Chapter 18
by @aryaahriyad
Wasan sarƙaƙiya.
By Aryaah Riyad..
Book one 1…
Chapter 18
Stars talented writers….
Opposite dinta ya zauna sannan ya daura kafa daya kan daya ya dawo da idonshi cikin nata. Tahira ce tayi saurin mikewa tana komawa inda yake tareda hugging dinshi tana fadin “ Daddy ka dawo? Kaga Alina saida naje na hado mata tea wai ashe kurba biyu kawai zatasha bataga wahalar danayi bah”.
Murmushi yamata yana shafa kanta cikin tattausar murya kana gani kasan yanaji da ita yace “ toh ke banda abinki ai bakowa keda irin cikinki ba dabaya gajiya dacin abinci, tunda tace ta koshi ai shikenan ko?”. Turo baki Tahira tayi tana juyar dakai ita a dole tayi fushi. Cikin kunkuni tace “ nidai cikina yana koshi da abinci saidai naku ne baya koshi”.
Banza da ita yayi yana kara maida kallonshi kan Alina. Ta kame tana dadanna waya. Soyake yaga menene take daddannawa haka a wayar tun dazu dake dauke mata hankali. Itako Alina bawani abu take a wayar ba, tsabar kawai ta nuna tanada abunyi ne yasa take daddanawa.
Yanata dan satan kallonta dan bayaso Tahira taga wani abu ganin Alina bawai zata fara magana bane yasa yay gyaran murya ciki ciki kafin yace “ Alina ya Ummi? Tananan lafiya? Ya twins? Da Laya shagwababbiya kamar Tahira?”.
Dan dariya tayi aranta a fili kuma tadan tabe baki kamar batason maganar sannan tace “ Oh Laya nanan tana rigingimunta, zan kawo muku ita ne kawai tahadu da Tahira dan abun nata gaba yakeyi yanzuma da Ummi ba lafiya sai da fada kullun ake samun lafiya”.
Subhanallah ya fada yana da tasowa daga kishingidar dayayi “ What? Ya akayi ban saniba? Meke damunta”.
Dan kara hade fuska tayi bata bashi ansa ba. Reaction dinshi yayi mata dadi sosai dan da biyu ta bige da zancen Laya ta fada rashin lafiyar mamah, dan tunani tafara ta fada mishi straight forward ne kawai ko tabari ya tambayo da kanshi? Bataso ta fada dan zai iya ganewa cewa daman abunda ya kawota kenan, amma kuma idan taki fada yazamana saiyazo ya nema da kanshi lokaci zai baci.
Cikin wata tsigar magana data tabbatar tana kallon idonshi yana kallon nata tayi tace “ Uhm i don’t really know gaskiya. Something like kamar ko heart transplant take needing cikin gaggawa but kasan yanda situation dinta yake its not like za’ayi mata abunda take bukata”.
Dan shiru yayi kamar mai nazari tanajin wani iri a zuciyanta ganin hakan. Sosai takejin kunan abun dan tunda take a rayuwarta bata taba shiga wani abu dazaisa saita kaskantar da kanta haka ta nema ba. Lallai kuwa Hussain dole ya kwashi kashinshi a hannu dan baza tayi mishi da wasa ba.
Cemata yayi yana zuwa sannan ya tashi yabar palourn. Sai a lokacin ta tuna da Tahira tajuya kanta kawai taganta tana sharbar hawaye. Mamaki ne ya kamata toh mekuma akayi ma wannan yarinyar? A hankali ta kira sunanta “ tahira? Me yasaki kuka?”.
Kamar tace mata yi kawai ta fashe da kukan. Da babu kara yanzu kuwa kamar an kunnata. Tashi tayi daga inda take ta koma kujerar da Tahira take tana dago fuskanta data boyeshi da hannu tana kukan. Dakyar tasamu ta tsagaita kukan tana shasheka tareda maida ajiyar zuciya cikeda rigima tace “ sis Alina Ummi batada lafiya baki fadamun ba? Yanzu yatake? Taji sauki? Tana hospital ne? Anbata magani?”. Ta jero mata tambayoyin tana waro mata idanu jiran ansarta.
Dan jim Alina tayi kafin tace “ no Babu abunda akayi mata tana gida”. Wani kukan tasaki voice dinta cikeda tausayi tace “ Saboda uncle Hussain ne yasa ba’a kaita hospital bah? Sis Alina kiyi hakuri kinji, komai zai wuce”.
Wani iri Alina taji itafa a duniya daya daga cikin abunda ta tsana shine a tausaya mata. Ita ba abar tausayi bace dan haka sosai taji maganar a ranta kawai ta tashi takoma inda take zaune ta ciro wayarta daidai nan daddy tahira ya dawo cikin palourn. Bai zauna ba saidai ya karaso inda suke yakalli Alina yace “ Alina ki kaita Qatar private hospital nayi magana da Medical Director dinsu ayi admitting dinta za’a samo mata heart daza ayi transplant din na bada dadewa ba Allah ya kara mata lafiya sainazo dubata”.
Ameen tace mishi sannan tace thanks. Da ok ya ansa dan baimayi zaton zatayi mishi godiya ba, dukda kuwa thanks kawai tace amma kwata kwata bai zata zatayi hakan ba.
Juyawa yayi ya fice Alina na sauke ajiyar zuciya. Plan dinta na farko yayi Aiki ba karya. Tayi mai saukin saura mai wahalan. Wannan kuma ba yau ba.
Saida ta tabbatar ya fita daga gidan sannan tayi ma Tahira sallama zata tafi. Sosai Tahira tayi mata rigima kafin tabarta ta tafi. Motarta ta shige taja ta fice daga gidan straight gida ta nufa. Message ne ya shigo wayarta da kamar bazata duba ba saikuma ta dauka. Daga unknown number ne akayi. Batako karasa karanta abunda aka rubuta ba tawani ja burki a tsakiyan titi tareda…..
Kuwait….
A bangaren Yazrin kuwa tana cikin wannan yanayin aka bude kofar dakinta. Da sauri ta dago kanta wata kuyanga ce ta shigo. Juyarda kanta tayi tana goge hawayen face dinta da bayan hannunta sannan ta juyo ta kalli kuyangar data fado mata daki batareda kwankwasawa ko sallama bah.
Bude baki tayi ta masife ta saidai ta fasa kawai dan bamata da energyn yin masifa a yanzu. Cikin shakakiyar murya tace “ ya akayi?”. Dukar da kanta kasa kuyangar tayi sannan tace “ Princess Yazrin ana kiranki a kasa”. Gyada mata kai Yazrin tayi sannan ta fice ta rufe nata kofa.
Mikewa tayi tana tunanin mekuma zaisa a kirata yanzu? Ko fadan da akayi mata bai isa bane sai ankara mata wani? Toilet ta shiga ta dauraye face dinta tana kallon yanda face dinta ya kumbura idanunta sunyi luhu luhu a kumbure sunyi ja. Kara watsa ruwan tayi a face din saidai ganin bawani abu zai kara ba yasa ta dauki mini face micro fiber towel ta goge face dinta sannan ta nufi closet ta cire kayan jikinta ta saka wata purple abaya akai ta zura fur room shoes dinta ta fice tana tafiya a hankali jikinta duk ya mace.
Kasa ta sauka zuwa main palour bata samu kowa ba. Komawa tayi palourn baki nan ta samu ridwan a ciki. Infact ba ridwan kadai ba ridwan tareda wannan kuyangar datazo kiranta zaune kan cinyarsa ya matse ta sai kokarin kwace kanta takeyi saidai karfi ba dayaba ko kyakyawan motsi bata iyawa, face dinta chabe da hawaye tana kuka tana jujjuya kai.
Sakin baki yazrin tayi kamar wanda tay suman tsaye, bata taba tsanmanin zataga irin wannan alfashar a gabanta ba, kenan dama abunda ake fada akan Ridwan kenan gaskiya ne? Neman mata yakeyi ko sunaso ko basaso? Lallai kuwa bazai gwada wannan iskancin a gabantaba.
Da sauri ta nufa inda suke tasa hannu da niyyar finciko kuyangar saidai dayake jikinta ba karfi kwata kwata sai batasamu ta iya jawota ba saima kusan fada musu datayi. Cikeda bacin rai tace “ Ridwan are you okey? Wannan wani irin zalunci ne da cin fuska? Ka saketa yanzunnan kafin na tara maka mutane”.
Wani shu’umin dariya ya saki yana karkata kanshi gefe daya kamar wani psychopath idanunshi babu alaman imani a ciki ya daga hannu ya buga ma yarinyar a wuyanta. Ihu tayi kafin ta fadi kasa sumammiya. Da wani irin gudu Yazrin ta karaso inda take ta tsugunna a gefenta tana girgizata. Ganin shiru alaman suman gaske ne yasa ta dago face dinta kawai taga ruwa akan table na gefensu dasu drinks.
Ruwan ta dauka sannan ta bude ta zuba mata hannunta narawa dayasa ruwan ya kwaro sosai a face dinta. Ihu tayi tanajan nunfashi tareda mikewa zaune. Take kuma ta fara tari alaman ta shake dan ruwan sosai ya kwarara, so tanajan nunfashin ya shige mata.
Buga bayanta yazrin tayi tafin tabata ragowar ruwan tasha. Ansa tayi tana kurbewa kamar kuka wanda aka tsikara kawai ta mike tsaye a razane tana kallon Ridwan daya nuna baimasa meke faruwa ba idanunshi nakan yazrin kamar zai chinyeta.
Da gudu Kuyangar ta fice daga dakin while Yazrin tabita da kallo kafin ta mike daga tsugunno datayi ta maida idanunta kan Ridwan. Jin zuciyanta na zafi ganin wai wannan mutumin akeso a aura mata yasa taji wasu hawaye na taruwa a idanunta saidai tay saurin juyarda face dinta daga kanshi karma yaga rauninta.
Kofa ta nufa dan bataga anfanin zamanta gurin wannan mara imanin ba, muryan shine ya isko kunninta babu alaman wasa yace “ Ke karfa kiga ina lallabaki kizata zaki rinka mun abunda kikaga dama, ba wanda kemun abunda kikemun na kyakeshi amma kema naga kinason na nuna miki mummunan side dina dabaki taba ganiba, zakuma kiyi nadaman ganinshi, karkiga a gidanku kike duk inda kike zan iyamiki abunda naga dama babu wanda zaice mun meyasa. Yarinya mara galihu ma kamarki”.
Tasan dacewa da gaske yakeyi, takumasan babu abunda za’ayi idan ta batamai, bakuma ta neman abunda zai bata mata lokaci koya zama silar dazaisa takasa bayyanarda wannan abunda ke littafin. Dan haka kawai ta juyo ta dawo face dinta ba yabo ba fallasa ta zauna a kujerar dake gefenshi.
Alama yamata akan ta dawo side dinshi ta zauna sai tayi kamar batasan yanayi bah ta dauko wayarta tafara latsawa. Hannunshi yasako tareda daurashi kan cinyarta. Kallon hannun ta tsaya yi na wasu yan seconds kafin ta ture hannun nashi tana kara matsawa gefe yanda hannunshi bazai kai inda take ba. Aranta addu’a takeyi Allah yasa ya rabu da ita, dan indai yacigaba toh batasan mezata iyamai bah. Ta tsani a taba ta bare shi data tsana, soyake yafara iskancin shi da ita, abunda bazata taba bariba kuwa komai zaiyi saidai yayi.
Murmushin gefen baki yayi kafin ya maida hannunshi kan hannun kujerar dayake kai ya dauko wayarshi da dayen yafara daddanawa. Sun dade a haka kowa nacikin wayarshi kafin ya tashi batareda yakulata ba koyayi mata sallama ya fice daga palorn.
Ajiyar zuciya ta sauke tana godewa Allah atleast ta tsira daga hannunshi. Mikewa tayi jiki bakwari tana tuna abunda yayi ma wannan kuyangar. Itakuma irin nata kaddarar kenan, auren mutun irin wannan. Tunani tafara inkuma bata iya solving littafin bafa? Hakanan zata hakura ta aureshi? Da sauri kuma ta girgiza kanta tana fadin Allahumma ajirni fi musibati, da tunanin kadai ya isa ya tsoratata bare kuma yafaru a gaske.
Tana fita sukaci karo da wata kuyanga, baya tayi tana kallonta daga sama dayake tafita tsawo tana dan hada rai, yau kwata kwata mood dinta a bace yake dan haka a gatsale tace “ Ke baki kallon gabanki ne?”. Zubewa kuyangar tayi a kasa tafara bata hakuri kamar anmata wahayin mutuwa. Dan babu dadi yazrin taji yasa tace mata ta mike sannan ta cigaba da tafiyarta zata hau elevator.
Da sauri kuyangar takara zuwa inda take a hanzarce tace fadin “ Princess yazrin, Sultana na kiranki a main palour”. Dan hada rai yazrin tayi aranta tana tunanin mekuma yasa ake kiranta? Juyowa tayi sannan tace “ Mezanyi ake kirana”.
Dan shiru tayi sannan muryanta nadan rawa idanunta a kasa tace “ Bansani ba kawai dai ance na kiraki zakiyi shaida ma Zeynab ne”.
Da ok dan tama gano menene. Kenan karar Ridwan Wannan kuyangar takei, dukda batasan waye zeynab dinba amma waye zatayi ma shaida. Juyawa tayi ta nufa main palour ta shiga zazzaund ta samu Mamah da Daddy dakuma Azlan sai Kuyangar a tsugunne kan carpet kanta a kasa.
Karasawa ciki tayi tanajin wani iri aranta ganin daddy. Abunda yayi mata kawai take tunawa saidai bata nuna ba ta karasa dan nesa dashi tace gata.
Guri ya nuna mata ta zauna a kujera dake dan nesa dasu tana ajiye wayarta tareda maida kallonta kan kuyangar. Wani tunani ne ya fado mata rai, bakomai bane sai wannan lettern da ake aiko mata. Inbata manta ba abu na karshe da yace mata tayi shine kada tayi shaida. Ba’ace ga abunda zata shaida ba so zaizama wannan ne kenan?.
Wani nunfashi taja tana daga kanta sama. Lallai akwai gurmi. Tama rasa tunanin mezatayi. Shin tabi na lettern ne ta fasa yin shaidan? Kokuma tayi? Amma kuma idan tayi batasan me zasuyi mata ba, zasu iya sawa daddy ya gane ta shiga office dinshi. Idan ko har hakan ta kasance toh lallai kashinta ya bushe, saidai kuma idan batayi shaidar ba lallai Kuyangar nan bazata yafe mata ba, zakuma ta shiga hakkinta.
Daddy ne ya gyara murya dasaida tsigan jikinta ya tashi. Dago da kallonta tayi gareshi cikin no nonsense voice yace “ Yazrin wannan kuyangar takawo korafi akan Ridwan cewa yaci zarafinta, sannan kinga hakan zakuma kiyi mata shaida.
Jitayi kanta ya kulle tama rasa mezatayi. Ganin idanun kowa akanta gakuma idon wannan kuyangar shima akanta tanajin kallon datake yimata.
( mekuke ganin yazrin zatayi? Shin zata bi son zuciyanta kokuma zata yi shaidar?).