KOWA YAƘI JI

Chapter 7

by @mamananalbarkace777

_PAGE7️⃣_*
Gajiya nayi da magiya da roƙon da ya ke min, hakan yasa na ajiye Na'im na tashi bance masa komai ba na fara aikin gyaran farlon,
Ya zauna yana bina da kallo a hankali yana wasa da Umar,

Ba'a ɗauki lokaci ba na gyara na gyare ko'ina har ɗakunan tsaf ina yi ina tuna abubuwa da yawa,
Nasa a raina zan zauna Anan ɗin kamar yadda ya roƙe ni amma bana jin zan iya sakin jikina nayi rayuwa kamar da,
Bayan na kammala na shiga bedroom ɗina Dana zauna a bakin gadon sai da na fashe da kuka saboda yadda zuciyata ta kasa jurewa,
Nan da nan wani zazzaɓi ya lullu'beni na kwanta tare da lullu'ba ina rawar sanyi dama ga yunwa dan yau gaba ɗaya ban sa wani abu a bakina ba,

A sanyaye ya shigo ɗakin hannun sa riƙe da filet ya ƙaraso bakin gadon idon shi akanta ganin yadda take numfarfashi da kuma yadda idanun ta  suka kumbura suka ƙara fitowa,
Akan dirowar da ke gefen gadon  ya ajiye  filet ɗin da ke hannun sa,
ya zauna a bakin gadon yana shaƙar dadɗan ƙamshin da ke tashi a ɗakin hakan ya tuna masa da abubuwa da yawa,
 ya juyo ya kai kallon shi ga Salim da ke gefe a zaune cikin  bada Umarni yace 
"Salim  tashi kaje farlo ka ɗauki abincin kaida Umar, ina Umar ɗin na yaje naga ban ganshi ba?"

" Umar yana baya yana wasa, bari na kira shi"
Ya nufi ƙofar tare da fita.

Matsowa yayi sosai kusa da Salmah ya zuba  mata ido yana kallon ta ganin yadda ta rame ta fige, Salma da take a direnta ko ina cas cas amma duk ta ƙare haka, kallon shi ya kai ga wuyanta ganin yadda rigar jikin ta ta zame wuyan ya mata yawa sosai  duk tayi wani irin ba'ki idanun sun ƙara fitowa  tubarkallah dama can akwai idanun,
In ba wanda ya mata farin sani bama babu mai cewa Salmah ce Salmah yar gayu, ga iya ɗaukar wanka.

Baisan lokacin da yaji wata ƙwalla na ƙoƙarin zuba mai ba, da sauri ya ɗauke kanshi yasa hannun sa ya ɗauke kwallar.

Nikam ganin yazo ya sani gaba kawai yana kallo na ina ganin yadda tausayi na da so ke lullu'be da kallon,  tausayin kanmu ya kama ni na lumshe idanuna ina jin yadda idanun sa ke yawo a jikina.

Sai dai ina tsoron abin da zai je ya dawo,
Bana tunanin inhar Maryam ta dawo zamu zauna lafiya zata bari wannan yanayin yayi tasiri, babban tsoro na bansan me take shirya wa ba, amma nasa a raina nima zan tashi na mik'e wajen addu'a akan Allah ya min tsari da ita da yarana.

Muyar shi da naji ita tasa na buɗe ido na,
"Ki tashi ki ci abincin kin ji ko za ki kiji ƙarfin jikin ki"

Ban amsa ba sai ɗagowa da nayi na watsa masa idanuna da suka rine ni kaɗai nasan halin da zuciyata da gangar jikina ke ciki,

"Kici abinci yace tare da ɗauko abincin ya jawo dashi gadon ya zauna gabana sosai tare da buɗe  filet ɗin da ya kawo ya turo shi gabana.

Ina daga kwancen wani k'amshin ya ratsa hancina hakan yasa na ɗago na kalli filet ɗin taliya ce jalof da taji kayan haɗi da bushashshen kifi  nasan shine ya dafa dan daga ganin dahuwar irin tashi ce, dan Haidar lokacin muna tare babu abinda baya tayani dan haka indai ɓangaren girki ne ya ƙware sosai,  Wani lokacin ma da kanshi in yana gida yakan ce na zauna yau shine zai mana abinci lokacin haka zan barshi nayi komawata na zauna ba tare da damuwa ba, kuma ko a gaban waye bana damuwa na sa shi yamin abu shima baya damuwa da idon mutane sam haka zai zage yamin.

Ji nayi wasu hawaye na tahowa tuna abubuwa da yawa da nayi nasan harda halinnan nawa a cikin abubuwan da suka jazamin shiga wannan rayuwar da nake ciki,  rashin damuwa ta da sa shi yamin abinda bai kamata ace a gaban kowa yana yi ba ,

Cikin kwantar da muryar tare da  tausayawa   ganin ina share hawaye yace 
"Kiyi haƙuri Salma nasan na cutar dake kiyi haƙuri kinji ga abincinnan ki daure kici pls"

Bana jin zan iya sa abincin nan a bakina sam dan a halin dana ke ciki ko yunwar ma bana ji  na yarda yunwa ma guri take samu.

Babu yadda baiyi dani ba naci abincin amma sam na ƙi ci har shayi yaje ya haɗo min da kanshi ya mik'o min kofin,
Ganin in ban shaba zan cutar da kaina ga yaro na tsotso yasa na tashi zaune bisa dole ba jingina da jikin gadon ina sauke numfashi,

Kallona ya ke kamar zai haɗe jikina da nashi ya ƙara matsowa cikin natsuwa ya kawo kofin wajen bakina da nufin ya bani, na kauda kai tare da miƙa hannu na amsa na shiga sha da kaina,
Ina jin lokacin daya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya ya ɗan ja baya kaɗan ya gyara zaman shi sosai.

Sai gashi na shanye shayin tas nan da nan wata zufa ta fara karyomin, bai barni ba kuma sai da ya lalla'ba Ni na ɗan ci taliyar, tukun ya ɗauke filet ɗin ya fice ya dawo hannun sa ɗauke da magunguna
Banyi mamaki ba dan nasan dama baya rabo dasu a ajiye,
Da kanshi ya ɓalla min maganin nasha ina ƙoƙarin kwantawa ya hanani ya wuce toilet ya haɗa min ruwan wanka mai ɗumi sai da yaga na shiga wankan tukun ya barni.

Ina fitowa na tarda baya ɗakin sai naga doguwar rigar abaya sabuwa dal da duk abinda zan buƙata a gefen gadon,
Jin wani abu nayi na yawo a zuciyata na rasa me ya kamata nayi farin ciki ko akasin,
Goge jikina nayi nasa kayan kawai ina jin jikina duk babu ƙwari,
Na koma kan gadon ba kwanta tare da lullu'be jikina da lallausan bargon dake kan gadon ina sauke wata sassanyar ajiyar zuciya nan da nan wani na nannauyan barci yayi awon gaba dani dama ba sallah zanyi ba.

*****************""*""

Cikin jin haushin  Ladidi ta shigo ta dangwar da ledar maganin a gaban ta tare da galla mata wata uwar harara  taja dogon tsaki ta fice.

Maryam dake danne dannen ta a waya daga kwance ta ɗan ɗago ta kalle ta bayan ta juya itama tsakin taja tare da yunk'urawa ta mik'e  zaune tana magana ita kaɗai tare da wani shige. Murmushi tace
"Shegiya katifa ce dai anbani kuma babu wata ƙatuwar da zata takuramin daga ke har Mamar ɗan kwana ɗayan da zanyi nayi gaba akewa baƙin ciki to Wallahi ba'a isa ba.

Abinda ya faru bayan Maryam tace bazata shiga ɗayan ɗakin ba, ita ma ladidi  tace wallahi bazata yarda Maryam ta kwanta a katifar Mama ba sai dai ta kwanta ɗakin da aka ce tunda dai bawani ya hanata zaman gidan mijinta ba, faɗa suka yi sosai itama Maryam ɗin ta shiga yiwa Ladidin gori akan gwara ita tayi auran ma ita da bata taɓa yiba fa sai yawon ta zubar da take, nan suka kaure da faɗa dukan su kowacce naji da ƙarfi.

Mama tana ɗaki duk tana jinsu bata yi magana ba sai da taga suna ƙoƙarin fara t dambe tsakanin su da Allah,  tukun ta fito gudun karsu tara musu mak'ota dan inda sabo sun saba kafin Maryam ɗin tayi aure basa damuwa su daku a gaban kowa.

Da ƙyar ta rabasu tana faɗin "Ko kunya bakwa ji daga haɗuwa zaku raba hali" taja hannun Ladidin suka shiga ɗaki Allah yasan me faɗa mata   sai gashi Ladidin da kanta ta ja akwatin Maryam ɗin ta shigar ɗakin tasa tsintsiya ta tattara ɗakin daya yi kaca'kaca dama ba wata tsiya bace a ɗakin, daga yar yololuwar katifar dake yashe sai buhun kayan su da  abubuwan da baza'a rasa ba.
Bayan nan  Mamar ta kunto kuɗi ta bawa Ladidin tace ta siyowa  Maryam ɗin magani cikin jin haushi take yin komai,

  Taɓe baki tayi ta janyo ledar maganin ta duba taga Paracetamol ne da wani daban amma ai ba'a shan magani sai anci abinci,  ita sai lokacin ma taji tana jin yunwa dan yau gaba ɗaya ko karyawa bata yi ba dan dama sakwarar da tace Salma ta mata ne tayi niya taci to kuma sai wannan abun takaicin ya faru.

Cikin tunanin abinda zata ci take tana ƙara jin baƙin cikin rashin samun cin sakwarar nan gashi yanzu dole dai abinda bata so zata nema taci, to mema ake sai dawa a unguwar nan banda su shinkafa da wake da mai da yaji dangin taliya y'ar murji sai kuma su alale, abubuwan da bata so sam tana ganin ta wuce da ajinsu da ace ma k'alau take da sai ta shiga cikin gari tayo takeaway ta samu taci, amma yanzu yadda take jin jikin ta bazata iya fita ko ina ba.

Shigowar mama da ke ɗauke da robar data tankad'e garin tuwon daran da za tai shi yasa ta ɗagowa.
 a yatsine tace
"Wai Mama mai zan samu inci ne? yunwa nake ji kinsan yau duka ban karya ba gashi ina son shan magani"

"To Allah yasa a samu abincin da zafi sai ki bawa Ladidi ta siyo miki"

"Wai kina nufin abincin saidawa zanci? Babu abinci a gidan nan"

"Ai kwa dai shid'in ne dai za a samu sai kuma awara nasan bilkisu ana la'asar take fitowa suya in zaki jira ta to"

"Cab Allah ya kiyaye ni da wani cin awara"
Ta faɗa tare da jefawa Mamar harara.

"To sai kije gidan Binta mai shinkafa da wake ko zaki samu dan gaskiya da wuri take ƙarewa dan ta iya daka yaji mai daɗi wani lokacin ma ana azahar ta ƙarewa"

"Haba Mama wane shinkafa da wake ina maganar ko karyawa banyi ba kina wani batun shinkafa da wake"

"Tsaki taja to uwar kinibibi nan dai ba gidan mijin ki bane sai kiyi haƙuri da duk abinda kika samu kici"

"In bani da yadda zanyi ko?" ta cewa Mamar cikin gatse.

Banza tayi da ita ta fice ta barta.

K'wafa Maryam ɗin tayi tare da tashi ta lalla'ba dan har yanzu inda Haidar ya ture ta ta bige wajen ƙugun ta ciwo yake mata,  ta fita ƙofar gida cikin katari ta samu wani yaro ta bashi kuɗi tace ya siyo mata kayan shayi  da biredi, haka yaje ya samu madara da sugar da lipton biredin kuma sai yan biyu irin  ƙananan nan wai duk unguwar basu da babban biredi.

Tsaki taja ta amsa  bisa dole tana zage'zage tana ƙara tsinewa Salma duk a sanadiyyar ta haka ta faru, ta ƙara cin alwashin inhar ta koma sai ta bautar da ita fiye da da sai ta biya bashin shekara ɗaya na wahalar da tayi sanadiyyar sata shan wahalar da tayi na kwana ɗaya.

Ruwan zafi ta d'iba a tsantsane dan tukunyar da Mamar ta ɗora tun wadda tayi tuwon jiya ce ba a wanke ba, sai da zata ɗora tuwon  yau ko wankuwa bata yi ba duk k'anzo haka ta kamfaci ruwan bisa dole ta jefa lipton ta zuba Sugar da madarar.

 Tana sha tana jan tsaki cikin bak'in ciki me ake da zaman gida yanzu da canne sai ta haɗa shayinta mai rai da lafiya kakkaura gashi yaji kayan k'amshi dan Salma ta iya dahuwar shayi, ta samu lafiyayyen biredin ta da k'wanta ga soyayyen dankali, amma wai ita ce yau take cin biredi zallah, haka dai ta gama ta kora maganin ta koma gefe ta kwanta saboda yadda kanta ke mata ciwo babu batun Sallah kwata kwata.

Sai kusan magriba Mama ta gama tuwon, ta shigo ɗakin alamun wanka tayi ta nufi buhun kayanta tana son shiryawa.

Maryam harta buɗe baki za ta yi magana sai ta fasa, ganin abinda ya fad'o daidai lokacin da Mamar ta kunce zanin ta dan tasa bra,
abin da taga ya fad'o daga zanin Mamar ne ya katse mata tambayar ta da take son yi akan ina Mamar zata, zaro ido tana kallon abun
Cikin mamaki  ta d'ago kanta ta kai kallo ga Mamar dake hidimar ta sai ta lura bata ma san ta yarda ba.

Cikin rawar jiki tasa hannu ta d'auke layar da ta gani, zuciyar ta na wani irin bugu wani irin tsoro na shigar ta da kuma tunani ka daban daban ganin irin layar dake cikin tukunyar  k'asan gadon ta, yaya akai  Mama keda irin ta  to ko dai itama wani zata sa ayiwa aiki?.

Sam bama ta kawowa ranta wai tata bace amma ta d'auke ta tura k'asan katifar da take kai tare da juyawa ta cigaba da abinda take,  koma dai mene ne ita bai dame taba inma layar mece ba zata bayar ba, haba ita fa Mama bata san ta girma ba sam yanzu haka wani bazawarin  nata take son ramkewa shi yasa ta amso taja tsaki tare da kwantawa.

Allah ya sani haushi abin ke bata yadda kamar Mama dake da shekaru kusan hamsin, budurwar zuciya da son duniya yasa ta gaza gane ta girmi duk wani abu da take, dan Mama babu ruwan ta tsayawa take waje zance da zawarawan ta,  dan sun rabu da mijinta to gidan dama nata ne shine ya bar mata gidan sai take cin karen ta babu babbaka saka ƙananun kaya  ba komai bane gareta,  ita komai gani take bata wuce da yin sa ba.

Tana daga kwance tana kallon ikon Allah, har Mamar ta  kammala shiryawa cikin wasu riga da sket na wani leshi da ɗinkin ya matuk'ar matseta K'irjin nan an d'ago su sama sun fito ta saman rigar sai nishi take, ta d'auki wani k'aramin gyale ta yafa tare da bulbula turare.

Cikin takaicinta Maryam data kasa shiru tace 
"Wai ke Mama ina zaki kike shiri haka?"

Ba tare da ta jiyo ba tace "Ina da bak'o ne"
 tare da nufar hanyar waje.

Da sauri Maryam ta mik'e ta sha gabanta tace
" Haba Mama wai ke baki san kin girma bane ki kalli jikin ki fa haka zaki fita?"

Cikin ɓacin rai ganin tana neman ɓata  mata lokaci tace
"Maryam bani hanya na wuce kafin ranki ya ɓaci"

Cikin harara Maryam tace
"Allah ya kyauta dai ya  kamata in mutum ya girma yasan ya girma" taja tsaki tare da matsawa ta bata hanya.


Bayan fitar Mama Ladidi  ta shigo rataye da jaka ko gyale babu, duk da bawani kayan arzik'i bane jikin ta, ta jefar da jakar hannun ta tare da yiwa Maryam kallon banza ta koma gefen tabarmar dake yashe a ɗakin ta zauna tana y'an waƙoƙin ta  ta buɗe jakar ta ta fito da wata leda.

Duk abinda take Maryam na kallon ta k'amshin lafiyayyen naman da yaji gashi ne ya buge ta ta k'ara bud'e k'ofofin hanci tana shak'a tare da ɗan d'ago kanta ta lek'a ledar.

Ladidi kam bama tasan tana yi ba ta fara aikawa  da cikin ta naman tana korawa da lemon ta me sanyi shima tare ta shigo dashi da naman.

Yawun Maryam tsinkewa kawai yake ji take kamar ta fusga taci dan wani irin kwad'ayi taji yana taso mata kamar bata taɓa cin nama ba sam a rayuwar ta take ji,
Can dai ta kasa daurewa ta tashi zaune wai ko Ladidin zata ganta ta bata koda tsoka biyu ce amma ina bama tasan tana yi ba,
Sai da ta cinye tas ta nad'e ledar ta mik'e ta nufi waje dan yarwa ta na waƙoƙin ta hankalin ta kwance.

Tsaki Maryam  taja lokacin da Ladidin ta dawo tana binta da wani irin kallo cike da jin haushi.

Wata uwar gyatsa Ladidi taja tare da hamma, ta zauna ta jingina da bango ta zari tsinke sakace ta shiga sakace hak'oran ta.

Kasa daurewa Maryam tayi tace
"Amma wallahi Ladidi yaune na tabbatar baki da mutumci da Imani yanzu ina kallo kika shigo da naman nan kika cinye a gaba na babu bismillah ai ido guba ne koda bazan ciba kya iya min bismillah ki ji ko zanci"

Dariya Ladidin ta fashe da ita dama tasan za'a rina tasan zai yi wuya Maryam ta kasa magana,  tasan halinta sarai da son nama ta kuma san bata jurewa in ta gan shi,  indai akace gashashshen nama ne tofa ba'a magana akan shi zata iya komai, shiyasa da gayya koda suka fita da Alhaji Bashir bayan sun  gama shan firar sa ƙofar gida, yace suje ya mata  y'ar siyayya,  suna hanyar dawowa gida bayan ta siyo mata kayan maƙulashe ya  tambaye ta kaza zai sai mata ko Nama ta zaɓi ɗaya,   tace ya sai mata gashashshen nama kodan ta bawa Maryam haushi dan tasan dai a darannan babu inda zata fita ta nemo nama irin shi, ita fa dawowar Maryam  kamar lokacin ɗaukar fansar abinda Maryam  ta mata ne yazo, dan bazata taɓa mantawa ba da irin cin kashin data mata lokacin da taje gidan ta ba dan tak'amar tana auran me kuɗi.

Bayan auran  Maryam ne da sati biyu  ta shirya bisa Umarnin Mama data ce taje taga Maryam ɗin tana lafiya.
Ta shirya badan taso ba ta tafi gidan Maryam ɗin, abin mamaki koda taje yadda ta tare ta a wulak'ance ya matuk'ar bata Mamaki da yadda ta share ta ta barta a falor zaune ta shige wajen mijin ta,
Tafi awa biyu zaune tukun can sai gata ta fito ta kalle ta a wulak'ance tana yatsina fuska tace
 "Wai dama baki tafi ba har yanzu?"

Tambayar ta ɓatawa Ladidi rai amma sai ta danne tace 
"Ban tafi ba"

"Ok to me kike jira?"
Tace tana mai zama kujerar dake kusa da ita tana wani yatsine fuskarta.

Taji haushi iya haushi to amma ita dake jin yunwa dole ta daure koda ɗan wani abunne tasamu tasa a cikin ta, duk da bata kasance mai kwad'ayi ba amma ganin tazo gidan y'ar uwar ta, tana tunanin tunda  Maryam ɗin tayi aure yanzu koda da suke rigima ai yanzu zata watsar da komai, sannan ga dad'ewar da suka yi basu ga juna ba,
 
Bayan ko ruwa bata sha ba tunda tazo, ai koda taci abinci tazo ai yaci ace taji yunwa dan lokacin ita bawani fita ta cika ba ga rayuwar sai a hankali ko k'wandala bata da ita a jikin ta tana ma saran in zata koma Maryam ta bata koda kuɗin mashin ne,
Cikin dauriya tace  
"Ban tafi ba Aunty Maryam ke nake jira ki zaki bada wani sak'o akaiwa  Mama"

"Au ni har wani sak'o zan baki ki kaiwa Mama bayan da zaki zo bata baki komai ki kawo min ba, to ai saiki tashi ki tafi ki bani waje mijina zai fito bana son ya fito ya ganki, tsakani da Allah gwara ki tattara ki tafi kema in kinyi zuciya ki fito da Miji kiyi aure, kinga ke sai ki dinga bawa Mamar sak'o ana kai mata"
Taja tsaki tana bin Ladidin da kallon banza tace 
"Gaki nan dai mace har mace amma kin jabge a gida kin ƙi fito da miji"

Maganar ta ce ta harzuk'a ladidin ta mik'e ta kalle ta ta girgiza kai
tace
 "Saboda na zo gidan ki ne ai kika min haka ko? to ke da kike cemin na girma banyi aure ba ke yaushe kika yi Auran? ina ce ko wata baki rufa ba in girma ne kin girmemin nesa ba kusa ba gwara ni auran ne banyi ba sannan ban zubda mutumci na a titi ba har yanzu da mutumci na a tare sani"

Fad'a ne yaso kacamewa tsakanin su, ganin ladidin na neman tona mata asiri gudun kar Haidar yaji irin rayuwar da tayi a baya yasa ta fatattaketa ta tafi.

Haka ta da'bo tun daga gidan Maryam d'in a ƙafa har gida,
bazata taɓa mantawa da wannan ranar ba a rayuwar ta kuma daga ranar bata ƙara zuwa gidan taba sai dai in ita tazo wajen Mama su haɗu, shima yana wuya ka ganta sai dai Mamar dake zuwa wajen ta dan tunda tayi auren take ganin kanta tafi ƙarfin gidan, abin na k'onawa Ladidi rai dan zubda mutumcin ta da Mamar take na zuwa wajen Maryam ɗin.

************************

Kamar yadda suka tsara gari na wayewa suka shirya da Maryam da Mama dan zuwa wajen Boka gamji kowacce da tata buk'atar a zuciyar ta.

Sai dai me bayan sun fita waje sun shiga Mota Mama ta laluba layar da ta soka a bra taji wayam,   nan fa ta tuna tayi wanka jiya ta canja kaya, a rikice take laluben jakarta.

Maryam da harta tada motar ganin yadda Mama ke neme'nema ta zuba mata ido duk da kuwa tasan abinda take nema sai ta jefa mata tambaya 
"Wai me kike nema ne Mama?"

"Kinga tsaya ni in shiga gida na fito ina zuwa" tace tare da 'balle murfin motar ta fita da sauri tayi cikin gida.

Maida kanta tayi ta jingina da kujerar motar tana mai cewa kya ma gaji ki dawo mu tafi ni zaki 'batawa lokaci ai gwara dana d'auke, haka kawai ina fama da matsalata ba a gama maganin taba ki zo da taki yau dai da iya tawa gamji zaiji"

Mama kam ganin bata ga layar ba hankalinta yayi matuƙar tashi,
Addu'a take tayi a zuciyar ta Allah yasa wani bai gani ba cikin su Maryam ko Ladidi, dan in Maryam ta gani asirin ta ya gama tonuwa, batasan mai zai faru ba  in  kuwa Ladidi ta gani tasan babu makawa bazata bata ba, dan ita a rayuwar ta ta tsani harkar biye'biyen bokayen da suke shiyasa babu yadda ba tayi da ita ba ta yarda su je wajen Boka Gamji a duba ta a bata maganin  da zata samu miji tayi aure amma tak'i yarda, a cewar ta aure lokacine in lokacin yinta yayi za ta yi ita dai a barta da shigar banza da kuma y'an kule'_kulen samarinta, a samu na siyan kayan kwalliya da d'an abinda za'asawa baki amma bata yarda tayi mai gaba daya ba sam.

Kasa daurewa tayi ta tarda Ladidi tana tattara ɗakin za tayi shara, nan ta dakatar da ita ta wuce ta a haukace ta shiga birkita ɗakin tana neman layar amma sama ko ƙasa bata gani b,  ganin haka yasa ta juyo da niyar ta tambayi ladidin, sai kuma ta fasa dan taya zata ce mata laya take nema,
Dole ta hak'ura ta fito ta shiga motar zufa na yanko mata dan Layar nan ita ce babban abinda ta dogara da ita wanda zaiyi sanadiyyar cikar burin ta,  tashin hankali iya tashin hankali ta shige shi.

Maryam ganin yadda take zufa yasa tace
 "Wai lafiya me kike nema ne har haka? Mama da kike had'a zufa" 

"Babu komai"
tace mata tare da cewa ki sauke ni gidan Hajiya  Hajara  tukun ke in yaso ki wuce wajen gamjin inada wata matsala in na saita ta zan biyo ki a baya"

"Kamar yaya na sauke ki gidan Hajiya Hajara?"
Cewar  Maryam ɗin. 

Hajiya Hajara wata k'awar Mama ce irin sosai da sosai ɗin nan, duk wasu manak'isa da tuggu zan iya cewa wajen ta Mama ta koya dan ita ɗin ba baya bace tana gidan ta ita kaɗai ne, duk da shekarun ta Amma mijin da take aure yaro ne k'arami baifi shekara 30 ba,  juya shi take son ranta tana kashe mishi kuɗi  dan tsohon mijinta da ya rasu yana da dukiya sosai duk da cewar bata haihu dashi ba amma ta samu gado mai yawa, sannan kuma ta satar masa dukiya ba kaɗan ba tun yana raye, saboda haka cin duniyar ta take hankali kwance bata da wata matsala.

Ganin Maryam bata da niyar Kaita yasa tace
"Kinga dan Allah muje ki sauke ni in yaso sai ki jirani in kammala sai mu tafin na yarda" 

Cikin dariyar mutunta Maryam ɗin ta daki sitiyarin motar tace
"Ahto yanzu naji magana amma tsakani da Allah Mama kina son ɓata min nawa lokacin, nifa nagaji da zaman gidan nan daga jiya zuwa yau duk jikina k'aik'ayi ya ke min saboda cizon wannan jarababben sauron gidan naku"

Suna tafiya tana mita, haka suka kama hanya ta sauke ta gidan Hajiya Hajarar tace
"Minti 10 na baki gaskiya ki fito"
tare da  kwantar da kujerar motar ta kwanta don ta jira ta.

Cikin murmushi jin dad'i tace
"Yanzu zan fito kin ji"

********

Ladidi kam bayan fitar Mama, ganin yadda mamar ta hargitsa ɗakin yasa ta shiga gyarashi sosai garin sharanne ta ɗaga k'asan katifar da mama ta birkita garin nema, sai taga wata k'atuwar laya tsaki taja tare dasa tsintsiya ta sharota ta kaita zuba a masai, tana mitar halin Mamar na shegen asirin tsiya ko wa tayi wa oho,
tana gama gyaran tayi kwanciyar ta hankali kwance.

********

Mama na shiga ta  tarda Hajiya Hajara a farlo zaune y'ar aikin ta na goge goge,
A rikice ta ƙarasa  ta nufi Hajiya Hajarar da ke hakimce a kujera, ko gaisawa basu gama yi ba ta shiga cewa
 "Ƙawata akwai matsala taso taso muje ciki dan Allah"

"Haba ke kuwa ki zauna mana muyi magana a nutse" ta kalli Yar aikin ta tace 
"Ke Bilki wuce ki bamu waje" 

"Kinga ki taso Maryam na cikin mota tana jirana ki taso mu je daga ciki zaifi sirri"

Wani kallo ta watsa mata tace
 "Wanne irin mu je ciki bayan mijina na nan,  kuma kinsan bana wasa da hakan ki zauna muyi maganar a nan wa zai zo? daga Ni sai ke"

Badan ta so ba ta gyara zama ta shiga rattabo mata bayani dalla dalla.


Maryam da ta gaji duba agogon hannun ta kawai take, ganin har Mintuna goma sha biyar sun shud'e bata fito ba yasa ta 'balle murfin motar, ta ja tsaki tana mitar dad'ewar da Mamar tayi, ta nufi cikin gidan dan ta mata magana ta fito su tafi.

Tana shirin sa k'afar ta farlon ta dakata,
Sakamakon abinda kunnuwan ta suka jyi mata, wata uwar zufa ce ta shiga  karyo mata jikinta na wata iriyar rawa ta ƙara ƙasa kunnen ta.

*_😍MANAN ƊAN ALBARKA CE😍✍️✍️_*