Rayuwar Hinaya

Chapter 3&4

by @pinkyjay


🔥Episode 3--&--4🔥



Haka Hinaya ta fito tana jan jiki ta ɗauke kokon ta fita har wani jiri ke ɗibar ta, saboda yunwa tun abincin rana bata koma cin komai ba sai ruwa kai take sha idan ta ji yunwa, baƙin titin ƙauyen ta tsaya inda sauran 'yan talla ke zama ita ma ta zauna,

wata mai suna Kande tace "Hinaya ga wani Alhaji can ya na jiranki koko yake son yin sadaka shine na gaya mai yanzu za ki zo." Ta Æ™arasa maganar tana kiran "Alhaji gata nan ta zo." 

Hinaya kuwa sai cema Kande tayi "Na gode sosai Kande Allah ya baki mai siye taki sana'ar." Ta ce "Amin Hinaya wai miye ya sameki duk jikinki a fashe ba dai wannan muguwar matar bata dena dukan ki ba.?" 


Hinaya ta ce "Kema dai Kande kesan babu wanda zaiyi min wannan dukan idan ba Inna ba." Kande tace "Allah ka isar miki Hinaya Allah ya baki miji kiyi aure ko za ki huta da wannan wahalar." 

Murmushi kawai Hinaya tayi saboda Alhajin ya iso yace kunun nawa ne haka kawai ta samu kanta da faÉ—ar na dubu É—aya ne ya zaro Æ´an É—ari biyu na 1k ya bata ya ce ta rabama Almajirai kunun, 


ya tafiyarsa haka Almajirai suka bi layi tana zuba musu kowa ya samu ta ragama kanta ta cire naira É—ari ta ba Kande kana ta siye dankali ta sha kunu, 

Kande ta ce "Gaskiya naji daÉ—in da kika ce na dubu É—aya ne saboda haka kega nima na siyar da awarata muje ki saye asusu ki cire ma wannan muguwar kuÉ—in kununta ki saka saura asusu ki ba Innata ta aje miki,



duk Alhaji ya siye kunu kina cire mata kuɗinta kina saka saura asusu, duk lokacin da kike buƙatar wani sai kizo Inna ta baki asusunki ki ɗibe kuɗi kiyi abinda ki ke so, kega za ki samu kuɗin hijabin makarnta,

saboda naƙi duk ya gurje har faɗa Malamai ke miki." Ajiyar zuciya Hinaya ta sauke ta ce "Na gode Kande da wannan shawara kega kuɗin kununta ɗari huɗu da ashirin ne, saboda haka ga sauran kuɗin ki siya min asusun, kiba Inna ta aje min ,

Idan ina yawan zuwa gidan ku Inna zata iya gane wani abu saboda haka duk na siyar ke zan ba ki tafi da su kawai." Kande ta ce"To shikenan Allah ya sa hakan ya zama alkhairy Hinaya." Ta ce "Amin." 


Kowa ya kama hanyar gidansu,


ko da ta shiga gidan ba kowa Inna ta fita unguwa saboda haka ta samu ta É—ora ruwan zafi ta gasa jikinta tayi fitowar ta kenan Babanta ya shigo da ledar kilin ya ce "Hinaya gashi ki wanke kayanki kafin Lami ta dawo ta karÉ“e ta hanaki wankin." 


KarÉ“a tayi kana tace "Na gode sosai Baba Allah ya Æ™ara rufa asiri duniya da lahira." Cike da jin daÉ—i ya amsa da Amin ita kuma jiki na rawa ta kwaso tsummanta da basu wuce kala biyar ba tafara wanki tas ta wanke ta shanya ta shiga gyran gidan, 


har ta gama lokacin azahar ya yi tayi sallah Inna bata dawo kayanta na bushewa ta kwashe ta kai É—akinta ta aje kan wata tsummar tabarma duk ta yage samanta take kwanciya, wutar da É—ora ruwan zafi, ta gyra ta É—ora tukunyar ruwa,


kana ta É—auko gari ta soma tankaÉ—e tana kammala ruwa na tafasa ta fara talgin tuwon, bayan ta gama ne ta daka daddawa da kayan yaji ta ajiye lokacin talgen ya yi ta tuÆ™a tuwon ta kwashe, kana ta É—ora miya, 


ta daka yakuwa ta kaɗa ta jidda miyar ta ƙara gyara wurin tas Hinaya akwai son tsafta Inna ce tsabar mugunta ke hanata wanka da wanki tayi ta yawo da dauɗa sai tayi sati jikinta baiga ruwa ba, sai ta fake idanunta ta watsu ruwa ta fito ba susu ba sabulu,


har bayan la'sar Inna bata dawo Hinaya ta ɗibe tuwo taci sai da ta ƙoshi yau kakarta ta yanke saƙa Inna bata nan,



_________Abuja City Unguwar Mai tama,

layin ƴan Majilisa, wani ɗan ƙareren gida ne da babu kamar sa kaf layin unguwar, saboda girma da haɗuwa kai da ganin ko Get ɗin gidan kasan kuɗi sun zauna wannan gida kutsa kaina nayi cikin gidan ma sha Allah party huɗu ne cikin gidan,



na farko na fara shiga inda na tadda wani katon parlo da ya ji kayan more rayuwa komai na parlon ya haɗu bazaka taɓa tunanin a Nijeriya kake ba saboda haɗuwar parlon da tsarinsa, wani tangamemen hoto na gani maƙale,

a parlon ya na yima Barka da zuwa An rubuta Alhaji Muhammad family sai jikin hoton wani babban mutum ne zaune da 'ya'yansa mata guda uku sai maza guda biyu wanda É—ayan ya fi zama babba, ga duk alama shine babban yayansu, sai wata mata kusa ga mutumen, 


Ma sha Allah sunyi kyau sosai amma ba kamar wannan guy ɗin saboda sam baya kama da su ya fi kama da Larabawa, Makkah, duk da kwayar idanunsa irin na mage ne in takwaice muku gayen ya haɗu sosai ta ko ina kamar shi ya zana kansa, ga dogon hanci da ƙaramin bakinsa,


ga sexy eyes É—insa, ga sumar kansa ta sha gyara kamar ba indiye, farine tas ya nada tsayi dai-dai kana ya na É—an jiki bazaka kiransa ramamme ba, fuskar kowa É—auke da murmushi amma banda shi, 


jin muryar wata mata dake zaune cikin parlon ya katse min kallon da nike ma hoton ta na kiran "Laure Laure." Wata Dattijuwa ce ta fito da alama da ga kitchen take ta dorƙusa gaban matar tana faɗin "Hajiya ƙarama gani." Wani banzan kallo Hajiya ƙarama tayi ma tsohuwar,


kana ta ce "Idan kun gama aiki kesan abinda wannan É—an iskan yaron keso kidafa mai Alhaji ya kirani jirginsu ya kusa sauka saura kiyi min abinda ban saka ki." To kawai Tsohuwar ta ce ta wuce kitchen ta same Shafa da suka aiki tare ta ce ,

"Shafa yau Haisam zai dawo shi da Alhaji ." Shafa cikin farin ciki da ya bayyana a fuskarta ta ce "Kai Iya amma naji daÉ—in wannan labari da ga yau iskancin su Siyama da Adam ya Æ™are hutun mu yazo." Iya ta ce "Sosai ko Allah dai ya kawo shi lafiya." 

cikin farin ciki suka ci-gaba da aikinsu 


wani matashi ne ya shigo cikin parlon ko sallama babu ya zauna kusa ga Hajiya ƙarama ya ce "Mom wani mugun labari nikeji wai Ya Haisam zai dawo.?" Hajiya ƙarama ta ce "Eh haka Dadynku ya sanar da ni jirginsu ya kusa sauka."

Cikin damuwa ya ce "Mom wai yaushe zakiyi muna maganin wannan banzar Haisam wallahi na tsane shi mugun É—an sa ido ne.?" Dariyar mugunta tayi kana ta ce "Karka damu Adam akwai abinda nike jira kaÉ—an zanyi maganinsa,


kamar yadda nayi muku alƙawari idan ya san wata bai san wata ba." Shima dariya yayi kana yace "shiyasa nike sonki Mom ke iya mugunta, Amna ce dake tsaye tana jin abinda Mom ɗin tasu ke faɗi ita da Yayansu ta ce "Mom kuji tsoron Allah wai me Ya Haisam ya tare muku ne,


baku da aiki sai lissafin cutar da zakuyi mai wallahi...."Ke! Sha sha rufe min bakinki wacce bata kishin uwarta, wallahi Amna idan kina saka min baki idan ina magana sai na illataki banza kawai wuce bani wuri." Mom ta ƙarasa maganar,


ta na nuna Amna da hannu Adam ya ce "Ai wallahi Mom da ke bari na fasa ma ta baki ." Ta ce "No barta kawai zanyi maganinta wallahi da asibiti na haifeta da nace sauya min ita akayi." haka suka cigaba da saƙa irin muguntar da zasuyi ma Haisam,



Ƙauye gwagwalada kuwa 

sai Æ™arfe shida Inna Lami ta dawo bata samu kowa ba a gidan saboda Hinaya ta fita makarantar Allo ta kusa sauka cike da masifa ta fara dube-dube ta ga wane aiki Hinaya batayi ba idan ta dawo ta ci ubanta amma har aikin da bata sakata ba tayi, 


Kitchen ta liƙa nan ma ta ga har abinci ta gama da ma yunwace ta dawo zuba tuwon tayi ta fara ci sai juya kai take alamar miyar tayi daɗi sosai, tana cin tuwon ne Hinaya tayi sallama ta shigo,


bata amsa sallamar ba sai cewa tayi "Ke ina kuÉ—in koko na.?" Ta ce "Gasu na ga ba kya nan ne." Ta buÉ—e jakar liltafanta ta ciro kuÉ—in ta bata kana ta shige É—aki ta aje jakar ta É—auke kwanon da Lami ta aje ta wanke kana ta É—auko liltafanta na boko ta fara dubawa saboda sun kusa fara jarabawa,


Wriets by pinky Darling Mrs J 👄