alamun rarrashi ya ce,"Na miki alƙaqari ba zan daɗe ba zan dawo ko dan saboda ke."
Ya ƙare maganar yana  nuna ta da hannunsa. 

Sosai maganarsa tayi mata daɗi har bata san sanda ta ɗago fuskarta duk ta cabe da hawaye ba, murmushi ya yi sannan ya miƙa mata farin saƙin dake gefansa ya ce," share hawayenki kinji."

Maƙe kafaɗa tayi alamar ba zata goge ba, sai hakan da tayi ya birgeshi saboda   kyawunta da ya ƙara baiyana a fili. "Ni ko?" ya faɗa a sanyaye.

Tura baki tayi sannan ta ɓalla masa harara. Dariya yayi sannan ya ce,"ƙazama me majina kawai."

Banza tayi dashi sannan taci gaba da kukanta.

Hannu yasa ya ɗaga fuskanta sannan ya haɗe rai kaman bashi ya gama dariya yanzu ba ya ce,"ba zaki bar kukan hakanan ba? Ko dai baki yarda dani bane?"

"na yarda da kai Hammah! amma na san wllahi ba zaka dawo ba mantawa zakayi damu."

Still yana kallon fuskarta bai ɗauke idanunsa ba, amma a can ƙasan ransa mamakikn wayon yarinyar ya keyi, kafin basirarta da maganganunta ya zarta shekarunta da zata samu wayewar ilimi a tareda ita tabbas da anyi cikakkiyar ƴar baiwa wadda bata da tsara. Ya so ace ya koyar da ita muhimman abubuwan da ya kamata ace ta sani, amma ubangiji bai bashi ikon hakan ba har lokacin tafiyarsa yazo.

Haƙiƙa tana buƙatar wadataccen ilimin addini wanda zai haska rayuwarta ta rabu da jahilcin da ya lulluɓe ƙuruciyarta, ba laifi yayi nasarar gyara mata wasu abubuwan a ɓangaren sallah, kuma Alhamdulillah a shekara ɗayan da yayi tare dasu yanzu Rabe tana iyayin salloli biyar a rana kamar yanda Annabin rahama ya koyar damu.

Idan ya tuna haka sai yaji sanyi a cikin ransa.

"Idan ka tafi zanyi kewarka sosai, zanyi kewar wanda kemin rakiya duk in da zanje, jin zafin tafiyarka a nan ɗina Hamma!" tayi maganar tana nuna masa ƙirjinta.

Sosai maganarta ta shigeshi har bai san sanda ya ƙureta da ido yana  kallonta ba sannan ya ce"nima Ina jinki a raina Rabi'atu! Ta yanda har cikin raina bana so na tafi na barki a nan, jini na ya hadu dake wannan ya sa kike da gurbi a cikin zuciyata kamar yanda Zainab take da shi"

"Hammah wacece Zainab?"

Murmushin gefan baki ya yi sannan ya ja hancinta ya ce,"she's my younger sister ina sonta sosai saboda tana iya haƙura da komai saboda farin cikina, shiyasa nakeji da ita a raina Except Fadilah."

Taɓe baki tayi sannan ta kauda kanta gefe saboda ba gane maganarsa take sosai ba, abu ɗaya kawai ta gane shine yana da alaƙa da ita.

Murmushi ya yi sannan yacigaba da cewa "duk duniyar nan Bayan Abie da Momy  ba wanda ya samu kusanci dani se ke Rabi'atu, kina da matsayi na musamman a zuciyar Muzaffar." ya yi maganar yana nuna mata ƙirjinsa.

Yanda ta nutsu tana sauraransa seka rantse tana fahimtar abinda yake faɗa mata dalla-dallah, ta Daɗe tana juya abin a ranta daga ƙarshe data kasa fassara maganar sai ta ƙara jefa masa wata tambayar da tasa har seda ya ɗago ya ƙara kallonta.

"Hamma dama ana Iya bawa mutum matsayi a zuciya?"

Da sauri ya ɗauke kansa daga barin kallonta sannan ya ce "No ba'ayi kawai dai na faɗa ne nima." ya faɗi haka yana ƙokarin kai hannunsa fuskarta. suna cikin wannan yanayi Jaddah ta bankaɗo cikin ɗakin ta ce, "to tsinanniya fito nan kiyi min aiki 
Kin shige ɗaki da garjejen namijin da a tsaye yafi ubanki ƙirar ƙarfi da tsayi kuna lalata, in banda masifa da jaraba irinta yaran zamani ina ke ina wannan gabjejen ƙato wanda ko babbar macen kirki ma sai taci baƙar wuya a hannunsa? Amma dan rashin kunya se liqe masa kike yi se kace ba BAFULATANA ba 
Shegiya me bin maza karuwan wofi."

sosai abin yayiwa muzaffar zafi a rai duk da bada hausa tayi maganar ba ya fahimci duk abinda ta faɗa, saboda tsahon shekarar da yayi dasu yana jin fulatanci sosai kuma yana iya mayar da martani, amma sai ya danne zuciyar sa yay kamar be gane abinda take faɗa ɗin ba. 

Rabe kuwa banda kuka ba abinda takeyi saboda zafin da kalaman Jaddah sukayi mata a zuciya, Sarai ta san abinda bin maza ke nufi ba abin arzuƙi bane dukda a ƙarancin shekarun ta bata san ya abin yake a aikace ba.

A hankali ya matasa kusa da ita yana kallonta yace "kiyi haƙuri in sha Allah wata rana se labari." 

Taɓe baki Jaddah tayi sannan ta karkace ta dinga zuba tijara son ranta sannan ta fice ta bar musu dakin. Sosai abin ya batawa muzaffar rai dan haka ya kasa cewa komai, cikin tatatausan lafazi ya ce," tashi kije ki shirya mutafi kiwo."

Tana jinsa amma sai tayi kamar bata ji me yace ba ta cigaba da kukanta, sosai kukanta ke huda masa zuciyarsa wannan ya sa ya tsaya kawai yana kallonta. 

Dan kanta ta rarrashi kanta tayi shiru, a haka Baffah yay sallama a ƙofar ɗakin ya shiga ya samesu, ko kaɗan beyi mamakin ganin su a tare ba sabda hakan ba sabon Abu bane. Da gudu Rabe  ta nufi Baffah ta rungumeshi se kuma ta sake fashewa da wani sabon kukan. cike da damuwa Baffah ya ɗagota yana kallon fiskarta ya ce "meya faru kuma?"
Bata CE komaiba sabda kukan yaci ƙarfin ta, ba taso ta sanar dashi abinda  Jaddah tayi masu, sai kawai ta nuna masa muzaffar da hannunta wanda ke tsaye daga gefe tace "Baffah wai Hamma ne yake faɗamini wai ze tafi garin su ya barmu!."ta ƙarashe mganar tana kuka.

Murmushi Baffah ya yi sannan ya dafa Kafadunta ya ce," haba kekuwa meyasa zakiyi haka?
Kadafa ki manta ke ɗin ƙanwarsa ce dole wata rana ze sake dawowa saboda ke ki daina kuka kinji mamana?"

Da sauri ta daga kanta alamar ta yarda da batun Baban nata, dan hka ta share hawayenta sannan ta koma kusa da muzaffar ta ce,"Hamma Baffah yace zaka dawo wata rana  ba zan sake yin kuka ba sbda Baffah ba ya min ƙarya komai ya fadamin gaskiya ne."

tunda ta fara maganar muzaffar ke kallonta sosai yake nazarin yarinyar gata karama amma tana da kaifin tunani wannan idan ta kai shekara 20 ya zata kasance? Lallai Rabi'atu tana da wayo kuma yana jinjina irin soyayyah dake tsakanin ta da mahaifin ta.

Murmushi ya yi  sannan ya ƙara Jan hancinta da hannunsa dikansu sukayi dariya sannan suka yiwa Baffah Sallama suka tafi kiwo tare.

***   ***   ***   ***
*_MUMBAI INDIA_*

ƙarfe 8:00 na dare agogon ƙasar ya buga, wata hamshaƙiyar matace ke Sakkowa da ga saman benan dake cikin ƙayataccen falon wanda ya cancanci da ayi masa laƙabi da aljannar duniya.

kunnenta a kange ya ke da wayarta ƙirar Iphone da alama waya takeyi, a hankali take sakkowa cikin isa da ƙasaita hannunta jere da wasu murɗaɗɗun zobuna na zinare, sanye taƙe cikin doguwar rigar less ɗan ubansu wanda yaji stones a jiki, a haka ta iso cikin falon ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon.

Da ga can ɓangaren Abie ya ce,"Aisha ya kamata komai yazo ƙarshe saboda na gaji da zamanki a wata ƙasar ta daban, don haka a cikin satin nan ya kamata ki dawo ƙarsarmu ta haihuwa mu zauna tare a nan cikin iyalai na."

Ɗaure Fuska Hajiya Aisha tayi sannan ta ce,"ina me baka haƙurin sanar da kai cewa ba zan iya barin ƙasar india in dawo Nigeria ba, don Allah Abie ka fahimceni kuma ka kwantar da hankalinka, zan baka lokaci ka samu kayi tunani akan maganata wata ƙila zaka sakko muci gaba da zaman mu kamar yanda muka saba, idan na dawo Nigeria wa zaicigaba da gudanar da kasuwancin mu na ƙasar nan?"

Kasa magana Abie yayi ya katse kiran saboda takaicin ta, wani irin abu yaji yana taso masa wanda yafi kama da ɓacin rai sannan ya jefar da wayar a gefansa.
"wllahi Aisha zanyi maganinki soon, ba zan ƙara bari ki shashantar dani ba dole ne ki dawo nan muddin kina son zaman aure dani." ya firta hakan yana murza goshinsa.

da ƙar ya iya miƙewa ya nufi toilet dan ya watsa ruwa, gabaɗaya tunaninsa ya tsaya cak babu wani abu da keyi masa daɗi komai ya fice masa a rai, a dadafe yayi wankan ya fito cikin mintunan goma ba ya gama shiryawa cikin riga da wando na farin yadin filtex, ba laifi kayan sun masa kyau dik da irin ramar dake kan fuskarsa da gangar jikinsa, kana kallon sa zaka fahimci baya cikin kwanciyar hankali a haka ya fito da ga part ɗinsa cikin shirin fita, Momy ya samu zaune a falo se fadilah da Zainab wadda ke zaune kusa da momy duk lamarin Duniya ya isheta.

Remote Fadilah ta ɗauka tana ƙoƙarin Kunna Ƙatuwa Tv bangon dake falon tamkar ba Ɗan uwanta ciki ɗaya ake shelar nema a kafafen yaɗa labarai da duk wani saƙo da lungu dake najeriya ba.

Kallonta kawai Abie keyi zuciyarsa na tafarfasa ya ce "ba zance miki komai ba Fadilah amma zanyi maganinki ta hanyar da shata miki layi da komai nawa, a sannan ne zaki shiga taitayinki." Abie ya faɗi hakan zuciyasa na zafi akan Halaiyar Fadilah

Ficewa ya yi daga falon harya fito harabar gidan Guards ɗinsa suka buɗe masa ƙofa sannan Driver yaja motar sauran suka mara musu baya suka ɗauki hanyar gidan Cp.

Momy najin fitarsa Wasu zafafan Hawaye suka shiga zubo Mata tana kallon Fadilah, A fisace Zainab ta tashi itama tana kallon Fadilah ta ce, "ban taɓa ganin irin wannan haukan ba wllh se'a kanki yaya Fadilah, wannan wani irin Rashin iman da son duniyai kike dashi? Karfa ki manta Yaya ɗan uwa ki ne Uwa ɗaya uba ɗaya amma kuma kike gwada masa wannan ƙiyayyar ta ba gaira ba dalili? Wllh ban taɓa ganin hka ba se'a Kanki wai ace mutum yana girma amma yana rasa hankali." Zainab ta faɗi hakan yayin da take kallon Fadilah tana huci.

Gadan-Gadan Fadilah tai kanta Hannunta ɗauke da Cokali me yatsu ta ce,"yau zan gwada miki raahin imanin don Ubanki.".

Zmc💋
***