TATSUNIYOYI

Epi-4

by @zahratulqalam51

TATSUNIYA.



By: 🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️


WANI SON MAI WUTA❤️‍🔥
Episode Four: Hukuncin Zargi


بسم الله الرحمن الرحيم



Al'ameen bai yi nisa ba, tuni mutanen Mai gari su ka iso kansa. 

Ba faɗa masa aka yi ba, ba tambaya, sai dai hannaye su ka riƙe shi, murya na tashi daga ko’ina, mutanen na cewa.

"Shi ne!"

“Kar ku bari ya tsere!”

“Wannan baƙon ne ya lalata mana ƙauye!”

AL’AMEEN ya tsaya cak, idanuwansa sun zagaya akan fuskokin mutane. 

Ya buɗe baki zai yi magana, amma hayaniya ta rufe muryarsa.

“Ku bar ni na yi bayani! Ban gane me ku ke tuhumata ba, ku saurareni!”

Amma wa zai ji? Tsoro ya riga ya rinjayi hankali.

Tafiya da shi su ka yi har zuwa gaban Mai gari.

An gabatar da AL’AMEEN a gaban Mai gari. Dattijo ne mai fuskar hikima, amma idanuwansa cike da shakku.

Mai gari ya ce da murya mai nauyi.

“Al’ameen, kai baƙo ne a wannan ƙauye. Tun bayan zuwanka, abubuwa marasa kyau su ke faruwa. Mutane suna tserewa, tsoro ya lullube gari. Me za ka ce a kai?”

AL’AMEEN ya ɗaga kai, zuciyarsa na bugawa, amma muryarsa ta kasance mai nutsuwa.

“Mai gari, wallahi ban san komai ba. Ban aikata laifi ba. Ban cutar da kowa ba.”

Hayaniya ta sake tashi.

“Ƙarya yake!”

“Yana ɓoye gaskiya don ya cutar da mu!”

“Matsafi ne! Ya zo ya tsafe mana ƙauye yana son gudu”

Mai gari ya ɗaga hannu sama.

“ayi Shiru!”

Kowa ya natsu, Mai gari ya sake cewa.

"Ina Habu? Fito ka maimata zargin da ka le akansa".

Sai Habu ya fito gaba, idanuwansa akan Al’ameen. Al'ameen ya yi mamaki, kamar ya taɓa kallon Habu à wani wuri, amma bai tuna ba.

Habu ya ce.

“Mai gari, ni da idona na gan shi tare da Malam Madu kafin ya bar ƙauye. Ni na ganshi da wancan mutumin, da Malam Auwalu… duk wanda ya haɗu da shi, washe gari sai ya bace!”

Mutane su ka yi ihu.

“Gaskiya ne!”

“wannan ma kaɗai hujja ce!”

AL’AMEEN ya girgiza kai, hankalinsa a tashe, abun da ya ke gudu ne ya afka da shi.

Mai gari ya kalle shi tsawon lokaci, sannan ya ce.

“Ko da ba ka yarda ba, tsoron jama’a ya fi ƙarfinka, hujjoji kuma sun bayyana.”

Sai Mai gari su ka tattauna a tsakani, sannan ya yanke hukunci.

“A kulle Al’ameen a kurkukun ƙauye. A sanar da jama’a cewa a cikin kwanaki uku za a yanke masa hukunci!.”

Maganar ta bazu a ƙauye kamar wutar jeji.

“An kama masihircin ƙauyenmu!”

“An kulle baƙon nan!”

*A gidansu Aisha* Labari ya isa kunnenta.

Duniya ta juya mata, ta shiga ƙunci tana faɗin.

“A’a… ƙarya ne! Ba gaskiya ba ne” ta furta da hawaye.

Amma mahaifinta ya ce da tsauri.

“’Yata, ki daina bin ruɗin zuciya. Wannan son da ki ke yi masa, wani son mai wuta ne kawai. So ne da zai cinye ki da mu kamar wuta, dama tun baya da manufarsa.”

Mahaifiyarta ta ƙara cewa da tausayi.

“Ki cireshi a ranki Aisha, Al'ameen ba alkhairi ba ne, yanzu haka ma ranar hukunci ya ke jira”

Aisha ta rushe da kuka ta ce.

“Ba zai iya aikata haka ba… wallahi ba shi bane! Zan je insame shi yanzu”

Ta so ta je ta gan shi, amma aka hanata. Mahaifinta ya ce.

“Ba za ki je ko’ina ba!”.

Kwana biyu sun shuɗe. Tun da aka kama Al'ameen babu wanda ya ƙara tserewa! Ƙauye ya fara samun natsuwa, amma natsuwa mai ɗauke da wani yanayi.

Ew faɗa a razane ya matso yana kallonta.

Aisha ta fashe da kuka. Al'ameen ya ji zafi a ransa, baya jin daɗin kukanta.

Ya rarrasheta. Shiru kaɗan ba mai magana.

Sai Aisha ta ɗaga kai ta dubeshi ta ce.


“Al’ameen, na san ba ka aikata ba, amma mutane ne sun kasa yarda. Yanzu don Allah… ka gaya min gaskiya. Shin da gaske ka haɗu da duk mutanen nan kafin abin ya faru da su?”

Ya sauke numfashi mai nauyi. Gaskiya ba a ɓoyeta, ya ce.

“Eh haka ne Aisha… na haɗu da su!.”

Aisha ta tsaya tana kallonsa da mamaki, me hakan ya ke nufi?.


_shin zargin mutane gaskiya ne?_
_ya Aisha za ta yi bayan jin wannan kalmar?_
 



🌹𝑍𝑎ℎ𝑟𝑎-𝑡𝑢𝑙-𝑄𝑎𝑙𝑎𝑚🖋️