Chapter 8
by @zmchubado
*BAFULATANA*
Zm~Chubaɗo
08
Miƙewa momy ta yi a fusace ta nufi Fadilah da ƙarfin tsiya ta ɓanɓare Zainab a hannunta sai kuka ta keyi sannan ta ɗauke ta da kyakkyawan mari sannan ta nunata da yatsa ta ce,"don uwarki nan gaba ki san irin Rashin tarbiyar da zakiyi a gabana, wacce irin baƙar zuciya gareki haka? In ba baƙar zuciya ba wani irin abu ne ya shiga kanki da iskancinki baya tashi sai akan ƴan uwanki? Wllhi Fadilah na fara tantama a kanki anya kuwa ke jinina ce?"
Ɗagowa Fadilah tayi da jajayen idanunta tana kallon Momy hawaye na zubo mata ta ce,"Momy yau ni kika mara akan Zainaba?"
A fusace ta ce,"na mareki Fadilah wllh muddin kikaci gaba da yin irin wannan rashin tarbiyar senayi miki abinda yafi haka muni shashasha kawai." Momy ta faɗi hakan a fusace sannan taja hannun Zainab suka bar mata falon.
sosai hakan yayiwa Fadilah zafi a rai lokaci kuda kuma ta kife akan ɗaya daga cikin kujerun falon ta fara gurzar kukan baƙin ciki kamar wadda uwarta ta mutu. Gabaɗaya ta rasa dalilin da yasa kowa baya sonta, duk abinda za tayi kowa laifinta ya ke gani sai kace daga sama ta faɗo ba haihuwarta Momy tayi ba? Irin waƴannan maganganun sune suka kasance a tinaninta.
A ɓangaren Abie kuwa direct office ɗin Cp ya nufa, ka sancewar akwai sanaiyya mai ƙarfi a tsakaninsu ne ya sa bai sha wahalar haɗuwa dashi ba. A hankali ya zauna a kan kujerar da aka ƙawata offishin dasu, cikin nutsuwa ya miƙawa Cp hannu sukayi musabaha cikin raha kamar yanda sika saba idan sun haɗu da juna, hirar mintuna biyar sikayi sannan Abie ya ɗaga kai ya kalli abokin nasa cikin maɗaukakiyar damuwa ya ce,"na rasa abinda yake min daɗi a cikin wannan duniyar Cp, komai ya tsayamin bana jin daɗin rayuwata kamar yanda na saba shekara ɗaya data wuce. har yanzu dai babu wata ƙwaƙƙwarar magana akan ɓatan yarona kullum abu guda kake gayamin zakuyi bincike."
Da fa kafaɗarsa Cp ya yi sannan ya ce " na san kana cikin damuwa abokina saboda ɓatan ɗa kamar muzaffar abu ne mai rikita zuciya ga kowani irin uba, amma don Allah karka wuce iyaka a maganarka tunda dai ka san muna iya bakin ƙoƙarin mu akan lamarin.
Sannan karka manta cewa Ubangiji yana jarraba imaninmu ta ɓangarori da dama musamman akan abinda zuciyarmu tagi ƙauna, na tabbata akwai hikimar data sa Allah ya yi maka wannan jarrabawar, wata ƙila ya ɗauke ɗanka ne don ya gwada imanin ka ne."
Rintse idanunsa Abie ya yi yana jin yanda maganar Cp ɗin take huda zuciyarsa, kallonsa Cp ya yi sannan ya ci gaba da cewa,"Na tabbata dukk irin son da kake yiwa Muzaffar da irin nuna damuwarka akansa bata kai irin damuwar da Annabi Ishaq (A.s) ya shiga a lokacin da ɗansa Annabi Yusuf (A.s) ya ɓata ba, ya shiga jarrabawar mai girma kuma zuciyarsa ta sosu dukda kasancewarsa Annabin Allah. amma haka ya yi haƙuri da jarrabawar data sameshi kuma ya miƙa al'amarinsa ga Allah a ƙarshe wani sakamako ya samu da ga Ubangijinsa?" Cp ya ƙare maganar yana tsareshi da idanu.
Sosai jikin Abie ya yi sanyi sakamakon tinin da yayi masa, cikin jin kunya ya ɗaga kai sama ya ce "ya ubangijina ka gafarta min kuskurena a gareka, Allah kayi min komai a rayuwata na alheri wanda wayona ko dabarata basu isa su bani ba, ya Allah na kasance ɗan adam mai ninƙaya a cikin ajizancina, raunina ya baiyana a lokacin da ka jarrabi imanina da ɓatan Muzaffar. Ya Allah na miƙa al'amarina gareka ka bani ikon cin wannan jarrabawar data sameni!" ya ƙare addu'ar hawaye na kwaranya a saman dattijuwar fuskarsa.
Da Ameen Cp y amsa sannan ya dube shi ya ce "in sha Allah za'a ganshi da ikon Allah, sannan zamu ƙara faɗaɗa binkicen mu a jahohi daban daban, roƙona kawai a gareka shine ka ƙara haƙuri na ɗan wani lokaci in sha Allah komai zeyi dedai."
Shawarwari Cp ya dinga bawa Abie da ga bisani kuma sukai sallama da juna cikin aminci da ƙaunar juna.
*** *** *** ***
*_RUGAR ARƊO_*
Zaune suke cikin Dajin da suka kutsa tareda dabbobinsu Rabe ta ɗaga kai ta kalleshi tace,"Hammah!"
A hankali ya ɗaga lumsassun idanunsa ya sauke mata su a fuskarta, ganin yanda ya ke kallonta ne ya sa tayi dariya cikin harshen fulatanci ta ce,"yau ina cikin madaukakin farin ciki sosai." tayi maganar tana murmushi sannan ta falla da gudu ta buɗa hannayenta tareda lumshe kyawawan idanunta.
Sosai ta bashi dariya don haka ya murmusa tareda sauke idanunsa akan ƙugunta wanda ta ɗaureshi ɗam a cikin zanin farin saki. Farar fatar cikinta yake kallo zuwa cibiyarta wadda shape ɗinta ya fito raɗau, a hankali iska ta fara kaɗa rigar dake jikinta cikin azama ya sauke idanunsa ƙasa yana saurarar yanda ƙirjinsa ke bugawa.
Jikinsa ne ya yi nauyi tamkar wanda aka ɗorawa ƙaton dutse, lokaci guda wata baƙuwar kasala tai masa mamayar ba zata. Yunƙurawa yayi da sauran ƙarfin da ya rage masa tamkar mai koyon magana ya ce,"don girman Allah stop wearing clothes like this ki nemi kayan arzuƙi ki ɗinga sakawa I’m begging you Rabi'atou." ya firta hakan a wahalce yana juya mata baya saboda baya so idanunsa su gano masa abinda zai kasa bacci a jikinta.
Jin sunanta da ya ambata ne ya sa ta biɗe idanunta tana kallon yanda ya juya mata baya, abu biyu taji a cikin maganarsa sunanta da ya kira da kuma kayan arzuƙi da taji yace, da sauri ta zagayo ta gabansa ta tsaya tana ƙiƙƙifta masa idanu tana ƙarewa handsome face ɗinsa kallo ta ce,"me kace?"
Da sauri ya sake juya mata baya yace,"nothing!"
Ƙara dawowa gabansa ta yi ta ce,"kayi magana don Allah me kace." tayi maganar yana langaɓar da kanta idanunta cikin nasa.
Juyawa ya yi da sauri ya ce,"muje kar mu ɓata lokaci a nan." ya yi maganar yana yin gaba ya barta a gurin zuciyarsa na harbawa da ƙarfi, sai da ya yi nisa da inda take sannan ya jingina bayansa da wata ƙatuwar bishiya ya ce,"This girl is going to drive me crazy with her foolishness." ya firta hakan yana ɗora hannunsa a saman ƙirjinsa ta ɓangaren hagu.
Ko da ta ƙaraso gurin bata kulashi ba tayi gaba abinta, saboda ya tafi ya barta a baya, murmushi ya yi sannan yabi bayanta ba tareda ya shigar da kansa cikin shirginta ba, sai da ya ji ya dawo normal sannan ya matsa kusa da ita yana ƙoƙarin takalarta ta hanyar fuxge sandar kiwon dake hannunta.
Binsa tayi da gudu cikin rashin sa'a tayi gaba zata faɗi ya riƙeta, ajiye sandar yayi sannan ya zaunar da ita a ƙasa ya ce,"ki dinga kula idan ba hakaba wata rana zakiji ciwo saboda rawar kanki." ya yi maganar yana ƙoƙarin kai hannunsa ƙafarta ta yi saurin janyewa.
Zama ya yi a gefanta ganin har lokacin bata dena kumburin da takeyi ba ya yi murmushi sannan ya kalleta cikin harshen fulatanci ya ce,"kiyi haƙurin Raben Hamma da Baffah." ya yi maganar yana wani karya wuya kamar yanda ya ga tanayi idan tana jin tsiya.
Haɗe rai tayi sannan ta juya masa baya kaman yanda ya mata ɗazu, dariya yayi mai sauti jin haka ya sa ta juyo tana kallonsa da wani excitement a fuskarta.
ya ce "meyasa ki farin ciki ɗazu?" Ya faɗi hakan yana kallonta
Sinkuyar da kanta ƙasa ta yi kamar ba za tayi maganar ba sai kuma ta ce,"Saboda ka biyoni kiwo a rana ta ƙarshe kafin ka tafi garinku, wannan shine ya sani farin ciki."
"kin tabbata hakane?" ya firta hakan a sanyaye.
"Eh mana saboda wannan babbar nasara ce a Rayuwata cikin zamantakewar da mukayi da kai, ni dai don Allah Hamma idan ka tafi karka manta Dani!" ta ƙare maganar hawaye na zubowa da ga idanunta.
Tunda ta fara maganar yake kallonta tareda maida hankalinsa kanta ya ce "duk irin mutumin da kika fassara ni dashi a cikin ranki to da irin wannan yanayin zan kasance, idan kikasa a ranki zan manta dake tabbas kuwa manta dake Rabi'atou, idan har cikin ranki kina jin cewa ba zan iya mantawa dake ba ni nayi miki alƙawarin zan dawo gareki komai daran daɗewa.!" ya firta hakan yana tsaida idanunsa cikin nata idon wanda ruwan hawaye ya ƙara ƙawata haskensu.
"Ba zaka manta dani ba?"
"Har abadah!" ya firta hakan cikin yaƙini.
A haka dai kiwon ya kasance a gantale kowa da abinda ya ke saƙawa a cikin ransa har suka dawo gida, tun daren Ranar Rabe bata sake shiga ɗakin ba har garin Allah ya waye muzaffar ya fara shirin tafiya, ko kaɗan ba taso ta haɗu dashi a lokacin tafiyarsa tafi so ta fara koyawa kanta haƙurin rashinsa a tareda ita.
Da wannan tunanin ta samawa kanta matsaya tun bayan fitowar alfijir da tayi Sallar Asuba tayi nesa da Rugarsu gabaɗaya, har Muzaffar ya kammala shirinsa ya fito sanye da farin Saƙin Fulani, Sosai kayan suka karɓi jikinsa tamkar dama can Bafulatanin ne.
Har a ransa cikin ransa yake so ya sake ganinta kafin tafiyarsa amma sai ya kasa tambayar Baffah ina take, shi kansa be san sabonsa da ita ya kai wannan matakin ba, amma sai zuciyarsa take ƙoƙarin kunyata shi akan abinda bai taɓa zaton zai faru tsakanin su nan kusa ba. Amma sai zuciyarta takaishi wani matsayi na daban wanda ya wuce na ƴan uwan taka kamar yanda ya jima da ajiye ƴar fillon.
A irin alkhairan da mahaifinta yayi masa bayaso shaƙuwarsa da ita ya Rushe wannan dangantakar a tsakaninsu. A haka suka fito daga ɗakin har bakin ƙofar bukkar jaddah Muzaffar ya tsaya for the first time tun zuwansa rugar ya durƙusawa ya kalleta cikin harshen fulatanci ya ce,"Jaddah ni zan tafi ina roƙon Allah ya saka muku da alkhairi bisa taimakon da kukayi mini, a zaman da nayi dake idan na taɓayi miki wani abu mara daɗi don Allah ki yafe mini." Ya faɗa mata haka sannan ya miƙewa daga ƙofar bukkar ya juya.
Taɓe baki Inna Jaddah tayi ta ce"o'o ɗannan ba kai mini komai ba, hasalima ni daɗin tafiyar taka nakeji saboda ban san tsiyar da take tareda kai ba, ni da zaka temakeni ma wllh idan ka fita da ga Rugar nan ka roƙi Allah ya mantar da kai hanyar shigowa garin nan gaba ɗaya." ta yi maganar tana raka bayansa da harara.
Murmushi yayi ba tareda ya juyo ba ya ce "in sha Allah zanyi Addu'ar Allah ya mantar dani ƙofar ɗakinki amma ba Rugar nan gabaɗaya ba." Be jira cewarta ba yayi gaba abinsa.
Har cikin zuciyarsa Baffah yake jin tafiyarsa saboda yanda sabon da sukayi da juna, Babur ɗin malam Iro moddibo ya karɓo Aro sannna ya ɗauki muzaffar a bayan Mashin ɗin suka tafi ya kaishi tashar dake cikin Gari.
Sai da ya shiga motar ya zauna sannan Baffah ya biya masa kuɗin mota bayan ya danƙa masa wasu kuɗin a hannunsa saboda guzuri, sannan ya juya idanunsa a cike da ƙwalla ze tafi, da sauri muzaffar ya buɗe motar ya sauka sannan yabi bayansa ya Ringumeshi.
Sun jina a haka sannan ya zare jikinsa daga ruƙon da Baffah ya yi masa ya kama annunsa ya ce "Bani da isassun kalmomin da zanyi godiya a gareka Baffah, amma ina roƙon Allah ya gina maka babban gida a gidan Aljanna!"
Zare hannunsa Baffah yayi daga nasa sannan ya juya da Sauri yana hawaye batareda ya juyo ba ya kunna mashin ɗin ya bar Gurin muzaffar na kallonsa.
Sosai zuciyarsa tayi mugun Rauni amma kuma bashi da wani zaɓi dole ne ya koma gida ko dan saboda iyayensa da sauran ƴan Uwansa. Yana nan tsaye motar ta cika suka kama hanya zuciyarsa a cike Fal da kewar Fulanin Dajin.......
*_Naga ƙaunar ku da Soyayyarku akan wannan littafin tareda Addu'o'in alkhairi, thank you for the love ubangiji yabar zumunci. Amma ku daure ku dinga yi mini react🤩
Comment
And
Share
Zmc💋
***