BLOOD CROWN (THE HEIRS APPARENT)

PAGE _______59

by @swrites22




            SWORD OF FIRE KINGDOM🔥


Ƙaton prison ne daga can karshen yankin masarautar, prison ɗin zagaye yake da manya manyan katti ko riga ta kasa sakuwa a jikinsu sai sword da kuma Archery da suka rataya a wuyansu da kafaɗa in banda muzurai ba abinda suke. Ƙofar wani cell aka buɗe, wani kyakyawan matashin saurayi ne ya fito daga ciki, kallo ɗaya zaka masa kasan baya farin cikin fitowar sa daga jail ɗin, ba kuma alamun nadamar abinda ya aikata aka kawo shi wurin a tattare dashi. Honey skin tone ne dashi wanda hakan yasa na fuskanci duk yawanci kalar mutanan masarautar haka suke sai wasunsu da suka kasance dark brown, yana da broad chest, well built body, sharp eyes, pointed noes, sensible ears and strong arms. Ahmad Haisha'an kenan yaro ne matashi da bazai haura 28 - 30 years ba a duniya, shi ɗin ɗane ɗaya tilo ga amintacciyar baiwar Queen Hirut mai suna Muru wadda a duk duniya ba abinda ta tsana sama da Haisha'an, duk da tana mahaifiyar sa ba komai tsakanin su sai kyara da tsangwama. Tun yana ƙarami Queen Hirut tasa aka kashe Mahaifin sa saboda kawai sun gano shi ɗin musulmi ne kuma baya bin Addinin su na bautar rana, ya taso cikin kaɗaici, shi kaɗai yake rayuwar sa sai abokin sa guda ɗaya Omaine, shi ma ɗa ne ga wani bawa a masarautar. Haisha'an ya qullaci abinda akawa mahaifinsa saisa ya tsani Queen Hirut fiye da komai a rayuwarsa sa, sosai yake takun saqa da ita da kuma mulkin nata, baya shakkar ya tsaya gabanta ya faɗa mata magana kowacce iri ce tun bai kai haka ba, wanda hakan yasa rabin rayuwar sa a prison yayi. 

Mahaifinsa a ɓoye ya shiga musulunci kuma a ɓoye yake aiwatar da addinin amma shi Haisha'an a bayyane yake aiwatar da addinin dan dama shi tunda ya taso a cikin Musulunci ya taso saboda ko da aka haife shi sai da mahaifin sa ya yi masa Adhan a kunnen sa a ɓoye, haka kuma ko da ya fara wayo yayi ƙoƙarin ganin ya koya masa duk wani abun da ya shafi Musulunci har zuwa lokacin da aka gano aka kashe shi a lokacin ne kuma Haisha'an ya ɗaura ɗamara ya cigaba da neman ilimin Addini sosai kafin ya fito fili ya nunawa mutanen nasu shi ma musulmi ne kamar mahaifinsa nasa, sai dai abun Mamaki Queen Hirut ta kasa sawa a kashe shi kamar yadda akawa mahaifinsa sai dai tasa a kaishi prison a bashi horo sannan ta fakewa mutanen ta da cewa Haisha'an yana da amfani a masarautar ko dan aikin da yake yi tuquru, saboda in ya tashi aiki kamar bai san ciwon kan sa ba, aikin da mutum goma zasuyi zai iya haɗawa a lokaci ɗaya, Amma a baɗini ba hakan bane, ko ma miye zamuji a gaba. WANNAN KENAN.

Bin Custody Officer ɗin yayi zuwa office ɗin su suka bashi kayayyakin sa ya canza ya ɗauki na ɗauka ya juya ya fita ba tare da yace dasu komai ba, a bakin qatuwar Ƙofar gate ɗin prison ɗin ya tarar da Omaine tsaye yana ganin sa ya taho da sauri cikin farin ciki ya rungume shi tare da faɗin, "Alhamdulillah ɗan uwa, ina tayamu murna a wannan karon ma, kasan da naji shiru har na fara tunanin ko na gota lissafi ba yau bane"....... Ya ƙarashe yana ɗagowa tare da bin Haisha'an ɗin da kallo, hannu Haisha'an ya kai kan kafaɗar Omaine ɗin ya ɗan bubbuga sai kuma ya ɗage kansa sama yana bin ko ina da kallo ganin canje canjen da aka sake samu, murya can ƙasan maqoshi ya ce, " Har yanzu matar nan bata mutu ba?"....... Da sauri Omaine ya rufe masa baki tare da riqo hannun sa ya fara ƙoƙarin jansa saidai ko motsi bai yi ba kamar wanda aka sassaqa ganin haka yasa Omaine ɗin faɗin, "Ka taimaka mu bar ƙofar prison ɗin nan Haisha'an, ka rufa mana asiri in dai ba so kake ka sake komawa ba".......... ɗage kafaɗunsa yayi cikin halin ko in kula ya ce, "Can yafi daɗi ai Omaine, saboda ƴancin da zaka samu a can babu shi anan".

Matsowa yayi kusa dashi tare da yin ƙasa da murya kamar me raɗa ya ce, "Dan ALLAH ka bar wannan zancen Haisha'an, ba ta yadda mutum zai ji dadi ya kuma samu nutsuwa yana garkame"..........Ta gefen ido ya kalli Omaine ɗin da duka dukansa a iya kafaɗar Haisha'an ɗin ya tsaya. "Kai yanzu da kake saken wani daɗi kakeji? Wace nutsuwa kake da ita? a yau ƙaramin kuskure kana iya yi ko iyayen ka ko wani mafi soyuwa a gareka ba ɓata lokaci ya baqunci lahira, Matar da babu imani a ranta, matar da ta maida ran mutum kamar ran kaza bayan ALLAH shi ne kaɗai me rayawa kuma shi ne me kashewa, amma kuma su suce su ne masu kashewa a lokacin da suke so? Ni da kai maza ne kuma mun san girman da ALLAH ya bamu, ya bamu matsayi na masu kulawa da shugabanni (Qawwamai) a kan iyalansu da al'ummarsu tare da jagoranci a gare su, amma ka duba yadda rayuwar mu ta kasance a Matsayin bayin su wanda basu da daraja a idanunsu".

Shi dai Omaine bai bi ta kan zancen ba duk da yasan Haisha'an ɗin yana kan gsky, amma yasan yana amsa masa to fa zai tayi ne har ALLAH ya kawo wanda zai tseguntawa Hirut yanzu azo a samu matsala, gashi shi ko zuwa akayi aka ce mata ya faɗi kaza to indai ya faɗa ɗin a gabanta zai maimaita, dan haka Omaine ya ce, "Yanzu ina muka nufa?".

"Zanje nayi wanka first sai mu zagaya bayan gari"......... "To abinci fa?". Omaine ɗin ya sake tambaya. Kallon gefen ido yayi masa suna cigaba da tafiya, kamar ba zai ce komai ba dan an dau kusan minti uku kafin ya ce, "Ai a wancan gidan sai na fara cin abinci na qoshi sannan a rarrabawa saura, tunda babu shegiyar da zata mulkeni saboda ni ne sarkin su a ciki"...........Ya faɗa cikin halin ko in kula shi kuwa Omaine jan bakin sa yaja ya zuge ganin Haisha'an ɗin kamar ma ƙara ƙeƙashewa zuciyar sa take.

Ɓangaren da ya kasance na ya'yan bayi suka nufa tare da wucewa ɗakin su Omaine ya buɗe suka suka shige. Kan gadon Omaine ya faɗa, shi Kuma Haisha'an ya wuce toilet ɗin bai jima ba ya fito ya bude sip ɗin da kayan sa ke ciki komai yana nan tsaf kamar yadda ya tafi ya barsu, kuma yasan aikin Omaine ne, a gurguje ya shirya saboda lokacin sallar la'asar da ya lura yayi, gaban gadon ya ƙarasa in da Omaine ke kwance ƙafafun sa a ƙasa. "Omaine! Omaine "........ Ya faɗa yana ɗan bugar ƙafar sa, buɗe ido Omaine da ya fara bacci yayi daƙyar tare da faɗin, "Har ka fito ne?". 

"Eh, Kaje kayi Alwala lokacin Sallah yayi "........ Nasan zakuce shin Omaine musulmi ne? Eh Omaine ya musulunta dashi da wasu daga cikin mutanan masarautar ta dalilin Haisha'an, sai dai su a ɓoye suke komai.

Tashi Omaine ɗin yayi ya wuce toilet dan zuwa ya ɗauro Alwala, da wani irin kallon me kama da na tausayi Haisha'an ya bishi, dan daga ganin yadda yake baccin ma kasan irin na wanda yasha aikin nan tuquru ya gaji ne, katse tunanin nasa yayi ta hanyar wucewa ya shimfiɗa musu Abun sallar sannan ya tsaya jiran Omaine ɗin ya fito sannan yaja su Sallar bayan sun idar Omaine ya ce, "To ni dai a gaskiya zan wuce naje na karɓa abinci, Dan kasan fa in dai ka sake aka gama rabo baka je ba to fa Saidai ka jira na dare".

Gyada masa kai yayi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma ya ce, "In ka gama ka same ni a can"........ Da " To". Omaine ya amsa sannan ya tashi ya fita, Shi ma Haisha'an ɗin tashi yayi ya dauka sword ɗinsa da Archery ya rataya sannan ya saka takalmin sa ya fita.

Tun daga nesa ya hango wata jar Ƙura data rufe hanya sai wani ƙara ke tashi daga can iyakar garin, ba tare da wani tsoro ba ya doshi wurin yana matsowa sautin kofatun dawakai na Ƙara ƙarfi a kunnuwan sa har yazo daf da iyakar yankin nasu sannan ya tsaya, suma suna zuwa basu ƙetara ba suka dakata a hankali Ƙurar ya fara raguwa, kallo ɗaya ya musu yasan daga Ina ne, ɗaya daga cikin su ne ya ɗaga abun busar sa zai busa kawai yaga kamar an yi sama da abun busar, da sauri ya ɗago idonsa ya sauka kan Haisha'an ɗin da ya sauke Arrow and bow ɗin sa ƙasa alamar shi ya harbi abun busar ya faɗi, kafin suce komai ya ɗaga murya yadda zasu iyajin sa tare da faɗin, " Sarauniya bata nan tayi tafiya, Dan haka in saqo ne Kuna iya bani domin na isar dashi wurin Crown princess".......... Kallon juna sukayi tare da danyin magana a junan su sannan ɗaya daga cikin su ya matso gaba kaɗan da dokin sa tare da ɗan kwantowa ya miqowa Haisha'an ɗin takardar dake hannun sa, shi ma takowa yayi Amma be ketara ba daga nan ɗin ya miqa hannu ya ƙarɓa shi Kuma mutumin ya juya akalar dokinsa sauran suka rufa masa baya .

Ɗaga takardar yayi ya kalla tambarin eagle dake jiki, rigar sa ya ɗage ta baya ya zira ta sannan ya juyo daidai isowar Azal tana sanye da skinny leather jeans tare da wata armless riga ta fata data kai mata har guiwarta, ƙafarta sanye da boot sai Daenerys's dress data ɗaura akan kayan nata tare da sanya hular rigar da akayiwa bakinta ado da gashin farar wolf. Deanerys dress wata riga ce me kamar alkyabba amma bata da kaurin alkyabba tana da ɗan maballi daga wuya. 

Tafiya take cikin gadara da nuna isa gefen ta Siberian tiger ta ce me suna Simba bayan ta Kuma bataliyar yan rakiyar ta ne, a gaban Haisha'an ta tsaya suna kallon cikin idanun juna wanda ba abinda ke fita daga cikin idanun kowannen su sai tsantsar tsana wa junan su, dawo da kallon ta tayi kan hannun sa ɗaya dake riqe da Arrow, Bayan sa ta kalla inda har lokacin akwai sauran ƙurar da bata gama washewa ba, bin wurin tayi da ido kamar me nazari kafin ta dawo da kallon ta kansa da Kai ta nuna masa bayan sa sannan cikin gadara ta ce, " Kai meke faruwa anan?"......... Juyawa yayi ya kalli bayan nasa kana cikin rainin wayo ya ce, " A Ina ?"......... Wani kallon banza ta masa kafin ta ɗaga sword din ta Wanda yake daban dana kowa a kyawu da ƙarfi, Dan daga Sandar Queen Hirut sai sword ɗin ta saboda su komai nasu daban ne dan an riga an gama dafa shi da siddabaru.

A kan wuyan sa ta Ɗaura sword ɗin tana wasa dashi kafin ta nufi fuskar sa, a kan kumatun sa ta tsaya tare da juya fuskar sa tana taku a hankali har ta Juya Haisha'an ya koma yana facing iyakar garin nasu ita kuma tana tsaye gefensa, Kan kafadar sa ta sauke sword ɗin nata kafin ta ce, "Can nake nufi".

"Lion ne da Bengel tigers suka yi rikici "......... Ya faɗa idonsa akan yatsun ƙafar sa da yake motsawa a hankali. Ɗan shuru tayi can Kuma ta janye sword ɗin nata ta juya ta fara tafiya  mutanan nata suka rufa mata baya. Bai juyo ba sai da ya tabbatar sun bar wurin sannan shi ma ya waiwayo, right side ɗin sa ya nufa, yayi tafiya me ɗan nisa kafin ya isa kan wani qaton dutse me matuƙar tsayi da faɗi dan kusan shi ya zagaye rabi garin ta bangaren gabas kuma a ƙarƙashin sa ne kurangina yake sassaqaqqen gunkin su Queen Hirut, zama yayi a kan dutsen yana kallon view ɗin masarautar tasu kafin ya sanya hannu a bayansa ya zaro takardar ya buɗe. 

Lokacin da ya gama karantawa ɗaga takardar yayi ya rabata gida biyu sannan ya sake rabata huɗu, kuci kuci yayi da ita kafin ya turata bakin sa ya taune, tsaki yaja yana faɗin, "Ku Kuma in kunji shuru ku ɗau matakin da ya muku. ALLAH yasa  ma aurellon ɗin ta yiwa garin tashi ɗaya kowa ya huta........" Bai ida rufe bakin sa ba yaga yar Aiken fada ta fito da masu mata rakiya akan giwayen su sunyi hanyar fita daga yankin nasu, da kallo ya bisu kafin ya sake jan tsaki ya ce, " Yan wahala kawai"............ " Su wa?". Juyowa yayi wurin Omaine da ya ƙaraso ya nemi wuri kusa dashi ya zauna, "Ina zasu ne?"......... Ya tambaya yana dawo da kallon sa gabaɗaya kan omaine. 

"Ina tunanin zasu tafi maida takardar raddi ne wa Aurellon"..........."Dama sun aiko da wata takardar kenan?".

"Sun Kara aiko wata ne?"..........  Shi ma omaine ɗin ya maida masa tambayar yana kallon sa, ɗauke kansa yayi da faɗin, "Ita kuwa waccan matar dake rawar jiki ko da yaushe tana kan gaba wurin assasa wuta wata rana sai ta faɗo ta karye, munafukai kawai, wata cocumber da ita kamar wadda aka dire"......... Dariya sosai Omaine ya shiga yi shi kuwa Haisha'an ko murmushi baiyi ba kamar ma bashi yayi maganar ba sai arrow ɗin da ya zaro ya shiga zane zane akan dutsen kamar me haɗa wani abu. "Amma whl Haisha'an baka da kirki, yanzu me matar can tayi ita fa kawai yar aike ce".

Ba tare da ya daina abinda yake ba ya ce, "Ai ban ma fara rashin kirki ba whl, yanzu ba mai Ƙara kulle ni dama can ba wai ikon ta ko ƙarfin mulkin ta bane yasa take sawa a rufeni, dan da na ga dama ko hour ashirin da huɗu ba zanyi ba zan fito, to yanzu ba zan ƙara komawa ba na fito kenan, amma ɗaya bayan ɗaya zanci uban duk wanda ya sake ya shiga harkata, itama wanna me zubin shansherar tara ta nake, duk lokacin da ta kai ni bango sai na shayar da su ruwan mamaki ". 

"Kaga Haisha'an Ina rabaka da li'iliti Azal, kasan yadda kaji sunan ta Azal to whl idan kuka haɗa hanya, Azal zata zame Maka a rayuwa. Ni dai kawai kayi hakuri Ka ɗauke idonka daga kan lamuran masarautar nan". 

"Inah bata neme ni ba ko?". Ya tambaya, sunkuyar da Kai Omaine yayi saboda baisan abinda zai faɗa masa ba game da tambayar da ya masa na cewa ko mahaifiyar sa ta neme shi.

"Shikenan ba sai kamin ƙarya ba Omaine na samu amsa ta, bakomai tashi muje ni in ganta".

Kamar omaine zai ce Kar yaje sai Kuma yayi shuru saboda yasan ko sunje ma wulakanta su zatayi taita faɗar maganganu marassa daɗi akan Haisha'an ɗin kamar ba ita ta haifeshi ba, Amma ba yadda zaiyi bai isa ya nunawa Haisha'an ɗin baya san zuwa wurin mahaifiyar tasa ba dan yasan hakan zai iya sawa su samu matsala a abotar su. Dan Haisha'an duk da mahaifiyar sa bata son sa shi yana son ta, duk da ta tsaneshi shi yana kaunar ta, duk da ta wofanta da rayuwar sa shi Kuma tana zuciyar sa, akanta zai iya samun matsala da kowa.



-----------------------√



Sahnish na nan tsaye shi da Shazeen har baba Ilerika ya iso. "Suna Ina?". Ya tambaya. "Suna ciki"......... Sahnish ɗin ya amsa masa, kallon cikin police station ɗin yayi kafin ya ce, " Akwai yan kuɗaɗe a wurin ka ne?"......... Da sauri ya laluma aljihun sa gabaɗaya kuɗin kasuwancin na sa ya ɗauko dubu sha biyar ne ya miqa masa, karɓa yayi sannan ya ce, "Biyoni muje"........ sai da ya tsaya ya zuge biyar ya canza musu aljihu ba tare dasu Sahnish ɗin sun lura ba sannan ya shige. " Salamu alaikum"....... Baba ilerika ya faɗa lokacin da ya shiga.

"Wa alaikum Salam"......... Suka amsa suna binsu da kallo idonsu na sauka kan Sahnish suka haɗe rai, Constable Junaid ya ce, "Kai wai ba munce Kaje bane sai gobe ".

Baba ilerika ne ya amshe da faɗin, "Ai tare muke officer, dashi da Wadda kuka tsare ɗin ai duk ya'ya na ne, a taimaka mana mu ganta Dan ALLAH officer, ya min bayanin komai Kuma in Sha ALLAH da safen zamu zo muga DPO amma yanzun muna so mu ganta"............"Ka ga baba na riga na faɗa masa ba zai yiwu ku ganta ba sai an sanar da DPO".

"Shikenan ba damuwa, amma officer Ina son ganin ka ya za'ayi ne ?".......... Kallon abokan aikin nasa yayi kafin ya ce, " Muje daga waje"..........ya ƙarashe yana fitowa daga bayan kantar suka fita waje tare da baba ilerika, kuɗin ya zaro daga aljihunsa a dunƙule, yana faɗin, " Ranka ya daɗe ga wannan ka sa kati, ɗan minti biyar ma yayi yawa"........ Ɗan basarwa yayi da faɗin, "Ahh ahh ka barshi kawai, muje tunda minti biyar kace".

"A'a baza ayi haka ba Ranka ya daɗe ka karɓa ɗin dai ba yawa".......... Ya faɗa Yana zura masa a aljihu, washe baki yayi kana ya ce, " Ai baba shi yaron naka ne duk bai yi wanna bayanin ba, yazo ya dage sai ya ganta mu Kuma kasan dole mu bi dokar DPO ".

"Karka damu officer kasan Yara, abinda yasa ma aka samu matsala bai Kirani bane da wuri"........Ya faɗa Yana bin bayan Constable suka wuce ciki, jan rigar Sahnish yayi da faɗin, " Muje "....... Binsa sukayi inda ya nuna musu wani table da faɗin su zauna bari ya fito da ita.

Hushaima kuwa tana tsaye cikin cell ɗin banda sauro ba abinda ke garzar ta ga wurin gabaɗaya daga ta zauna sai kuɗin cizo ya fara gallara mata gashi ba ruwa ba abinci, Amma tsabar zuciya ko yunwar bata ji kawai tunanin ta yadda zata rama wanna cin mutuncin da yarinyar ta mata, ko tunanin tana raye ko ta mutu batayi ba. Kai jamaa ni kaina zuciyar Hushaima ta fara bani tsoro fa, maganar Constable ta ji Yana faɗin, "Ke fito ga Yan uwanki sunzo ganin ki, minti biyar kuke dashi"......... Batace komai ba ta fito ya wuce gaba tabi bayansa, da gudu Shazeen ta nufi wurin ta tare da rungume ƙafafunta tana faɗin, "Aunty Hushaima Ina kika tafi kika barmu yau mun Sha wahalar neman ki ni da yaya"......... Murmushin yaqe tayi tana riqo hannun Shazeen ɗin tare da kallon Sahnish da ya karaso wajen su. " Hushaima ya akayi hakan ta faru?"......... ɗauke kanta tayi tana kallon wani wuri kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta shiga bashi labarin abinda ya faru a taƙaice, kafin ta dawo da kallonta kansa. "Whl summa tallahi na rantse da Ubangijin sammai da ƙassai Sahnish yarinyar nan sai tayi nadamar rayuwarta, tunda ta sake ta ƙetara iyaka ta sai tasan ni daban nake da sauran mutane, sai na rama ramuwa mafi muni, sai na sata kukan da sai hawayen ta ya qafe"........... Ta yi Maganar cikin qunar zuciya. Da wani irin yanayi Sahnish yake kallon ta shi ya san wacece Hushaima bata rantse bama aka ɓata mata saita rama ballantana wannan da tayi rantsuwa me girma haka, sai kawai ya rasa abun cewa sai kallon ta da yake kamar wata hoto, Baba ilerika da yazo wurin ne ya ce, "kiyi hakuri Hushaima".

Wani one side smiling tayi tare da juyawa wurin Baba ilerika ta ce, "Baka san abinda aka min bane baba ilerika, amma bakomai ina ɗan sandan nan, Sahnish kaje ya baka jakata ka ɗau makullin ɗaki na saboda Shazeen ko zata ɗauki kayanta saboda na makaranta....... kaga wani abu zai shiga kunnen Ka"........Ta ƙarashe tana ɗan matsawa ta kama kunnen kamar zata cire masa wani abu a hankali ta ce, "Akwai kuɗi a jakar ku ɗauka ko zaku buqaci wani abu"........ Kwata kwata Baba ilerika bai ankare magana Hushaima ta wa Sahnish ɗin ba .

Constable ne ya zo yana faɗin, "Lokaci fa yayi"........." Eh ai yanzu zasu wuce"........ Hushaima ta faɗa tana gyarawa Shazeen hijab ɗin ta ta kalli Sahnish da faɗin, "Ka kula da kanka kuma ka kula da Shazeen".

"Hushaima yanzu anan zamu barki a gaskiya bazan iya tafiya ba saidai a haɗamu a cell ɗin duka".......... Sahnish Ya faɗa Muryar sa na karyewa. A dake ta ce, "Kai kallo nan karka sake kace zaka min kuka, namiji kake ko baka sani ba ne, ka nuna min haka ta hanyar ƙoƙari na fita anan wurin, dan shi ne kaɗai ƙaunar da zaka nuna min ba wai ka tsaya zaka min kuka ba".

"Wai tun yaushe kike nan Hushaima?".......Baba ilerika ya tambaya. "Tun wuraren 12pm ne"........ Ta bashi amsa sharply. "Kaii abu baiyi daɗi ba sam, yanzu tun wannan lokacin kike nan ba ruwa ba abinci".

"Zanje na siyo mata wani abu yanzu".......... Sahnish ya faɗa tare da duban Constable ya ce, " tace ka bani jakarta in ɗauki dan makulli a ciki ".

"To Shazeen ga yaya duk abinda kike so ki fada masa ni yau bazan kwana tare da ku ba kinji".........."Ni gaskiya bazan bi yaya ba aunty Hushaima kizo mu tafi tare dake"........ Ta ƙarashe tana jan hannun Hushaiman alamar tazo su tafi.

"Wuce wuce muje"......... Constable ya faɗa yana tisa ƙeyarta, bata ƙara cewa komai ba sai kallon Sahnish da tayi sannan ta juya ta wuce .


*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT,  2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER ***.*