Rayuwar Hinaya

Chapter 1&2

by @pinkyjay

RAUWAR HINAYA 😭 

Heart torchi story 💔
 Hot love and romantic 👄

Sorry and wriets by✍️
( Zainab Abdullahi Usman )

Pinky Darling Mrs Jay 🌹 



✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
💫💫💫💫💫💫
✨✨✨✨
🌟🌟🌟
💫💫

I love 
you Ammienah👄👄👄👄👄


🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥🔥
🔥🔥🔥🔥








Alhamdulillah 🙏 Allah na gode ma da kabani iKon fara rubuta wannan liltafi lafiya Allah ka bani ikon gamawa lafiya 🙏



RAUWAR HINAYA ƙirƙirarren labarine banyi shi don wani ko wata ba nayi shine saboda ilmantarwa da faɗakarwa ta re da bada nishaɗi idan labarin ya yi dai-dai da rayuwar ki/ka to arashi ne, 

Wannan littafin mallakin mai shine ban yarda wani ko wata su sauya min shi ba ta kowace siga batare da izinina ba, sai masu karatun litattafai a You tube duk wanda ya karanta min liltafi ba da izinina ba hukuma zata rabamu,  


gareku masu sayar da littattafan marubuta da fitar dasu batare da izininsu ba duk wanda ya fitar min da liltafi ko ya siyar na bar shi da Allah !


***
 kuyi following channel ɗina anan zaku rinƙa samun littatafaina
____________________________


***
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A) 
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
 (*we stand together*)
         🤝🤝🤝

Bismillahi Rahamanin Raheem 💫

Free pages 



Episode --1--&--2


________Wata mata ce zauna bakin murhun wuta riƙe da ludayin damun kunu, da wani ma dai daicin bukitin roba a gabanta, fuskarta a murtuƙe babu alamar fara'a a fuskarta, ta buɗe baki tana kiran "HINAYA wallahi idan na zo na sameki a ɗakin jikinki zai gaya miki banza sha-sha mai kama da mayu." 


Yarinyar da takira da Hinaya ce ta fito cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki ta na sanya wani hijab rabinsa duk ayage yake, duk ya ji jiki, ta na faɗin "Yi haƙuri Inna kaya na tsaya sauyawa ne." Kallo na ƙare ma yarinyar bazata wuce shekaru goma sha huɗu zuwa sha biyar ba, 


fara ce tas bata da tsayi sosai kana bata da jiki kyakkyawa ce sosai ta na da dara daran idanu da siririn hanci dogo da ƙaramin baki mai ɗauke da jajayen lips, tana da cikar gashin gira da na idanu, sai sumar kanta har saman goshinta, hijab ɗin da ta saka ƙarami ne hakan ya bani damar ganin jelar gashin kanta,


da ke kwance har kusan mazaunanta, ma sha Allah na faɗa saboda yarinyar ta haɗu ta kowace siga, sai abu ɗaya da na lura da shi babu alamar tsaftar jiki da tufafi atare da ita, 

ƙarasawa tayi gaban Innar ta durƙusa ta na jiran abinda Innar zata faɗa, wani wawan rankwashi ne Inna tayi ma tsakiyar kai, sai da ta saki ihu Innar ta buge ma ta baki ta ce "Idan kika kuskura ki ka yimin kuka sai na fanɗare miki fatar jiki, ta shi wuce zuwa rafi ki ɗibomin ruwa, idan kika daɗe kega kokon nan ko Ubanki bazai sha shi ba."


haka Hinaya ta wuce ta ɗauki tulu zuwa rafi fitowar ta kenan ta haɗu da Mero ƙawarta suka wuce tare Mero ta ce "Hinaya lafiya kuwa naga tun fitowar mu ko magana babu.?" Sai lokacin wasu hawaye suka sauko kan fuskarta ta ce "Ba komai Mero kaina ne ke ciyo." "To Allah ya baki lafiya Hinaya ." 

har suka ƙarasa rafi suka ɗebo ruwa a hanyarsu ta dawowa ne Husaini ɗan mai gari ya tare musu hanya jikin Hinaya ya fara karkarwa saboda idan ta fita tallan kokon da Inna ke ɗora ma ta , tana jin yadda ƴan matan wurin ke zagin Husaini ɗan iska ne number ɗaya, 


bashi da aiki sai lalata yaran mutane, Mai gari kuma baya magana ko ka kai ƙara aikin banza, saboda haka kowa ki tsoronsa ya addabi kowa har matan aure , Hinaya ya kalla ya na lashe baki kamar maye, ya ce "Ke zonan." Ya na nuna Hinaya ja da baya ta fara yi, har ta fara zubar da hawaye, 



da ya ga bazata zo ba ya fara takawa inda take Mero na ganin haka tayi ta kanta, ta bar Hinaya, ganin ya na gab da kamo ta,
 ta sakar mai tulun ruwan ga kai ta kwasa da gudu, sai ƙofar gidansu, shi kuma Hussaini nan ya zuɓe ƙasa dafe da kansa da ke jini, haka ya tashi ya kama hanyar gidansu,


Hinaya kuwa banda sauke lumfashi babu abinda takeyi tasan yau ta shiga uku wurin Inna ta fasa ma ta tulu, ta jima nan tsaye har Babanta ya fito, ganinta ƙofar gida tsaye yasan akwai abinda tayi cikin sanyin murya mai cike da tausayi ya ce "HINAYA lafiya ina ruwan da kika je ɗiba.?" 


Kallonsa tayi kana cikin Muryar kuka ta faɗa mai abinda ya faru hannunta yaja zuwa cikin gidan gabanta na dukan uku-uku, zaune suka tarar da Inna kan tabarma tana cin ɗumame kallo ta kare musu kana ta ce "Ke ina ruwan da ki kaje ɗiba.?" Baban ya ce "Ai ɗan Mai gari ne ya tare ta zai keta ma ta mutunci shine ta buga mai tulun ya fashe,



saboda haka Lami kiyi haƙuri dan Allah karki dake ta, ke..."Kutumar uba tulun nawa ta buga mai ya fashe wallahi kaji na rantse sai na fidda kuɗin tuluna a jikinta tun da kai tsaya tayi ma ka tutu bazaka iya biyana ba, ka wuce zuwa inda na aike ka kafin fushina ya sauka a kanka." 


haka Baba ya juya ya fita zuciyarsa na suya, duk yadda yaso ya takama Lami burki baya iyawa da ya shigo cikin gidan, Hinaya kuwa wuri ta samu ta raɓe tana jiran hukunci, ai Lami na gama cin ɗumame ta janyo wata ƙatuwar dorina tayi kan Hinaya,


hannuwanta ta ja har cikin ɗaki ta ringa jibgarta ta na ihu tana ba Inna haƙuri amma a banza sai da tayi ma ta mugun duka ta fasa ma ta jiki kana ta ɗebo gishiri da barkono ta ringa zuba ma ta a jiki tsabar azaba ko kuka Hinaya ta dena sai ajiyar zuciya takeyi,

Inna ta ce maza ta shi ga koko nan ki fita zuwa tallah kirki yadda ki dawo min da saura gaba ɗaya za ki siyar da shi." Ta juya ta fita,


Writes by pinky Darling Mrs Jay 🌹 more comments more typing ✍️