PAGE 31--35
by @swrites22
" na mareshi amma saboda karya kunyata gaban friends dinsa yasa yace shi ya mareni ni kuma yake son na kunyata well tabe baki tayi tare da riqe waist tana gyara tsayuwar ta , kamar daga sama sukaji karar mari tass tass dan babu wanda ya lura da lokacin data juya kawai karar Marin sukaji, naif da Marin yazo masa unexpectedly har saida yasa shi dafe bango nuna shi tayi da hannu tana fadin " ba ko wani gaja irinka nake shiga harkar sa ba saboda ba komai nake dauka ba, ba ruwana da mutum ko shi waye allah kawai nake tsoro na tsani a yimin karya wanna marin na maka shine saboda ya zama warning a gareka kan karyar da kayi dan kawai nai man suna ko , toh bari kaji don't you ever cross my line or else I will embarrass you fiye da yadda baka zato bakasan halina ba ko murmushi tayi sannan ta ci gaba I'm sure by now sai dai kabawa wasu labari stupid kawai tana gama fadin haka ta juyo da sauri aka fara watsewa kallon najwa tayi wacce ta dafe kumatun ta da hannu biyu a tsorace kamar ita aka mara , Kamo hannun nata tayi ta nufi gate dan dama itace last paper dinsu.
Suna isa bakin gate din ta saki hannun najwan da har lokacin take cikin shock jan hancinta tayi da dan karfi , yar kara tayi " auuchhh miye ni kuma na miki zaki ciremin hanci , wrist watch dinta ta duba sannan ta maida dubanta ga najwa tana fadin " let's go nasan yanzu driver na waje duk da lokacin tashin bai yi ba amma tunda mun gama me za muyi .
Binta najwa tayi kamar agwagwa da yayanta suna fita suka tarar da driver da securities na jiran su , bayan sun shiga motar ne seena take bawa najwa labarin abinda ya faru shuru najwa tayi tana sauraren ta har ta gama sannan ta kalleta tana fadin "amma odahalf ya kamata ki ajje wanna halin a gefe wallahi Kar azo a samu matsala nasan wanna shine mai laifi amman dama ina taso na miki magana whl ki daina shiga fadan da ba naki ba wanna yan class din namu da kike gani suna wani zuga ki kina tare masu fada sufa kallon wawiya suke miki wadda bata san Inda ke Mata ciwo ba, wani banzan kallo ta watsawa najwa ba tare da tace komai ba.
murmushi najwan tayi "kwarai da gaske mai sa su baza su tarewa kansu ba karfi kika fisu ko baki kika fisu kawai dan kinga suna shishshige Miki suna nuna suna sonki ke kuma saiki hau kai ki zauna bafa kowa bane yake sonka har cikin zuciyar sa dan yana nan² da Kai amma maganar gsky banajin dadi yadda ake dukan ki tare da baki punishment please ki daina biye masu ki nutsu dan Allah .
tabe baki tayi tace " umm a farko kamar matsala naji kin ambata ko?
" eh matsala mana kinga idan principal din mu ya gaji da baki punishment ya fadawa daddy abinda kikeyi fa ko yayi suspension dinki whl daddy ba zaiji dadi ba ki daiyi tunani.
juyar da kanta tayi wajen window ba tare data sake cewa komai ba riko hannun ta najwa tayi "my sister please promise me kin daina shiga abinda ba ruwanki and kinga abinda ya faru yau wasu da gangan ma zasu sake tsokano ki ni inaso kawai kiyi minding business dinki muyi abinda ya kaimu ko a class din ya zama yadda kike wa mazan haka zaki na treating Matan ki dai na sake masu fuska ki nuna masu kema yanzu kinsan ciwon kanki.
" naji naj
"ba naji zaki ce ba cewa za kiyi u promise shuru ta sake yi , bata fuska najwan tayi kamar za tayi kuka tace odahalfffff magana fa nake juyowa tayi ta kalleta tare da cewa " I promise murmushi tayi tana fadin " that's my odahalf mata daya a gidan emir daga ke ansa sakata, hararar ta tayi ita kuma tasa dariya suka cigaba da wata hirar har suka isa gida.
Bude kofar motar tayi ta fita ba tare data jira naj din ba tun daga kofar parlour ta cire mini hijab din tare da cizge ribbon din gaba daya dariya najwa dake bayanta tayi da fadin Kai odahalf bakya jure zafi ko kadan.
" ke barni kawai yadda ake ranar nan jina ke kamar nayi ihu whl takarashe tana Kara sauri dan ji take kamar ta kyafta ido ta ganta cikin falo saboda ranar da ake kwadawa rikota najwa tayi har tana kokarin faduwa tayi saurin dafe bango tana fadin " ke naj kinyi hauka ne kike kokarin yasar dani kasa miye .
hararar wasa ta aika mata tare da cewa " ah ah kin manta asibitin mahaukata ne a kaina ke wai bakiyi observing kamar muna da baki bane.
" Tho su ta zuwa mana ina ruwana ko wurin mu suka zo
"Ke fa matsalata dake kenan
"Tho kuma daga kinga baqin mota sai kice muna da baki
"Auwoo tho ashe ma kin gani
"Eh nagani , ke har kin manta ne last week ya adnan ke cewa sabbin motocin da daddy ya saya sun karaso har yace muje mu gani lokacin Muna karatu muka ce masa sai washe gari kuma muka manta toh inajin ko fita zaayi da su ne kuma ma in banda abinki ke da kikasan kina da yaya sarkin kwashe kwashe miye na maganar ta fadi tana shige wa parlourn.
rufa mata baya tayi tana fadin "Ke ai ni na ma manta whl kwata² sai yanzu ma da kika tunamin.
" Ta tabbata Kin tsuf........kafin ta karasa taji ihun najwan daga bayan ta tana fadin oyoyo oyoyoooo yayana finally our ya sadam is back maqalewa tayi jikin bango saboda yadda ta tsorata da ihun najwan da tuni ta wuce wurin yayan nata
Wani siririn tsaki taja ciki ciki tana bin mutanen dake parlourn da kallo, wani irin faduwa gabanta yayi lokacin da tayi Ido hudu da sadam daya tsuro Mata ido tabbas ko a mafarki baza ta taba manta fuskar sa ba toh mai ya kawoshi nan wata zuciyar tace shine yayan najwa mana
"seenah baby! Baby!! firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data tafi tare da yin kasa da kanta ganin duk sun zubo mata Ido
"Kika tsaya anan karaso mana " Nina ya fada cira kafarta tayi ta fara tafiya daker tana sauraran yadda zuciyar ta ke bugawa da sauri² harta karasa cikin parlourn gaban kujerar da nina ke zaune ta zauna wurin kafarta tana Mai daura kanta akan lap din ninan .
adnan yace yau kuma shagwabar ta motsa Kenan murguda masa baki tayi ba tare da tace komai ba dariya yayi yana nuna Mata sadam da Ido dauke kanta tayi kamar bata gani ba .
Nina tace baby ga yayan ku emir dazun ya iso lokacin kuna school
bata fuska Najwa tayi da fadin shine nina ko ki sanar mana yau zai dawo ko, sadam dinne yace in ma an gaya miki me zakimin kuma ma yanzu ba gashi an miki suprise ba dariya tayi tana fadin ba haka dai na so ba but I'm delighted.
"Emir Ka gane wanna Nina ta fada tana nuna seenah
Dan shuru yayi kamai Mai tunani kafin ya girgiza Kai a hankali ya budi baki da fadin gsky ban shaida ba.
"Kaga illar rashin zuminci ko tho cousin dinka ce haseenah yar auntyn Ku Fatima tunda baka shaida ta ba .
"Kai niina yanzu wanna marar jin maganar ce ta girma haka Masha Allah, i can remember wani lokaci munje gembu tare da daddy ni ko hajjo ce ta aiketa ta karbo kunu ne ko miye kawai yarinyar nan ta shigo a guje ko lura da mutum batayi ba sai jin kwanon nayi a kaina gaba daya abinda ke ciki ya wanke min jiki
Dariya su Najwa keyi sosai ita da Adnan Nina kuwa murmushi tayi kawai yayinda Najwa tace emir kuma ya kayi
Adnan yace kema dai kinsan ba yadda zaiyi tunda hajjo na nan
Seenah kuwa kunya ce ta kamata kamar ta nitse a hankali ta dago idanun ta da niyyar satar kallon sa dai dai shima ya dago nasa kallon cikin idanun juna sukayi na dan wani lokaci kafin Seenah ta fara sauke nata idon cikin dan jin nauyin kamata da yayi tana kallon sa ciki ciki tace ina wuni ba yabo ba fallasa yace lpy y karatu.
Najwa tace emir kai da wa ko waya kake dan duk cikin su ba Wanda yaji ina wunin da seena ta fada shima ta hanyar daya gane saboda idonsa na kanta ne yaga ta motsa bakin ya kuma gane me ta fada , dan murmushi yayi kawai ba tare da ya sake cewa komai ba.
dago kanta tayi kamar za tayi kuka tace Nina zafiiiii .
najwa tace sai kiyi kuma duk AC dake parlourn nan kice wani zafi ke kenan bakyasan zafi ko kadan tho a kaiki bakin ruwa mana.
Nina tace to a garin su bata san wani abu wai shi zafi ba kullum a cikin lunlumi da iska me dadi suke ba dole yaji garin namu kamar tana oven ba.
Adnan ne yace ni tukunna ma ina hijabin fatan dai ba haka Kuka taho ba najwa tace ba gashi nan a hannun ta ba tun a bakin kofa ta cire shi.
" Ehh kwarai abun naki nayi ne "
tashi tayi tana fadin nina bayin watsa ruwa ko naji dadin jikina bacci ma nake ji whl.
**********************
Ko da ta shiga dakin gado ta fada kusan 20 mins ta rasa mai take tunani gaba daya wani iri take jinta kamar tayi kuka dakyar ta daure ta tashi ta fada toilet ta sakar ma kanta ruwa .
Tana fitowa ta zura doguwar riga marar nauyi tayi sallar azahar ta sake fada wa gado dan ko yunwa ma ba taji bacci ne kawai yake cinta dan tunda tayi sallar fajr bata koma ba tanata karatu, bata dade da kwanciya ba kuwa baccin yayi awon gaba da ita.
najwa kuwa tana tare da sadam tana bashi labarin abubuwan da suka faru da baya nan har da labarin seenah amma ta boye masa cewa matsayin seena a wajensa kamar yadda daddy ya hana fada masa , murmushi kawai yake tare da mamaki jin cewa har yanzu rigimar na nan a zuciyar sa yace in her appearance she looks so innocent saida aka fara Kiran sallar laasar sannan ya tashi yana fadin barin je inyi sallah in huta Najwa anjima ma karasa .
School bag dinta ta dauka ta wuce daki itama wanka kawai tayi ta shirya dan dama ba sallah za tayi ba , karasa wa tayi bakin gado ta dakawa seena duka a cinya tana fadin " ke tashi kika wani shigo daki kika makale cikin baccin tace "wai miye ne kika zo zaki hanani hutawa kuma .
" hutawa ahh lalle ke dalla tashi ace mijinki ya dawo kina nan kina bacci haka ake tarbar mijin kin wani zo kin baje
" bansan iskanci najwa whl zan Miki rashin mutunci idan baki barni ba na huta ba
" ai kuwa bazan barki ba saikin tashi whl ta fada tana hayewa tsakiyar gadon ta fara tashin ta haikan odahalf odahalffff seenah MATAR SADAMMM matar yaya tashi tayi ta zauna a hasale ji take kamar ta rufeta da duka ko ta huce "to gani na tashi saiki fadan uban mai zan miki , oh sai ma yanzu kika tuna dani ko toh ai saiki tashi ki koma Inda kika fito .
rike haba najwa tayi "toh fa yi hakuri bani nakar zomon ba ko rataya ma ban karba na gane Inda kika dosa tun dazu fa na shigo kina bacci saisa nace barin barki ki huta (tai mata karya) yanzu kuma naga anyi sallar laasar kuma kinsan ba kyau baccin yamma gashi ko sallar ma bakiyi ba, haba odahalf tawa ni kadai ai emir bai isa ya shiga tsakanin mu ba .
"mtweee ke kika sani kuma ta fada tana tashi ta wuce toilet tayi alwala ta fito , gaban mirror ta nufa ta daure gashinta da ribbon ta dauki hijab tayi sallah sannan ta kalli najwan tana fadin kinci abinci ?
" Inafa ai kinsan ban iya cin abinci ba tare da odahalf ba.
" hmmm kyade fadi gaskiya watakil ma kinci tare da dan gaban goshin naki.
"Allah banci ba najwa ta fada sounded serious "
" to tashi muje kanwar emir
"ke ban dake Kenan oh na manta ashe ke matar emir ce ta karashe tana dariya , ita dai bata kula ta ba ta ajje hijabin ta fice.
dinning suka nufa suka debo abincin a plate daya suka sa spoons suka koma parlour.
kadan seena taci abincin ta tashi ta hau kujera , kallon ta najwa tayi da fadin har kinyi mai kenan ?
" na koshi mana barni haka whl cikina ciwo yake ni na rasa ma meke damuna, cikin damuwa najwa tace sannu ko kinci wani abu ne dazu lokacin break ?
" ba abinda naci whl , tashi tayi dauke da plate din tana fadin sannu tho barin je in fadawa nina ko akwai wani maganin da zata baki .
Bata jima ba suka dawo tare da Nina karasawa kujerar da take kwance ta dukunkune kamar maijin sanyi Nina tayi tare da dago kanta ta dora kan cinyar ta tana fadin " subahanallah duk ciwon cikin ne haka , mai taci ne najwa ?
"whl ni dai tun breakfast da mukayi da safe ko da muka fito break ma cake kawai muka ci kuma na tambayeta ko taci wani abun daban tace ba taci ba yanzu ma mun debo abinci dan tsakura tayi kawai tace wai baza ta iya ci ba, dan shiru nina tayi sai kuma tace je ki hado Mata tea amma karki sa madara .
Da tho ta amsa tana wucewa bata wani dade ba ta dawo dauke da cup din tea ta mika ma nina karba tayi sannan ta tashi seenan ta mika mata "karbi kisha sai muje in duba miki maganin ulser ko itace take damunki, karba tayi ta kurba kadan tana Yatsina fuska
Nina ta sake cewa kafa Kai zakiyi ki shanye ki tashi muje daki abinda ba zafi ma sosai , daga cup din tayi ta shanye tana sake bata fuska sannan ta tashi tabi nina suka wuce dakin .
Saida ta sha maganin ta kwanta sannan ninan ta fice kitchen don in dai kwanan ta ne bata bari masu aiki kadai suyi wa daddy abinci saidai su tayata, najwa kuma ta zauna kusa da seena tana Mata sannu.
Ai maganin da tasha ma kamar kara Mata ciwon yayi murkususu kawai take tana kuka da gudu najwa taje ta Kira nina .
Rikota Ninan tayi tana fadin sannu har yanzun cikin ne ko hospital zamu je, ganin yadda take dafe ciki tana kamewa ya sata jawo wayarta dake gefen bedside ta dannawa Adnan Kira saidai wayar sa a kashe maida Kiran tayi zuwa Kan sadam ringing biyu ya daga ba tare da ta bi ta Kan sallamar da yake ba tace emir zo dakina yanzu Maza plz tana fadin haka ta kashe tana kallon seenan dake hawaye dan karfin kukan ma babu a wanna yanayin sadam ya shigo hankalin sa a tashe amma ganin Nina zaune lpy ya sashi sauke ajiya zuciya kafin yayi magana Nina ta rigashi da fadin duba min ita emir bari naje na sanar da daddyn Ku na dawo inaga gwara mu tafi asibiti kawai ta fada tana ficewa
Karasawa yayi gaban gadon Yana tambayar Najwa me ya sameta cikin rawar jiki tace ciwon ciki ne
"Ciwon ciki ! Ya nanata
Ganin tana kokarin fadowa kasa daga Kan gadon ya sashi matsawa kamar Mai shirin kama Kura ya tarota ta fado Kan hannayen sa ta fada kokarin gyara Mata kwanciyar yake ta cukumo rigar sa cikin fitar hayyaci tana kokarin cusa kanta a kirjin sa dan jim yayi kafin ya zauna bakin gado har lokacin tana riqe dashi kanta na Kan kirjinsa tana jujjuyawa jin shuru ya sashi kallon ta da sauri ya kalli Najwa dake hawaye itama yace ban ruwa yi sauri .
toilet ta nufa tsabar sauri a hannunta ta taro ruwan lokacin data kawo ruwan kokarin miqewa yake da ita a jikinsa hannayen najwan ya jawo gaba daya zuwa Kan fuskar seenan sai lokacin Najwa ta lura da Seenah suma tayi da gudu ta fita tana Kiran nina.
Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ruwan ya sauka Kan fuskarta idanunta a lumshe sai ga Najwa ta dawo tare da niina
Hankali tashe tace emir meke faruwa meya sameta
Saida ya harari Najwa kafin yace Nina ki kwantar da hankalin ki fa ba wani abu bane idon ta biyu
"Tho na fadawa daddyn ma yace doctor hashim zaizo ya dubata
"Ba damuwa niina kije ki zauna karki tada hankalin ki dan Allah
Zama tayi gefen su tana kallon seenan da har lokacin take kadandane kamar dodon Kodi tana sauke numfashi a hankali
Ba a fi min biyar ba doctor hashim ya karaso daddy ne ya Kira da fadin su fito falo doctor ya iso.
sadam ne ya daukota da kansa bisa umarnin nina suka fito a nan doctor hashim din ya dubata tare da Mata tambayoyi sannan ya bata magunguna yana fadin hajiya karku damu ba wata matsala bace period ne ya zo Mata kuma da alama wannan shine karon farko data fara saisa amma yanzu ga magunguna nan daga ta sha zata warware da izinin Allah
"Tho doctor mun gode fa Allah ya saka da alheri
"Ni ne da godia hajiya allah ya bata lpy " ya fada Yana daukan kayan aikinsa suka fice tare da daddy zuwa harabar gidan suka bar su Nina a nan
Da taimakon sadam ta sha magani kafin ya miqe kallon sa niina tayi da fadin kaje Ka sauya Kayan Ka kai ma
Zaiyi magana idonsa ya sauka Kan ash din rigar sa da tayi staining kallon seenah da idonta ke rufe yayi tare da kallon niina da takewa seenan sannu ya dubi Najwa da sauri ta juya fuskarta tana kokarin kunshe dariyar ta karta fito .
Bai Kara magana ba ya wuce Yana balle button din rigar yana kokarin shiga bangaren su Adnan ya shigo idonsa ne ya sauka Kan rigar ta sa "meya faru emir ya fada da damuwa Yana kallon sa
Ko kallon sa baiyi ba ya wuce Yana kokarin ganin ya cire rigar ba tare data taba fatar jikinsa ba kamar yabi bayan sa sai kuma ya fasa ya wuce ciki niina kadai ya samu a falo itama tana kokarin fita ganin sa y sata tsaya
"Nina meya samu emir Naga jini a jikin sa
"Lpy kawai tace tana kokarin wuce shi ya sake cewa amma Nina t........
"Sai kaje Ka tambaye shi tho tunda baka yarda ba
Da kallo ya bita har ta bar falon kafin ya daga kafadun sa ya zube Kan kujera Yana jawo remote.
da taimakon Najwa suka karasa dakin inda ta zame ta zauna a kasa tanajin ciwon na lafawa ita kuma Najwa ta nufi socket na heater ta kunna sannan ta wuce ta dauko Mata sabon pant da pad ta ajje Mata bakin gadon ta wuce bathroom din ta hada mata ruwan wanka ta fito a yanda ta barta a haka ta sameta cike da tausayawa tace " tashi kije kiyi wankan ko .
" ke nifa gsky ba zanyi wanka da ruwan zafi ba
Sakin baki Najwa tayi tana kallon ta kafin tace " eh lalle kin fara dawowa hayyacin ki amma idan kikayi wanka da ruwan zafin ai zai taimaka maki sosai kuma ruwan ma baiyi zafi sosai ba kawai dumi² ne I'm sure zai Miki dadi.
" ni dai da zafin nan bazan kara wani zafin ba ga zafin gari ga na ruwa sai kace Wadda take jego tho ko masu jegon yanzu sun waye basa wannan wankan azabar.
" toh ai kuwa saisa zakiga jikinsu baya karfi bare su samu isasshiyar lpy, ni dai whl ina fada miki dole ki rage san sanyin nan idan kina period ke ko haka kawai ma mace bai kamata ace komai sai mai sanyi ba hakan nada illa sosai ga lafiyar ta kece shan kankara kece shan ruwan sanyi kece wanka da ruwan sanyi kama ruwa da ruwan sanyi toh whl tunda wuri ma ki rage kafin ya fara tambayar ki, yanzu dai ki daure ki tashi kije kiyi wankan kar ruwan ya ida hucewa , yatsina fuska tayi ta kalleta da fadin "tho miye kuma kika shafa min a pad ?
"Man zaitun ne dallah kuma nima ai kinga ina amfani dashi .
"amfanin me yakeyi tho ?
dafe kanta tayi alamar gajiya da maganar tace oh yaaaa seenah amm toh saboda yana kariya wajen kashe duk wata kwayar cuta dazata sauka a pad din a maimakon ta koma jikin mutum wanna man zaitun din zai kashesu kuma yana karawa mace lpy ko da ace ba a lokacin period bane idan tana amfani dashi , hmmmm kawai tace ta dauki abinda najwan ta ajje mata ta wuce bathroom din tana tafiya a hankali saboda rashin karfin jiki.
Zama najwa tayi bakin gadon tana sauke ajiyar zuciya kai seenah seenah rigima ce whl sai kuma tasa dariya tare da kwanciya " ko ya emir yayi da aika aikar Seenah tashi tayi ta fita .
Tana kokarin sauka Nina na hawowa tace " naj ya jikin nata
" Da sauki Nina har ma ta shiga wanka
"Tho Allah ya Kara sauki , ni kwata kwata kinga tunanin hakan baizo kaina ba tunda ban taba jin tayi irin wanna ciwon ba tunda tazo
"Eh Nina kinga ai doc yace saboda na farko ne saisa ni nayi mamaki ma
" Ai ba abun mamaki bane najwa kinga ai kowa da irin yanayin jikin sa da kuma halittar sa ga maganin ta nan ni bari naje na watsa ruwa ta fada tana wucewa zuwa dakinta
komawa dakin najwa tayi ta zauna jiran ta harta fito ta shirya ta sake Ka mata tea tasha ta kwanta kwanciya suna hira kadan ² Kiran da najwa taji adnan na kwala mata ne yasa ta tashi ta fita.