RIYANN

Chapter 8

by @pinkyjay

🌷 RIYANN 🌷 
Free page

PAGE 10&11🦋

______Haka aka cigaba da zaman ta'aziya gaba Riyann ta rame sai haske da tayi sosai saboda bata cin abinci sosai sai Daddy ya sa ta agaba kana ta tsakura ta aje ranar Assabr akayi addu'ar bakwai misalin ƙarfe tara na safe nan Daddy ya sa Malam Kabiru ya raba ma mutane goro da alawa,

kana Liman ya yi shelar za'a É—aura auren Mahmmad Naufal Ibrahim da Aminatu Abdullahi Riyann, akan sadaki dubu É—ari biyar, Malam Kabiru shine waliyin Ango sai Daddy Ibrahim shine waliyin Amarya, 
lokacin da Naufal ya je shilar da Liman keyi kamar ya kurma ihu saboda baƙin ciki, tun jiya Daddy ya faɗa mai zai haɗa aurensa da Riyann, amma sam bai ƴarda ba sai yanzu, cikin ransa ya ke magana ,

tun da Daddy ya kuskura ya haÉ—a wannan auren batare da Æ´ardarsa ba wallahi sai musguna ma wannan yarinya saboda ya ga yadda Daddy ke ji da ita, kamar kwai, sam ya tsaneta wallahi baya Æ™aunarta ko ka É—an, wani murmushin mugunta ya yi, dai-dai lokacin aka gama É—aurin auren, kana Daddy ya shige cikin gida ya na kiran 

"Mamana! Mamana." Lokacin Riyann ta fito wanka saboda Zainab ce da Saude suka sa ta a gaba dole ta yi wanka, hannunta ya ja zuwa É—akin Umma lokacin Naufal na ciki, kuÉ—in sadakinta ya bata kana ya gyara murya ya fara magana, "Naufal." Ya ce "Na'am Daddy." Kana ya ce "Mamana." Ita ma ta amsa, kana ya ce,

Na haɗa aurenku ba don komai ba sai don zumunci ku ya ɗaure kana yanzu banda kowa idan ba Riyann ba, kaf dangina na Uwa da Uba babu ko ɗaya, ɗan uwana da nike matuƙar so da ƙauna ya tafi ya barni amma ya bar min jininsa saboda haka dole ne inkula da ita fiye da kulawar da nike baku, bata da wani gata sama da ni yanzu sai kuma kai da ƙannenka ,


Ina so kariÆ™e min amanar É—iyata Naufal kataya ni kula da amanar da Allah ya bani karÆ™eta amana karka cutar da min Æ´a wallahi Naufal kaji na rantse duk ka cutar da ita sai nayima abinda baka taÉ“a zato, kana jina ko.?" "Eh Daddy zan kula in sha Allah." "To sai ke Mamana, Naufal yanzu ba iya Yayanki bane mijinki ne, 


Aljannar ki na Æ™arÆ™ashin Æ™afafunsa, kiyi mai biyayya duk abinda ya sa ki indai bai abin bai saÉ“ama addini ba, karkiyi mai rashin kunya, karki yadda kirena mijinki karki yadda wata Æ™awa ta san sirrin mijinki, ki kula sosai kana duk abinda ya yi miki ki faÉ—amin, ni zan É—auki mataki Kinji Mamana." Hawaye ne taf a idanunta ta ce 


"In sha Allah Daddy bazaka taɓa jin matsla ta ɓangarena ba." "Alhmdllah! naji daɗi sosai Mamana da ma nasan in sha Allah bazaki bani kunya ba, Allah Ubangijin ya yi muku albarka ya sa ma wannan aure naku albarka, Allah kajiƙan magabatanmu Allah ya nuna min kun haifu min jikoki." Kunya ce ta hana Riyann magana,

Naufal ma baiyi magana ba, saboda sam be burin haihuwa da wannan yarinya da ko ƙidan dangi bata gama ba, me zai tsinta ajikinta,bayan haushi Allah ma ya tsare shi da kwanciyar aure da wannan ƙaramar yarinya mezaiyi da ita, Daddy ne ya katse mai tunani ya ce "Naufal magana ka ke.?" Saboda ya ji sautin maganarsa amma ba sosai ba saboda bai fahimci abinda ya ke cewa ba,


"A'a Daddy banyi magana ba." "To shikenan Mamana mutafi, sarai Riyann ta ji abinda Naufal ke faɗa amma shi bai sa ni saboda zancen zuci ne ya fito fili, ita kuma ko ya ya mutum ya yi magana zataji Allah ya yi mata wannan baiwar, ɗakinta ta shiga ta iske Zainab ta fitar ma ta da atamfa riga da sekit na atamfa ja da ɓaki,


baƙaramin kyau ta yi ma Riyann ba, da ma kunsan kyakkyawar ce haka ta shirya tsaf ta zauna su Saude na kanta da hira, Daddy ko ya na fita wurin Malam Kabiru ya je ya kaisa gunakin Baffa da ya siye guda huɗu uku da sunan Riyann ɗaya kuma da sunan Naufal, sai da Daddy ya yi kwalla, ya na jinjina karamci irin na ɗan uwansa, tabbas ya yi rashi da har abada bazai mai da ba,


nan dai ya ba Malam Kabiru amanar gunakin ta re da shidun mutune hadda mai gari, nan ya ce duk wata zai rinƙa turo kuɗi ana biyan masu kula da gonakin, kana ya koma gida washegari ranar Lahadi Zainab ta raka Riyann maƙota ta yi musu sallama, saboda tafiya zasuyi, kana suka dawo gida ta haɗa kayanta, da duk wani abu da ta ke buƙata,


kana suka fito Daddy ya rufe gidan ya ba Malam Kabiru key sun shiga mota kenan sai ga Innar Saude ta na yi mu su hannu suka tsaya kana Riyann ta fito, ta ce "Lafiya Inna.?" "Lafiya lau da ma mantuwa na yi ga abinda Umma ta ce asiyo miki, da kuɗin da ta ke tarawa wurina, wata ƙatuwar sarƙa ce ta zinari da agogo, sai kuma kuɗi, masu yawa,


kana ta ce "Kina shanu guda uku da awaki gudu biyar, danike kula da su ta ce duk na ki ne, saboda haka duk lokacin da ki ka buƙaci abinki sai kizo ko ki aiko." Cikin kuka ta ce "Allah Sarki Ummana Allah ya jiƙanki da rahama ke da Baffana, ina sonku sosai." Kuka ya ce ƙarfin ta Daddy needs ya fito ya mai da ta mota kana sukayi sallama da Inna,


akan zasu dawo wani lokaci, haka Riyann ta rungume sarƙar ta na kuka sai lallashinta Zainab da Daddy ke yi, takaice duk ya cika Naufal yanzu wannan yarinya ake lallashi, wani kuka ta ƙara fashewa da shi gani sun fito cikin ƙauyen sun hau babbar hanya ta barin garin zuwa Kano tumbin Giwa ko da me kazo anfika,

tun da suka hau hanya sai tayi shiru ta na kalle -kalle saboda bata taɓa fita ko da tashar ƙauyen Ba da, bacci ne ya kwashe ta bata falka ba sai da ta ji Zainab na tashinta da ga bacci sun iso cikin gari Unguwar Darmanawa, suka shiga, dai-dai wani ƙaton get nan Naufal ya danna hon get Man ya taso ya buɗe saboda ya san Naufal ne kaɗai ke irin wannan hon,


Riyann kuwa sai baza idanu ta ke ta na kallon abubuwan da ke cikin gidan, ya haɗu sosai Daddy ya kashe mai dukiya mai yawan gaske, wata mata ce fara dogowa kyakkyawa ce sosai kamar shuwa Arab ta fito ɗauke da tsohon ciki ta na murmushi har ta ƙaraso wurin su lokacin sun fito cikin mota sannu da zuwa ta yi ma Daddy kana ta rungume Riyann ta na cewa ,


"Sannu da hanya ƴata ya ki ke.?" Itama Riyann rungumeta ta yi haka kawai ta ji ƙaunar matar ta shiga ranta sosai ita ma Hajiya Ummie haka ta ji, Zainab ce ta yi gyaran murya cikin shagwaɓa ta ce "Ummie ni bazaki rungumeni ba.?" Dariya Ummie ta yi ta na sakin Riyann ta rungume Zainab, Naufal ne ya kawar da kansa gefe,


"Ya na cewa "Ton yanzu nasan matsayina a gidan nan." Dariya Ummie ta yi ta riƙo hannunsa ta ce "Haba My son ai kai na daban ne am sorry." ta rungumesa, dariya Daddy ya yi kana ya ce "Mamana mushiga ciki saboda na ga abin nasu bazai ƙare ba." Hannunta ya ja sukayi gaba kana su Zainab na bayansu, Iliya ne ya kwaso kayansu dake bayan mota,

wani ƙayatatcen parlon ne suka shiga da ya ji kayan mo re rauwa aljanar duniya, komai na cikin parlon da ga ƙasar Dubai aka siyo shi, fadar irin kyau da tsarowar sa ɓata lokaci ne, wani babban hoto ne a farkon shigowa parlon Daddy ne da Baffa da Umma sai Naufal lokacin ya na ƙarami, gaba ɗaya sai murmushi, sukeyi aka aka ɗauke hoton,


lokacin su Baffa sun kawo ma Daddy ziyara ne akan ya samu matar aure akayi hoton sai kuma wasu hotona na su Zainab da Naufal da Daddy sosai hotonan suka burge Riyann Daddy ya ce "Mamana kina son hoto ne.?" ÆŠaga mai kai ta yi ya ce "To shikenan Zainab kishirya min Mamana gobe mai hoto zaizo ya yi muna."




Cikin murna ta ce "To Daddy." Iliya ne ya shigo da kayansu ciki kana ya fita, Atika mai aki ta kawo musu abinci saboda Daddy ya ce saman kafet zasu ci abinci,