BAFULATANA🐄

Chapter 11

by @zmchubado

BAFULATANA

Zm~Chubaɗo


Alhamdulillah! Yau na ɗanji dama'dama, na gode ƙwarai da addu'o'in ku Allah ya bar zumunci. Page ɗin dai bai da tsaho ayi haquri zuwa lokacin da Ubangiji zai bani lfy cikakkiya. I love u all🥰


011

idanuntane  suka ciko da  ƙwalla cikin ƙanƙanin lokaci ziciyarta tayi rauni,  farin ciki mara misali ya yiwa zuciyarta mamayar bazata, cikin sauri da azama ta isa inda yake tsaye idanunta na tsiyayar kwallah ta tsaya, lokaci guda kuma ta miƙa hannunta na dama zuwaga kyakkyawar fuskarsa tana me sakin kukan data jima tana dannewa, rungumeshi tayi ƙam a jikinta tana kuka sosai. 

Jikinsa ne yayi bala'in sanyi lokaci guda kuma yaji tausayinta na mamaye duk wata gaɓa dake jikinsa ya ce,"mom don Allah ki daina kuka pls, farin ciki ya kamata kiyi ba kuka ba don Allah kiyi shiru!"

Zare jikinta tayi daga nasa tana me  zubar da hawaye wanda yafi kamada na farin ciki da tsananin kewarsa da tayi ta ce,"ina ka shiga tsahon wannan lokacin ka barmu da ciwuka a zukatan mu?"

Share mata hawayen yayi da farin hanky ɗin dake hannunsa sannan ya kama hannunta suka ƙarasa cikin falon ya zaunar da ita Tareda zube ƙafafunsa a ƙasa suna masu fuskantar juna ya ce,"wannan maganar bata yanzu bace Momy ni dai fatana bai wuce ki kwantar da hankalinki ki daina  wannan kukan da kikeyi ba, Wallahi momy, your crying really affects me a lot. I don’t like seeing you cry it makes my heart very restless and worried. Kiyi haƙuri Please."

Ajiyar zuciya Abie ya sauke sannan ya kalleta ya ce,"kiyi haƙuri ki bar kukan hakanan tunda dai damuwar tamu ta yaye gabaɗaya semu godewa Allah."

Zainab ce ta shigo falon fuskarta a haɗe kamar za ta yi kuka batareda ta lura da Muzaffar wanda ke zaune a ƙasan kafet ɗin da yayima falon kawanya ba ta kalli Abie ta ce,"don Allah Abie kalli abinda ya Fadilah tama wayana Don kawai na gaya mata gaskiya."  Ta faɗi hakan idanunta na cikowa da ƙwallar takaici.

Hannu Abie ya miƙa mata alamar tazo gareshi ba musu kuwa ta nufeshi ta zauna a gefansa tana sakin kukan data jima tana dannewa,  murmushi Abie yayi  sannan yace "ya isa haka nan in dai wayace silar zubar hawayen zainaban Abie to ya zama ɗole a gareni in siya miki duk wayar da kikeso."

  "A'a Abie ninan zan Siya mata waya ba sai ka wahalar da kanka ba tunda har tana dani."     Muzaffar ya faɗi hakan yana murmushi.

Da wani irin mamaki da kaɗuwa Zainab ta kalli Direction ɗin da muzaffar ɗin ke zaune se faman murmushi yake mata, da gudu ta miƙe daga gefan Abie ta nufi muzaffar ta rungumeshi tana ƙara sautin kukanta, wanda ya rikiɗe ya koma na zallar farin ciki, zareta ya yi daga jikinta yana binta da hararar wasa ya ce"The way you’re crying, you sound like a small child.."

Bige masa hannu tayi tana turo baki ta ƙara Hugging nasa sosai. Dariya kawai Abie yayi sannan ya miƙe yana kallon muzaffar yace "oya tashi muje falona I want to talk to you about something."  Miƙewa yayi  da sauri ya ce,"to ranka ya daɗe Alhaji Abie." Gabaɗayan falon dariya sukayi sannan Abie ya kama hannunsa sukabar falon zuwa harabar gidan ta baya inda makeken  Guiding ɗinsu wanda aka ƙawata da abubuwan rayuwa na jin daɗi kala daban-daban.

*_MUMBAI INDIA_*

Zaune take cikin makeken falonta na alfarma hannunta ɗauke da System wadda ke ajiye a gefanta idanunta manne da glasshin ƙara ƙarfin gani, da ga yanda ta nutsu tana kallon system ɗin kaɗai zaka fahimci a kwai abinda takeyi me matiƙar mahimmanci a ciki, wayarta ce ta ɗauki ruri wanda hakan ya sa ta ɗago dara'daran idanunta tana kallon wayar,  Abie shine sunan daya baiyana akan screen ɗin wayar.

Ɗan murmushi tayi irin na manyan matan da suka fara manyanta sannan ta dakatar da Abinda takeyi ta fara ƙoƙarin amsa wayar still tana murmushi.
Da ga ɓangaren Abie ya ce "Assalamu'alaikum!" Ajiyar zuciya ta sauke mai zurfi sannan Hajiya Aisha ta ce,"wa'alaikumussalam Abie ya gda ya kuma aiki?"

Zuciyarsa a dake yace,"lfy lau Aisha yakamata fa ki fahimci cewar dukkan abinda na gaya miki akan dawowarki Nigeria bawai ina wasa bane, banaso ki ƙureni  har nayi miki abinda tun ƙuciyarmu dake banyi miki ba, kullum lamarinki ƙara gaba yakeyi a duk lokacin da nayi miki maganar dawowa Nigeria, to wllh kiji ki sani muddin baki bi Umarni na a wannan lokacin ba wllh ba zan sake nemanki ba! Inyaso duk abinda kikaga yafi miki sai kiyi."  Tun kafin tayi magana Abie ya katse wayar yana huci.

Ƙurawa wayar idanu tayi lokaci guda kuma ta Fashe da wani irin kuka, cikeda rashin sanin mafitar da ya kamata ta kama, sai a yanzu take ganin wautar kanta data bari saɓani ya samu gurɓi a tsakaninta da mijinta, mai ya sameta haka? Mai ya shiga kanta data fara jayayyah da Umarnin mijinta?.  Sai da tayi me isarta sannan ta share hawayenta ta mike ba tareda ta kashe System ɗinba ta haura upstairs, toilet ta shiga ta ɗauro Alwala saboda gabatowar lokacin sallar Zuhur, bata jima a toilet ɗin ba ta fito Direct kan daddumar dake shimfiɗe a ɗakin daga kusurwarn gado ta nufa bayan ta ɗauki farin dogon hijabin da take sallar dashi sai ƙamshi yake bazawa, ta kabbara sallar, ta jima kafin ta idar nan ma seda ta shafe awa guda tana addu'o'inta sannan ta shafa.  Wayarta ta janyo ta shiga kiran Muzaffar harta masa 2 miss call amma be ɗagaba dole ta haƙura ta fice daga ɗakin tana me nanata maganar da Abie ya gama faɗa mata a ƙoƙon zuciyarta, har cikin ranta takejin cewar ta tsani Nigeria irin tsanarda ko'a mafarki bata taɓa ganin irinta ba!   Shin meyasa Abie yake ƙoƙarin tilasta mata komawa ƙasarta ta haihuwa gamida yi mata barazana akan hakan?

Wannan shine abinda ya faru a ƙasar india tsakanin Abie da Hajiya Aisha

*_RUGAR ARƊO_*
Rayuwa ta juya mata sosai fiyeda yanda ta santa a baya, ko wace rana ta kan tsaya a bakin hanya tana kallon masu shiga da masu fita tareda sanya ran cewa zata ganshi ya dawo kamar yanda ya yi mata aƙawari. Amma haka zata gama tsaiwarta a gurin ta koma gida washe gari ta ƙara dawowa ta tsaya.

Yauma a zaune take ta haɗe kanta da gwiwa tana aikin daya aureta a ƴan kwanakin nan wato tunani, Baffah ne ya fito cikin shirin tafiya kiwo tsayawa yayi daga ɗan nesa da ita yana kallonta gabaɗaya ta gama ramewa babu abinda ya rage a kan fuskarta se dogon hanci da idanu, sosai yake tausaya mata dukda cewar ya gama karantar abinda ke kwance cikin ƙwayar idanunta a matsayinsa na uba gareta dolene ya fahimci damuwarta koda baze iya tsinana mata komai a kai ba.

A hankali yake ɗaga ƙafafuwansa waƴanda sukayi masa nauyi harya isa gareta ya durƙusa kan ƙafafunsa ya kai hannunsa kan fuskarta, ɗagowa tayi a sanyaye suka haɗa ido da mahaifin nata lokaci guda kuma ta saki wani irin kuka wanda ya taso kai tsaye daga ƙasan zuciyarsa. Shiru moddibo yayi yana me bubbuga bayanta ba tareda yayi yunƙurin hanata kukan ba, a haka Jaddah ta fito ta samesu, taɓe baki tayi daga inda take cikin harshen Fulatanci tace,"indai kuka ne wllh yanzu kika fara tunda kika biyewa kaɗo ya kaiki ya baro, kin biye masa ya gama lalataki ya yi tafiyarsa, ai yanzu kika fara kuka don wllhi baki ga komai ba."

A fusace modɗibo ya kalleta zuciyarsa na tafasa ya ce"Haba Jaddah! har zuwa wani lokaci  zaki ɗauka kina ƙara rura wutar hassadar dake ci a cikin zuciyarki?  Wllh inaji miki tsoron ranar da zaki girbi abubuwan da kike shukawa da hannunki."

Taɓe baki tayi tana binsa da wani ɗan iskan kallo wanda yafi kamada na rainin hankali ta ce, "meko zan girba wanda ya wuce alkhairi?  Wllh moddibo bazan girbi komai ba sai alkhairi." Ta faɗi hakan tana barin gurin.

Da ido kawai Moddibo yabita batareda ya iya furta koda kallama guda ba,  ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Ya Allah kayi mana tsari da cutar hassada wadda zata makantar da ganin mu zuwa wani al'amari na daban.!" 

A halin da yake ciki a yanzu abubuwa da yawane suke addabar zuciyarsa wanda shi kansa ya rasa ta hanyar daze iya warwaresu face ya miƙa lamarinsa ga Rabbissamawati wal'ardi.
Hannunta ya kama suka nufi garken shanunsu, shida kansa ya kwance shanun sannan ya kaɗasu suka tafi kiwo zuciyar ko wannanesu a dagule, saɓanin Rabi'atu wadda soyayyar muzaffar ta gama zagaye duk wata gaɓa ta jini dake cikin jikinta.

        ********

Al'amarin muzaffar kuwa sosai yake gudanar da abubuwan dake gabansa yama manta da rayuwar da yayi shekara ɗaya a wani daji tareda wasu fulani masu karamci, shi kansa be fiye samun lokacin kansa ba har aka shafe wata Shida cur yana yawo a ƙasashen duniya don bunƙasa hannun jari da kasuwancin mahaifinsa......... A ɗan wannan lokacin daga dawowarsa zuwa yanzu baze iya cewa ga lokacin da ya zauna ya huta na lokaci mai tsayi ba.

Amma lokaci zuwa lokaci yakan tuna da ita har ma yayi murmushi, musamman wautarta da wasu abubuwan. Abin da yafi komai tsaya masa a rai shine karamcin da Baffah yayi masa.  Haƙiƙa zuciyar ɗan Adam kan ginu da abubuwa guda biyu, na ɗaya shine tuna halacci na biyu kuma hassada, amma me wayo kan iya magancewa kansa cutar hassada ne ta hanyar cusawa kansa yada da dukkan abinda wani yafishi dashi komai ƙanƙantarsa, abu mafi mahimmanci kuma shine addu'a tareda qara himma wajen roƙon Allah akan ya cire maka ciwon hassada komai ƙanƙantarsa a Zuciyarka,wllh idan ka ginu akan hakan babu abinda ze dameka balle ya ɗaga maka hankali ko meneneshi😊 


Comment
Nd
Share

ZMC💋
***