Chapter 15
by @zmchubado
BAFULATANA
Zm~Chubaɗo
015
Da kallo Hajar ta bi shi tana mai tausayin kanta a nan gaba. Allah shine shedarta a kan irin son da take masa tun ranar da ta fara ganinsa zuciyarta ta amsa, ba ta jin cewa za ta iya jure rashinsa a rayuwarta.
Share hawayen da ke zubo mata ta yi, sannan ta ƙara gyara zamanta a kan kujerar da take zaune a kai. yau dai kam ta lasar wa kanta takobin cewa ba za ta taɓa barin falon nan ba har sai ta ji matsayinta a gurin Muzaffar, ko da hakan zai zama wani abu mai zaman kansa ne a tsakaninsu. Tambaya ɗaya ce ta ke mata yawo a zuciyarta, "wacece wannan Fulani girl ɗin da taji ya na ambaton sunanta a gaban idonta ba tare da shakka ba?"
Zamewa tayi ta jingina bayanta da jikin kujerar tana jin yanda zuciyarta ƙe harbawa, haka taita saƙawa da kwancewa a zuciyarta tana tunanin hanyar da zata bi don ta mallaki zuciyarsa. Wasa-wasa sai da ta shafe awanni uku cur zaune a falon ba tare da uban gaiyayyar ya san tana falon ba, har ya yi baccinsa ya tashi sannan ya yi wanka ya canza kaya zuwa marasa nauyi.
Sosai kayan suka dace da zubin jikinsa tamkar dama dan shi aka yi su. Komai nasa tsaf-tsaf yake kana kallonsa ka ga namiji ɗan'ƙwalisa shi, shi ya sa yake classy guy. Silifas ya ɗauko a cikin shoe rack baƙi samfurin Batozy ya sanya a ƙafarsa, hakan ne ya sake fito da ainihin hasken fatarsa. Duk inda ya gifta ƙamshin turarensa ne ke tashi, A nitse yake takawa har ya fita daga bedroom ɗin ya ƙarasa cikin falon. Tsayawa ya yi yana kallon Hajar wadda ke barci, da mamaki kwance a kan fuskarsa ya ce, “Ya salam! Wannan wace irin yarinya ce haka?”
Haɗe rai ya yi sosai sannan ya sa hannu ya buga gefen kujerar yana kallon reaction na fuskarta.
Firgigit ta tashi ta zauna tana hamma ta kalleshi sannan ta fara ƙoƙarin gyara mayafinta, mamakine ya ƙara kashe shi sai kawai ya zuba mata idanu yana kallon ikon Allah ya ce, “Me kike yi har yanzu baki tafi gidan ku ba? Mai yasa zaki kwanta mini a falo bayan kinsan ke ba muharramata bace?”
Tura baki tayi ta ce,“Taya zan tafi bayan har yanzu ban san matsayina a garinka ba?” ta faɗi hakan idanunta na shirin kawo ƙwalla.
“Look Hajarah! ya kamata ace zuwa yanzu kin gama fahimtar inda na dosa. Ni yanzu ba soyayya bace a gabana kuma koda ace zanyi soyayyar gaskiya ba zanyi dake ba, saboda tsarina da naki ba iri ɗaya bane zaman mu a ƙarƙashin inuwa ɗaya zaiyi matiƙar wahala."
"Amma ai zan iya zama da kai duk yanda ka kasance saboda ina sonka." Hajar ta firta hakan ruwan hawayen da take dannewa sika zubo.
"Ya Allah!" Muzaffar ya firta cikin ƙosawa.
Tsaiwarsa ya gyara sannan ya harɗe hannunsa a ƙirji ya ce," tunda na gaya miki abin da ya kamata ace kin gane, amma kinki fahimta to wllhi ni bansan yanda zanyi dake ba” Ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idonta.
To his souprise sai Kawai yaga ta fashe masa da kuka al’amarin da ya ƙara ɗaga masa hankali kenan. Sai kawai ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon a kiɗime yana kallonta, A rayuwarsa ya tsani kukan mace, balle kuma ace shi ne silar kukan. Da sauri ya ce,“kinga don Allah yihaƙuri ki daina kuka kar wani ya shigo ya zata wani abin nayi miki, so why are you shedding tears? I need to tell you what’s really in my heart kuma na riga na gaya miki tsakanina da Allah, Yanzu ki je gida. In sha Allah idan na dawo da ga India satin gaba mai zuwa zan zo gidanku sai mu yi maganar a can”
Da sauri ta ɗaga kai tana share hawayen da ke idonta, ta miƙe tsaye. Kusan a tare suka fita daga part ɗinsa, duk yanda yayi da ita akan ta tafi ba sai taje part ɗin momy ba amma haka ta nace sai ita dole sai ta shiga, hakan ya yi gaba ta bishi a baya sika shiga falon.
Har cikin zuciyarsa beji daɗi daya samu momy a falon ba, amma ba yanda ya iya haka ya samu guri ya zauna sai kawai ya zaro wayarsa ya fara dannawa, ta gefan idanunta Hajar ta kalleshi ganin ya zauna kan three siter ɗin dake falon sai ta ƙarasa ta fara ƙoƙarin zama a kusa dashi. Cikin azama ya dakatar da ita tareda ajiye wayar dake hannunsa ya ce,"ke meye haka? Out of all the space in this whole living room, you couldn’t find anywhere to sit except next to me?" yayi maganar cikin ɗaure fuska.
Momy wadda tun shigowarsu take waya jin abinda Muzaffar ke faɗi yasa ta katse wayar ta ce, “Hajiyar Asma'u bari za mu yi magana zuwa gobe.” Daga nan ta katse kiran tana binsu da kallo.
Sunkuyar da kai Hajar ta yi, cikin nuna jin kunya ta ce,“Mom zan wuce gida.”
Shiru mom tayi tana ƙare mata kallo a nitse, mamaki gamida al'ajabine sika cika mata zuciya, "yanzu duk wannan awannin da aka kwashe dama yarinyar nan tana cikin gidan nan tareda shi?." Mom ta tambayi kanta a cikin zuciyarta.
Ajiyar zuciya momy ta sauke mai zurfi sannan ta ɗaga kai ta ce, “Ki gaishe da mamanki.” daga haka bata ƙara cewa komai ba, ta miƙe ta nufi dining ba tare da ta kalli inda Muzaffar ke zaune ba. Sosai ya sha jinin jikinsa da irin kallon tuhumar da Momy ta raka hajar dashi.
Miƙewa yayi a hankali ya isa daining aria ɗin ya ce, “Momy! Wllh ba ba abinda kike tunani bane tsakanina da ita!”
Tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba ta ce, “Au, gaya mini ma ka keyi, don ka raina ni? to uban me yarinyar take yi a part ɗinka har tsawon wannan awannin kuna tare?”
Da sauri ya ce, “Mom zargina kikeyi?”
Ba tare da ta kalle shi ba ta ce, “No, at all, but bari Abie ya dawo dole ne a tsayar da maganar auranka, ko ma da wace yarinya ne. Saboda ni ba zan ɗauki iskancin nan a gidana ba, and let me tell you something Muzaffar, wallahi dole ne ka yi aure muddin baka son ganin ɓacin raina.”
Da sauri ya ce, “Momy aure kuma? But sai nake ganin kamar yayi kusa”
“Ya ishe ni haka malam, ka wuce kawai ka ba ni guri.”
Jikinsa a mace ya bar falon ransa a matuƙar ɓace. Yana fita harabar gidan ya nufi mota zai shiga, da sauri Selomon ya nufe shi zai buɗe masa ƙofar motar ya dakatar da shi ya ce, “Bani key kawai yau ni kaɗai zan fita.” Ba musu ya miƙa masa keyn, ya shiga motar ya buga mata key ya fice daga gidan gaba ɗaya. A ransa yace dole ne ya zauna da Abie suyi magana tun kafin Mom ta rigashi yin hakan. Ya san Abie zai fahimce shi don ba zai masa dole a kan abin da ba ya so ba ko kaɗan. Tsaki ya ja lokacin da Hajar ta faɗo masa a rai ya ce, “duk abinda ya faru ita ce sila mtsww”
Murmushin mugunta ya yi da ya tuna Zainab, tabbas ya san ita ce ta haɗa masa wannan tarkon, tunda ai sai da ya gaya mata tacewa Hajar ɗin baya gida amma ta tura masa ita part ɗinsa. Wllhi sai ya hukunta ta a kan abinda tayi masa.
*** *** *** *** ***
RUGAR ARƊO.
Duk yanda Jaddah ke tsammanin girman bala’in da ke faruwa a garin Ashe, abin ya wuce zato da tunaninta, amma duk da hakan ba ta yi tunanin komawa da baya ba. Still hankalinta yana kan dukiyar da Moddibo ya jima yana tarawa. Ba ta dire ko ina ba sai cikin Bukkar Baffah, nan ta fara birkita ɗakin ta ko’ina tana neman jakar saƙin da yake zuba kuɗaɗensa masu nauyin gaske a ciki. Gaba ɗaya ta gama burkita ko’ina amma bata ga komai ba, don dole ta dakata da binciken jakar ta tsaya tana tunani.
Tabbas ɗazu da suna gudu ta ga jakar a bayan Rabe, kenan hakan yana nufin duk kuɗaɗen Baffah ya bai wa ƴarsa ta gudu da su?
Kurma ihu ta yi tamkar mahaukaciya sabon kamu sannan ta fita daga bukkar tana mai nadamar dawowar da ta yi. Lallai ya zame mata dole ta bi bayan Rabe ta yi mata mugun duka sannan ta ƙwace jakar daga hannunta, in ya so ta shiga duniya daga nan ta buɗe sabuwar rayuwa. Juyawa ta yi da nufin barin gurin, kamar daga sama ta ga manyan ƙarti majiya ƙarfi sun kewaye ta, kowannensu riƙe da bindiga ƙirar AK47 suna kallonta, nan take hanjin cikinta suka yamutse.
Ba ta ƙara sarewa ba sai data ga su Malam Iro duk an ɗaɗɗaure su, jini na zuba daga gefen cikinsa, anan ne fa ta ƙara firgicewa kuma ta fashe da kukan nadar dawowar da tayi.
Moddibo da ke tsugune bisa gwiwarsa duk an tamke shi da igiya, kansa na zubar da jini ya ɗago gajiyayyyun idanunsa da ƙyar, jirin jini na ɗibarsa ya zuba mata idanu cikin yanayi irin na fitar hayyaci. Nan take Jaddah ta ɗora hannu a kanta ta kurma wani uban ihu.
Ɗaya daga cikin ƴan fashin ne ya ɗaga hannu ya zabga mata wani lafiyayyen mari. Nan take jaddah ta tsuke bakinta tana wani zare idanu saboda azabar marin daya wanka mata, Babban cikinsu ne ya kalli wanda ya mare ta ya ce da shi, “Kai Saage, maza jefa mini ita a ɗaki zan ɗan rage zafi da ita.”
Gabanta ne ya yi wata irin faɗuwa, lokaci guda kuma ta zuɓe a ƙasa tana roƙonsu kan cewa su rufa mata asiri kar su keta mata haddi. Wani sabon marin ya sake watsa mata, take gefen bakinta ya fashe ya fara jini.
Tana ji tana gani wannan ƙaton ya wurgata cikin Bukkar Moddibo, ogansu ya yi mata fyade a gaban idon mutanen da ke gurin. Wani irin kukan azaba da baƙin ciki Jaddah ke yi saboda baƙin ciki. Bayan ya samu nutsuwa da ita ne ya fito waje yana gyara zaman wandon da ke jikinsa, ya kalli yaransa ya ce, “Idan dame buƙata a cikinku sai ya antaya shima ya yi juyen baƙin mansa.”
Jiki na rawa Saage ya ce, “Oga, nima ina da buƙatar romon tsohuwar.” Dariya suka fashe da ita, sannan Saage ya antaya ciki shima ya huce takaicinsa a kan Jaddah. A taƙaice dai sai da mutum huɗu suka yi wa jaddah fyade, tana ji kuma tana gani, babu yadda ta iya.
A wannan rana jadda ta yi kukan da ba ta san adadinsa ba, haka kuma ta yi dana-sani mara misaltuwa a rayuwarta. Nan take nadama ta yi mata dirar mikiya a lokacin da komai ya lalace mata, taso ace ƙaddarar data sameta Rabe ta faɗawa ba ita ba, amma sai gashi reshe ya juye da mujiya cikin ƙanƙanin lokaci.
A CAN ƁANGAREN RABE KUWA:
Jingina ta yi da wannan bishiyar da ke gefenta tare da zubawa sarautar Allah idanu. Wani irin kuka ne ya taso mata a lokacin da ta tuna da halin da ta bar ahalinta a ciki. Babban abin da yake ƙara ɗaga mata hankali shi ne rayuwar da za tayi a nan gaba tare da mutanen da ba ta taɓa saninsu ba. Sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta miƙe ta gyara zaman jakar da ke kafaɗarta, wadda Baffah ya bata, sannan ta ci gaba da tafiya tana kuka. Sai da ta yi tafiya mai ni san gaske sannan ta fito titi.
Bin ko’ina take da kallo, lokaci guda mamaki ya bayyana ƙarara a kan fuskarta. Sunkuyawa ta yi tana shafa titin da yatsun hannunta a ɗan tsorace, da sauri ta janye hannunta tare da ja da baya kaɗan, still idanunta yana kan shimfiɗaɗɗen titin.
Mamaki ta ke yi yanda akai akazo akayi siminti a baƙiƙirin irin wannan a inda babu kowa?
A iya rayuwarta ba ta taɓa ganin titi ba, shi ya sa ganinsa a yau ya zame mata tamkar sabon abu a rayuwarta. Tana nan tsaye taƙi gaba taƙi baya sai kallonsa takeyi, ba zato ba tsammani wata haɗaɗɗiyar mota ƙirar Ford ta sako kai. Da wani irin mugun gudu Rabe ta kwasa tana ihu ta yi cikin daji zuciyarta tamkar zata dako tsalle ta fito, tun da take a rayuwarta bata san wani abu wai shi mota ba, sai dai a labari kuma shima hasashenta takeyi na wani abu daban amma irin wannan wanda ta gani da idanunta ba.
Har ta nausa cikin dajin ta ɓuya a bayan wata ƙatuwar bishiyar marke zuciyarta bata daina bugawa ba, sannan hoton abinda ta gani yana tafiya akan baƙin simintin titin be gushe da ga idanunta ba, Ganin abin takeyi tamkar wata halittar ce ta daban wadda babu irinta a cikin duniyarsu.
Sai da ta tabbatar data daina jin ƙarar motar sannan ta fito, ta durƙushe a ƙasan bishiyar hannunta ƙanƙame da jakar saƙin nan dai da mahaifinta ya ba ta. Ta jima a gurin har duhu ya farayi samnan ta yunƙura ta miƙe tamkar mai koyon tafiya ta ƙara fitowa daga cikin dajin tana ƙarewa shimfiɗaɗɗen titin kallo.
A hankali ta ɗaga ƙafarta ta taka titin a hankali don gani take a kowane lokaci za ta iya burmawa ciki idan ta taka da ƙarfi. Tana cikin wannan halin hadari ya mamaye sararin samaniya tareda iska mai ƙarfin gaske, da ƙarfi iskar ke kaɗawa tareda ratsin walƙiya wadda ta sabbaba tsawa mai ƙarfi, cikin gajeran lokaci
Ruwan sama ya kece tamkar da bakin ƙwarya, don dole haka ta koma cikin dajin tabar kan titin don neman mafaka, wata ƙatuwar bishiyar Gamji ta samu ta naɗe zaninta sannan ta haye samanta bishiyar ta lafe ta yi shiru. A hankali ruwan dake kwaranya ta jikin ganyen bishiyar ya fara sauka akan kyakkyawar fuskarta zuwa gangar jikinta.
Lumshe manyan idanunta tayi tana jin yanda jikinta ya fara rawa saboda sanyi, a wannan lokacin tuni jikinta ya fara rawa saboda yanda sanyin ruwan ya gama ratsa gangar jikinta, amma data tuna girman tashin hankalin dake sarƙafe da rayuwarta sai taji ƙarfin gwiwarta yana ƙara nunkuwa fiyeda lokacin da tayi bankwana da Baffanta, kuka ne ya kufce mata a hankali ta fara rerawa haɗe da tunanin makomar rayuwarta…
*** *** *** ***
ABUJA NIGERIA.
Sai wajen 8:00 pm sannan Muzaffar ya dawo gida. Direct falon Abie ya nufa, sai dai yana shiga falon ya ga Mom a gefen Abien. Gabansa ne ya faɗi amma kuma sai ya dake ya yi murmushi ya ƙarasa cikin falon da sallama. Da sakin fuska gami da ƙauna mai girma Abie ya ce,“Zo kusa dani yarona.”
Da sauri ya isa gare shi ya zauna daga ƙasan ƙafafun Abien tare da kwantar da kansa a saman ƙafafunsa. Murmushi kawai Mom ta yi ta ɗauke kanta a lokacin da kiran waya ya shigo mata.
Kallon Abie tayi ta ga hankalinsa gaba ɗaya yana kan ɗansa, hakan ya sa ta yi murmushi ta miƙe ta fita tare da kara wayar a kunnenta. Sosai hakan ya yi wa Muzaffar daɗi, don haka ya miƙe ya koma kan kujera kusa da Abie ya kama hannunsa cikin nasa ya damƙe su guri guda ya ce, “Abie! Wllhi ji nake tamkar nafi kowa sa'ar samun mahaifi irinka. Abie, ka cike mini duk wani gurbi da nake dashi a rayuwata, but I don’t know why nakeji a jikina tamkar na rasa wani abu mai mahimmanci a tareda ni. har yanzu kuma na kasa gane menene wannan abin da na rasa ɗin!”
Murmushi Abie ya yi mai cike da dattako sannan ya ce, “So tari a rayuwa mu kan yi kewar abubuwa da yawa a cikin rayuwarmu, musamman ma ace waɗanda muke ƙauna.”
“Ƙauna kuma, Abie?” Muzaffar ya faɗi hakan cike da rashin gamsuwa.
Murmushi Abie ya sake yi a karo na biyu ya ce, “A matsayina na abokinka kuma mahaifi , ina mai ba ka shawarar ka koma ka saurari zuciyarka yayin daka keɓance kanka kai kaɗai. To a nan ne za ka fahimci cewa lallai abin da na sanar da kai game da feelings ɗinka, soyayya ce mai tsananin ƙarfi da tasiri.”
“Abie, what exactly are you trying to say?” Muzaffar ya faɗi hakan yayin da ya ƙara kafe Abie da daren idanunsa.
Murmushi Abie ya sake yi a karo na uku sannan ya ci gaba da cewa,"Think carefully, my son. And listen to your heart. Surely this is a strong love. Ba gamagarin soyayya bace wannan ƙaunace yaro, irin ƙaunar da ubangiji ya sanya a tsakanin jini sa tsoka, na san yanzu ba zaka fahimta ba amma nan gaba kaɗan zaka fahimci komai idan lokaci ya bamu damar da muka jima muna nema.”
Wani irin zaro idanu Muzaffar ya yi, tamkar wanda aka gaya masa wani babban tashin hankali. Ya kalli Abie tare da sauke ajiyar zuciya ya ce, “Yanzu kam na fahimci abin da kake nufi Abie. But why nake jin sauyi a cikin rayuwata daga shekarun baya zuwa yanzu?
Ni kam tabbas ina ji a jikina akwai wani abu mai muhimmanci wanda ya zarta kalmar kewa a rayuwata, Abie don Allah mene ne shi?”
Kallon tsaf Abie ke bin Muzaffar da shi sannan ya miƙe ya ce, “Na ga alama idan na biye maka to za mu shekara da kai a nan ba tare da ka gaji ka jefa min sinƙin-sinƙin tambayoyinka ba. Oya tashi ka tafi, gobe 6:00 am in sha Allah jirginku zai tashi.”
Langaɓar da kai Muzaffar ya yi ya ce, “No, Abie, ni dai ba na son tafiya a private jet ɗin company, na fi so na tafi a normal jirgi kamar kowa…” Kallon da Abie ya watsa masa ne ya sa shi haɗiye maganar da ya yi niyar faɗa. Miƙewa ya yi tare da yima Abie side hug sannan ya fice daga falon zuwa ɓangarensa.
Kasancewar ya yi sallar isha’arsa a inda ya je yasa ya fara rage kayan jikinsa ya faɗa toilet. Wanka ya yi ya fito jikinsa duk a mace sannan ya shiryawa cikin pjamas masu laushi Ash, sannan ya kwanta bacci.
Washe gari tun sassafe ya tashi ya shirya cikin wata arniyar italian suits ƴar gaske mai azabar kyau, baƙa wuluk da ita sai ɗaukar idanu take yi. Sannan ya tsaya a gaban mudubin da ke ɗakin ya gyara gashin kansa mai laushi da santsi, A wannan lokacin kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci duk inda kyau ya kai to ya isa a buga misali dashi. komai na Muzaffar da yayi amfani dashi samfurin ƙasar Italia ne.
A nitse ya fito daga part ɗinsa cikin takunsa na isa da ƙasaita ya nufi falon Mom. Bai sameta a falon ba sai Fadilah da ke zaune cikin kayan baccinta mai launin milk tana kallon news a TV. Wuce ta ya yi ba tare da ya kalleta ba ya haura upstairs, saboda bashi da lokacinta sam Ya tsani mutum marar respect a rayuwarsa, shi ya sa ma ya fita sabganta.
Ƙofar ɗakin Mom ya ƙwanƙwasa, sai data ba shi izinin shiga sannan ya kunna kai cikin bedroom ɗin da sallama. A zaune ya sameta a gefen rantsatsen gadonta tana jiran ya ƙaraso. Gefenta ta nuna masa alamar ya ƙaraso ya zauna, ba musu ya yi yadda ta umarce shi.
Ɗan jim ta yi kaɗan sannan ta dubeshi cike da damuwa ta ce, “Har ka shirya kenan sai tafiya?” Da kulawa ya ce, “Ae Mom, na gama zan wuce kenan.” Gefen fuskarsa ta shafa kaɗan sannan ta ce, “Allah ubangiji ya ba da sa’a, ya sa kuma ka je lafiya ka dawo gida lafiya.” Da amin ya amsa mata sannan ya miƙe ya ce, “sai na dawo.”
Har ya kai bakin ƙofar fita idanunta na kansa sannan ta ce, “Make sure you don’t have any trust in Hajiya Aisha har ka dawo gidan nan, domin kuwa har yanzu ban gama yarda da ita ba, ka ji ko?”
Ɗan jim ya yi a ransa yana mamakin abin da ya sa Mom har yanzu ba ta son ya dinga shiga sabgar Hajiya Aisha. Ya daɗe yana lura da cewa duk sanda zai tafi wata ƙasa Mom bata damuwa, amma da zarar ta ji zai je India, daga ranar duk sai ta sauya ta shiga damuwa. Shin wai meye a tsakaninsu da ita da bai sani ba?
Comment
Nd
Share
Love you all guys
ZMC💋
***