BAFULATANA🐄

Chapter 9

by @zmchubado

*BAFULATANA*

Zm~Chubaɗo

09

Tun da ya shiga cikin motar sai kasa nutsuwa zuciyarsa ta tsananta bugu fiye da farko, a hankali ya lumshe idanunsa for the first time a rayuwarsa zai yi doguwar tafiya a motar haya, lokacin da ya jingina bayansa da sit ɗin motar abu biyu ne keyi masa yawo cikin zuciya.

Na farko shine ƙwallar da ya gani a maƙale cikin idon Baffah wanda ya keda tabbacin ƙaunar da yakeyi masa ce silar hakan, abu na biyu kuma shine sabon da ya bari ya shiga tsakaninsa da ƙaramar yarinyar da ko'a mafarki bai taɓa zaton zau iya samamata gurbi a cikin zuciyarsa ba, saboda shi a tsarinsa babu maganar Soyayya a cikinsa, shin yanzu a wani hali zata kasance bayan tafiyarsa?

Ajiyar zuciya ya sauke a karo mara adadi basu iso garin Abuja ba se ƙarfe 8 na dare, kuɗin da modɗibo ya bashi ya kalla sannan ya tare Taxi yace "Maitama zaka kaini. Daga haka ya buɗe motar ya shiga ciki suka ɗauki hanyar Maitama, har Suka isa cikin Maitama Muzaffar na tunanin makomar Yanda Rabe Zata kasance a sanadin tafiyarsa. Me taxi ɗine ya katseshi ta hanyar cewa "malam mun iso maitama fa a ina zan ajiye ka?

Shiru yayi kimanin ƴan sakanni sannan ya faɗa mishi inda ze kaishi, a bakin ƙofar makeken get ɗin gidansu me motar ya faka sannan Muzaffar ya fito tareda miƙa masa kuɗin motar, yana karɓa yaja motar yayi gaba abinshi a ransa yana mamakin ganganci irin na wannan Bafulatani

A nitse yake takawa har ya isa jikin Get ɗin tareda Sanya babban yatsansa na hannun damansa a jikin tompprint ɗin dake Jikin Get ɗin take get ɗin ya buɗe kansa, yana shiga cikin gidan kafin Get ɗin ya ida rufewa ya juya yana kallon waje yace "Nande feri miwarti in sha Allah Rabi'atou! Mimeɗataye yejutugo beko awanniyam. Zan dawo dole watarana zan koma gareki my Fulani girl." 
A nitse yake tafiya gabaɗaya jikinsa babu ƙwari har ya isa farfajiyar gidan, tun kafin ya sake ɗaga ƙafarsa guards ɗin dake tsaron gidan ta ciki suka kewayeshi suna tambayar shi waye kuma ina zashi?

Shiru yayi kawai yana kallonsu don bai san ta ina zai fara amsa masu tambayoyin da sika rikitashi dasu ba, takaicinsu ne ya cikashi amma still ya kasa cewa komai sai kallonsu kawai da yakeyi. Kayan jikinsa ya kalla lokaci guda kuma ya maida hannunsa kan lallausar Sumarsa data fara fitowa sosai kuma tayi yawa saboda Askin da Baffah yayi masa lokacin da ya tsince shi.

yace,"tambayar za kuyi ta jerowa kokuma amsar kuke so in baku?" Muzaffar ya faɗi hakan yayinda yake gyara tsaiwarsa irin wadda ya sabayi a duk lokacin da yaci nasara a kan abinda yasa a gabansa.

Take idanunsu ya firfito wajen yayinda kunnuwansu sukai Arba da Amon muryar muzaffar me cikeda tsantsar izza gamida yarda da kai, zubewa su kai a ƙasa gabaɗayansu suna masu ban haƙuri a gareshi tareda murnar dawowarsa, kallon tsaf yayi masu sannan ya daɗa gyara tsaiwarsa ya ce"na gode amma ina saƙon da zan baku, banaso kowa ya san ina cikin gidannan don Allah." Ya gaya masu haka sannan ya juya a hankali ya fara tafiya.

Da sauri ɗaya da ga cikin Guards me Suna Selomon ya ce,"but why? kullumfa se babban megida ya shiga damuwa wasu lokutan ma har kuka ya keyi saboda ɓacrwarka, amma kana ganin hakan baze zama matsala ga lafiyarsa ba?"

Tsayawa ya yi cak ba tareda ya juyo ba ya ce,"abinda na bada umarni kenan Selomon kuma duk wanda ya saɓawa ƙa'idata a bakin akinsa." Ya faɗa yana barin gurin cikin nutsuwa hannayensa zube cikin aljihun wandonsa.

Direct Side ɗinsa ya nufa tareda murɗa haɗaɗɗen Handile ɗin dake jikin ƙofar, Masha Allah haƙiƙa wannan falo ya gama ƙawatuwa da dukkan ababan ƙyaleƙyale na Duniya, dukda cewar babu wani tarkace a falon amma komai na cikinsa i s very Expensive and classy, hular dake rataye a bayansa ya cire tareda hurgata a saman manyan Royal chairs ɗin dake falon masu launin Golden da yarfan Ruwan Zinare, maida kallonsa yayi kan makekiyar tv ɗin dake falon wanda take very slim babu wani tudu a tareda ita, ɗan tsaki yaja kaɗan sannan ya wuce Bedroom ɗinsa. 

Nan ma faɗar irin haɗuwar ɗakin wllh ɓata lokaci ne a gareni tareda ku masu karatu, amma hasashen haɗuwar ɗakin C.E.O of xafar ɗin ya rage gareku readers😂 kunsan abinku da matashi me jini a jika kuma ɗan ƙwalisa me citta a hannu dole ne komai nasa ya zama Very Expensive and classy.

Toilet ya nufa Direct ya buɗe shima nan ɗin dai ba'a magana domin kuwa babban guri ne me zaman kansa wanda ya haɗa da kayan ƙawa na ban mamaki, babban jakuzi ne daga can gefe se kuma wani falelen abu daga gefe wanda yafi kama da bahon tare ruwa,amma shi yana da girma sosai don mutum ze iya shigewa cikinsa complite.

Gefansa kuma wata slim drower ce wadda aka zuba towels farare masu azabar kyau gamida burgewa, Direct kusa da wannan abun me kamada bahon wankan ya nufa sannan ya kara hannunsa daga gefan wani Rami dake jikin abin take ruwa ya fara ɓulɓulowa daga cikin abin, kafin kace me tuni Ruwan ya gama taruwa kuma still ruwan da zafinsa daidai yin wankan mutum, zare rigar dake jikinsa yayi sannan ya raba kansa da wandon saƙin dake jikinsa.

Nan take murɗaɗɗen jikinsa gamida faffaɗan ƙirjinsa suka baiyana, se'a lokacin na fahimci cewar lallai matashin ma'abocin cikar zati ne gamida haiba duba da irin yanda zanen 6part ɗin dake cikinsa suka baiyana a fili, cikin bahon ya shiga ya zauna tareda lumshe manyan idanunsa saboda yanda zafin Ruwan yake ratsa duk wata gaba dake jikinsa, seda ya shafe kusan 30mnt a haka sannan ya fito ya danna wani buttum dake jikin abin ruwan ya tsiyaye sannan ya shiga jakuxi ɗin yayi wanka ya ɗauro wani babban towel a jikinsa tareda ratayo wani ƙaramin towel ɗin a wuyansa.

Goge gashin kansa yayi da ƙaramin towel ɗin dake wuyansa sannan ya buɗe Makekiyar closets ɗinshi dake manne a jikin bangon ɗakin, ɓangaren ƙananan kayansa ya bude ya zaro wasu pijamas Ash color masu taushi ya saka a jikinsa.
Sannan ya tada Sallar magrib dake kansa sannan yayi isha gaminda shafa'i da wutiri, seda ya gama tasbihinsa sannan ya miƙe a matiƙar gajiye yayiwa kansa masuki a kan ƙaton bed ɗinsa wanda yayiwa ɗakin ƙawanya, yana kwanciya wani wahalalllen baccin gajiya ya ɗaukeshi.

Ɓangaren Abie kuwa sosai suka sake dagewa da Addu'o'i akan ɓatan ɗan nasu, Momy ce zaune bisa Daining ta zubawa abincin da zainab ta zuba mata idanu batareda takai koda cokali ɗaya bakinta ba, hakama Abie wanda ke gefan momyn cike da damuwa Zainab ta kalli iyayen nata tace "Haba Abie don Allah ya kamata kuyi haƙuri da jarrabawar da Allah ya aiko mana, idan har ku iyayenmu kunasa damuwa a zukatanku irin haka mukuma idan wani abun ya sameku a sanadin hakan ya kuke tsammanin zamuyi da Rayuwar mu?"

Ajiyar zuciya Abie ya sauke lokaci guda kuma ƙwalla ta samu gurɓi a cikin ƙwayar idonsa ya ce "ki yi haƙuri daughter ni kaina abin ne yakeso yafi ƙarfina, wllhi kaina duk ya kulle sabida ɓatan yaron nan ta ya zan kwantar da hankalina?"

"Amma Abie ai...." 

Ƙarar wayar Abie ce ta gauraye falon gaba ɗaya ya sa Zainab ta yi shiru tana kallon Abie ɗin, Ƙurawa wayar idanu yayi yana kallon screen ɗin tareda sunan wanda ke kiran nashi, abokin kasuwancinsu ne wanda zasu zauna dasu gobe da safe akan harkar kasuwanci kuma ya tabbatar idan mutumin ya san Muzaffar bayanan tabbas zecire hannun jarinsa dake Companynsu, wanda hakan babbar asara zai janyowa kamfanin.

Fadilah dake cin abincinta hankali kwance ta ɗaga kai ta kalli Abie tace "ka ɗaga wayar hankalinka kwance kuyi magana dashi Abie, saboda idan har yayi magana dani gobe ba zai sake ambaton sunan yaya ba sai dai kaji yana kiran sunan MD Fadilah."

Taɓe baki Zainb tayi ta ce "ga dukkan alamu kwaɗayin neman kujerar C.E.O yasa Fadilah Abdulwahab ta fara yaudarar kanta wajen haɗa ƙwarewarta data namijin duniya." ta faɗi haka tana ƙyalƙyalewa da dariya.

A Fusace Fadilah tayi kanta, zainab ta mike da gudu ta haura sama ta shige ɗakinta ta murza key, sannan ta ƙara fashewa da dariya ita kuma fadila sai buga mata ƙofar dakin take kamar zata ɓalla. Haka Fadilah ta gama tsaiwarta tana jaraba harta gaji tabar gurin Zainab na dariya bata daina ba.

Ba yanda Dady ya iya dole ya ɗaga wayar kuma ya basu tabbacin cewa Muzaffar ze halacci meeting ɗin 11am dot. Kallonsa kawai momy keyi fuskarta ɗauke da mamki tace"haba Abie meyasa za kayi alƙawarin da ba zaka iya cikawa ba?"

Kamar zeyi kuka yace "To ya zanyi dasu fisabilillahi? Nikam banida wata mafita wadda tafi haka." Miƙewa momy tayi tabar masa falon don ba zata juri irin wannan sanya ran na Abie, a haka lamarin ya kasance da ga bisani Abie ya miƙe yabi bayanta.

*** *** *** ***
*_RUGAR ARƊO_*

Tun da ya tafi komai ya daina yi mata daɗi, wannan dalilin ya sa ta ɗaura ɗamarar cire sabon da tayi dashi a cikin ranta amma sai hakan yafi ƙarfinta, sai kawai ta fashe da kuka saboda bata san halinda Rayuwarta kasance ba a nan gaba, bata taɓa zaton cewar shaƙuwarta dashi takai wannan matakin ba amma kuma se gashin lamarin ya zarta tunaninta da Fahimtarta, a yanda takejin zuciyarta a halin yanzu komai ze iya faruwa da ita.

A wannan daren tayi kuka kamar Ranta ze fita da ga ƙarshe ta haƙura ta miƙawa Allah lamarinsa, da ace ta san irin halin da zata shiga kenan da tun farko bata barin sun saba da juna ba, a haka wani wahalallen bacci yay Awon gaba da ita bisa ƙaramar katifar ciyawar dake ɗakin.

******

Abuja Nigeria

Washe gari ko Sallah Asuba Muzaffar be samu ba saboda baccin gajiyar da yasha kansa, a gaggauce ya tashi yayi Sallar Asuba ko tasbihi beyi ba ya miƙe ya koma gado ya kwanta, be farka ba se waje ƙarfe goma na safe, wanka ya shiga sannan ya fito ya tsaya a gaban wata ƙaramar drower din dake gefan closets ɗinsa. Wali emvlop ya zaro ya buɗe ya fara duba Abubuwan da yay missing a sanadin ɓatansa, tsaki yaja kaɗan lokacin da ya gama karanta saƙon dake cikin emvlop ɗin.

Mayar da takaddun ya yi sannan ya buɗe ƙatuwar closets ɗinsa wadda ke ɗauke da Haɗaɗɗun korian Suite ɗinsa masu masifar kyau da tsada, wata baƙar Suite ya zaro a jikin hanga ɗinta ya jefata kan gadosannan ya fara shiryawa cikin Sauri, cikin mintunan da ba zasu gaza 10 ba ya kamala shiryawa, wayarsa dake gefan gado ya ɗauka ya shiga kiran Samuwal.

Samuwal na ɗaga wayar Muzaffar ya ce,"I've finished getting ready, and I don't want us to delay."

"ok sir!" in ji samuwal

Katse wayar muzaffar yayi sannan ya tsaya a gaban mirior yana gyara lallausar sumar dake kansa, cikin mintina kaɗan su Samuwal suka iso gidan bayan fitarsu Abie da Fadilah.

Motocine a jere kimanin guda 5 ƙirar Formatic C350, tun kamin ya fito Suka firfito suna jiran fitowarsa, a nitse ya kammala shiryawa cikin black suite ɗin wanda tabi jikinsa ta kwanta, sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu ƙamshi ya fito yana ƙoƙarin ɗaura agogon fatar dake hannunsa, a nitse yake tafiya cikin isa da ƙaisata ya fito harabar gidan, kai tsaye motar da samuw ya buɗe masa ya shiga ya zauna, sannan suka ɗauki hanyar Compayn Zuciyarsa a dake.



Wllhi zazzaɓi nake fama dashi saisa kukaji ni shiru .

Zmc💋
***