Chapter 6
by @pinkyjay
RIYANN
Free page
PAGE 7
___________"To muje na raka ki." Tafiya suke su na hira, rabin hirar duk Ilolo ne keyi ma Riyann ita, saboda duk rashin jinta bata da yawan surutu magana bata da meta ba sosai, wani lokaci hak Umma zata yi mata magana amma baza ta tanka mata ba, idan wani abu ne sai dai tashi, tayi, sun iso ƙofar gidansu Saude ta shige ta barsa nan, ya na jiranta,
da sallama ta shiga cikin muryata mai sanyi, da daɗin sauraro, Inna ce ta amsa ta na "A'a Riyann ce agidan namu.?" Ɗan murmushi, ta yi kana ta ce "Eh Inna ni ce Umma ta aiko gashi ta ce sai ta zo anjinma, zaku yi magana." "To ba komai Allah ya kaimu lafiya." Ta amsa da "Amin ina Saude.?" "Ta shiga wanka yanzu zata fito."
Ɗakin Saude ta shiga ta zauna, zamanta kenan Saude na fitowa, "Riyann ya ki ke.?" "Ina lafiya." Ta amsa ataƙaice, Saude ta ce "Riyann ke ji abinda ya samu Salame kuwa.?" "Bata da lafiya ne.?" "Eh Aljana ce ta yi mata mugun duka." "Ayya ban sa ni ba ai da na shiga na duba ta." "To bari mutafi tare da ma can zanje in biya wurin ki." "Ko."
Ta na gama shiryawa suka fito Inna na yi musu Adawo lafiya, ƙofar gida suka tadda Ilolo ya na jiranta, ko kallonsa batayi ba ta ce "Katafi kawai ta re da Saude zamu fita." Ya san halin Riyann bai yi gardama ba ya tafi, badon ya so ba, saboda ya na kasancewa tare da ita, ya na ma samarin ƙauyen kwalelensu,
Saude ta kalli Riyann ta ce "Wai ba kece Yayanki da ke birni za ki aure ba ɗan gayu amma na ganki da Ilolo.?" "Eh kawai bansan yadda zan faɗa mai, anyi min miji ba, kega ya na matukar sona, gaskiya sai idan Yaya Naufal ɗin yazo shida su Anty Zainab idan na ga Ilolo ya fishi kyau, to bazan aure sa ba."
"Lallai Riyann baki da hankali, aiko da jin sunansa kesan ya haɗu, mai kyau ne, gashi ɗan birni ya iya turanci ko ba haka Umma tace miki ba.?" " Haka ne fa, ni na manta, gaba ɗaya." Dai-dai nan suka iso ƙofar gidansu Salame, suka shiga da sallama, bakowa tsakar gida, saboda haka ɗakin Salame suka shiga,
Kwance suka sameta sai bacci ta ke ga shatin dukan da Riyann ta yi mata nan, ya yi ja,kan fatarta, sai lokacin Riyann taji tausayin ƙawar ta ta, amma sai ta basar , Saude ce ta ɗan buge ƙafar Salame aiko ta zabura da ƙarfi, ta na faɗin "Inna gata nan ta dawo zata kashe ni." Sauɗe ce ta riƙeta ta ce "Ke mune fa ba kowa ba."
Sai lokacin ta buɗe idanunta ta ga Riyann da Saude, ne wata ajiyar zuciya ta sauke, kana suka gaisa da yi mata ya jiki, kallon Riyann ta yi idanu cike da kwalla, ya ce "Don Allah Riyann kiyafemim saboda maganar da na faɗa miki jiya wannan abin ya faru da ni, don Allah kiba Aljanunki haƙuri bazan koma ba."
Cikin rashin fahimta Saude ta kalli Riyann amma sam Riyann ta ƙi yarda su haɗa idanu, saboda tasan Saude zata gano ta, sai cewa ta yi"Haba Salame kidena faɗar haka, wallahi bansan abinda ya faru ba kuma ni bansa Aljana ta yi miki haka, hasali ma, ni banida wasu Aljanu, Allah ya tsare gaba kawai." Suka amsa da amin,
sun jima gidan har Inna ta dawo suka gaisa kana suka wace gidansu Riyann, sai da Saude ta gaida Umma kana ta shiga ɗakin Riyann, "Yanzu Riyann duk haƙurin da na ba ki sai da ki ka yi ma Salame haka.?" Banza ta yi da Saude sai ma ta ɗauko mata kayan da Baffa ya kawo mata da ya je birni, itama Saude bata kulata ba,
sai cewa ta yi "Ni zan tafi gida, na ga bakida lokaci na." Ta san halin Saude zata iya tafiya, "Haba ƙawata kiyi haƙuri bazan koma ba, kawai bani son ana haɗa ni da Aljanu." "To ai na ba ki haƙuri amma sai da ki ka daki ƴar mutane, wallahi Riyann ki natsu saboda idan ki ka mutu....."Haba Saude kidena faɗar haka don Allah bazan mutu ba na dena." Dariya Saude ta yi saboda tasan lagon Riyann sam bata son mutuwa,
duk akayi mutuwa gidan da ta ke shiga to tabar gidan har abada, bazata koma shiharsa ba, in dai kayi mata zancen mutuwa duk abinda kasata shi zata yi babu gardama, sosai ta yi ma Riyann faɗa kana suka cigaba da hira, Umma na jinsu sosai ta ji daɗin faɗan da Saude ta yi mata, saboda ko ita, abin Riyann na damunta,
ba damar kayi mata faɗa, sai tasan yadda ta yi ta wahalar da kai, saboda akwai ranar da ta zabga mata gishiri da barkono cikin miya ta yi mata faɗa, washegari, ta zuba mata ƙarara cikin ruwan wanka, ranar wuni ta yi soshe-soshe duk ta haukace, shi ya sa bata ta dena ya mata faɗa sai da ta lallaɓa ta,
Saude bata bar gidan sai bayan sallar azahar, akan sai sun haɗu makaranta, yau ta zauren zasu je, ba harda ba, ƙarfe huɗu, ta yi ma Umma sallama ta fita zuwa makaranta, ga hanya suka haɗu da Saude kana suka wuce, Malam Ishaq ne ya tare su latti saboda kawai mugun ta, ya zane su, kana su ka wace suka zauna,kamar ƙaddara ya aike Riyann ta karɓu mai abinci cikin gida aiko da murna ta ɗauke jakarta ta tafi,
ta na karɓu abincin ta tsaya soron gida ta buɗe jakarta, ta zuba mai wani garin magani, cikin miya, ta saka kare ta juya sai da ya haɗe kana ta kawo mai, ta koma ta zaune, Malam Ishaq kuwa ya baje ƙafafuwa, ya fara kwasar tuwun gero da miyar taushe, wani juye ya ji cikinsa ya yi, sai da gudu ya cika wando sa da iska sai cikin gida,
ko buta bai ɗauka ba ya shige ban ɗaki ya fara zuƙa zawo, ya jima kafin ya kira matarsa Laure ta kawo mai ruwa kana ya fito ya koma ƙofar gida ya cigaba da cin tuwunsa, wannan karon bai ankara ba sai ji kake bat bat gudawa, da tusoshi na fita sai warin tsiya, yara dai kuwa suke Malam ya kashe zaune,
duk kunya ta damesa gashi zawon bai dena fita ba, Riyann kuwa kamar ta taka rawa saboda jin daɗi, haka Malam ya da fa jikin gini ya ta shi, zai shiga cikin gida nan yara suka koma fashewa da kuwa da dariya, kamar gudawa jira ya ke Malam ya tashi sai gashi ya koma zuwa sai zuba ya ke ta ƙafafuwan wandonsa, wani wari, da ke tashi,
ko magana Malam ya kasa yi, saboda yadda cikinsa ke juyawa, abin ba a magana, 🤣
Wriets by pinky Darling 🌷 ~Matar Jay ~