Chapter 14
by @zmchubado
BAFULATANA
Zm~Chubaɗo
014
Nausawa tayi cikin jejin, babu abin da takeyi sai kuka, saboda rabuwar da tayi da mahaifinta. Jefa ƙafarta kawai takeyi, ba tare da ta san inda take jefata ba. Ga dare ya fara yi, babu komai cikin dajin face kukan gyare da na tsuntsaye.
Kasancewarta Bafulatanar Daji, hakan ya sa bata ji tsoro ba, domin dama a cikin dabbobi ta tashi kuma a can take rayuwa. Saboda haka babu wani baƙon abu a gareta. Babban abin da zuciyarta ta yarda da shi shi ne, there’s nothing that can happen to her because her father’s prayers are still with her. Da wannan tunanin take tafiya, duk da cewa zuciyarta na ciwo.
Ta sani sarai cewa ita kaɗaice ta ragewa mahaifinta a halin yanzu, haka kuma ƙaunar da yake mata babba ce ƙwarai. Bata jin zai iya sadaukar da wannan babbar ƙaunar da yake mata a banza ba, domin ruwa baya tsami banza, in ji ƴan magana. Dole yana da dalilinsa mai ƙarfi da har ya sa suka rabu a wannan lokaci.
Ƙirjinta ne ya amsa da sauri lokaci guda, ta zube a kan gwiwoyinta tare da ɗora hannunta na dama a saitin zuciyarta. Rarrafawa tayi tana gyara zaman jakar saƙin da Moddibo ya rataya mata a kafaɗarta, ba tare da ta bari jakar ta faɗi ba. A haka ta jingina bayanta da wata ƙatuwar bishiya, tana maida numfashi.
*** *** ***
ABUJA, NIGERIA
Yau tun da sanyin safiya, Muzaffar ya gama shirinsa cikin wata ash ɗin Korean suit mai tsayin gwiwa, kasancewar garin na ɗan sanyi sosai. Tsaye yake a gaban makeken dressing mirror ɗin da ke manne a jikin bangon ɗakinsa, yana gyara zaman agogon Rolex da ke hannunsa. Ƙurawa kansa ido yayi, kamar mai son gano wani abu a tattare da kansa. Ya lumshe idanunsa, sannan ya buɗe su, abin da ya sa idanunsa suka sauka kan tabon ciwon da lallausan gashin kansa ya fara rufewa.
Hannunsa ya kai gurin, ya janye lumsasshen gashin kansa yana kallon tabon, lokaci guda ya dafe kansa yana cewa, “Ya Rabbi!”
Juyawa yayi da sauri ya fita daga bedroom ɗinsa zuwa falo. Da ya fito falon ma tsayawa yayi cak, domin ya kasa tuna ainihin abin da ya fito dauka daga ɗakin. Zibewa yayi a kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun royal chairs da suka kawata falon.
Wayarsa ce ta ɗauki ƙara. Ya duba ya ga sunan Abie yana yawo a kan screen na wayar. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi sannan ya amsa kiran.
Abie yace, “gobe ne meeting ɗin da za a gabatar a India. Ya kamata ka fara shiri, domin gobe da yardar Ubangiji lallai ya kamata ka kasance a wurin da za'ai yi komai, saboda Hajiya Aisha she’s not feeling fine.”
“In sha Allah zan yi ƙoƙarin yin hakan, Abie. Amma ka turo min number ɗinta domin na kirata na dubata,” Muzaffar ya faɗa.
“Ok, zan turo maka,” Abie ya faɗi hakan yana katse kiran.
Ajiye wayar Muzaffar yayi, sai kawai ya samu kansa cikin wani baƙon yanayi da ya kasa misaltawa. Ajiyar zuciya ya sake saukewa karo na biyu a lokacin da babban amininsa, Edris Muhammad Jalingo ya faɗo masa a rai. Wayar da ke gefensa ya zaro lokaci guda ya fara lalubo number ɗin Edris tare da danna kira. Sai dai har kiran ya katse bai ɗaga ba, sai da ya sake kira karo na biyu sannan ya ɗaga.
“Shugaban masu kirkin duniya ya kake?” Edrees ya faɗa.
Tsaki Muzaffar ya ɗan ja sannan yace,“Fine ya kake?”
“I’m fine, and you?” Edrees ya amsa, yana gyara zamansa.
Muzaffar ya sauke ajiyar zuciya sannan yace, “Ban sani ba, ɗan rainin hankali you know what?”
Edrees da ke zaune a babban falonsa ya ƙara damƙe remote ɗin dake hannunsa yace, “How could I know bayan ba ka gaya min ba? Kaga malam, forget about what I did to you please, let’s talk.”
Muzaffar yace, “Na ji, amma yanzu ban son magana da kai, saboda kai ba ka nemana sai matsalarka ta taso. Yanzu kuma ban da lokacin ka. Idan ka matsu da magana da ni, sai ka jira ranar da zan dawo Abuja, domin yanzu I’m not in Abuja.”
Jan numfashi Muzaffar yayi sannan ya yi murmushi yace, “Ok, ba damuwa. Ni ma gobe zan wuce India, maybe next time.” Ya faɗa yana katse wayar da murmushi a saman fuskarsa.
Zainab ce ta shigo falon sanye da doguwar riga milk colour, ta yafa mayafi a kanta tace, “Bro kazo in ji Momy sannan kuma you have a visitor.”
Ɗan buɗe idanunsa yayi yace, “Who?”
Zainab na dariya tace, “Uhmmm, I think it’s Cp daughter.”
Taɓe baki yayi yace, “Kuma sai tace miki wurina tazo?”
Da sauri Zainab tace, “Eh mana saboda kai kaɗai ta tambaya data shigo, and sai na ga kamar…”
“It’s ok zee ki gaya mata ba na nan, na fita,” Muzaffar ya katseta.
Fita Zainab tayi tana dariya, a main parlour ta samu Hajar Muhammad Jalingo suna hira da Mom. Tace mata, “Yace na gaya miki ki same shi a part ɗinsa, he’s too busy doing something.”
Murmushi Hajar tayi wanda ya ƙara mata kyau, sannan ta nufi ɓangaren Muzaffar. A nitse ta murɗa handle na ƙofar falon tare da sallama ta shiga ciki. Hakan yayi daidai da miƙewarsa, yana buɗe botiran gaban suit ɗin da ke jikinsa. Juyowa yayi yana kallon bakin ƙofar, ya tsaya yana kallonta da mamaki a kyakkyawar fuskarsa.
Tunanin da ya fara zuwa masa shi ne, ta yaya yarinyar nan ta san hanyar part ɗinsa?
Takowa ta fara yi a hankali har ta iso tsakiyar falon da murmushi a fuskarta. Tace, “Fatan na same ka lafiya?”
Ɗan jima yayi yana kallonta sannan yace, “Fine, and you?”
Murmushi kawai tayi tace, “Fine, kwana biyu.” Ta faɗa tana ƙoƙarin zama.
Da sauri ya dakatar da ita yace, “No, ba zama zanyi ba don fita zan yi, ina da aiki a office.” Ya faɗa yana sauya yanayin fuskarsa.
Kamar zata yi kuka tace, “Muzaffar, meye laifina don kawai ina son ka? Shikenan sai ka dinga mini wulaƙanci? don Allah ka taɓa tunanin yadda nake ji a raina game da kai?”
Ajiyar zuciya ta sauke kaɗan yayin da idanunta suka ciko da ƙwalla. Tace, “Ba zan ga laifinka ba ko kaɗan, tunda tsarinka ne rashin bai wa mace mahimmanci a rayuwarka. Amma ina so ka tuna abu guda ɗaya: duk mutumin da ya nuna maka kulawa a rayuwa, har ya sadaukar da lokacinsa a kanka yafi ƙarfin wulaƙanci ko rashin girmamawa daga gareka, balle ka jinginar da shi tsawon lokaci ba tare da ka tuna da shi ba.
All I know is I love you, Muzaffar Abdulwahab!”
Ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi lokacin da kalamanta na ƙarshe suka sauka a kunnuwansa. Lokaci guda ya dafe kansa da hannayensa duka. Wani baƙon yanayi ya samu matsuguni a cikin zuciyarsa. Zama yayi jagwab a kan kujera yana sauke numfashi.
A hankali siraran leɓɓansa sukafara motsawa cikin husky voice ɗinsa yace,“I’m so sorry, Fulani girl. Ban kasance mai cika alƙawari a gare ki ba. I’m sorry for what I did to you, nayi miki alƙawari amma na gaza cikawa. In sha Allah nan kusa zan zan sauke nauyin dake kaina soon.”
Ƙura masa ido Hajar tayi, tana kallonsa da hawaye cike taf a idanunta. Tace, “Who is that Fulani girl? Please, I want to know something about her. Who is she?”
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta, lokaci guda kuma ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa ya buɗe ya shiga ciki. Hajar ta bishi da kallo tana tausaya wa kanta bisa son mutumin da bata taɓa samun kulawa daga gare shi ba, ko da sau ɗaya.
Zmc
***