BAFULATANA🐄

Chapter 12

by @zmchubado

*BAFULATANA*


*Zm~Chubaɗo*

012

Zaune yake cikin kyakkyawan office ɗinshi wanda aka ƙawatashi da abubuwa na more rayuwa, wa ƴanda suke tafiya dedai da zamani, idanunsa a ɓoye cikin wani bakin glass samfurin  prada, gabaɗaya ya maida hnkalinsa kan system  ɗin dake gabansa tsaki yaɗan ja kaɗan tareda zare baƙin glass ɗin da ya rufe idanunsa dashi, donya tabbatar da abinda idanun nasa suka gane masa,  wara  manyan idanunsa yayi kaɗan yana kallon sababbin tsare-tsaren da aka samu a cikin shekara dayan da ya rasa a cikin Rayuwarsa, lokaci guda ya  jijiyar kansa ta miƙe saboda ɓacin rai, miƙewa ya yi ya nufi office ɗin  Accounter Salahudden.
Duk inda yabi kallonsa kawai ma'aikatan keyi tareda risinawa suna kwasar gaisuwar a gareshi, faɗaɗa murmushin yaƙen da ya ɗora akan fuskarsa yayi sannan ya amsa musu gaisuwar a haka har ya isa office ɗin Accounter ɗin.

Tun kafin ya isa cikin office ɗin Salahudden ke kallonsa ta glass ɗin daya raba tsakanin cikin office ɗin da wajansa, ɗaure fuska Muzaffar yayi sannan ya tura ƙofar ya shiga cikin takunsa me fallasa kwarjinin da ubangiji yayi masa, direct gaban table ɗin dake jibge da uban files se kuma system ya nufa idanunsa  cikin na Salahudden.

Da sauri Salahudden ya miƙe yana murmushi ya ce,"Ran C.e.o ya daɗe yau kaine da kanka a cikin office ɗina? ai da ba kazo da kanka ba ka turo an kira ni inyaso ni sena kawo kaina gareka Allah ya taimakeka."

Taɓe baki Muzaffar yayi yana kallonsa a ransa yana me jinjinawa ƙwarewarsa wajen iya kafcen wasan kwaikwayo  ya ce,"Accounter a ƙa'idar wannan Companyn tun kafin haihuwata zuwa yanzu, ba'a taɓa fitar da kuɗi komai ƙanƙantarsa  ba tareda an shigar da record na abinda yasa aka fitar da kuɗaɗaɗen a rubuce ba  matsayin sheda.  mai yasa ka fitar da million 60 batareda sani na ba?"

Zaro ido Salahuddeen yayi yana kallonsa da manyan idanunsa, lokaci guda kuma wani irin gumi ya shiga keto masa tamkar an sheƙa masa ruwa a daburce ya ce,"Ammm.....Ae.....dadd..dama..inaso...uuhmm..."

"ka dakatar da wannan dramar da kake ƙoƙarin shiryawa a gabana Salahuddeen!."  Muzaffar ya katseshi ta hanyar daka masa wata uwar tsawa  cikin ɓacin rai ya ce, "zaka gayamin dalilin fitar kuɗin ko kuma sena sa an Rubuta maka takaddar Sallama da ga aikin ka?"

Miƙewa Salahudden yayi da sauri ya zagayo inda muzaffar ke tsaye ya ce "aa don Allah! Ka dubi girman Allah kar kayi mini haka na roƙeƙa, wllh ba laifina bane fin ƙarfina akayi dole yasa na  taimaka mata muka fitar da kuɗin ba tareda saninka ba, idan ka koreni wllh kayiwa rayuwata illa ta ɓangarori da dama, pls kayi haƙuri ka yafe mini wllh zan maka bayanin yanda akai komai ya faru!"

Kallon sheƙeƙe yakebin Salahudden ɗin dashi, lokaci guda ya ce,"wannan matsalarka ce kaida wanda kuka aikata ɗin, oya tashi ka bani cikakakken bayani akan fitar kuɗin da kuma sunan wanda yasa ka fitar da kuɗin." Jikinsa na rawa ya juya ya fara neman takardun kasancewar abin be wani daɗe ba yasa ya binkitosu cikin sauƙi ya miƙa masa, karɓa yayi ya fara dubawa take sunan  Md Fadilah Abdulwahab ya baiyana a jikin takardan ƙuru-ƙuru, a matsayin wadda aka haɗa hannu da ita wajen fitar da kuɗin.

Wani shaiɗanin murmushi ne yay Escaping lips ɗinsa ya kalli Accounter yace "karka taɓa tsammanin zan ƙyaleka ban hukuntaka ba akn abinda kuka aikata kaida Md, it possible hukuncin dana yanke mata kaima shi zan zartar akanka ba tareda na banbanta hakan ba, tunda har ka iya biye mata kuka haɗa hannu wajen gudanar da zanbo cikin Aminci A cikin  wannan Company, dole ne ku karɓi hukunci." Ya faɗi hakan yana wani datse lips ɗinsa da white tooth ɗinsa da suka ƙara haska kyakkyawar fuskarsa.

Juyawa yayi ya fice tareda takardun a hannunsa ranshi a ɓace. Dole ne ya ɗauki mataki akan Fadilah a wannan karon don baze ci gaba da zuba mata idanu tana aikata duk abinda taga dama ba,  this time ta fara wuce iyakarta.

Be dire ko ina ba se Office ɗinshi tareda zuɓe takardun a saman table ɗinsa, sannan ya zauna ya jawo system ɗinshi gabansa ya fara daddannawa, cikin mintunan da ba zasu gaza 4 ba ya kammala rubuta  gajeran saƙon da yake rubutawa, sannan ya turashi ta wani Email Address ya miƙe ya fice bayan ya rufe System ɗin.  Tun kafin ya fito saƙon korar Fadilah Abdulwahab Abdullah ya cika Companyn abinka da zamani na kimiya da fasaha.

Fadilah dake zaune cikin office ɗinta tana gudanar da Aiyukanta, a hankali ta ɗaga idanunta ta zubawa wayarta saboda ƙarar saƙon daya shigo mata a wannan lokacin, tsaki taja me sauti sannan ta jawo wayar ta buɗe saƙon ta fara karantawa, take idanunta suka firfito saboda tashin hankalin data samu kanta a ciki, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne ya turniƙeta nan take wata sabuwar wutar tsanar muzaffar ta fara kwaranya a saman zuciyarta.  Miƙewa tayi a hasale ta nufi  ƙofar fita daga office ɗin tana huci tamkar zata tashi sama, Direct office ɗin Abie ta nufa ƙwalla kwance a ƙwayar idanunta.

Duk inda ta nufa se dai kaga ana juyawa ana kallonta masu yi mata dariya a ɓoye nayi, hakama masu jajanta mata ma nayi, wannan baƙin cikin ne yasa tana shiga office ɗin Abie ta fashe da kukan baƙin ciki da takaici a lokacin da taga kujerar zaman Abie ɗin babu kowa a kai, hakanne ya bata tabbacin ya tafi gida, kife kanta tayi akan gwiwarta ta shiga gurzar kuka bisa wannan abin kunyar da muzaffar ya jawo mata a idon mutanan dake ƙasanta.

Zuciya ce ta kwasheta ta fito daga office ɗin har idanunta na Rufewa saboda fishi da ɓacin Rai, ta nufi ƙofar fita daga companyn da wani irin mugun gudu ta ƙarasa fitowa a lokacin data hangi Muzaffar na ƙoƙarin shiga mota gurds ɗinsa na tsaye alamar gida Zashi.

Kamar ƙiftawar idanu se gata a gabansa lokaci guda kuma ta damƙi wuyan Korean suits ɗin dake jikinsa, ta fara ƙoƙarin fito dashi tana binsa da kallon tsana.

Wani irin ɓacin rai ne ya tasowa Muzaffar lokaci guda ya fito daga motar tareda watsa mata wasu lafiyayyun maruka a fuskarta, lokaci guda kuma yasa ƙafa ya tokareta take tayi baya lu zata faɗi, yay saurin  riƙota yana huci yace "komai yazo ƙarshe fadilah tunda kika ƙureni na dora hannuna a jikinki.tunda na lura ke mahaukaciya ce wadda bata san inda ke mata ciwo ba, nan gaba ki sake kwatanta mini irin wannan stupidity ɗin I will make sure to teach you a good lesson that you will never forget it in your life." Ya faɗi hakan yayin da yake tureta daga jikinsa cikin fushi.

Kifewa tayi a gurin tana kuka  shikuma ya rufe motar suka bar harabar companyn, gabaɗaya mamakin halaiyarta yake yi, Wllh da ace ba'a gida Momy ta haifeta ba da sai yace canza masu ita akayi sam ita ba jininsu bace saboda baƙin Halinta. A haka suka isa gida abinda tayi masa bai bar zuciyarsa ba ko kaɗan.

Ta jima tana kuka a gurin sannan ta miƙe ta nufi motarta ta shiga gurds ɗinta mutum biyu na take mata baya a motarsu suka nufi gida zuciyarta na suya.   

A nasa ɓangaren kuwa har yazo gida ya kasa sukuni, sosai yakejin haushin kansa da har ya iya ɗaga hannu ya doki ƙanwarsa  wadda suka fito ciki ɗaya saboda wani ƙaramin laifi data aikata masa na kama masa wuyan riga a cikkn jama'a, nan take yaji wani irin tausayinta na kwaranyowa daga ƙasan zuciyarsa, a haka suka kai gida Ransa duk babu daɗi, Direct part ɗinsa ya wuce saboda be shirya yin  magana da kowa ba saboda yanda Fadilah ta ɓata masa mood ɗinsa na yau.

Bayan dawowarsa da minti goma se ga Fadilah ma ta dawo, buɗe motar tayi ta fita tana kuka batareda ta jira gurds ɗinta sin buɗe mata ba kamar yanda ta saba, cikin gidan ta nufa da cogalelen takalminta tana kuka a haka ta shiga falon ko Sallama babu, gabaɗayansu ido suka zuba mata daga Momy har Abie zainab kuwa baki ta saki da hanci tana kwasar kallo saboda a iya zaman da sukayi tare kafin ta tafi India bata taɓa ganin Fadilah tana kuka irin haka ba se yau itako meya sameta haka?

Bata kula kowa ba ta kwasa da gudu ta nufi Upstairs tana ƙara sautin kukanta Al'amarin daya ƙara ɗagawa su Abie hankali kenan sukabi bayanta,  duk yanda sukaso su cimma Fadilah abin ya faskara tana shiga ɗakinta ta murza key ta faɗa gado ta shiga rusa wani sabon kukan baƙin cikin,  duk irin rarrashi da ban bakin dasu Abie keyi kanta buɗe musu ƙofar fur Fadilah taƙi buɗewa dole yasa suka haƙura suka barta.

         *******

*RUGAR ARƊO*

Zuwa yanzu Baffah ya gama sarewa da lamarin Rabe saboda yanda yarinyar ta ƙara ramewa ta fita haiyacinta tamkar mai ciwon zamani, bata da aiki se kuka da keɓe kanta daga shiga cikin mutane, wannan al'amarin ne yake ƙara ɗaga masa hankali, ko abincin kirki bata iya ci yau tunda sanyi safiya take fama da wani irin ciwon ƙirji me matiƙar zafi, ga wani irin nauyi da saitin zuciyarta keyi mata.

Ko kaɗan bataso ta nuna gazawarta a idon Mahaifinta wadda yanke kallonta a matsayin sanyin idaniya a gareshi, ta san dolene idan ya fahimci halin da take ciki beze taɓa samun kwanciyar hankali ba shiyasa ta zaɓi ta boye masa lalurarta, sai dai abinda bata sani ba wanda ya rigaka kwama dole ne ya rigaka tashi.

Sa rai ya fahimci komai kuma ya san inda ta dosa amma sai ya yi mata ta babba da yaro ya nuna mata bai san komai akan matsalarta ba, kwance take kan katifar ciyawarta idnunta na kallon saman bukkar. wasu zafafan hawayene suka shiga zubo mata a lokacin data tuna abinda ya faru a tsakaninta da Muzaffar ranar da suka tafi kiwo na ƙarshe dashi.

    *Flash back*

tunda suka tafi kiwo bashi da aikin daya wuce kallonta, haka kawai yaji cewar yana shi'awar kallon nata dik inda tabi  idanunsa na kanta tamkar baze dena kallonta ba,  ita kuwa sabgar gabanta kawai take ba tareda ta lura da irin kallon da yake binta dashi ba, tana ɗagowa a karon farko idanunsu ya sarƙe cikin na juna........
A hankali ta buɗe baki ta ce,"Hamma! meyasa kake yawan kallona a ƴan kwanakin nan?"

Murmushi ya yi sannan ya ce"sabda zanyi kewarki ne sosai."

Cikin rashin Fahimta take kallon sa ta ce,"me hakan ke nufi?"

Dariyace ta kamashi amma seya danne ya ce "abinda kikaji nace shi ɗin dai nake nufi."

Wata irin Dariya ce ta kamata sosai irin wadda bata tabayin kamarta ba,  a Iya zaman da yayi tareda dasu, da ƙyar ta iya saita kanta ta dena dariyar tana kallonsa ta ce,"amma Kaɗo ka iya tsiya Aradu."

Tunda ta fara dariyar yake kallonta  kamar  zeyi kuka yace, "meyasa kike dariya irin haka bakisan yawan dariya yana gusar da imani ba?"

Murmushi tayi tace "abinda ka faɗa ne ya bani  dariya, Aradu she naji Kalmar tayi min  daban a shikin kaina."

Hade rai yayi ya ce," to kada ki sake mini irin wannan dariyar bana so, kinji yanda kika tsorata ni kuwa?"
Sunkuyar dakai tayi sannan ta riƙe kunnuwanta guda biyu,  kamar yanda ya keyi mata idan ya ɓata mata rai ta tsuguna ƙasa ta ce,"waɗu munyal Hamma am!"

Dariya ta bashi sosai dan haka yay murmushi tare da Jan kumatunta ya ce "uhm that's my Fulani girl... shikenan na haƙura amma kaɗan."
Dariya sukayi gaba ɗayansu, a haka wannan Ranar ta kasance daban a garesu koma a kirata da Rana ta musamman a gareta.

A zaman da tayi dashi kullum ƙara samun kusanci yake da zuciyarta batareda ita kanta ta san hakan ba, wasu Zafafan hawayene suka shiga zubo mata a lokacin data farka daga duniya tunanin data Afka, akan matashin ɗan kasuwar mejida kuɗi da ƙwalisa. wanda a gurinta ya kasance mutum na daban wanda take kallo a matsayin waliyin da ya inganta rayuwar ibadarta data mahaifinta, wannan ya sa ta bashi babban matsayi a zuciyarta. Saɓanin shi da ya mance da batun wata fulani girl dake Rayuwa a wani babban daji wanda be gina masa wani muhali a cikin tasa zuciyar daze iya tunawa nan kusa ba.

Zuwa yanzu kam ta riga ta sare cewar Hamma ba zai cika alƙawarinsa a gareta kuwa ba, A cewarsa yace ze dawo gareta  komai daran daɗewa koda kuwa ba nan kusa ba, yau gashi ya kwarari kusan shekara da tafiya, ba tareda ya waiwayi inda take ba.  

Burinta a yanzu shine Allah yasa a duk inda yake ya kasance a cikin Farin ciki da ingantacciyar rayuwar da zai iya tunawa da ita ko bayan mutuwarta ne.....

Ba zata gaza ba zataci gaba da jiransa na iya tsahon rayuwarta! 

    *** *** ***

       *Abujah* 

Tunda ya dawo ya kasa gudanar da komai  saboda ɓacin ran daya dawo dashi daga office, ajiyar zuciya ya sauke me nauyin gaske sannan ya miƙe ya faɗa toilet donyin wanka be jima ba ya fito ɗaure da towel ɗaya a ƙungunsa ƙarami kuma bisa wuyansa,  goge jikinsa yayi tsaf batareda ya shafa maiba ya buɗe tafkekiyar drower ɗinsa dake manne a jikin katafaren bangon dake ɗakin ya fito da wasu ƙananan kaya marasa nauyi ya sanya a jikinsa, tareda yin cumming lallausar Sumar dake kansa ya fita harabar gidan.

Da Zainab yaci karo tana mishi murmushi tace  "bro Anul! Abie da momy ne sukace nazo na dubaka ko lfy sunji ka dawo amma bakazo kayi lunch ba." Dafa kafaɗanta yayi suka fara tafiya tare har suka isa maine falo ɗin Momy suna ɗan taɓa hira sannan ya ce" Cutie jeki haɗamin ouds pls banson cin komai yau"

Da kallo Momy ta bishi wanda yafi kamada na mamaki ta ce,"Son a kwai abinda ke damunka kenan tunda naji kace Zainab ta haɗa maka ouds me yake damunka?"

Ajiyar zuciya ya sauke kaɗan sannan yaja ɗaya daga cikin kujerun dake zagaye da daining ɗin yace "Mom ba wani babban al'amari bane fa." Haɗe rai tayi tana kallonsa da sauri ya janye idonsa ya kalli Abie ya ce "pls Abie kace mom ta bar yimin irin wannan kallon don Allah wllh xan faɗa mata komai."

Murmushi abie yayi  me cikeda dattako sannan yace "to naji gaya mana meke faruwa."

Ɗan jim yayi sannan ya shiga sanar da Abie kaf abinda ya faru a tsakaninsa da Fadilah ba tareda ya rage komai ba.  Ƙura masa ido mom tayi bakinta a buɗe saboda tsabar mamaki da Kaɗuwa...........





Zmc💋
***