BAFULATANA🐄

Chapter 10

by @zmchubado

BAFULATANA

Zm~Chubaɗo

010

Gudu suke sosai akan tinti inda shi kuma muzaffar lokaci bayan lokaci yake kallon agogon Fatar dake ɗaure a tsintsiyar Hannunsa, a haka sika iso katafaren Companyn, inda aka tanada don ajiye motoci suka isa sukai parking cikin jerin gwano, cikin hanzari guards ɗin suka fito suka tsatstsaya suna masu jiran Umarni, samuwal ne ya ƙaraso jikin motar da muzaffar ke ciki ya buɗe masa sannan ya fito yana me gyara zaman Korean Suite ɗin dake jikinsa.

A nitse ya ɗaga idanunsa yana kallon companyn kimanin mintuna 2  sannan ya fara tafiya a hankali zuwa cikin Companyn Guards ɗinsa na take masa baya, a bakin conference hall ɗin da suka saba meeting da manyan masu hannun jarin dake Companyn ya tsaya Dai-dai lokacin da Fadilah ta miƙe tana gabatar da jawabinta wanda take da tabbaci akan ze kawowa Companyn nasu cigaba.

Tana cikin jawabin ƙofar glass ɗin dake gurin ta buɗe take muzaffar ya baiyana yana me takowa zuwa inda mutanan dake cikin gurin suke zaune, wani irin zaro idanu Fadilah tayi saboda tsaɓar firgici da mamakin da yayi mata mamayar ba zata, Lokaci guda kuma maganar da take ƙoƙarin faɗa ta maƙale mata a maƙoshinta, shi ko Abie gabaɗaya yama kasa motsin kirki illah kafeshi da yayi da idanunsa yana kallon tilon ɗan nasa tamkar a mafarki, Muxaffar be dire a ko ina ba se'a gaban Magigin da Fadilah ta saita tareda zareshi ya juya yana kallonta da lumsassun idanunsa, lokaci guda kuma ya ɗauke idonsa a kanta ya fara gudanar da jawabinsa cikin ingantaccen turancinsa mai daɗin sauraro.

Yanda yake jawabin sai ka rantse zama shekara ɗayan da yayi tareda su Baffah zaman bitar jawabin da yake gabatarwa ɗin kawai yayi, wani malolon takaici ne ya tasoma Fadilah ya tokare mata Maƙoshi, a fusace ta Raɓa ta gefansa ta wuce ta koma gefan Abie ta xauna lokaci guda kuma ta fashe da kuka.

Ko ta kanta Abie bebi ba saboda yanda zuciyarsa ta cika da tsananin farin ciki, kallonsa kawai Abie keyi fuskarsa a ɗauke da wani ƙayataccen murmushi lokaci guda kuma ya zube ƙasa yana me sujjadar nuna godiyarsa ga Ubangiji,  awa ɗaya cur suka kwashe tare dasu  Vikram Aditiya sannan suka futo daga Meeting ɗin kowa fuskarsa ɗauke da Murmushi saɓanin Md Fadilah wadda ta cika tai fam, Suna fita Abie ya kama hannun ɗansa ya riƙe gam lokaci guda ya fashe da kuka ya ce," ina ka shiga tsahon wannan lokacin ka barmu da fargabar nemanka? Shin ka san a wani irin hali muka shiga kuwa?"

Jikinsa ne yay masifar sanyi har bai san sanda ƙwalla ta cika ƙwayar idanunsa ba, cikin wani irin raunin murya ya ce,"Abie ba da gangan nayi ba, ƙaddarar rayuwa ce ta jefani cikin wata duniyar daban wanda bani da ikon kyauce mata, Abie tsautsayi na haɗu dashi a hanyata na dawowa daga taraba." 

Hannunsa Abie ya kama cikin nasa sannan ya ƙara fashewa da kuka ya ce,"mun azabtu ƙwarai harma mun fara yanke ƙauna aƙan zaka dawo garemu." abie ya faɗi hakan yana ƙare ƙanƙame hannunsa cikin nashi.

Risinawa yayi tareda zube  gwiwoyinsa biyu a ƙasa sannan ya haɗe hannayensa biyu alamar roƙo still yana kallon Abie ɗin ya ce," nayi kuskure da ban waiwayi gida ba tsahon wannan lokacin, na sanyaka kuka a lokuta mabanbanta Abie amma duk banyi hakan da nufi ba, Allah ya ƙaddara sai na shafe shekara guda sannan zan ƙara dawowa cikin familyna but don Girman Allah Abie ka yafemin plsss!"

Hannunsa ya sanya yana sharewa Abie hawayen dake Sakko masa yace" wannna hawayen kaɗai ya isa yasa naga badaidai ba a Rayuwata Abie, don Allah kayi haƙuri kuma ka yafemin laifina. Ajiyar zuciya Abie ya Sauke ba tareda ya iya tsayar da ƙwallar dake sakko masa ba ya ce,"Amma ina ka tafi tsahon shekara ɗaya baka waiwayemu ba?"

Kasa kallon Abie ya yi lokaci guda kuma y kalli ƙofar glass ɗin dake office ɗin ya ga babu kowa a gurin sannan ya kama hannun Abie ya ce,"zancen dogone amma zan sanar da kai komai idan muka koma gida." Ya faɗi hakan yana miƙewa da sauri yana bin ko wace kusurwa dake cikin office ɗin Abie da manyan lumsassun idanunsa.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce,"Abie zan koma gida yanzu tunda na gama gabatar da abinda ya kawoni, na san momy ma tana da nata tarin tambayoyin da zatai mini. but don Allah Abie idan munje gida karka barta tayi min wata tambaya wadda zata bani wahalar amsawa akan wannan al'amari pls Abie."

Cikeda ƙosawa da maganganunsa Abie yace "dole ne ka amsa mana duk tambayoyin da suke bakin mu tunda har ka iya barin mu ka tafi wani gurin ba tareda sanin mu ba, karfa ka manta rabon da na sake sanyaka a idanuna tun daran wata litinin da muka Rabu dakai akan washe gari zaka wuce taraba sai yanzu, don haka ya zama wajibi ka sanar dani gidan Uban da ka tafi ba tareda sanin iyayenka ba in dai har nine Ubanka ba wani ba!"

Zaro ido Muzaffar ya yi zuciyarsa na bugawa jin abinda Abie ɗin yace, tabbas yau dai kam bashi da wata mafitar da zata sa Abie ya janye ƙudirinsa na seya sanar dashi inda yaje, baya jin ze iya sanar da Abie ainihin abinda yake ɓoye masa sabida yasan zuciyarsa da kunnuwansa ba zasu taɓa iya ɗaukar maganar ba. Don haka seya kafe Abie da manyan idanunsa ya Fashe mishi da kuka kamar Allah ya Aikoshi.

Nan take hankalin Abie yay masifar tashi ya miƙe da sauri yana tambayarsa dalilin kukan nasa, a zuciyar muzaffar ba ƙaramin dariya abin ya bashi ba amma da yake ɗan duniya ne seya sake Rushema Abie da wani ɗan iskan kukan dayafi na farko ya ce,"don Allah Abie ka dena tambayana akan inda naje pls idan lokaci yayi i promise zan sanar da kai komai don Allah ka yarda dani Abie trust me don Allah." Ya faɗa yana shirin ƙara sakin wani sabon kukan.

Da sauri Abie ya dakatar dashi ta hanyar rungumeshi yana faɗin "is Ok son kukan ya isa haka tunda dai Allah ya dawo mana da kai lfy ai shikenan."

dariya muzaffar yayi mara sauti sannan ya zare jikinsa daga na Abie a shagwaɓe yace,"Abie pls let's go home I want to see my mom."

Murmushi Abie ya saki sannan ya Kama hannunsa ya riƙe gam ya ce,"da fatan ka tanadi bayanan da zakayiwa ƴan jaridar da nasa a tara maka su a waje, ɗan wara idanunsa yayi kaɗan sannan ya laso lips ɗinsa kaɗan yace "uhmm Abie nikam ban shirya magana da su ba don Allah a bari se gobe."

Jansa Abie ya yi suka fita yana masa dariya har farfajiyar gurinda ƴan jaridar suke nan da nan suka shiga jera masa tambayoyi yana basu amsa har kimanin mintuna goma sannna suka sarara masa. Nan da nan kuwa zancen baiyanar Muzaffar ɗin ya cika gari lungu da kuma saƙo.

Bayan sun kammala hirar da ƴan jaridar ne suka shiga mota ɗaya tareda Abie, still yana riƙe da hannunsa guards ɗin muzaffar na take musu baya sannan motocin suka fara fita a cikin jerin gwano kamar yanda suka saba.

Duk abinda ke faruwa Fadilah na kallo ta window ɗin glass ɗin dake office ɗinta fuskarta duk tayi ja alamar ta jima tana kukan ɓaƙin cikin data ɗorawa kanta a banza a wofi, lokaci guda ta sake haɗe kanta da gwiwa ta ƙara fashewa da kuka inda wani ɓangare na zuciyarta ya samu gurbin cika da zallar tsanar Muzaffar ɗin. Kamar mahaukaciya ta ɗauki system ɗin dake kan table ɗin dake gabanta tayi jifa da ita ta bugi bango ta fashe sannan ta ɗora hannu aka cikin ɗaga murya ta ce,"meyasa kake shiga tsakanina da ɗaukakata ne Muzaffar? Wllh na tsaneka na tsaneka kamar yanda na tsani mutuwata, saboda kaine mutum na farko a Rayuwata daya zame minu katangar tsakani na da ɗaukakar da nake nema a duniya!' Ta faɗa tana ihu kamar zararriya.

Ɓangaren muzaffar da Abie kuwa hankalinsu kwance suka iso katafaren gidan, wani ɗan ƙaramin Abu me kamada rimote Abie ya matsa take get ɗin ya buɗe moticin suka danna kai zuwa ciki, a hanzarce Samuwal suka furfuto kana suka buɗewa uba da ɗan motar suka fito, a nitse Muzaffar ya zagayo ta side ɗin abie tareda kama hannunsa suka nufi main falon dake gudan, kana kallonsu za kaga zallar kamar da suke da juna tamkar an tsaga kara.

Da sallama suka shiga falon wanda hakan ya yi dedai da fitowar Momy da ga khitchine hannunta ɗauke da glass cup, take ta saki kofin ya faɗi ƙasa ya tarwatse bakinta na rawa ta shiga nuna ƙofar falon ba tareda ta iya furta komai ba..........


Wllh har yanzu jikina bai warware ba kuyi haquri dani zuwa lokacin da zan ji sauqi.

***
Comment 
Nd
Share

💋