GAJERIUN LABARAI

WASIYAR KANWATA

by @jikankaila2014

WASIYAR KANWATA 

Daga Jibrin Yusuf Kaila 

Wani abu da ya faru dani da ƙanwata ,wanda ba zan iya taɓa mantawa dashi ba, wanda sai da ta mutu abin yake damuna, wanda har yanzu inde na tuno, ko da dare ne bana iya komawa barci sai bayan sallar asuba, saboda damuwa, har abin ya fara taɓa lafiyata, kusan likitoci sun gargarde ni da na cire shi a raina, amma ina saboda ya zama jiki a rayuwata. Kusan abin yana faruwa agun Yayu maza da ƙanansu mata, zan faɗi wannan abin ba don na tona kai na asiri ba , sai dai don na faɗakar da yan uwa maza, na san maza zasu ɗauka kamar shirme amma game tunani yasan abin babban matsala ce da take damun iyali. Cikin abin da bana so raini hakan yasa ban fiya wasa da yara ba, kuma hakan a fahimtata wannan ra'ayine dade ne,ina ɗaukar tamkar shi ne tunani mai kyau wanda hakan ya saɓa da ra'ayina, don fahintata mace tana da raini kuma shi yasa bana wasa da yara dama ƙanwata, , bana sakar da fuska ta balle ta ga fuskar wasa,don ban da gaisuwa sai dan meko min da ungo kawai abin da yake haɗa mu da ita kawai.

 Duk da lokuta da dama , Ummata tana mun gargadi akan wannan hali nawa, wani lokacin sai ɗan gyara wallahi daga baya sai na watsar kun rai da hali zanan dutse. Sau da dama tana son ta zo guna mu yi hira , sai dai ban sakar mata fuska ba, idan ta zo ta na fara mun hira yanzu zan ce "Bani waje", don ita macece mai zance sai dai wata rana zancen yana mun daɗi amma haka nake basarwa .Na yi wata budurwa da ta gwarani sosai kuma Allah ya jarabeni da son ta, na yi tunanin duniyar nan wata hanya zan bi na ga na shawo kan budurwata. Kawai wata zuciyar tace na je gun ƙanwata ko zata iya taimaka mun, amma wata zuciyar tace " kar ka je zata iya raina ka" Daga baya kawai na yanke shawarar na je, ai kuwa da ta bani shawarwari da gargadi akan wasu halayena da nake yiwa budurwar tawa, abun na ga ya mun amfani, don yanzu matar dake gidana, Ita ce budurwar da ta bani shawara akanta.

Mu biyu iyayen mu suka haifa , kuma tun daga kan mu , basu sake samun karuwa ba, an sha faɗa mahaifinmu ya ƙara aure, amma yace mu din ma ya ishe shi, kawai Allah ya mana albarka, yau kusan mahaifina ya kai shekaru 68 ita kuwa mahaifiyata ta kai shekaru 54 kuma haka suke rayuwa tare da mu. Kwatsam wani sai yanayinta ya fara sanjawa har ta kai da kwanciya ,wasa-wasa har ana kai ta Chemis kawai sai aka ga rashin lafiyar bana Chemis ba ne, kawai na yanke shawara akan a kai ta asibiti, don duba lafiyarta , da mu ka je likita sai ya tura mu Lab, don ayi test results ai kuwa yana fitowa samakon, abin da likita ya faɗa mana, ya matuƙar ya sanja tunanina, kusa lokacin har sai jiri ya fara iɓa na. Mahaifiyata kuwa sai da aka kwantar da ita a asibiti, shi kuwa mahaifina abin de ba a ce komi don jininsa sai da ya hau.Na takaice mu ku gajeriya wai tana juna biyu ba aure gare ta balle ace a gidan mijin ta kwaso. A fisace na je na same ta na ce" Wannan juna biyu na waye!!" kafin ta bani amsa mutane sun rike ni don a lokacin itama a kwance take na kara faɗa mata "Wannan juna biyu na waye !!!" amsar da ta bani shi ta kara maimaita min wato " Abokinka ne !! " na kara faɗa rai bace "Abokina!!! Waye abokina.. amsar da take kokarin faɗa mun mutane suka dakatar dani tare da jana don fita dani daga Ward da take, ba a jimawa ba kusan 4 hous kawai sai na ji an kirani, wai ta rasu.Na yi salati kawai ban tsinci kai na ba sai bayan da aka yi suturata harma an binne ta ...

 Babban abin da yafi ta da mun hankalina shin waye ya yiwa ƙanwata ciki!!! .Kwana uku da rasuwarta bayan an watse kusan nima na ɗan ware jikina yayi sauki, na shi ga ɗakinta, katsam ina dube-duben wani abu da ummanmu ta aike ni, na ɗauko a ɗakin nata , kawai sai na ga wata takarda mai ɗauke da sunana mai suna WASIYAR KANWAR KA tare da sunana, na ɗan yi tiris ,na ɗauko jikina sai ya fara karkarwa, haka na yi ta maza da na bude ...

         WASIYA TA GARE KA YAYANA

Assalamu alaikum 

Cikin girmamawa tare da yi maka fatan tsawon rai, hakika ina ƙaunarka da ƙaunar da kowace ƙanwata take yiwa Yayanta,ina girmamaka kuma kai ma ka sani , ina sauke duk wani haki da kowace kanwa ta gari take yiwa Yayunta, amma kai kasa sauke nauyin da Allah ya dora maka a matsayin ka na yayana, don saboda gudun raini, ka kasa fahintar raini da ja a jiki. Na san za ka ji ko kuma za ka gani ina ɗauke da juna biyu, kuma abokin kane yayi mun hakan ya faru saboda rashin jana a jiki ya jawo haka, nasan zaka sha mamaki, idan na faɗa ma zaka sha mamaki.A garin neman wanda zai bani shawara da kuma wani matsalata take damuna...

Wasiya ta farko itace a hukunta shi da hukuncin mai tsanani, don fyaɗe ya mun, kuma ina neman gafara da iyayena dasu yafe mun , kai ma ka yafe mun...

Sauran bayanin ka duba kasan jakata zaka ga hotonsa ....

Daga Ƙanwar mai son ka har abada

Na gode 

Sai dai abin takaici na yi duban duniya, amma ban ga hoton abokina, da ya yi mugun aikin ba, kuma ya ci amanata amma duk dakin sai da na bincika kayan dakin, amma ban gani ba, yanzu kullum duk sallah sai na roki Allah ya tona masa asiri....


Ƙarshe