BAFULATANA🐄

Chapter 13

by @zmchubado

*BAFULATANA*


Zm~Chubaɗo

013

Daga irin kallon da momy take masa Abie ya Fahimci irin mamakin dake kwance a saman fuskarta, a fusace momy ta ƙara tsaida idonta akansa ta ce,"amma kai dai anyi sakarai wllh tunda baka karya mata ƙafafu ba, ni wllh Abie lamarin yarinyar nan ya fara ɗagamin hankali musamman ɗabi'unta, wllh da ace ba'a gida na haifeta ba tsaf zance canzamin ita  akai wannan wace irin jarrabar rayuwace haka?"

Dakatar da ita Abie yayi ta hanyar ɗaga mata hannu ya ce,"look malama karki ɓatamin zuriya da miyagun maganganunki, a madadin kiyi mata Addu'ah dan meyasa zaki dinga aibata ta haka? karfa ki manta fushin iyaye tareda kalamansu ƴaƴansu yana da matiƙar tasiri a rayuwarsu, don haka karki sake furta komai akanta muddin ba alkhairi bane. In sha Allah komai zeyi daidai watarana zata canza halinta daga yanda take zuwa halaye masu kyau."

Jiki a mace mom ta  miƙe ta nufi upstairs ɗakin Fadilah ranta amatiƙar ɓace, tura ƙofar tayi tareda tsayawa a bakin ƙofar tana bin kowace kusurwa dake ɗakin da kallo.

Zaune ta hangeta ta haɗe kai da gwiwa a kan lallausan kafet ɗin dake ɗakin fuskarta duk ta caɓe da hawaye, ƙarasawa mom tayi tana binta da wani ɗan iskan kallo wanda yasa hanjin cikin  Fadilah motsawa,  wani sabon marin mom ta ɗauketa dashi wanda yasa har seda kanta ya bugu da allon gadon dake ɗakin sannan ta nunata da yatsa ta ce,"ban san wani irin baƙin haline ke bibiyar zuciyarki ba fadilah! Ke wace irin mara mutunci  ce da zaki saka hannu ki shaƙi wuyan rigar yayanki wanda ya girme miki fiyeda shekaru biyar?  Duk haƙuri irin nasa seda kika ƙureshi ya ɗaga hannu ya mareki why?"

Kuka kawai takeyi  hannunta riƙe da fuskarta wadda ta caɓe da ruwan hawaye da majina, mom bata bar ɗakin ba seda tayiwa Fadilah tatas sannan ta fita zuwa downstairs inda tabar su Abie, jikin zainab a mace ta kalli Muzaffar ta ce"don Allah yaya ka yafewa ya Fadilah abinda taimaka, na san zuwa yanzu tayi nadamar abinda ta aikata."

Murmushin gefan baki ya yi don har lokacin mamakin abinda ta aikata masa bai bar zuciyarsa ba, ganin yanda zee ɗin ta damu ne ya sa yace "karki damu i already forgive her tun kafin nazo gida, so karki sama kanki damuwa ki manta da maganar kawai."

Dariya tayi shi dai Abie cin Abincinsa kawai yake harya gama bece dasu ƙala ba, a haka kowa ya gama cin Abincin da abinda yake aiyanawa a ransa. Se yamma liƙis Fadila ta fito daga ɗaki duk fiskarta ta kumbura abinka da farar mace lol, shima yunwace ta matsa mata shiyasa ta fito donta samawa kanta abinda zataci, Zaynab ta Samu ita kaɗai a falon se kuma Hajara me aikinsu wadda ta ɗan fara manyanta suna hira, ɗauke kanta tayi kamar bata gansu ba ta nufi khitchine tana raba ido ko zata samu abinda zata zubawa ƴaƴan hanjinta, tsayawa tayi tana bin ko ina da kallo amma bata ga wani abu dafaffe ba, kwaɗawa Hajara kira ta shigayi kamar zata tashi gidan, da hanzari Hajara ta iso kicin ɗin tana faɗin"Gani ranki shi daɗe me kike so?"

Wani kallon sheƙeƙe ta bita dashi tace "ki dafanin endomie yanzu ki kawo min ɗaki." bata jira cewarta ba ta juya tabar khitchin ɗin tana wani ɗaga kai kamar zata tashi sama,  harta kama step zainab tayi Saurin cewa "oh Allah ya Fadilah Ashe kuma haka abu ya faru babu daɗinji, kaico amma gaskiya na jajanta miki don daga ganin fuskar nan taki ta maru ba kaɗan b." Tun kafin ta rufe baki Fadilah tayo kanta gadan-gadan tana huci.

Da sauri zaynab ta miƙe tayi waje da gudu tana ihu, da Abie sukaci karo yana ƙoƙarin shigowa falon  kunnensa ɗauke da waya zaynab tayi bayansa tana tura baki ta ce "uhmm Abie kaga ya Fadilah ko?"

Takaici ne ya kamashi lokaci guda kuma ya zare wayar daga kunnensa yana binsu da kallo batareda yace dasu ƙala ba, su da kansu sukasha jinin jikinsu  Jiki a mace zainab ta ce,"we are sorry Abie baramu ƙara ba."

Raɓawa Abie yayi ta gefansu ya wuce tareda mayar da wayarsa kunnensa yaci gaba da wayanshi.

*** *** *** *** ***
*RUGAR ARƊO*

Zuwa yanzu Raɓe ta gama fitar da ran cewar Muzaffar ze dawo gareta kamar yanda ya alƙawaranta mata hakan, ta daɗe da sawa a ranta cewa ya daɗe da mantawa da ita,  moddibo ne zaune kan tabarmar kaba yana shan Fura Jaddah ta fito ta zauna daga gefansa suna ɗan taɓa hira kamar abin arzuƙi.

kamar daga sama suka fara jin ƙarar harbin bindiga dabda gabatowar almuru, da wani irin sauri Rabe dake bakin murhu ta miƙe tana raba idanu saboda bugawar da zuciyarta ta farayi, bata ankara ba taji Baffah ya fuzgi hannunta suka shige bukkarsa a matiƙar kiɗime, wata ƙatuwar Boronsa ya ɗaukko a rataye ya sakaƙala mata ita a kafaɗarta  lokaci guda ya kama kafaɗunta da duka hannayensa biyu yana kallonta cikin maɗaukakin tashin hankali ya ce,"da alama mafarkin dana jima inayi ishara ce a garemu mamana, haƙiƙa mafarkin bayin Allah gaskiya ne, abinda ubangi ya jima yana nuna mini a mafarkina shine ke shirin faruwa damu, babu shakka ranar Rabuwata dake yazo mamana!  Rabuwarmu tazo a cikin yanayin da gabaɗayanmu ba zamu so hakan ba, sedai babu yadda muka iya da abinda ubangiji ya tsara mana, bani da yadda na iya dole ne nayi duk me yuwuwa a matsayina na mahaifinki naga cewar kin tsira daga wannan babbar  masifar data tunkaro mu gudun kar tarihi ya maimaita kansa."

Tunda ya fara magana ta kiɗime hankalinta ya ninka farko a tashi sai kawai ta fashe da kuka ta kama hannunsa ta riƙe gam ta ce,"amma Baffah mai yasa se kalmar rabuwace zata fito daga  bakinka a lokacin da nafi kowa buƙatarka a rayuwata?  wllh Baffah shekaruna sun gaza ba zan iya fahimtar kalmar da kake nanata min ta Rabuwa ba.....  Don girman Allah kada ka bari bakinka ya sake furta wannan kalmar saboda zuciyata da gangar jikina ba zasu iya fahimtar abinda kakeso su fahimta ba!"  Ta faɗi hakan tana ƙara sautin kukanta.

A wannan lokacin tini kururuwar jama'ar dake rugar ta fara cika kunnuwa, tareda kusantowar ƙarar harbin bindigar wajen bukkokinsu, fusgeta Baffah yayi daga jikinsa lokaci guda ya daka mata tsawa ya ce,"lallai ya zama wajibi ki saurareni a matsayina na mahaifinki, idan Allah ya hukunta cewar zamu sake haɗuwa tabbas zamu haɗu  amma kuma idan ya raba ganawa a tsakanin mu lallai ki kasance me kare martabar mutuncin ki har zuwa inda daya dace,  sannan idan ƙaddara ta sake haɗaki da Muzaffar lallai ki gaya masa cewar idan yana da hali to ya cika alƙawarin daya ɗaukarmini a kanki, idan kuma ƙaddara bata haɗaku ba karki kuskura ki ƙara tako ƙafarki cikin nahiyarnan har ƙarshen rayuwarki........!"     Ya faɗi hakan hawaye na zubowa akan dattijuwar fuskarsa.

Wani irin tausayinta yakeji se dai bayajin ze iya barinta a taredashi a wannan halin saboda ba ze juri ganin mutuwarta a gaban idanunsa ba, ya sani cewar abu ne mawuyaci mace ta  rayu a inda babu wani nata kuma ta rayu ciki salama  kokuma cikin Aminci batareda ta lalace ba, sedai babu yadda ya iya dole hakan shine mafita a garesu gabaɗaya.   

Ɗaga hannunsa yayi sama yana kuka yace "ya ubangiji ga Amanar daka bani nan ƴata dana haifa, ya Rabbissamawati wal'ardi ka kulamin da ita a duk halinda zata samu kanta a ciki, ya Allah kada ka barta da iyawarta ka Iya mata da iyawarka ya Allah!"

zata sake magana kenan ya dakatar da ita ta hanyar jan hannunta suka fito daga bukkar yana share hawayensa.

Koda suka fito basu cimma Jaddah a gidan ba,  hakanne yasa Baffah leƙawa ɗakinta don ya  tabbatar da tana ciki kokuma ta tsere, can ya hangeta ta haye kan katifar ciyawarta jikinta banda rawa babu abinda yakeyi, takawa yayi da sauri ya fuzgota tana tirjewa a haka ya janyota suka fito, gabaɗaya babu abinda ke tashi a rugar face sautin harɓin bindigar da ƴan fashin ke amfani da ita, baka ganin komai se ƙurar jar ƙasar dake tashi a gurin, hakanne ya haifar da hargitsewar dabbobinsu, hatta  shanunsu duk sun kwance sun bazama cikin daji a gigice.

Cikin jeji moddibo ya nausa dasu banda gudu babu abinda sukeyi a haka har suka fara nisa da rugar, fusge  hannunta Jaddah tayi daga cikin na Baffah tace "Sakarni Moddibo wllh ban ƙara ko taku guda daga nan, kana nufin haka zamu bar dukiyarmu da kuma ƴan uwanmu ɓarayi na kashesu kamar tsintsaye?"

Hawaye ne ya zubo masa a lokacin daya tina Wasiyar mahaifinsa na cewar" a duk sanda masifa ta afka muku modibbo da zarar ka samu nasarar fita daga gurin da masifar ke faruwa kai da iyalanka koda wasa karka bar ɗayansu ya koma inda abin ke faruwa idan kuwa har hakan ta faru lallai ɗayanku ze mutu idan kuma har ba'a mutu ba to zaku tabka babbar Asara cikin biyu za'ai ɗaya."

Fashewa yayi da kuka ya janyo Rabe yana kuka ya Rungumeta lokaci guda kuma ya zare jikinsa daga nata ya ce,"Mamana kiyi nisa da wannan jihar nisa me tsahon gaske! sannan ki sanya a ranki cewar idan da rabo wata rana zamu sake haɗuwa."   Juyawa yayi da sauri zebi bayan Jadda da hanzari ta riƙe hannunsa tana kuka ta ce,"kayi mini alƙawarin zaka jirani har lokacin da ƙaddarar data rabamu zata dawo dani Baffah." Zeyi magana ta dakatar dashi ta ƙara cewa," ni dai kayimin alƙawarin cewar zaka jirani har lokacin da zan dawo a raye batareda muwa ta riske ka ba."

Gabaɗayansu kuka sukeyi me taɓa zuciyar duk wani me imani, da sauri ya ɗaga mata kai yace "nayi miki alƙawari mamana tabbas zan jiraki har zuwa ranar da ƙaddara zata dawo mini dake. Yana faɗin haka ta saki hannunsa tana kuka ta juya ba tareda ta sake waiwayensa ba ta nausa cikin jeji batareda sanin inda ta nufa ba.

Zubewa yayi a ƙasa ya fara sharɓar kuka musamman daya tuna alƙawarin daya ɗaukarwa ɗiyarsa wadda be taɓa gaya mata abinda yake ba gaskiya ba daga bakinsa, se gashi yau an wayi gari yayi mata alƙwarin da baze iya cika matashi ba.

Ya jima yana kukan sannan ya miƙe yabi bayan Jaddah yana me ƙara jaddada Amanar Rabi'atou ga ubangijinsa....







Comment
Nd
Share

Zmc💋
***