ME KA TABA MUN
ME KA TAƁA MUN
Daga Jibrin Yusuf Kaila
Idan akwai wata shawara da zan baka game da matarka bai wuce ka guji abin hannunta ba, domin ni abin misali ne a gare ka. Ba wai ina tona wa kaina asiri ba ne, sai dai don na ankarar da 'yan'uwana maza ga sha'anin mata. Babu shakka mata sharrin su ko fitinar su tafi ta tsohuwar mota. A gefe guda idan Allah Ya hore maka mace tagari to, tamkar Ubangiji Ya baka kyautar duniya ne! Domin samuwar natsuwar ɗa namiji ita ce dacewa da mace tagari. Daga lokacin da ka fara zaƙewa da kayanta koda kuwa duk abin take so kana mata to, daga lokacin ka sayawa kanka rigar rashin daraja, koda kuwa da tarin tulin alkhairan da ka mata ne.
Ka tsoraci kayan mace, koda kuwa ita take baka, ka manta da abin da ka ke mata ko ka yi mata wanda ya haɗa da iyayenta da kuma ahalinta. A ƙarshe dai abin da za ta ce maka shi ne, "Me ka taɓa yi min?"
Bari na baka wani taƙaitaccen labarina, ni da matata Hanifa. Hanifa mace ce da ta taso a gidan marasa galihu, duk da dai suna da tarbiyya bakin iyawa. Babansu yana tsaye akan duk wasu al'amuransu, duk kuwa da ba masu ƙarfi ba ne sosai. Baban Hanifa sunansa Malam Mato, mutum ne da yake sana'ar facin babura, da ita ne kuma yake ciyar da iyalinsa. Babarsu kuwa Iya Lami mace ce mai sana'ar tuyar ƙosai. Hanifa kuwa ita kaɗai ce a gidansu mace tana da ƙannenta biyu, Jawad da Abdulyassar suna matakin firamare, ita kuma tana matakin babbar sakandire, aji na biyu (SS 2). Sai dai halin rayuwa ya sa ta daina zuwa.
Shiga ta rayuwarta ya sa wasu al'amuran na ƙunci suka ragu, tunda Allah Ya sa na ganta na samu ganawa da iyayenta, na shiga hidimta mata, duk da a lokacin ban samu aikin gwamnati ba. A lokacin ina aikin hidimar ƙasa a ƙauyensu a wajen mahaifiyarta muke zuwa karin kumallo, a wajen ne na fara ganin ta, kuma hakan ya sa na nuna ina sonta.
Tunda na ji an ce ba ta zuwa makaranta hakan ya sa na yi ƙoƙarin ganin iyayenta, don su bani dama na mayar da ita makaranta, domin na lura yarinyar tana da ƙoƙari kuma tana da son karatu. Na sha ganin tana karatun littafin Hausa da ƙananan littattafan labarai na turanci, wanda hakan ya yi matuƙar birgini. Lokacin da na tambaye ta a wacce makaranta take, sai ta ce bata zuwa kowacce a sannan, don haka na sa ta a makarantar da nake hidimar ƙasa, Rimi Girls Secondary School Farin Gida. Tabbas ta ji daɗi, har iyayenta sun yi godiya. A haka ta cigaba da karatu har zuwa lokacin da na kammala hidimar ƙasar da nake yi, yayin da a lokacin ita ta kuma ta shiga ajin ƙarshe (SS 3). Ban yi ƙasa a gwiwa ba, lokacin zuwa lokaci ina zuwa ƙauyen domin ganin ta. Baya ga sabgar sha'anin karatu, na rage musu wasu nauye-nauye na sabgar gida, haka ne ya sa na ƙara karɓuwa a gidansu sosai, suna girmama ni.
A kwana a tashi Hanifa ta kammala makaranta, ni kuma sai na yi ƙoƙarin ganin manya sun shiga cikin maganar. A satin da za a je tambayar aurena da ita babanta ya gamu da rashin lafiya wacce silar haka ya sa aka dakatar da zancen, saboda rashin lafiyar sa. Ba zan ce zan yabi kaina ba, amma babu wani magani da za a rubutawa mahaifinta ba tare da na biya ba, ko ina garin ko bana nan, don ƙauyen da suke na kusa da garin mu ne. Silar haka ne ya sa na saya mata waya saboda duk maganin da aka rubuta sai ta tura min, ni kuma sai na sayo musu.
Aliyu Chemist, wani shago ne mai ɗan girma da ake sayar da magunguna manya da ƙanana, wani lokaci ma har duba marasa lafiya suke yi, ana kwantar da su ana ƙara musu ruwa. A nan nake sayayyar duk wani magani da nake buƙata, don haka ina ware musu kuɗi saboda duk matsalar magani ta gaggawa. Babanta kullum a cikin sa min albarka yake, tare da yi min fatan Allah Ya bamu zaman lafiya, yana nuna min ƙwarin gwiwarsa na ganin ko bayan ransa zan iya riƙe masa ýar sa, da yake matuƙar ƙauna.
Wata uku suka yi a asibiti ana jinyar babanta. Bayan ya koma gida, ya bani umarni na tura da magabatana, akan batun aurenmu. Wannan lamarin ya yi matuƙar faranta min rai, na ji daɗi sosai, domin ni daman a shirye nake. Tuni na haɗa kayan lefe na. Ba a jima ba kuwa aka yi auren mu.
Cikin ikon Allah, wata shida da auren mu na samu aiki tare da Hukumar Kula da Kadarorin Gwamnati. Tabbas abin ya yi min daɗi, domin daman sana'ar da nake dogaro da ita ta sayar da lemon sanyi ce, kuma na kusa cinye ɗan jarin da nake juyawa saboda jinyar baban Hanifa. Muna da shekara guda da aure, Hanifa ta haifi 'yan biyu mace da namiji. Haka ya sa na yake shawarar a sanyawa namijin sunan babanta, ita kuwa macen a sa sunan babarta. Haka kuwa aka yi kowa ya yi farinciki, duk kuwa da ýan'uwana basu so hakan ba.
A hankali nauyi ya fara yawa a kaina, saɓanin a baya. Har yanzu ina kula da iyayen matata, ga nawa iyayen, ga kuma iyalina. Kun san yadda goyon ýanbiyu yake da wahala. Yau da gobe jarin da nake juyawa a kasuwa ya fara baya, albashina kuma ba wani isa ta yake yi ba. Ina cikin wannan hali ne kuma, Allah Ya sake jarabta ta da wani ibtila'i, inda aka dakatar da ni daga aiki, sakamakon wani bincike da ake yi a ofishin mu na ɓatan wasu kuɗaɗe. A lokacin da wannan matsala ta same ni, matata tana da sana'a kuma Alhamdulillah Allah Ya bata luɗufin kasuwa, hakan ya sa take tallafawa da lamuran gida. Bayan wani lokaci, aka mayar da ni wajen aiki, al'amura suka fara warwarewa a hankali. Ba a fi wata biyu da komawa ta aiki ba, matata Hanifa ta fara tambayata akan kuɗin da take bi na, tana mita kan cewa wai kullum sai in riƙa cewa zan bata, amma ban iya biyan ta ba. Kuma tana da gaskiya, domin abin da nake samu ba ya isa ta, saboda yawan basussuka da ke kaina.
Wata ranar Litinin da daddare ina kwance ta tashe ni, kusan sha biyu da rabi na dare tana tambayata kuɗin ta. Saboda wai ta ji an ce, an ƙara min albashi, sannan an biya ni kuɗaɗen albashina da aka riƙe, lokacin da aka dakatar da ni a wajen aiki. Na nuna mata gaskiya ba a bani duka ba, amma tabbas an bani wani abu a ciki. Atafau, Hanifa ta ƙeƙasa ƙasa, fur ta dage kan sai na biya ta kuɗinta, raina ya yi matuƙar ɓaci. Wata kalma da ta gaya min ce ta ƙara harzuƙa ni, raina ya ɓaci. Duk da haƙuri na sai da ta yi sanadiyar da na saketa, har saki uku!
Tambayarta na yi na ce, "Yanzu duk abinda na miki a baya kin manta, har ki ke neman ɗaga min hankali akan kuɗinki?"
Kalmar da ta fito daga bakinta ita ce tasa na yanke shawarar sakinta.
"ME KA TAƁA MIN?
Ƙarshe