GAJERIUN LABARAI

SHI NE NASARATA

by @jikankaila2014

SHI NE NASARA TA 

Daga Jibrin Yusuf Kaila 

Gun taron yayi tsit:ana sauraren Lubabatu Audu Gwarzowar gasar hikaya,tana bada labarin kalubalan da ta fuskanta, fara rubuce-rubuce ta,kafin ta samu nasarar lashe kyautar BAKANDAMIYA READING CLUB,wanda ake yi duk karshen shekara a December.

Ta cigaba da bayani,kamar yadda aka umarce ta,ta bada labarin kalubalan ta fuskanta a rubuce-rubucen da ta yi.

"Hakika lokacin na fara rubuce-rubuce a gidan mu:ban samu karfin gwiwa ba,don gani ake shirme na ke yi,duk lokacin da ina rubutu sai ana ce mun 'yar takarda da biro,har sunan ya fara bina 'yar takarda,da kyar Babana ya hana sunan,saboda zane-zane da rubutu da na ke.

Ni mace ce wanda ta kasance mai yawan karance-karance littatafai na (Novel) da na Hausa :Irin Magana jari,Uwar gulma, littafin iliya ɗan mai ƙarfi,haka idan Babana ya gama karanta jarida Aminiya ina karanta labarin Bashir Yahuza Malumfashi da yake wallafa a jaridar,a cikin labarin da yake wallafa akwai Zinatu Matar Gwamna,Labarin faɗi-Tashin Yar Gwagwarmaya dadai sauransu".

                                 
 Ta na zuwa karshen gabar nan,sai aka kwashe da dariya aka fara kira 'yar takarda!!!.ta yi gyara murya ta cigaba da bada labari kamar haka.

"Wani abu da ba zaman ta ba manta a rayuwa ta ba shine:A lokacin da na wallafa wani gajeren labari a (Social Media)wanda silar labarin sai da aka kama ni,wanda sai da aka kai ni Gidan Ɗan kande (Prinson) Alkali ya yanke min hukuncin gidan Ɗan kande, na wata biyu da sati ɗaya, don na fito da wani siri akan yaudara da ake yiwa al'umma akan Chairman ɗin garin mu.

Aka mun bita-da-kulle,hakika wannan abu ya tsaya mun a rai,sai da na ji rubuce-rubucen da na ke,ya fita daga kai na, ji na yi na tsani rubutu a rayuwata.

Hakan ya ƙara hura wutar tsanar da ake yi da rubuce-rubuce da na ke, domin daman gani ake wahala na ke yi,wanda ake ga ina bata lokaci.Da maida hankali na yi akan abu da zai amfane ni, ba rubuce-rubucen da na ke,dana fi haka..

Wasu chalama suke yi a gaba na da bayan idona...

Amma samun shigowar Abban Humaira rayuwa ta,ya bani ƙarfin gwiwa a rubutu na shine silar tsani cigaba rubuce-rubuce na."
 
Tayi gyaran murya ta cigaba, lokacin da gun taron yayi tsit ana sauraran ta.

"Ko shiga na Gidan Ɗan kande,ya yi kokarin ganin cewa an fito dani,kuma ya kashe kuɗi masu yawa, wanda har dangin suka ce na asiri ce shi....

Hakika samun mijin nagari:tabbbas dace ne, kuma rabo ne,abin jin daɗi ga kowace mace a rayuwar duniya.Samun Abban Humaira wani jirgi ne na musamman,wanda ina fatan" kowace mace ta samu mijin kamar Abban Humaira.

A yau ina bisa durkusa gwiwa ta ƙasa a gaban mijina, Ina sanar da ku cewa wannan kyauta da na samu, Ina mika ta ga mijina Baban Humaira domin SHI NE NASARA TA".

Ƙarshe