KOWA YAƘI JI

Chapter 8

by @mamananalbarkace777

_PAGE 8️⃣_*

Har suka Isa Maryam na  ƙoƙari wajen ganin ta shanye abinda ke damun ta kamar yadda suka Saba sun rattabo bayanai dallah dallah,
 Sai dai abin da ya bawa Mama mamaki Jin da tayi Maryam Tace tana son magana da gamji ita kaɗai Mama ta d'an Basu waje.

Cikin mamaki Mama take kallon Maryam kamar zata ce wani Abu, sai maganar ta ta mak'ale Jin da tayi Gamji ya daka mata tsawa akan ta basu waje,
Kamar zata yi Kuka haka ta tashi tana kallon Maryam zuciyar ta na mata saƙe saƙe  har ta kai bakin bukkar tana tambayar kanta,
shin me Maryam take nufi data fita,?
bata da mai bata amsa,
Sai dai tun da taji gamji ya daka mata tsawa akan ta fita tsoro ya kama ta, bata mantawa akwai lokacin daya taɓa mata wata magana akan Maryam tana tsoron abinda take zargi ya tabba, tana zaune ta sak'a ta kwance tuna  Maryam bazata ta a yarda ba yasa hankalin ta yad'an kwanta,
saboda tsananin tsanar da ta yiwa Gamji da k'yamar shi da take,
 Kuma shima ya sani hakan na cikin dalilin da yasa yasha alwashi akan ta kodan cika dad'ad'd'an burin shi na shekara da shekaru,

Ganin fitowar Maryam  da Mama tayi tana gyara zaman wuyan rigarta ba ƙaramin firgita ta yayi ba, ta gwalalo Ido tana binta da kallo daga sama har ƙasa  ita ba yarinya bace tabbas tasan Mai afkuwa ta afku,
Maganar da Maryam tayi ce ta katse Mata tunanin ta tace
 "Muje ko Mama"

"Wanne irin mu je Maryam me kika yi?"
Cewar Mama tana tsatstsareta da ido.

Ɗauke kai Maryam tayi cikin son ta danni zuciyarta tace
"Nifa kinga Mama in zaki taho ki taho, ko nayi tafiya tane kina da yadda za ki yi ki dawo gida?"

Mama  baƙin ciki da takaici ya kamata na rashin samun abubuwa da yawa, har ta buɗe baki za tayi magana tuna yamma tayi kuma tasan Maryam zata aikata abinda tace yasa ta wuce kawai bata ce komai ba.

Har suka ɗauki hanya bakin Mama ya kasa cewa uffan, in ba hancin  ta ne ke mata  sai ta ji kamar  wari Maryam take,tun tana daurewa sai taji abin kamar ƙaruwa ya ke,
Can ta kasa riƙe abinda ke ranta tace 
"Wai Maryam me Kika faɗawa  Gamji ne da harni kaina ba zaki iya faɗa a gaba na ba?"

Sai da tayi kamar ba zata kulata ba can dai tace
"Babu komai kawai na jaddada masa buƙata ta ne dan yafi maida hankali kan aikin"

Zaro Ido Mama tayi waje tace
" Maryam baki da hankali sai kika masa me?"

Dariyar takaici Maryam ɗin tayi ta kauda kanta tare da cewa 
"Nifa  ba yarinya bace da zaki tsare ni da tambaya kamar bansan me nake ba"

"Ni kike cewa ke ba yarinya bace Maryam?"

Wani kallon baki isa ba ta bita da shi tare da kan tsaki ta cigaba da tuƙin ba tare da ta ƙara cewa komai ba,
kasa magana Mama tayi har suka sauka tana mamakin canjawar Maryam ɗin.

Suna shiga gida  Maryam ko ɗaki bata shiga ba ta wuce toilet kai tsaye, dan ita kanta daurewa take warin jikin ta ya fara hawa  kanta, amma tunawa da alƙawarin gamji da kuma komen ta gidan Haidar yasa ta saki wani makirin murmushi,
 Tare da  cire kayan jikin ta a tsantsane ta shiga dirzar jikin ta kamar zata ɗaye fatar, sai da taji zuciyar ta ta gamsu da wankan tukun ta fito inda ta bar Mama tsakar gida haka ta dawo ta tarda ta tsaye tana kaiwa da kawowa.

Ƙwafa Maryam a zuciyar ta tace tunani yanzu Kika fara shi muguwa kawai.

Zuba mata ido Mama tayi ganin ta fito zuciyarta na wani irin bugawa, shikenan abinda take zargi ya tabba,
Ita kam Maryam ɗaki ta yi shigewa abinta tana jinta wasai tasan ta kusa cika burinta,
Sai kuma maganin Mama da za tayi tunda ta lura bata san abinda take ba.

********
Salim da ya kawo min Na'im yana kuka ne ya tashe ni daga nannauyan barcin daya ɗauke ni, 
Alhamdulillahi tashi na na nemi zazzaɓin na rasa sai kasala da bata gama saki na ba.

Fitowata farlo naga ashe har anyi magriba na tambayi Salim Abban su fa yace min ya tafi masallaci,

Bai shigo ba sai da aka yi isha'i da ledoji riƙe a hannun sa na takeaway,
Haka muka ci abincin muka ƙoshi na tattara yara muka shige ɗaki na barshi a farlon zaune yana kallo,
bai takura ba shima ya shige ɗaya ɗakin ya kwanta abin shi.

Haƙiƙa wannan daren nayi barci mai cike da natsuwa wadda na daɗe ban samu irin taba,
Da asuba na tashi kamar yadda na saba na tashi su Salim su kayi Sallah nima nayi,
Ina idarwa na fito na shiga aiki kamar yadda na saba sai dai yau ina jin na daban saboda wa kaina nake aikin, saɓanin da da aikin ina yin shine a matsayin bauta,
Nan da nan na kammala haɗa lafiyayyen abincin karin ban wahalar da kaina wajen jerawa a dining ba tunda yarana basu san daɗin hakan ba, na ɗauki abincin na ajiye a tsakar farlon, na Abban su na kai dining na jere masa da filas ɗin shayi tunda shi ya saba sha anin shi.

Muna cikin karyawa ya fito daga ɗakin shi cikin shirin fita Ofis sanye da riga da wandon suit rigar saman bak'a ce wandon ma haka sai yar cikin data kasance fara,
Yayi kyau sosai cikin shigar sai k'amshin daddaɗan turare,

Ganin ya kusa ƙarasowa kuma shima ya tsare ni da ido yasa na janye nawa idon a hankali, 
Ina jin zuciyata na bugawa tsohon tsumin ƙaunar shi na taso min wani kyau naga yamin na musamman na tuna inda dane yadda yazo ya same mu haka zan je gare shi na rungume shi cikin farin ciki da walwala, amma yanzu ina sai wani yanayi da nake ji wanda bazan iya fassara shi ba.

Salim ne ya fara gaida shi sai Umar ganin hakan nima na ɗago sai naga gaba ɗaya idanun sa suna kaina,
Cikin jin nauyin kallon da ya ke bina da shi nace
"Ina kwana"

Amsawa yayi tare da zama kan kujerar dake kusa dani tare da faɗin 
"Me yasa kuke cin abinci a ƙasa baki kai dining ba?"

Madadin na bashi amsa sai kawai nace
"A zuba ma abincin ne?"

Tashi yayi shima ya nufi dining ɗin da kanshi, ganin haka nima na tashi naje haɗa masa komai, bayan ya gama yace min zaije ofis yana son ɗaukar hutun sati biyu saboda ya zauna gida ya kula da yaran shi su saba da juna,
A dawo lafiya nace masa yayi mana sallama ya tafi.

Bayan tafiyar shi ne na tashi na shiga gyaran inda muka ɓata na yiwa yara wanka na koma ɗakin mu nada na ɗauko musu tsofaffin kayan su suka sa haka tunda babu wasu kaya anan

Da rana na ɗora abincin rana da yake yi debo mana kayan abincin sashin Maryam a cewar shi gobe ya ke son nima ya siyo min nawa,
Shinkafa da lafiya da miya da Nama na mana, kasancewar akwai sauran frunts a daya siyo na jiya ja haɗa mana lemo da yaji kayan ƙamshi nasa a firji dan dama nima inada firjina,
Nan da nan na gyara komai ya ɗauki seti nima nayi wanka tsofaffin kayana na saka dan bazan iya maida doguwar rigar jiya ba tunda bani da wasu kayan, Ni mutun ce mai kyankyami duk halin da nake ciki bana wasa da tsaftace jikina bana sa kaya sau biyu duk in nayi wanka sai na canja kaya,

Wajen ƙarfe biyu ya dawo niƙi-niƙi da siyayya haka ta dinga shigowa dasu, kayan sawar yarana ne da duk wasu abubuwan buƙata nima haka ya jibgomin siyayya kamar bai san ciwon kuɗin ba, godiya na masa nasa yaran suka masa godiya suma,
Ya bamu haƙuri tare da cewa gobe in Sha Allahu zai koma ya ƙaro mana wasu yau yana sauri ne,
Duk da naga yawan kayan amma nasan in dai Haidar ne kaɗan ba gani kan yadda ya saba kashewa iyalin sa kuɗi shi a wajen sa hakan ba komai bane,

Abincin na zubo masa yaci yana mai samin albarka har lokacin bai saki jikin saba duk a sanyaye ya ke komai,
Ganin ban cirewa yaran kayan jikin su ba yasa yamin magana akan nima na cire na jikina na canja tare da yaran,
Nuna masa nayi sai na kammala abincin dare tunda dai lokaci yaja ganin kamar bai ji daɗin hakan da nace  ba, sai naja yaran na ƙara musu wanka nima nayi muka canja kayan muka dawo farlo muka zauna duk da ba wata magana ke shiga tsakanin mu ba, sai shi da ya ke ta ƙoƙarin jan yaran jikin sa inda tuni Umari fa an sake harda su ɗane cinyar Abban nasu.

Salim dai bai gama sakin jikin sa ba sai wasa da Na'im da ya ke,
Har zuwa lokacin ɗora abincin dare na shiga kitchen dan ɗorawa.

*******

Bayan kwana biyu Alhamdulillahi zance kawai dan komai ya fara daidaita tsakanin mu cikin hukuncin Allah, wuni muke tare da yara dashi in nayi abinci na zuba masa nima muci da yara, Salim ma tuni ya saki jiki da Abban nashi da dare mu shige ɗaki nida yarana shima ya wuce nashi, bai taɓa gigin ƙara taɓa hannuna ba tun abinda yaga yana faruwa in ya taɓa, duk da lokuta da dama yana yi kamar zai taɓa ɗin.

Misalin ƙarfe biyar na yamma,  zaune mu ke ni da Umar a farlo da ke wasa gefena  sai Na'im na dake kwance kujera yana barci, Abbansu ya fita da Salim dan yayo musu siyayya kamar yadda yace,  Alhamdulillah tun da abin ya faru yana ta k'ok'ari wajen ganin ya kyautata mana ta ko ina dan da safiyar yau yaje kasuwa yayo mana siyayyar kayan abinci da wasu abubuwan buk'atun,    baya fita ko ina  yana gida ko ina nayi yana biye dani duk a k'ok'arin sa na ganin ya wanke laifukan daya min to nima dai duk taurin zuciyata tausayi ya ke bani, hakan da ya ke kuma ya wanke da yawa daga cikin k'uncin da nake ciki, 
 banga alamun dawowar Maryam ba amma ban cire rai da dawowar ta ba haka daga ni har shi babu wanda yawa wani maganar Maryam ɗin,
Na kuma sawa raina koda  zata dawo bazan zauna tamin abinda ta min a baya ba sam.

Yankan farce nake ina Allah Allah na kammala na ɗora abincin dare, jin shirun da Umar yayi daga wana motar wasan da ya ke yasa na ɗago, hankalina ne yakai kan Umar da inna yanke farcen sai yasa hannu ya ɗauke wanda na yanke d'in yasa a wata leda dake riƙe a hannun sa, na ɗauka wasan shi ya ke sai na maida kai na na cigaba da yankan farce na.

Can sai naga ya tashi ya tafi can bayan kujera ta ya tura ledar da ya saka farcen yana dariya yana magana da kanshi ƙasa ƙasa hakan yasa na daka masa tsawa nace
"Kai me za kai da farce naga kasa a leda harda 'boyewa maza bani ba a wasa da farce bakasan najasa bane bani nan" nace ina mai mik'ewa na nufeshi.

Abinka da yaro sai ya fasa kuka dana amsa yana faɗin Umma ki barmin abuna Mama ce fa tace in kin yanke na samo mata zata bani sweet" ya ƙarasa faɗar hakan yana mai yak'ara fashewa da kuka.

Jikina na ne ya shiga  karkarwa wani tsoro da fargaba suka dirar min bakina na rawa nace
 "Wace Mamar ce tace ka kawo mata?"
Ina jin wata zufa na yanko min duk da sanyin AC dake aiki,

Yana kuka  ya ke sanar min wai Mama dai dana sani ce tace mishi in ina yankan  farce ya kwashe ya ɓoye mata da  gashi na in nayi tsifa zata bashi alewa dayawa.

Kuka kawai na fashe da shi bayan nagama jin wannan sabuwar masifar Mama dai dana sani to ita kuma me take nema? Me na tsare mata sannan ma tarasa dawa zata haɗa kai ta cuceni sai ɗana na cikina, dan taga  yaro ne bai da wayo bai san komai ba, kuka nake sosai na ma rasa abinda zance sam duk wani tunani na ya dod'e ina ƙara jin tsoro  duniyar ma baki ɗaya na ƙara shiga ta.

Ina cikin kukan ne naji ringin ɗin k'aramar wayar Abbansu da ya bari a gida, kamar bazan duba mai kiran ba  sai na tuna yace zai kira ya tambaye Ni Abinda ya manta, Ina ƙoƙarin had'iye kukan na ƙarasa wajen wayar sai naga sunan shine na ɗaga tare da karawa a kunne na ina daidaita muryata dan karya fahimci kuka nake.

Jin muryar a rikice  ba tashi ba da kuma yasa na dafe k'irjina, abinda kunnuwa na suka jiye minne bayan na d'aga kiran yasa bansan lokacin da na yi cilli da wayar ba,
 tare da tashi da sauri na shiga neman Hijabina na goya Na'im  na fusgi hannun Umar a rikice ina jin wani sabon tashin hankali na rkitomin zuciyata kamar zata fashe ta fito daga k'irjina , 

Shikenan shikenan tawa ta k'are shikenan
Shikenan ni bani da sa'a a rayuwata 
Shikenan duk wani jin dad'in duniyar nan bani da rabo a ciki na shiga ukuna ina zansa rayuwata, shine kawai Abinda nake furtawa, kuka nake wiwi ko kulle get d'in gidan ban iya ba na nufi hanyar bakin titi a ƙafa kamar wata zararriya, tafiya kawai nake  banma san inda nake cilla k'afa taba sam,
Nama manta da irin nisan wajen da aka kwatanta min  a wayar, ganin yadda Umar ya kama kukan saboda gajiyar tafiya yasa na tsaida mai a daidaita nama manta  ko kuɗi bani da shi sai da na shiga na fad'ai mai inda zai kaini  ya ce kuɗin ki ɗari biyar tukun na tuna,

"Malam ka taimakeni dan Allah ka kaini kyauta"

"Kinga malama ficemin a nan in baki da kuɗi"
shine abinda yace min cikin tijara nan ya fara faffad'amin magnganu nasan bani da kuɗi na tsaida shi, ya sauke Ni a tsakiyar hanya yayi tafiyar shi.

Da ƙyar na samu wani bawan Allah ya biyamin shima na tsaida wani  adaidaita ne yana ciki,  yaji ina neman taimako mai mashin ɗin na k'ok'arin tafiya jin bani da kuɗi shima yana ta mita,  ganin yadda hankali na sam baya jikina yasa ya tausaya min  yace na shigo ya biya min.

Ina sauka a  adaidata kenan d'agowar nan da zanyi ina ƙoƙarin kama hannun Umar da ke son zuwa bakin titi mu tafi idanuna suka sauka a kan abinda ban taɓa tsammani ba ban taɓa kawowa ba zan ƙara gani  a rayuwa ta ba, na riga da na rufe babin nan na riga dana fauwalawa Allah komai na miƙa lamarina gare shi nasan shi zai min maganin komai.

Amma bisa ga rahamar shi sai gashi na kara ganin su, ban gama wannan mamakin ba naga wata mata fara kyakykyawa  ta fito daga ƙofar  Asibitin Sanye take da  kayan likitoci da suka mata matuk'ar kyau na waro idanuna a rud'e nayi wajen da nufin tsallakawa titi na ƙarasa wajen su ina jin zuciya cikin wani mad'aukacin  farin ciki,
 Banyi aune ba wata mota da ta taho ta bigeni ban ƙara sanin inda kaina ya ke ba.

Sannun da naji ana min ita  ta tabbatar min da Suma nayi Koda aka mik'omin Na,im amsa nayi na k'ok'arta na tashi  Ina bin kowa da kallo,

Mutanen wajen na faɗin 
"Ba kiji ciwo ba dai ko?"

Ban amsawa kowa ba
Idona nakai wajen da na gansu wayam babu kowa,

Wani irin tashin hankali ya shigeni lokaci guda ko dai basu na gani ba?,
Mutumin da ya bigeni ganin hankalina baya kanshi yaga kuma na mik'e sai ya bani haƙuri ya tafiyar shi,

Wata Mata ke rik'e da hannuna ganin na kasa   tsayawa da kyau Ina tangal tangal tace 
"Lafiya baiwar Allah za ki iya tafiya ko?"

Gyad'a mata kai nayi kawai na fara takawa ina zagaya wajen dan neman su, 
Kamo ni tayi da sauri ganin ina ƙoƙarin ƙara shiga titin tace
"Haba baiwar Allah za ki jiwa kanki ciwo ki jiwa yaron da ke goye a bayan ki kuma,  badan Allah yasa Ina kusa da ke ba da za ki faɗi da kin cuci ɗan mutane,  komai na rayuwar nan hakurui ake da shi karki sake damuwar duniya tasa ki dilmiya kanki cikin wani hali gwara ki fauwalawa Allah kowa da kike gani akwai jarrabawar shi, in wani Abu ne ya same ki wani na cikin halin daya linka naki"

Jinta nake kawai Amma hankalina baya tare da abinda take faɗa, ganin taƙi saki na yasa na janye hannu na daga nata tare da kama hannun Umar dake gefe Yana matse k'walla.

Ko damuwa da kallon inda take banba nace "Nagode" cikin dashashshiyar murya nayi gaba,
Dube duben duniya nayi banga alamun ko 'bur'bushin su ba, bisa dole na ja jikina tare da sa k'afata cikin asibitin don na tuna abinda ya kawo ni.

Sai dai na shafa wayar da zan Kira naji a wane 'bangare suke naji wayam babu ita.

Dama ankira ni ne aka ce me wayar yayi had'ari Wanda ya Kira ɗin ya fad'amin sunan asibitin ya kashe.

Banbi takan neman wayar ba dan nasan sanadiyyar bigewa ta wani yayi sama da faɗi da ita, da tambaya  aka nuna min  ɓangaren  Emagency amma na duba duk basa wajen,

Wani 'bangare aka nuna min waɗanda ba su jigata ba ne a wajen,
Ba k'aramin kwanciya hankalina yayi ba da N
naga ankawo ni nan, haka Ina bin gado gado har na Iso inda na na Haidar yake koda na had'a Ido da fuskar shi Yana barci sai naji hankalina ya ƙara kwanciya, 
Salim na gadon dake gefen shi shima barcin ya ya ke,
Wata ajiyar zuciya na sauke ganin ba wani rauni suka samu ba sosai gefen fuskar Salim  ne daga wajen kunnen shi naga Ansa bandeji, sai Abban shi shi kuma K'afar shi ce naga an masa ɗinki a wajen gwiwar shi dan har wandon jikin shi an yaga daga nan banga komai ba.

Bayan na gama duba su
Jan kujerar dake bakin gadon Salim nayi na kaita jikin lokar da ke tsakiyar gadajen na zauna na jawo Umar jikina na rungume su tare da Na,im dake ta sauke ajiyar zuciya,
Jin mutsu mutsun Na,Im yayi yawa yasa na saki Umar nasawa Na,im Mama a baki.dan nasan yunwa yake ji,

Ina zaune in sak'a wannan in kunce wancan tunanika iri,iri ne suka dinga rige,rige rikitomin, abubuwa da yawa na dawo min wadanda sun riga da sun wuce amma ni a waje na kullum na tuna so sabbi suke dawo min musamman  yau da nagan su da da idona tabbas sune sune Amma me suke anan?,  tambayar da bani da amsar ta kuma bani da mai bani amsa.

Motsawar da Salim yayi ne yana kiran ruwa ruwa yasa na dawo hayyaci na, nayi saurin yin kanshi Ina k'ok'arin ɗaga shi tare da jeramai sannu idanuna cike da hawaye, na d'auko ruwan inda aka ajiye tare da ɓalle murfin goran na kafa mishi a baki da sauri ya kama sha kamar wanda ya shekara bai sha ruwa ba.

Maganar mu ita ta farkar da Abban shi shima Yana ta k'ok'arin tashi amma k'afar  ta masa nauyi sai ya kasa,
Sakin Salim nayi na k'arasa kanshi na kai hannu dan na taimaka mishi ya tashi,
amma me jin wani uban shokin  muka yi wanda ya linka na da hakan yasa nayi saurin sakin hannun shi ina yarfe shima da sauri ya koma ya kwanta Yace wash hannuna

Sai lokacin na tuna da abun dake faruwa in na ta'ba shi,
Babu yadda muka iya na koma gefe Ina kallon shi shima bai k'ara yunk'urin tashin ba dan shi kad'ai yasan azabar da yaji dana taɓa shi.

Zuwan wani likita shi ya katse mana shirun dake tsakanin mu dan babu wanda ya iya furta komai cikin mu tun sannun da nace masa Yace yawwa kowa da abun dake damun shi a zuciyar sa.

Ni tunani na lula shi kuwa Allah yasan me nene dalilin shirun nashi,
likitann ne ya tallafa masa ya ɗaga shi ya jingina shi da filo ya gama duba shi ya tafi ya barmu jirgin jigum.

Salim ne keta faman damuna kanshi na ciwo koda likita ya duba shi sai yace min normal ne zai daina buguwar da yayi ce, nan hankalina ya kwanta,

Ganin shirun Abban su yayi yawa sai na alak'anta hakan da ciwon da yake ji ban wani damu ba dan nima tawa ta isheni, tunanin abinda na gani har yanzu bai barni ba,

Da wajen ƙarfe tara na dare likita yazo k'ara duba shi ya rubuta mana sallama tare da rubuta magungunan da zamu siya musamman Salim dake damun mu da kanshi kanshi, tunda dama ba wani rauni suka ji ba.

Bisa dole mu ka tari adaidaita dan motar shi anan muka barta  ta samu Yar matsala bayan nan ma ba iya tuk'i zaiyi ba koda babu matsala,
har muka ɗau hanya ba um babu um um sai Salim daya kwantar da kanshi gefen kafad'ata yana sauke wani irin numfashi.

Muna sauka ya sallami mai mashin ɗin muka shiga gidan dana barshi a hangame yadda na barshi haka muka dawo muka same shi,
Na riga shi shiga dan haka ɗaki na na wuce kai tsaye, shima bai ce min komai ba ya nufi na shi  ɗakin Umar na biye dashi a baya,

  Wata uwar tsawa da naji ya daka ya sani dakatawa daga k'ok'arin cire hijabin da nake na nufo waje cikin hanzari.

Sai dai me Umar na gani yashe a ƙasa yasa k'afa yana shurin shi yana faɗin kar ya sake ya tako masa ɗaki, ina ƙarasowa yana shigewa ɗakin ya bashi a wajen yana kuka.

A guje na k'arasa na taro Umar dake wani irin kuka har yana shid'ewa saboda yadda ya ture shi, Umar nawa yake da har zai ture shi ya haure shi da ƙafa?,

Wani irin ɓacin rai ne naji ya taso min tare da takaici da bak'in cikin da bazan iya misaltawa ba duk abubuwan da nake shanyewa ji nayi bazan iya jurewa ba wannan karon ina bazan iya ba, zan shanye bak'in cikin kowa akan y'ay'ana Amma banda nashi,

Tashi nayi na suri Umar na takewa Haidar Baya a fusace kafin ya kai ga rufe  k'ofar na Isa da sauri nasa hannu na tura k'ofar da k'arfi

_*😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE😍✍️✍️*_

*Dan magana da marubuciyar  ****
*_KOWA YAK'I JI._*

*_😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE😍✍️✍️_*

*_KARAMCI WRITER'S ASSOCIATION_*
*(Karamci tushen mu'amala ta gari)*

*_PAGE9️⃣_*

Jin yadda na turo ƙofar yasa ya dakata daga yunk'urin rufe ƙofar da ya ke ya ɗago idanun sa da suka rine suka yi wani irin ja ya watso min,
 in ba gizo idanuna ke min ba sai naga kamar har wasu irin ruwa ne suka taru cikin idanun sa  saboda tsananin fushi da masifar dake cin sa,
Sai dai sam hakan bai firgitani ba inda dane nasan hakan zai firgita ni yanzu Ina jin na wucewa.

Cikin Wata kakkaurar murya yace
"lafiya kika biyo ni?"

Ban bari ya ƙarasa ba, raina a matuƙar ɓace nace cikin d'aga murya
"Haidar me Umar ya maka da zaka ture shi harda hauri saboda rashin Imani wanne abu muka maka a rayuwa da ka tsanemu yau tsanar har ta kai ka fara taɓa lafiyar ƴaƴan cikin ka, haba mana  ka dawo da hankalin ka Haidar  Me kake so damu Ina kake so mu shig.."

Ban k'arasa magana ta ba naji ya sauke min wani irin gigitaccen mari sai da naga wuta ta gilma min, ga wani irin rad'aɗi da uban zafi da suka ziyarci fuskata, jina na yi kamar bani da kumatu a tare dani, nasa hannu  na shafa kumatun har ya tashi ga zafi kamar wadda aka watsawa wuta.

Shi kanshi da yayi marin wata iriyar ƙara ya saki yana yarfe hannun shi yaja baya ya watsi min rinannun idanun shi ya nunani cikin kakkausar murya yace
"Wato kinyi abinda bazan iya taɓa jikin ki ba kenan ke gogaggiya ko?"

Ni dai ina tsaye mamakin marin da ya sauke min bai gama saki na ba, me kenan ko dai wani abin suka ƙara masa da suka birkita shi, Innanillahi wa inna ilaihirraji'un kawai nake iya furtawa saboda tashin hankali neman hawaye nayi na rasa a idanuna.

Ganin yadda nake kallon shi yasa ya hasala tare da cewa
"Wallahi Salman na tsane ku na tsane ku ku taimaka min ku tattara ku bar gidan nan dan Allah, ji nake kamar in kashe ku ko zan huta da abinda nake ji ki taimaka min Salmah"
Ya ƙarasa faɗar hakan tare da zube gwiwowin shi a ƙasan wajen ya saki wani rikitaccen kuka tunda nake da shi ban taɓa ganin ya yi kuka ba, sai hakan yasa naji gaba ɗaya na shiga wani hali musamman yadda ya ke shashsheƙa kamar wani ƙaramin yaro,
Nan da nan wani tausayin sa ya kamani na rasa me ya kamata nayi sai kawai na foshe shi  ina ji a raina koma meye sai dai ya faru bazan bari a raba mu ba.

Ban kai ga kaiwa wajen shi ba ya ɗago rinannun idanun shi cikin karaji yace
"Karki ƙaraso nace dan Allah" yana wani layi kamar wanda ya sha kayan maye,
ban dakata har sai da na ƙarasa wajen shi, babu zato naji anyi cilli da Ni kamar wani kwano na bigi bangon na faɗi kaina ya bugu, wata ƙara na saki saboda azabar data ratsani, kafin na miƙe yayo kaina ya kawo hannun shi ya ɗago Ni da nufin duka na sai dai bisa dole ya sake ni dan yadda ya ji shokin ya ja shi.

Ganin yadda ya haukace yana neme neme sai tsoro ya kamani na tashi a rikice ina neman hanyar gudu dan tuni Umar shima ya ɓuya a bayan kujera.

"Ba zaki gudu ba ko Salmah?" yace tare da nurar  hanyar kitchen nasan madoki ya ke nema, ganin yanayin da ya ke magana kaɗai ya tabbatar min an koma gidan jiya ko nace fiye ma, Haidar dai baya cikin hankalin sa sam baya  hayyaci sa, ɗan mutumcin da muka fara kenan babu shi yanzu ai ban bari na kai ƙarshen tunanin ba ganin tahowar shi gadan gadan riƙe da muciya yasa na fusgi hannun Umar ganin bala,i Ido,da Ido nayi ɗaki na a guje ina shiga na rufe ƙofar tare da barin makullin a jiki ina sauke wani irin numfashi zuciyata na bugawa da ƙarfin gaske,
na koma na mak'ale  jikin bango jikina na wata iriyar rawa Ina zaro Ido, bugun ƙofar ya shiga yi a haukace yana faɗin na zo na buɗe masa Kofar sai ya illatani yau sai yaga ƙarshe na daga ni har Ƴan iskan yaran da na cika masa gida dasu duk sai ya kashemu kowa ya huta.

Rawa kawai jikina keyi addu,o,a kuwa babu kalar wadda banba dan daga na kamo wannan bana sanin na saki sai na kamo wata, hankali na a matuƙar tashe yake. 

Nishin da Salim ya ke ne yasa na kai kallona kan gadon inda na kwantar da shi tun dawowar mu, da sauri nayi kanshi ganin abinda ya ke na tallafo kanshi na ɗora a cinyata gaba ɗaya ya fita cikin hayyacin sa, dan wani irin numfashi  ya ke yana riƙe da kansa da hannuwan sa duka biyun
yana wasu irin sambatu marasa kai.

Jijjiga shi nake ina kiran sunan shi Salim Salim Ina bai ma jina sai wani irin gurnani da ya ke abin babu daɗin ji,
Cikin wani sabon tashin hankalin na rungume shi tare da fashewa da wani k'akk'arfan kuka wanda ya taso daga ƙasan zuciyata, cikin kukan nake faɗin 
"Ya Allah ka sassauta min halin da nake ciki ya Allah ka kawo min agajin ka da taimakon ka ya rabbi bazan iya ba kaine mai iyawa bayin ka ya Allah ka ji'banci lamarin baiwar ka Salma bani da gata sai kai Allah bani da kowa sai kai Allah ka yaye min abinda ke damuna ka kareni da yarana da mijina daga dukkan sharrin masu sharri Allah kana ganin su kana jin su Allah kai Kasan yadda za ka yi dasu Allah na kawo ƙarar  bayin ka waɗanda ke cutar dani Allah su cutar dani Allah sun rabani da mijina sun raba uba da ƴaƴan sa Allah ka kawo mana ɗauki" 

Cikin fitar hayyaci nake kukan har lokacin ina jin yadda Haidar ke bugun Kofar kamar zai ɓalla ta,

Ganin yadda Salim ke ƙara ke yi yasa wani tunani shiga ta da gudu na tashi Allah ya taimake ni naga kofin da na bawa Na'im shayi dashi ɗazu kafin mu fita,
toilet na shiga na tara kofin a famfo na d'ebo ruwan na dawo na zauna addu'o'i na shiga yi ina hurawa a ruwan na kama bakin shi da ƙyar na shiga zuba mai ruwan yana shanye da wasu na bin gefe suna zubewa na shafa mai sauran da ya rage  a fuska, cikin ikon Allah sai gashi ya fara sauke ajiyar zuciya ya saki hannun da ya riƙe kan nashi dashi a hankali ya rufe idon shi.

Wata ajiyar zuciya ce ta kubce min ganin kamar barci ya ɗauke shi yasa na sauke kanshi,na kwantar kan gadon ina shirin sauka naji ya riƙe hannuna, da sauri  na dawo na zauna na shiga  dadda'ba shi Ina "Salim Salim" sai naga barci ya ɗauke shi ban tashi ba sai da naga yayi nisa tukun na lalla'ba na sauka zuwa lokacin mai buga ƙofar ya gaji ya tafi.

Na zauna nayi shiru ina tariyo abubuwan da suka faru lafiya muka rabu da Haidar, to me kenan hakan ke nufi? sun  ƙara birkita min shi  kenan ko yaya? dama nasani ba zasu barmu mu huta ba ba zasu k'yalemu ba,
amma Kuma shi Salim fa meya same shi? sauri nayi wajen kautar da tunanin da naji ya faɗo min Ina neman tsari da hakan,  na sawa raina kawai buguwar da likita yace yayi ne ta haddasa masa hakan,

Tunani me ya kamata nayi na fara meye  mafita akan zamana gidannan ada Inna zauna na jure duk wata wuya da cin kashi saboda yarana da kuma zaton watarana komai zai koma dai,dai a yanzu fa? yaya zanyi tunda ya fara neman rayuwar mu, ga wata irin unguwa muke da babu wanda ke shiga harkar mu,
zaman me zanyi?
Shin zaman jiran ya kashemu zanyi kenan kowa ma ya huta ko kuwa yaya?
ko mafita zan nemawa kaina mu samu mu tsira da rayuwar mu, haƙiƙa ina son na rayu kodan innemi yafiyar waɗanda na ɓatawa ban sani ba ko hakk'in hakan ke bibiyar rayuwa ta, Astagfurullah na furta ina ƙara tubarwa Ubangiji na akan irin wautar dana aikatawa rayuwa ta a baya.

Tunawa da banyi sallar isha'i ba yasa na tashi na shiga toilet na yo alwala  jikina duk ba ƙwari na tada sallar ina layi saboda tsabar yunwar da nake ji ga gajiya,
Ina idar da sallah Umar da dama tuni yayi barcin tsoro ya farka ya dasa min kukan yunwa yake ji.

Tashin hankali yanzu me zan bashi yaci bama shi kaɗai ba dukan mu muna buk'atar abinda zamu sawa cikin mu Amma tayaya Ina zamu samu?.

Lallalashin sa nayi da ƙyar yayi shiru na rungume shi ina shafa kanshi cikin ikon Allah na samu ya koma na kwantar da shi na tashi na koma kan sallaya na shiga kaiwa Allah kukana yanzu nasan babu abinda zai fitar dani sai Allah.

*HAIDAR*

Ganin duk irin bugun da ya ke wa ƙofar taƙi buɗewa yasa ya juya zuciyarsa na tafasa yana jin jikin sa kamar ana hura masa wuta ya nufi ɗakin sa, yana shiga ya zube kan gadon shi hannayen sa duka biyu dafe da kanshi yana jin kamar zai rabe biyu, ga ƙafar shi da ke masa wani irin radaɗin zafi da zugi ga wata yunwa da ya ke ji abubuwan suka haɗu suka masa rubdugu, nan da nan wani zazzafan zazzaɓi ya rufe shi ya shiga rawar sanyi yana son jawo bargo ya lullu'ba amma ya kasa motsawa baki ɗaya.

Ina Nan zaune kan abin sallah har aka kira sallar farko, na na tashi ina jin jikina kamar wadda ake turawa na nufi ƙofar dan na fita na nema mana abinda zamu ci tunda bazai yiwu muyi ta zama a haka ba, sai da na rufe yaran ta waje na zare makullin na soka a cikin rigata, na lalleƙa farlon sosai naga babu kowa tukun na fito saɗaf saɗaf na nufi kitchen, kallon ƙofar ɗakin shi nayi na ganta a rufe alamar bai tashi ba, cikin  hanzari na ke aiwatar da komai na a hankali dan kar aji motsi na.

Nan da nan na ɗora ruwan zafi na dafa farar taliyar leda biyu dan na riga dana tsara abinda zanyi, ina yi ina leƙawa farlon ko dan gudun samun saɓani, shayi na dafa da yaji kayan ƙamshi na juye a flask na d'ebar masa taliyar kaɗan na ajiye da shayin dan ina son gwadawa ko abinda nake son yi zai yiwu,  saɗaf saɗaf na wuce ɗaki da duk abinda nasan zan buƙata na maida ƙofar na rufe ina sauke ajiyar zuciya, lokacin an fara kiran Assalatu dan haka alwala nayo bayan na idar da Sallah tashi yara mu kayi zaman mu a ɗakin sam banyi gigin ƙara lek'owa ba.

Duka wunin ranar a ɗaki na muka yi shi, duk son Umar da yawo bai ko nuna yana dan ya tsorata tun abinda ya faru jiya,
Babban tashin hankali na Salim da ke ta kukan kanshi zai fashe duk ya rikice min na rasa ina zan sa raina naji daɗi, daga karshe na yanke in dai ya fita Masallaci zan ɗauki yaron na maida shi asibiti a duba shi.

Haidar bai farka ba sai wajen ƙarfe shida na safe, ya mik'e da ƙyar yana jin kanshi na sara masa kamar ana buga masa guduma, 
A hankali ya sakko daga gadon yana jikin shi babu ƙwari tuna bai yi Sallah jiya ba yasa ya nufi toilet cikin hanzari yana son tuna abinda ya faru amma sam ƙwaƙwalwar shi ta kasa tuna mishi komai,
Ya dai san lokacin da ya fita gida har zuwa had'arin da ya faru da suka fita siyayya, har ya kusa bige wani tsoho da ya shigo gaban motar shi garin ya kaucewa mutumin ne motar ta ƙwace masa daga nan bai ƙara sanin me ya faru ba, sai yanzu daya farka ya ganshi a gida, duk tunanin shi bai iya tuna komai ba mamakin shi daya waya kawo shi gida?.

Yana idar da Sallar ya tashi ya fito farlon, yayi mamakin ganin shi wayam kamar ma babu wanda ya fito a cikin su, a hankali ya nufi ɗakin Salmah ya tura jin shi a rufe yasa ya fara k'wank'wasa ƙofar.

Ina zaune kan Salim a cinyata ina faman tofa masa addu'a saboda har zabure zabure yake yanzu, in na masa addu'ar ne yake ɗan samun sauƙi ya daina.

Jin ana bugun ƙofa yasa naji hanjin cikina ya murɗa a tsorace, nayi shiru ina kallon ƙofar naƙi magana,

Haka ya dinga k'wank'wasawa ya fara kiran sunana nayi biris na ƙyale shi, yayi zaton ma ko basa ciki ne amma jin motsin Salim da sambatu da ya ke yasa cikin tashin hankali ya fara bugun ƙofar, dan a hankali abubuwan da suka faru suka fara dawo mishi har yadda yayi jifa da ita komai ya fara dawowa kan shi dalla dalla.

 Dafe kanshi yayi cikin tsananin damuwa ya shiga mata magiyar ta taimaka ta buɗe ya na son ganin Na'im ne dan Allah.


*****

_*😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE😍✍️✍️*_