Kuncin zuci
by @bintuuu
Shiru Na'ima tayi a kwancen takasa bude idonta ta gaisa dasu Mamman dake zaune a sofas din dakin, wani irin kunya ce take nuqurqusanta kamar ta tsaga kasa ta shige taekji, tananan kwance ahakan ta sakejin muryan su Mummy da Murja sun shigo suna fadin "sannu Amarya" nan ma Na'ima ta qara damqe idanunta dan daman a juye take bata fuskantarsu, Anty Amnah ce ta dawo dakin sai Mamma ta miqe tace zasu tafi itada Antyn while Fatima zata zauna, miqewa su Mummyn sukayi tace "bari mu koma can din muma, ai nazata idonta biyu ne ma" amsawa Anty Amnah tayi da haka suka fice daga dakin sai ta qarasa gurin Na'iman tareda zagayowa daidai inda fuskanta ke kallo tace "Daughter ya jikin?" Luf Na'ima ta sakeyi bata bude idon ma ba sai Antyn tayi murmushi ta kalli Fatima dake zaunen tace "Bari in barku, zan shigo anjima, inada aiki yanzu" Fatima ta amsa da "toh Anty ba damuwa" da haka Anty Amnah ta fita daga dakin, sunanan zaune shiru Na'ima ta dan bude idonta kadan tana kallon wall din dakin sukaji an sake bude kofan, ganin Ahmad yasa Fatiman sake cewa "Ina wuni Yaya" casually ya amsa yana kallon gadon, hannunsa riqe da leda babba, ganin ya nufi gadon yasa Fatiman miqewa ta nufi kofan fita daga dakin, sai da ya jira ta fitan ya ajiye ledan hannunsa sannan ya duqa kansa yana leqen Na'iman wanda tun Jin qamshin turarensa ta sake rufe idanunta, ahankali yace "Babe" sai ta damqe idanunta bata kulasa ba, hannunsa yakai zai juyo da fuskarsa sai ta qi basa daman yin hakan, miqewa yayi sai ya zagaya ta dayan gefen gadon ya sake duqawa ahankali ya hade goshinsu guri daya, shiru sukayi ahakan suna shaqan numfashin juna, sai can kamar me rada Ahmad yace "My luscious" sai sannan Na'ima ta bude idanunta direct suka shiga cikin nasa, wani irin abu taji ya bi jikinta tun da kafarta har kanta dalilin irin kallon da yake mata, da sauri ta saqe damqe idanunta, ahankali tace "Nidai ka tafi" sai yayi murmushi kadan tareda sarqe yatsunsu guri daya yace "kiyi hakuri kinji" "Bansani bane Babe" sai ya matsa daidai kunnenta ya rada mata "You're too sweet for me to hold myself" ai da sauri ta turasa baya tana kukan shagwaba tace "Ni wallahi ka fita" sai ya dora kansa a qirjinta yana murmushi, yace "Toh kiyi hakuri, hakan bazai sake faruwa ba kinji" shiru Na'ima tayi sai kuma ahankali ta kai hannunta cikin sumar kansa tana shafawa a hankali sukayi shiru ahakan babu me magana, can ya dago kansa yana kallonta ahankali yace "You're a Gem Na'eemah...My Gem" sai ta dan tsaya kallonsa while shima yana kallonta cikin bugawan zuci, wani irin sonta yakejin yana hauhawa a zuciyarsa a wannan lokacin, sai ya kai yatsansa yana shafa girarta cikin kwantar da murya yace "You completely undo me Na'eemah" "Zuciyata takice gaba daya" tana kallonsan ta damqe hannunsa daya dake cikin nata, jin kalaman take suna samun mazauni me kyau acikin zuciyarta, sai ya sauqo da yatsansa zuwa lips dinta yana shafawa ahankali bai bar kallonta ba, dan duqar da idonta tayi daga kallonsa sai yace "tashi kici abinci kinji" ta girgiza kai ahankali tace "na qoshi" sai ya saqe duqowa yace "Babu abunda kika ci Babe" juya kanta tayi bata amsa ba nan ya sake cewa "zanje gida yanzu, me kikeson in kawo miki" tace "Babu" da haka kuma taqi juyawa ta kallesa har ya miqe ya nufi fita daga dakin, bai dade da fita ba Fatima ta dawo dakin, tana kallon Na'iman tace "Sannu Anty, ya jikin?" kasa amsawa Na'iman tayi da farko dan itadai wannan lamarin kunya yake bata matuqa, ganin Fatiman ta zauna a kujeran jikin gadon tana kallonta yasa tace "Yasu Hamra?" Fatima ta amsa da "Na barota a gida gun babanta" sai Na'ima ta gyada kai sukayi shiru nan ma, bude ledojin Anty Fatima tayi sai tace "Yaya yace in tabbatar kinci abincin nan Anty" sai Na'ima tayi qaramin murmushi batace komai ba ta fara qoqarin miqewa Fatiman tace "Akwai abunda kikeso ne?" tace "A'a zanyi sallah ne" sai Fatima tace "Bari na hada miki ruwan tukunna" da haka ta nufi bandaki, da ta dawo sai Na'iman ta miqe cikin mazewa ta fara takawa a hankali ta shiga bandakin, sai da ta tabbatar da gyara jikinta sannan ta fito, nan aka turo kofar Mami da Nafisa suka shigo, aikuwa tana ganinsu sai hawaye yazo mata, da sauri suka qarasa gareta Mami tace "Sannu Habibti, sannu kinji" da haka ta kamo hannunta suka nufi gadon ta zaunar da ita, sai kawai Na'iman ta fara kukan lalaci, Fatima na kallonta tana murmushi, nan suka saka ta a tsakiya suna mata sannu, Nafisa tace "Bobo numfashin meye ne yanzun, ba kin cemin ya daina miki ba" Mami tayi saurin cewa "Shi rashin lafiya in ya tashi dawowa yasan da haka ne?" sai Nafisa tace "tun da muka koma makaranta ya daina mata fa Mami" murmushi Fatima tayi tana kallonsu tace "Ciwo ba ruwansa da wannan sis" Mami tace "Rabu da Baby da'alla" Nafisa ta kalli Na'iman tace "Sannu, Allah ya baki lafiya" sai Na'iman ta share hawayen ta tareda gyada kai kawai, nan Mami tace ta kwanta sai tace zatayi sallah tukunna...
Har dare suna zaune tare da ita a dakin, zuwa sannan Lantana ta kawo mata farfesun kayan cikin da Mami ta sa tayo mata shi in zata zo, su Abu da Al'ameen suma samun guri sukayi anan dakin aka kama hira kuma, sai hakan yasa Na'iman warware wa sosai suna hiran tana amsawa da murmushi ga bowl din pepper soup din da Mamin ta zuba mata a gabanta suna ci tareda Nafisa dake zaune kan gadon tayi baqe baqe abunta, Abba ne ya shigo dakin Ahmad da faruk na biye dashi, Na'ima ta duqar da kanta tanajin kunyan na cikata, addua take Allah yasa Abba baisan abunda ya farun ba, sai taji yace "Sannu daughter" sai ya kalli Ahmad yace "Me yayi triggering dinta haka, panic attack is a serious case fa, you have to be careful Son" Ahmad ya duqar da kansa sai Mami tace "Tsorata tayi shiyasa, kasan zaman kadaici" sai Abba yace "Allah ya kare na gaba, sannu ko" Na'ima ta gyada kai har sannan bata dago ba, Faruk ma sannu ya mata sannan suka ce zasu koma, nan su Abu ma suka miqe zasu bisu sai Mami tace da Nafisa "Baby ki zauna anan din" tace "Eh Mami daman anan zan kwana" sai tace "Okay" da haka su Abban suka sake yin sannu ga Na'iman sannan suka fita aka bar Ahmad tsaye, gaisheda Mamin yayi batareda ya kalli idonta ba, itama tana tattare plates acikin basket ta amsa da "Lafiya" dan itama dai nauyinsa takeji yanzu, sai da ta gama hade plates dinda suka ci abincin sannan ta miqe dan su Abu anan dakin sukaci abincin suma, sai ta kalli Na'iman tace "Habibti sai da safe ko, ki kula kinji" cike da kunya ta gyada kai dan Mamin ce ta rinqa hada mata ruwan dumin tana shiga tun zuwansu, da haka Mamin ta fita tana musu sallama, sai Ahmad ya ajiye ledan hannunsa sannan ya nemi guri kan sofa ya zauna yana kallonta, Nafisa ce ta gyara zamanta akan gadon tanajin awkwardness kuma, sai can ta sauqa tace "Yaya bari naje dubo Laila" ya gyada kai alamun toh sannan ta fice tana gyara gyalenta, shiru sukayi bayan fitan Nafisan kan Na'ima a sunkuye sai ya miqe ya qaraso gareta, zama yayi a bakin gadon ya riqo hannunta yace "How are you feeling dear?" bata ce komai ba yana kallonta yayi murmushi ya sake cewa "Me kikeci babu bismillah" sai sannan tayi murmushi ta tura masa bowl din gabansa tace "Kaci" dan dariya yayi sai ya dauko daya cikin spoon tareda kai mata bakinta, juya kai tayi tace "Nakoshi ai" sai yace "Dayan nan kawai kinji" qin karba tayi sai ya kai bakinsa yaci, yana kallonta yace "Anan nakeson in kwana, ya zamuyi da Nafisa?" tace "Uhm Uhm katafi abunka" ahankali yace "Bakyason mu kwana tare Babe" ta amsa da "A'a nidai ka tafi" sai yayi murmushi kawai, Nafisa ce ta dawo dakin dan zama cikinsu Mummy da Lailan ba nata bane, samun guri tayi ta zauna sai can kuma Anty Amnah ta shigo dakin, saida ta gama gwada Bp'n Na'iman sannan tace "Doctor Chris is on night duty, you can call him in wani abun ya taso, zan riqeta saboda monitoring numfashin nata ne ma amma zuwa gobe ma in komai ya daidaita zaku iya tafiya" Ahmad ya gyada kai tareda fadin "thank you" sai ta dubi Na'iman tace "sannu Na'ima, Allah ya qara sauqi ko" ta amsa da "Amin" ahankali, sallama Anty Amnahn ta musu amma bata kai ga fita ba ta kusa cin karo da Murja da tashigo adan figice tace "Jikin nata ya tashi fa Anty" sai Anty Amnah ta fita da sauri murjan ta bi bayanta, miqewa Nafisa tayi ta bi bayansu da saurinta itama, sai Na'ima ta kalli Ahmad dake zaune a bakin gadon yana kallon kofan, juyowa yayi suka hada ido tace "Kaje ka dubata please" sai ya girgiza kai yace "I'm not a doctor Na'eemah, me zan mata in naje?" nan Na'ima ta fara kokarin sauqowa daga gadon tace "Muje Dan Allah, she's your sister fa" bata jira cewarsa ba ta kamo hannunsa sai ya miqe suka fitan tana riqe da shi, sai da ta jashi har kofan dakin Lailan sannan ta sakesa tace ya shiga sai ya kalleta yace "ke bazaki shiga ba" ta girgiza kai tace "A'a kaidin ka shiga" sai ya kamo hannunta shima ya bude kofan suka shiga dakin tare, samu Lailan sukayi Anty Amnah ya dubata ga breather a maqela a hancinta tana fitan numfashi da qarfi, da sauri Na'ima ta zare hannunta daga cikin na Ahmad amma ganinta gefen Ahmad din yasa Laila ta fusge abun hancin nata tace "Dan uwarki ki fita, mayyaaa" Anty Amnah tace "Lailaaa!!" tace "Ta fita wallahi ko in hallakata, ni ba 'yaruwata bace, ba 'yar'uwar kowa bace a familyn nan 'yar bariki kawai" rai a bace Ahmad ya doshi gadon sai Anty Amnah ta miqe tana taresa, a tsawace Mummy tace "Barsa ya tabamin 'ya a gadon Asibitin sai yaga yanda zan rama mata akan bazawarar kilakin matar tasa, maqaryaciyar banza kawai" Anty Amnah ta juya ta kalleta tace "Nice maqaryaciyar kenan, tunda a bakina kikaji yarinyar budurwa ce" Nafisa ta ware Ido tana kallonsu, sai Na'ima ta juya da sauri ta fice daga dakin, Ahmad bai jira hargagin da Mummy ta fara ba ya bi bayan Na'iman, murya a sama Laila take fadin "Mayyaa, wallahi sai na rabaki da naki farincikin a rayuwa, wallahi sai na ga bayanki kema" Ahmad bai sauraresu ba yabi bayan Na'iman da take hawaye, a corridor'n asibitin ya riqota ta juyo hawayen na zuba a idonta tace "I can't stay here, zan bi Mami, ka kaini gurin Mami" da sauri yace "No Baby, you won't leave me" tace "Ahmad bazan zauna a asibitin nan ba, please ka kaini gurin Mami" cikin lallashi yace "Tunda bakyason asibitin, I'll call a nurse ta kula dake a gidanmu, mu tafi gidanmu kinji" kafin ta basa amsa Anty Amnah ta fito daga dakin tare da Nafisa, sai da suka qaraso gurinsu Ahmad yace "We're going home Anty, I'll call a nurse to take care of her" Anty Amnah tace "Hakan ma ba damuwa, zan aika muku nurse daya zuwa gobe ta rinqa dubatan, amma ka kirani fa in kaga numfashin ta yayi nauyi ko wani abun" sai ya gyada kai tareda kama hannun Na'iman ya jata suka tafi dakinsu while Nafisa na biye dasu a baya tana saqe saqe arai, saida Nafisa ta tattare musu kayansu, sannan suka fita haraban Asibitin dan Anty Amnah ta koma dakin Lailan, Na'ima ji take kamar tayi kuka dan har ga Allah tasan da Mami na nan zata tafi da ita, Allah Allah take ace Nafisan batazo da mota ba yanda in suka kaita can gidan zataji dadin yin escape itama, sai adduanta bata karbu ba dan kuwa ga motan Nafisan nan a fake da ita sukazo tareda Mamin sai ta koma cikin ta su Al'ameen, Sallama Nafisan ta musu sai tayi hugging Na'iman tace "Allah ya qara sauki, zanzo soon" sai Na'ima ta gyada kai hawaye na zuwa mata, da haka Ahmad ya taimaka mata ta shiga motan shima yayi sallama da Nafisan ya shiga front seat suka bar asibitin, Ahanya ma shiru sukayi sai ya kamo hannunta ahankali yana wasa da yatsunta, tana jinsa amma bata juyo ba sai yace "Babe bazaki kulani ba" nan ma shiru, da haka suka qarasa gidan wajen karfe tara da rabi na daren har sannan babu wanda ya sake magana cikinsu kuma, sai da suka shiga falon yaga ta nufi stairs tana tafiya ahankali sannan ya bi bayanta ya riqota yace "Babe" sai sannan ta kallesa sai yace "karki saka maganan da ta fada ko daya a ranki please" sai ga hawaye sun kawo idonta tace "Akanka tasha pills din ko?" sai yayi shiru da fari, can kuma yace "Let's not talk about this now" aikuwa nan hawayen suka zubo wa Na'iman tace "Bazan iya jurewa ba wannan karon, da me irin halinta na sha fama abaya, but not this time" sai yayi saurin rugumeta yace "Not this time wife, Billahi ke kadai nake so" dagowa tayi tana kallonsa tace "Dagaske nake bazan iya jurewa ba in ka aureta, I Love you Ahmad" sai ya hade bakinsa da nata a matsayin amsarsa, kissing dinta ya shiga yi a hankali sai itama ta saqalo hannunta a wuyansa tana Jin saqonsa na isa ko Ina a jikinta, sai da ya tabbatar ta nutsu sannan ya barta nan ma ya sake rungumeta tayi luf a qirjinsa, yana shafa bayanta ahankali yace "I choose you Na'eemah, tun fil azal ke nakeso kuma da ke kadai nake son in rayu, ban tabajin sonta ko na zarra ba, ki yarda dani Dan Allah" sai ta gyada kai a hankali ta sake tightening riqon bayansa da tayi, sun fi minti 3 ahaka sannan ya fara kokarin daukanta yace "Yanzu muje inga abunda ya faru da hanyata" cike da kunya ta fara turasa, a shagwabe tace "Nidai ka kaini gurin Mami" ya girgiza kai yana murmushi yace "Nizan kula da matata" sai ta juya tana murmushi zata hau stairs din yayi saurin daukarta ya wuce part dinsa da ita, akan gadonsa ya kwantar da ita tana kallon yanda ya gyara ko ina, sai ya nufi toilet bai dade ba ya dawo dakin nan ma ya wuce closet dinsa duk tana kallonsa, fitowa yayi sanye da T-shirt me laushi da three quarter ajikinsa sai ya riqo towel dinsa a hannu ya qaraso gurinta, hijab din nata ya fara cire mata sai tace "zanyi wankan acan dakin" yace "A'a kiyi anan" ahankali ta miqe sai ta karbi towel din zata tafi bandakin da kayan jikinta sai yayi murmushi yace "bari dai kiga ni nayi aikin" batayi aune ba taji ya fara jan zip din riganta tayi sauri juyawa tace "nidai kabari in cire a bandakin" yana murmushin yace "bazan kalleki ba fa, kingani" sai ya rufe ido ya sake cewa "kingani ahaka zan tayaki cirewa" kawai ta dan fara dariya while shima haka, tana girgiza kai tace "Wai nan wayo zakamin" sai ya bude idanun nasa yace "Au wai kin gane daman" nan ma tayi wani dariyan sai ya riqo waist dinta suna dariyan atare yana kallon idanunta, wani irin qaunarta ne ke sake kutsawa cikin zuciyarsa, sai da suka lafa sannan yayi qanqan da murya yace "Muje in duba miki kinji" sai ta kai hannu tadan bugi qirjinsa tace "Ahmaad" yayi murmushi yace "Dan kadan zangani fa" sai ta fara qoqarin barin jikinsa kawai ya dauketa ya nufi babban toilet din nasa da ita, nan toilet din suka hau rigima shi ya dage sai ya cire mata kayan ita kuma ta dage sai ya fita, tana kukan shagwaba tace "Ni na fasa wankan ma" kawai taga ya fara sauqe mata rigan, saita juya masa baya tana kare qirjinta tace "Wayyo Allah na" yana dariya ya qarasa sauqe rigan zuwa qasa sai ya tsaya kawai yana kallon bayan nata gaba dayansa, nan dariyan ta dauke kuma ganin wasu irin tabo a bayan nata, tar yake ganinsu cikin haske zuciyarsa na rawa, Jin yayi shiru yasa Na'iman dan juyo dakai tana kallonsa, da wuri ta tsugunna ta rarumo rigan nata zata saka kawai taga idanun Ahmad sun fara maiqo kamar na hawaye...
Yau kuyi hakuri dani mutanen arziqi, akan gudu nayi chaptern nan ban nutsu nayi editing ba.