Chapter 9
*_PAGE9️⃣_*
Jin yadda na turo ƙofar yasa ya dakata daga yunk'urin rufe ƙofar da ya ke ya ɗago idanun sa da suka rine suka yi wani irin ja ya watso min,
in ba gizo idanuna ke min ba sai naga kamar har wasu irin ruwa ne suka taru cikin idanun sa saboda tsananin fushi da masifar dake cin sa,
Sai dai sam hakan bai firgitani ba inda dane nasan hakan zai firgita ni yanzu Ina jin na wucewa.
Cikin Wata kakkaurar murya yace
"lafiya kika biyo ni?"
Ban bari ya ƙarasa ba, raina a matuƙar ɓace nace cikin d'aga murya
"Haidar me Umar ya maka da zaka ture shi harda hauri saboda rashin Imani wanne abu muka maka a rayuwa da ka tsanemu yau tsanar har ta kai ka fara taɓa lafiyar ƴaƴan cikin ka, haba mana ka dawo da hankalin ka Haidar Me kake so damu Ina kake so mu shig.."
Ban k'arasa magana ta ba naji ya sauke min wani irin gigitaccen mari sai da naga wuta ta gilma min, ga wani irin rad'aɗi da uban zafi da suka ziyarci fuskata, jina na yi kamar bani da kumatu a tare dani, nasa hannu na shafa kumatun har ya tashi ga zafi kamar wadda aka watsawa wuta.
Shi kanshi da yayi marin wata iriyar ƙara ya saki yana yarfe hannun shi yaja baya ya watsi min rinannun idanun shi ya nunani cikin kakkausar murya yace
"Wato kinyi abinda bazan iya taɓa jikin ki ba kenan ke gogaggiya ko?"
Ni dai ina tsaye mamakin marin da ya sauke min bai gama saki na ba, me kenan ko dai wani abin suka ƙara masa da suka birkita shi, Innanillahi wa inna ilaihirraji'un kawai nake iya furtawa saboda tashin hankali neman hawaye nayi na rasa a idanuna.
Ganin yadda nake kallon shi yasa ya hasala tare da cewa
"Wallahi Salman na tsane ku na tsane ku ku taimaka min ku tattara ku bar gidan nan dan Allah, ji nake kamar in kashe ku ko zan huta da abinda nake ji ki taimaka min Salmah"
Ya ƙarasa faɗar hakan tare da zube gwiwowin shi a ƙasan wajen ya saki wani rikitaccen kuka tunda nake da shi ban taɓa ganin ya yi kuka ba, sai hakan yasa naji gaba ɗaya na shiga wani hali musamman yadda ya ke shashsheƙa kamar wani ƙaramin yaro,
Nan da nan wani tausayin sa ya kamani na rasa me ya kamata nayi sai kawai na foshe shi ina ji a raina koma meye sai dai ya faru bazan bari a raba mu ba.
Ban kai ga kaiwa wajen shi ba ya ɗago rinannun idanun shi cikin karaji yace
"Karki ƙaraso nace dan Allah" yana wani layi kamar wanda ya sha kayan maye,
ban dakata har sai da na ƙarasa wajen shi, babu zato naji anyi cilli da Ni kamar wani kwano na bigi bangon na faɗi kaina ya bugu, wata ƙara na saki saboda azabar data ratsani, kafin na miƙe yayo kaina ya kawo hannun shi ya ɗago Ni da nufin duka na sai dai bisa dole ya sake ni dan yadda ya ji shokin ya ja shi.
Ganin yadda ya haukace yana neme neme sai tsoro ya kamani na tashi a rikice ina neman hanyar gudu dan tuni Umar shima ya ɓuya a bayan kujera.
"Ba zaki gudu ba ko Salmah?" yace tare da nurar hanyar kitchen nasan madoki ya ke nema, ganin yanayin da ya ke magana kaɗai ya tabbatar min an koma gidan jiya ko nace fiye ma, Haidar dai baya cikin hankalin sa sam baya hayyaci sa, ɗan mutumcin da muka fara kenan babu shi yanzu ai ban bari na kai ƙarshen tunanin ba ganin tahowar shi gadan gadan riƙe da muciya yasa na fusgi hannun Umar ganin bala,i Ido,da Ido nayi ɗaki na a guje ina shiga na rufe ƙofar tare da barin makullin a jiki ina sauke wani irin numfashi zuciyata na bugawa da ƙarfin gaske,
na koma na mak'ale jikin bango jikina na wata iriyar rawa Ina zaro Ido, bugun ƙofar ya shiga yi a haukace yana faɗin na zo na buɗe masa Kofar sai ya illatani yau sai yaga ƙarshe na daga ni har Ƴan iskan yaran da na cika masa gida dasu duk sai ya kashemu kowa ya huta.
Rawa kawai jikina keyi addu,o,a kuwa babu kalar wadda banba dan daga na kamo wannan bana sanin na saki sai na kamo wata, hankali na a matuƙar tashe yake.
Nishin da Salim ya ke ne yasa na kai kallona kan gadon inda na kwantar da shi tun dawowar mu, da sauri nayi kanshi ganin abinda ya ke na tallafo kanshi na ɗora a cinyata gaba ɗaya ya fita cikin hayyacin sa, dan wani irin numfashi ya ke yana riƙe da kansa da hannuwan sa duka biyun
yana wasu irin sambatu marasa kai.
Jijjiga shi nake ina kiran sunan shi Salim Salim Ina bai ma jina sai wani irin gurnani da ya ke abin babu daɗin ji,
Cikin wani sabon tashin hankalin na rungume shi tare da fashewa da wani k'akk'arfan kuka wanda ya taso daga ƙasan zuciyata, cikin kukan nake faɗin
"Ya Allah ka sassauta min halin da nake ciki ya Allah ka kawo min agajin ka da taimakon ka ya rabbi bazan iya ba kaine mai iyawa bayin ka ya Allah ka ji'banci lamarin baiwar ka Salma bani da gata sai kai Allah bani da kowa sai kai Allah ka yaye min abinda ke damuna ka kareni da yarana da mijina daga dukkan sharrin masu sharri Allah kana ganin su kana jin su Allah kai Kasan yadda za ka yi dasu Allah na kawo ƙarar bayin ka waɗanda ke cutar dani Allah su cutar dani Allah sun rabani da mijina sun raba uba da ƴaƴan sa Allah ka kawo mana ɗauki"
Cikin fitar hayyaci nake kukan har lokacin ina jin yadda Haidar ke bugun Kofar kamar zai ɓalla ta,
Ganin yadda Salim ke ƙara ke yi yasa wani tunani shiga ta da gudu na tashi Allah ya taimake ni naga kofin da na bawa Na'im shayi dashi ɗazu kafin mu fita,
toilet na shiga na tara kofin a famfo na d'ebo ruwan na dawo na zauna addu'o'i na shiga yi ina hurawa a ruwan na kama bakin shi da ƙyar na shiga zuba mai ruwan yana shanye da wasu na bin gefe suna zubewa na shafa mai sauran da ya rage a fuska, cikin ikon Allah sai gashi ya fara sauke ajiyar zuciya ya saki hannun da ya riƙe kan nashi dashi a hankali ya rufe idon shi.
Wata ajiyar zuciya ce ta kubce min ganin kamar barci ya ɗauke shi yasa na sauke kanshi,na kwantar kan gadon ina shirin sauka naji ya riƙe hannuna, da sauri na dawo na zauna na shiga dadda'ba shi Ina "Salim Salim" sai naga barci ya ɗauke shi ban tashi ba sai da naga yayi nisa tukun na lalla'ba na sauka zuwa lokacin mai buga ƙofar ya gaji ya tafi.
Na zauna nayi shiru ina tariyo abubuwan da suka faru lafiya muka rabu da Haidar, to me kenan hakan ke nufi? sun ƙara birkita min shi kenan ko yaya? dama nasani ba zasu barmu mu huta ba ba zasu k'yalemu ba,
amma Kuma shi Salim fa meya same shi? sauri nayi wajen kautar da tunanin da naji ya faɗo min Ina neman tsari da hakan, na sawa raina kawai buguwar da likita yace yayi ne ta haddasa masa hakan,
Tunani me ya kamata nayi na fara meye mafita akan zamana gidannan ada Inna zauna na jure duk wata wuya da cin kashi saboda yarana da kuma zaton watarana komai zai koma dai,dai a yanzu fa? yaya zanyi tunda ya fara neman rayuwar mu, ga wata irin unguwa muke da babu wanda ke shiga harkar mu,
zaman me zanyi?
Shin zaman jiran ya kashemu zanyi kenan kowa ma ya huta ko kuwa yaya?
ko mafita zan nemawa kaina mu samu mu tsira da rayuwar mu, haƙiƙa ina son na rayu kodan innemi yafiyar waɗanda na ɓatawa ban sani ba ko hakk'in hakan ke bibiyar rayuwa ta, Astagfurullah na furta ina ƙara tubarwa Ubangiji na akan irin wautar dana aikatawa rayuwa ta a baya.
Tunawa da banyi sallar isha'i ba yasa na tashi na shiga toilet na yo alwala jikina duk ba ƙwari na tada sallar ina layi saboda tsabar yunwar da nake ji ga gajiya,
Ina idar da sallah Umar da dama tuni yayi barcin tsoro ya farka ya dasa min kukan yunwa yake ji.
Tashin hankali yanzu me zan bashi yaci bama shi kaɗai ba dukan mu muna buk'atar abinda zamu sawa cikin mu Amma tayaya Ina zamu samu?.
Lallalashin sa nayi da ƙyar yayi shiru na rungume shi ina shafa kanshi cikin ikon Allah na samu ya koma na kwantar da shi na tashi na koma kan sallaya na shiga kaiwa Allah kukana yanzu nasan babu abinda zai fitar dani sai Allah.
*HAIDAR*
Ganin duk irin bugun da ya ke wa ƙofar taƙi buɗewa yasa ya juya zuciyarsa na tafasa yana jin jikin sa kamar ana hura masa wuta ya nufi ɗakin sa, yana shiga ya zube kan gadon shi hannayen sa duka biyu dafe da kanshi yana jin kamar zai rabe biyu, ga ƙafar shi da ke masa wani irin radaɗin zafi da zugi ga wata yunwa da ya ke ji abubuwan suka haɗu suka masa rubdugu, nan da nan wani zazzafan zazzaɓi ya rufe shi ya shiga rawar sanyi yana son jawo bargo ya lullu'ba amma ya kasa motsawa baki ɗaya.
Ina Nan zaune kan abin sallah har aka kira sallar farko, na na tashi ina jin jikina kamar wadda ake turawa na nufi ƙofar dan na fita na nema mana abinda zamu ci tunda bazai yiwu muyi ta zama a haka ba, sai da na rufe yaran ta waje na zare makullin na soka a cikin rigata, na lalleƙa farlon sosai naga babu kowa tukun na fito saɗaf saɗaf na nufi kitchen, kallon ƙofar ɗakin shi nayi na ganta a rufe alamar bai tashi ba, cikin hanzari na ke aiwatar da komai na a hankali dan kar aji motsi na.
Nan da nan na ɗora ruwan zafi na dafa farar taliyar leda biyu dan na riga dana tsara abinda zanyi, ina yi ina leƙawa farlon ko dan gudun samun saɓani, shayi na dafa da yaji kayan ƙamshi na juye a flask na d'ebar masa taliyar kaɗan na ajiye da shayin dan ina son gwadawa ko abinda nake son yi zai yiwu, saɗaf saɗaf na wuce ɗaki da duk abinda nasan zan buƙata na maida ƙofar na rufe ina sauke ajiyar zuciya, lokacin an fara kiran Assalatu dan haka alwala nayo bayan na idar da Sallah tashi yara mu kayi zaman mu a ɗakin sam banyi gigin ƙara lek'owa ba.
Duka wunin ranar a ɗaki na muka yi shi, duk son Umar da yawo bai ko nuna yana dan ya tsorata tun abinda ya faru jiya,
Babban tashin hankali na Salim da ke ta kukan kanshi zai fashe duk ya rikice min na rasa ina zan sa raina naji daɗi, daga karshe na yanke in dai ya fita Masallaci zan ɗauki yaron na maida shi asibiti a duba shi.
Haidar bai farka ba sai wajen ƙarfe shida na safe, ya mik'e da ƙyar yana jin kanshi na sara masa kamar ana buga masa guduma,
A hankali ya sakko daga gadon yana jikin shi babu ƙwari tuna bai yi Sallah jiya ba yasa ya nufi toilet cikin hanzari yana son tuna abinda ya faru amma sam ƙwaƙwalwar shi ta kasa tuna mishi komai,
Ya dai san lokacin da ya fita gida har zuwa had'arin da ya faru da suka fita siyayya, har ya kusa bige wani tsoho da ya shigo gaban motar shi garin ya kaucewa mutumin ne motar ta ƙwace masa daga nan bai ƙara sanin me ya faru ba, sai yanzu daya farka ya ganshi a gida, duk tunanin shi bai iya tuna komai ba mamakin shi daya waya kawo shi gida?.
Yana idar da Sallar ya tashi ya fito farlon, yayi mamakin ganin shi wayam kamar ma babu wanda ya fito a cikin su, a hankali ya nufi ɗakin Salmah ya tura jin shi a rufe yasa ya fara k'wank'wasa ƙofar.
Ina zaune kan Salim a cinyata ina faman tofa masa addu'a saboda har zabure zabure yake yanzu, in na masa addu'ar ne yake ɗan samun sauƙi ya daina.
Jin ana bugun ƙofa yasa naji hanjin cikina ya murɗa a tsorace, nayi shiru ina kallon ƙofar naƙi magana,
Haka ya dinga k'wank'wasawa ya fara kiran sunana nayi biris na ƙyale shi, yayi zaton ma ko basa ciki ne amma jin motsin Salim da sambatu da ya ke yasa cikin tashin hankali ya fara bugun ƙofar, dan a hankali abubuwan da suka faru suka fara dawo mishi har yadda yayi jifa da ita komai ya fara dawowa kan shi dalla dalla.
Dafe kanshi yayi cikin tsananin damuwa ya shiga mata magiyar ta taimaka ta buɗe ya na son ganin Na'im ne dan Allah.
*****
_*😍MAMAN 'DAN ALBARKA CE😍✍️✍️*_