Kuncin zuci
by @bintuuu
Tsayawa kallon sa tayi sai ya dauke idonsa a nutse ya juya zai fita daga toilet din kansa a qasa, har ya fice bata daina kallon bayansa ba, cike da sanyin jiki ta sake rigan ta sauka qasa tafara hawaye dan babu tantama hawaye tagani a idon Ahmad, tana share idanunta ta cire lingeries din dake jikinta ta shiga cikin bath din, kwanciya tayi aciki fuskanta na kallon sama ta rufe idanunta tanajin hawaye na zuwa mata, sai da ta dauki kusan 15 minutes sannan ta fito daga cikin ruwan, nan ma wanka tayi da ruwan dumin under his shower sannan ta saka babban towel dinsa da ya sauqa mata sosai sannan ta fita, aikuwa sai ta gansa tsaye a kofar toilet din hannunsa riqe da wani towel din yana jiran fitowarsa, ganin yanda yake kaucewa kallon idanunta yasa ta gane yayi hawaye, did Ahmad just cry because of her?.....matsowa yayi gareta sai ya hau goge mata gashinta da towel din hannun nasa duk tana kallonsa, sai da ya gama goge mata ruwan dake gashin nata sannan ya kama hannunta suka qarasa gadonsa ya zaunar da ita tana noqewa cikin towel din, ahankali yace "Wanne ne cream din da kike shafawan, naje dubo miki kuma bangane ba" ahankali tace "ka barni in tafi can din in shirya" sai sannan ya dago kai ya kalleta, ganin idanunsa sun dan chanja kala yasa ta kaiwan hannunta ahankali ta shafa gefen beard dinsa suna kallon juna cikin ido, cikin sanyin murya tace "Ya wuce fa Ahmad, komai ya wuce" sai ya girgiza kai yace "Not when i keep seeing those scars on you Na'eemah, ji nake na tsani kaina, I should've talk to you that very first day dana fara ganinki" sai tayi murmushi tace "Haka Allah ya tsara, it's in the past now..ba gashi muna tare ba yanzu" hannunsa yakai ya sarqo waist dinta ya juyo da ita gaba daya garesa, ahankali yace "Abu daya zaisa in yafe masa" tana kallonsa tace "Menene?" sai ya duqo ahankali yace "Bai shiga gonata ba" da sauri ta dora kanta a qirjinsa tana dariya sai yace "I won in life Na'eemah, this is called 'winning'...ban taba jin nayi nasara babba akan abu ba irin wannan" sai ya dago da fuskanta da hannunsa biyu yana kallonta yace "I'm the happiest Man today, i had the greatest win in life" sai ta rufe idanunta tana murmushi kawai ya hau yi mata rain kisses a fuska suna dariya qasa qasa ita da shi din, sai da ya gama sannan ya miqar da ita suka tafi can dakin nata, shi ya duba mata kayan baccin da zata saka sannan ta nuna masa mayukan nata ya debosu ya dawo gareta tareda zama a gefenta yafara kokarin shafa mata, nan ta karba tace zatayi da kanta dan sai kallonta yake daure da towel din, sai da ta duqa zata shafa a man a kafanta taga yana kallon bosom dinta, da sauri ta ware towel din dake daure a kanta ta yafa a kafadarta har ya sauqa zuwa qirjin nata, sai Ahmad ya kalli gashinta da ya zuba zuwa bayanta, ahankali ya kai hannu yana shafawa while tana shafa man, shiru sukayi ahakan yanata kallonta sai can Naima ta dago kai ta kallesa jin ya fara sauqo da hannunsa wani wajen kuma, matsawa tayi daga kusa dashi sai yayi murmushi kawai ya miqe ya fice daga dakin, downstairs ya nufa sai ya dauki ledan abincin dake nan kan center table wanda ya dawo dashi daga asibitin, kitchen ya nufa ya dauki plate ya wanke sannan ya zuba mata, wani plate din ya sake dauka ya nufi fridge ya dauko fruits suma ya wankesu tas sannan ya hada da bottle water ya koma dakin nata riqe dasu ahannu, samu yayi ta saka kayan baccin masu laushi tana zaune a falon waya kare akunnenta tana magana da Mami, zama yayi gefenta yana sauraronta har ta gama sannan ya miqa mata abincin yace "Here..eat this" karba tayi cikin sanyin jiki yana kallonta, saida ta fara ci sannan ta dago ahankali tace "kaifa" ya girgiza kai yace "Naqoshi" sai ya fara shan fruit din da ya kawo matan suna zaunen, bayan sun gama tafara kokarin miqewa zata kai plates din nan ma ya hanata ya dauka ya fice tana kallonsa, sai da ya tabbatar ta gama duk routines dinta ta kwanta sannan ya gyara mata blanket sai yace mata zaije yayi changing shima saita gyada kai tana rufe ido alamun bacci, yana murmushi ya fita daga dakin, dakinsa ya koma sai da yayi wanka ya fito yana goge jikinsa yayi stiff a tsayen dalilin tunawa da Papers din da smoke ya basa dake motansa, aikuwa yana gama shirin bacci cikin pajamas dinsa ya nufi can parking space, tun kafin ya qarasa ya danna remote din motan dake riqe hannunsa tayi qara sau biyu daga can qarshen lot din, ya nufe ta ya bude yana bincikiwa, nan cikin drawernsa ya dauko file din yana duba jiki dan tabbatarwa ko shine, da haka ya rufe motan ya koma cikin gida, anan main falo ya zauna yafara ciro takardun cikin envelope din ya zuba akan glass table din gabansa yana nazarinsu, hotunan yafara diba yana dubawa da daddaya, kowanne dauke yake da Saddam da different 'yanmata, wani gasunan sun je cin abinci, wasu kuma a a qasashen waje, sai da yakusan kai wa qarshen kawai yayi stiff yana kallon wanda Laila ke ciki ita dashi a guri kamar yatch yaka, Ahmad was shock a wannan lokacin, Laila and Saddam? sai ya miqe riqe da hoton ya nufi kitchen bai dade ba ya fito hannunsa da bottle water yana sha yana kallon hoton har sannan, ran se yake wani irin baci a wannan lokacin, abun qanwar tashi har yakai haka?..then it finally crash on him, itace accomplice din Saddam, ita ta bashi information din Na'ima suka yada a media, ita ta aika takardun nan gurin baba kenan?..sai kawai ya ajiye ruwan yana jin bacin rai har da mamaki ma, zama ya sakeyi yana duban takardun sai ya dauka ya fara karantawa, har qarfe Sha biyu na zaune a falon yana nazarin takardun wanda suka kasance har da na company'n Saddam din, dakinsa ya koma ya dauko wayarsa sannan ya dawo nan din, kira ya dannawa smoke yana dauka yace "Naga papers din but i need you to find Tiyagah as soon as possible please" daga can Smoke yace "Am still on it, guy din yana da wayo ne dayawa" Ahmad yace "kayi duk yanda zakayi Smoke..I need that guy soon, shi kadai yake da final amsoshina" sai smoke yace "Nima nayi tunanin haka, wannan pictures din nasa an daukesu ne bayan faruwan incident din da kwana biyu" Ahmad ya dan hade gira in confusion yace "Taje Lagos?" ya amsa da "Yes, she stays with him for two days" Ahmad yayi shiru sai can yace "Ka nemomin yaron nan da wuri please" smoke yace "Angama" da haka Ahmad ya kashe wayan yana dan mamakin qanwar tasa, tattare takardun yayi ya maidasu ma'ajiyansu sannan ya miqe tareda nufan stairs dan zuwa ajiye su a dakinsa, sai da ya kullesu cikin safe dinsa dake nan cikin walk in closet dinsa sannan ya fito ya nufi part din Na'ima, samunta yayi tana baccin ta hankali kwance ga hasken bedside lamp yana dan hasko fuskanta, murmushi yayi ya qarasa gareta ya zauna bakin gadon sai ya fara gyara mata hulan ta daya zame daga kanta, dan motsawa tayi ta bude ido tana kallonsa sai ya duqo yayi kissing goshinta ahankali yace "Good night jewel" rufe idonta tayi ta koma baccin sai shima ya daga duvet din ya shiga tareda matsawa gareta ya rungumota, har kusan 1 na dare beyi bacci ba yana tunanin abunda ya farun, in ya tuna abunda yaji lokacin da aka dauke Na'iman da kuma yanda suka sameta sai yaji wani zafi na taso masa arai da tausayinta, babban burinsa a wannan lokacin shine yasan wanda yake neman ganin bayan matarsa qarfi da yaji, sai ya saqe rungumota yayi kissing kanta, da haka shima baccin ya daukesa...
Washegari da asuba shi ya rigata tashi sai ya sauqa daga gadon ahankali yana karanto addu'an tashi, har yayo alwala a toilet dinta bata tashi ba sai ya qaraso ya duqo fuskarsa saitin nata yana shafa mata ruwan fuskan nasa while yana murmushi, yamutse fuska tayi jiin ruwa afuskanta sai ta bude ido da wuri, ganin haka sai ya miqe yana danne dariyansa, miqewa zaune tayi ta lalubo hulanta ta saka sai yace "zanje masjid" ta gyada kai alamun toh sannan ya fita zuwa part dinsa dan yayi changing kayan jikinsa, da ya dawo daga sallahn ya samu tana zaune bisa sallaya hannunta riqe da Qur'ani tana karatu, zama yayi kusa da ita hannun riqe da tasbaha, sai da ya jira ta idar ta rufe sannan yace "Ya kika tashi?" tace "Ina kwana" ya amsa da "Lafiya jewel, how was your night" tayi murmushi bata amsa ba, da haka suka koma wani baccin amma guraren 7 ya farka, nan ma ya sauqa a hankali ya fice daga dakin, kitchen ya nufa direct nan kuma ya rasa ta ina zai fara bayan ya shigan, he really want make her breakfast in bed, sai ya kama waist dinsa yana bin kitchen din da kallo, beside fridge da ya iya budewa ya dauko kayan marmari besan ya ake amfani da sauran electronics din ba, sai ya koma falonsa ya dawo hannunsa riqe da babban iphad dinsa yayi onning data ya shiga YouTube, sai da ya samo video yanda ake hada simple breakfast sannan ya ajiyeta nan kan kitchen island din ya dafa hannunsa yana kallo at the same time yana haddan komai, nade hannun rigansa yayi nan ya hau aiki tsakaninsa da Allah, yana cikin kada kwai yaji anyi knocking kofan falon again aka danna door bell, ajiye komai yayi ya fitan yana budewa yayi Ido hudu da Husna hannunta riqe da basket, tana ganinsa tace "Good morning Yaya" ya amsa da "Lafiya" da haka ya bata hanya ta shigo tana fadin "Mamma tace nakai wa Anty breakfast a asibiti kuma ashe an sallameta" sai yace "jiya muka dawo" da haka ta nufi dining area ta ajiye sai ya sake cewa "kai kitchen" ta amsa da toh ta nufi can din yana biye da ita, samu tayi kitchen din a hautsine sai tace " Wow...Yaya da ka kirani na muku ai" yace "Qarasa wancan toh" ya nuna mata kwan da ya hada, sai tayi murmushi ta qarasa ta cigaba, zama yayi a kujeran jikin kitchen island din suna magana jefi jefi akan karatun ta da ta kusa gamawa, sai da ta hada masa irin tea dinda suke masa a gida sannan ta soya iya qwan tace masa zata zuba musu wanda ta kawon sai ya gyada kai yana kai cup din bakinsa, sai kuma anutse yace "How did they let u in?" tace "Na'am?" yace "The gate securities" sai tayi murmushi tace "Wai sunga kamata dakai" bai ce komai ba ya cigaba da sipping tea din, shi tafara serving yaci abincin sama sama anan kitchen din sannan ta qarasa hada komai a babban plate ta fara qoqarin dauka zata kai wa Na'iman yace "Let me" sai ta gyada kai tana murmushi, da haka ya miqe ya karba daga hannunta ya fice tana kallonsa har sannan da murmushi a fuskanta, Allah ya bata me irin halin yayanta take fata a wannan lokacin dan sha'awa hakan ya bata matuqa.....Shigansa ya samu tana bacci har sannan sai ya ajiye abincin a kan bedside drawer sannan ya zauna a bakin gadon tareda kai hannu yana shafa fuskanta, nan ta motsa sannan ta bude ido sai ya duqo yace "Babe" sai ya kai bakinsa kumatunta yayi pecking dinta yace "Morning" nan ta fara qoqarin miqewa zaune tayi dan miqa duk yana kallonta sai ta juya ya dauko plate ya miqo mata shi yana murmushi yace "Breakfast in bed" murmushi Na'ima ta fara ganin full breakfast me kyau a plate din har da bottle water a gefe da cup, sai ya ajiye mata a cinya yana kallon yanayinta ganin sai murmushi take, dago kai tayi ta kallesa, cikin sanyin murya tace "Thank you Honey boo" ware idanu Ahmad yayi, sai ya matso kadan yace "Repeat that.. Babe" tana dan dariya ta fara girgiza kai sai yace "Please repeat it" bata bar dariyan ba ta maida hankalinta kan plate din tafara ci duk yana kallonta, sai tace "Muci mana" girgiza kai yayi yana murmushin satisfaction, dan ganin ta so hakan sai ya faranta masa rai sosai, sai da tayi nisa da ci sannan ta kallesa tace "You made this?" yana nuna different dishes din yace "Wannan Mamma ce ta aiko, wannan kuma" ya nuna scrambled eggs din "Shi nafara kokarin yi sai Husna tazo, ita ta qarasa" yana dan dariya ya qarasa maganan sai Na'ima ta ware ido tace "What? Ina take?" ya gyada kafada yace "She's downstairs" da sauri Na'ima ta daga plate din daga jikinta ta miqa masa tana fadin "shine baka fadamin ba, muka shanyata" ajiye plate din yayi kan bedside drawer yace "she'll wait ai" tana tafiya ahankali ta shige cikin closet dinta tana fadin "Ba dadi hakan fa" sai Ahmad ya cire loafers dinsa ya gyara kwanciyarsa a gadon tareda jawo wayarsa yana dannawa hankali kwance, da haka Na'ima ta fito sanye da doguwar riga ajikinta ta fice daga dakin yananan kwance a gadon.....
Nayi posting final one din a WhatsApp shiyasa zan yi muku anan ma, in sha Allah zuwa next week around 13th ko 14th din zan turo sauran da suka kammala in yaso ko ban gama ba sai bayan azumin in Allah ya kaimu..ku qara hakuri dani please 😻