GAJERIUN LABARAI

Chapter 1

by @jikankaila2014

ABOKINA NA ƊAUKE KA .. 

Daga Jibrin Yusuf Kaila 

Duk da na sha alwashin cewa banga yarinyar da ta isa ta birkita tunani ba,amma yau Ajwa Abdulhamid ta sani ina zubar da ƙwalla wanda cike yake da zubar da hawaye mai masifar zafi a zuciya, wanda tsananin abin da ta mun ya sa na ke sunbatu mai kama da ciwan hauka, ina cewa Ajwa mi yasa ki ka mun haka a rayuwa ta,ni ban cancanci haka ba ...
.

Ni tela ne mai ɗinki kayan maza da mata amma na fiyi kayan maza, duk wani ɗinki na gidan su Ajwa ni na ke yi,sai ta kawo na yi musu,duk da ni ban fiya son ɗin ka kayan mata ba,kai na ƙawayan ta ma Inde suna alaqa da ita ni na ke musu, kuma duk wannan abun ba na karbar naira biyar ta su..Duk wani kuɗina agunta ya ke ƙarewa. Duk sanda aka ce ba ta da lafiya toh fa ni bani da sukunin ko nutsuwa rai, har sai ta samu sauki.Duk kantinan da ake sai da Sharwama da kayan makulashe sai na ziyarar ce shi, don faranta mata rai don samun lafiyar ta,duk maganin da zata sha ni na ke siyowa. 

 Abokaina sun sha cewa asiri ta yi mun,amma kullum Inde suka faɗi haka ƙoƙari na ke na kare ta, ban son na ji an kushe ta.Akwai wani lokaci da na ga ana yayin wayar hannu,wanda yawanci ƴan mata ne su ke mallakar ta,haka na yi kuri na siyar da wani keken ɗinkina butterfly, na cika na siyo mata wayar, kuɗin wayar ya kai 160k , ko gidan mu ban faɗa mu su ba. Wayar da na ke da ita bata wuce 60k ba.,duk wani abu da na mallaka kan iya sayar da shi, Inde zai sa ta jin farin ciki a rayuwar ta, kuma komi nene.

Ranar Valentine, rana ce ta masoya wanda kowani masoyi ya ke bawa abun ƙaunar sa kyauta,kuma rana ce ta farin ciki, amma ni de rana ce ta da ta zame mun ranar baƙin ciki a gare ni.14 /2 /2024 rana ce da na ke burin ta zo mun, don na tanadar Masoyiya Ajwa wata kyauta ta musamman ,sai dai rana ce da ta koma ranar baƙi ciki a rayuwa ta, domin Ajwa ta yaudari ni bayan mun hadu da ita na miƙa mata kyautar da na yi mata tanadi don sanya ta farin ciki, mun yi ɗan kalame na masoya mun rabu.

Bayan na je gidan na zauna na buɗe whatssap ɗina sai na ga sakonta na katin ɗaurin auranta, na duba da kyau na ga katin auran ta ne, a satin da zai zo, ta ce "Ka yi hakuri daman aboki na ɗauke ka.Tuni na yanke jiki na faɗi, sai a asibiti kalmar nan ta tsaye mun a rai wai ABOKI NA ƊAUKE KA...